← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 95

Sashe 74

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

FU'AD ne ya tsayar dashi da cewa ,toh ita cemaka tayi Tana daga irin wad'an Nan matan ? Sai ko Husna tace kasani Nina ai mace ce"
Sai FU'AD ya harareta ke kinsan dai nasanki ko karki biyema wanan kimin karya ko Halin Nan naki ya k'arasa maganar da Mata nuni da tashiga hankalinta,ta kalleshi ta watsar tana cewa nidai a bani isashe lokaci ingama komai a tsanake Ni ji nakema fa kamar Kar na koma........ Bata rufe Baki ba musbahu yace....

Kaji ko? Kaji magana ta ko?

Sai ko FU'AD ya kulu Dan musbahun nema yafi k'ular dashi yace "me naji da maganarka da guntun Kashi duk d'aya ke Kuma wallahi Baki Isa ba kuma ya zama Dole mutafi tare ko kingama shiri ko Baki Gama ba inkika k'ara ganina a gidan Nan kisani nayi zuwan k'arshe Dole ki biyoni mu tafi Zan ga Wanda yakeda iko dake Bayan Ni.......

Afusace FU'AD yace "Kai Kuma sai ka taso uban hasashe in Kuma kaga waje sai kayita zama , musbahu cewa yayi aa abokina muyi tsiya muyi dad'i zikaji banaso ka tafi kana fushi Dani ko ita Zo muyi maganar fahimta ya dawo da FU'AD d'in....

Yace ,baiwar ALLAH matar abokina ,Kinga dai komai ya faru bisa kuskure Dan ALLAH komai ya zama tarihi kibi mijinki ku zauna lafiya Kinga da auren shi akanki ,shima ya amsa ya Kuma karb'a yasan da aurenki akanshi ya Kuma shirya Baki kulawa fiye da ta baya da ya Baki Dan ze shayar dake zumar so zallah Mara sirki........ FU'AD yaji kingkhan na sakin layi sai yace "Kai kafa tsaya matsayinka karka fad'i Abin da be fito daga gareni ba toma wai Kai waya aikeka can inda ka nufa ? Kawai ka Gama fad'an Abin da zaka fad'a maganar ka har ta k'are ka Fara had'awa da shifcin gizo kawai nadai Gaya Mata ta zama cikin shiri konawa tare Dole babu shawara babu lalab'awa sai umarni ya mik'e ya saka Kai .....

Kingkhan ne ya dinga rarashinta Yana Mai k'aryar Yana sonta wallahi Kuna ze kula da ita kawai dai tayi gagawan karantar shi da sanin mulkin shi da sanin waye shi inta San Haka ta gama dashi ya Mata sallama ya bi abokin nashi FU'AD waje......

Bayan Husna tabar wajen FU'AD d'akin matar Nan ta shiga ta fad'a jikinta tanata kuka Dan da Tana tsoronta da d'ari_d'ari da ita yanzu ko ta Dena ,Husna na kuka Tana cewa wallahi Ina tunanin komawa hanunka FU'AD duk da nayi imani da mumcy bazata barka kacigaba da min Abin da kamin a baya ba Amman Naga kamar ka sake k'aro wulak'anci inko hakane Dole Nima na Shiga kasuwar Rashi mutunci dan siyo kalan nawa wulak'anci kana gabzamin na mayar maka da martani da naji zaman bazemin ba na dawo india abuna Dan Naga 'yan uwa masu sona nikam nagama maraishin dangi insha ALLAH."

Husna sai ji tayi matar na rarashin ta ta hanyar jijigata da hannun ta tana hawaye itama...

Husna da sauri ta d'ago ta kalli matar sai ta sake saka hannunta Tana sharema Husna hawaye ,Husna hanunta ta Kama Tana murmushi cikin kuka Tana cewa ,wai kinji abinda nake fad'ane?

Ido kawai matar ta zuba Mata ,Husna sake Mata tambayar tayi Tana kamo hannun matar ,shiru matar tayi Tana k'arema Husna kallo,har sai da Ammin ta shigo ta samesu a Haka sai da Ammin ta kusa minti 3 Tana kallon ikon ALLAH tana mamakin tsak'uwar da ke tsakanin su day wasu abubuwa da ita tabarma kanta sani kawai sai can tace......

"Husna Ina mijin naki kiketa kuka keda yayan da ba jinki takeyi ba?

Husna d'agowa tayi Tana cewa "dama kin shigo ammi? Tana share hawaye ,sai cewa Ammin tayi Dena share hawayen ki yi abunki Kya Kori rad'adin da kikeji a zuciyar ki kukan ma ai da amfanin shi , in na mamakin yadda yaya take tayaki kuka Akwai shak'uwa a tsakanin ku da ta bijiro kwanan Nan Haka ALLAH yake ikon shi .....

Sai Husna tace "me kike nufi Ammin?
Sai Ammin tace "Ina nufin jinin kune ya had'u kawai"
[4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA*

```RUBUTAWA DA TSARAWA```
BY
*FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB*
( Maman shaheed)

💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥

Pg58

*Wanan page din gaba dayanshi na namcy nane wato ummu Qaseem*❤😍🌹

Sai Ammi tace "Ina nufin jinin kune ya had'u kawai"

Husna bawai Dan ta gamsu ba tabar maganar ne kawai.

Koda Ammi ta tambayi Husna FU'AD cikin Halin ko in kula tace "sun tafi"

Ammi Kiran Husna tayi gefe a cikin d'akin tanata rarashin ta da Bata hak'uri akan FU'AD da Mata Al'k'awarin bak'in ciki da b'acin ran da Tasha a baya da izinin ALLAH yazo k'arshe duk wani Abu daze faru tsakanin ta da FU'AD indan na sirrin sune tayi k'ok'arin shanyewa da adanama cikinta Dan ciki badan abinci kawai akayishi ba'

Sanan duk Wanda take buk'atar shawara k'ofa abud'e take ,Wanda Kuma zata iya magance shi da kanta tayi k'ok'arin magancewa batare da ta nemi agajin kowa ba zaman Aure ya gaji Haka,sosai Husna ta d'auki nasihar aunty huwaila tayi naam dashi Kuma.

***********
Mumcy ta Isa k'asar mu ta gado wato Nigeria lafiya, Tasha tarba wajen k'anwarta balaraba da ma'aikatan gidan sanan su Jameel da sa'adiya suka Mata nasu bangajiyar ta waya dake suna Abuja.

Sanaya Bata Zo ba sai da akaje Kai Mata abinci akace Mata mumcy ta dawo, shine ta d'ebo 'yan matan kafafuwanta tazo Dan ta tambaya akace Banda FU'AD suka dawo ,shine tazo Jin dalili?

Bayan ta gaishe da mumcy ta yi shiru sai mumcy ce tace "karkiga FU'AD be dawo ba tare zasu dawo da Husna kinsan Tana can indiya taje wajen aunty ta huwaila shine zasu dawo tare duk da ba tare suka tafi ba ,Dan mumcy Bata tab'a Gaya Mata b'atan Husna ba.

Sanaya yak'e tayi tace "toh babu komai ai ,Amman bazasu wuce Nan da 5dys ba Koh?

Mumcy "eh toh banace ba Amman bazasu wuce hakan ba insha ALLAH"

Sanaya "toh ALLAH yasa" ta tashi zata koma sashin ta .....

Sai mumcy ta dawo da ita "nikam sanaya bakya gajiya da zama ke kad'ai d'inan da kikeyi? Ko wani cikin ma'aikatan Nan kinki sakin jiki dashi bare abokiyar zamanki inaganin zaman kadaitan Babu dad'i ......

Sanaya"a ai inda sabo na Saba some times ban fiye son hayaniya ba nafi son naganni Ni kad'ai nayi bacci na tashi nad'an rik'e phone d'ina mugaisa da fanc sai fita outing in Ina sha'awa,is normal ai na Saba karki damu"

Mumcy "ok ba'a kwacema yaro garma ai ,u are mature basai na forcing d'inki ba Akan Abin da ba ra'ayinki ba"

Sanaya "karki damu fa innaga Ina sha'awar hakan zanzo na nemi wata da zatayi daidai da ra'ayina ko nasa anema min a waje Dan Akwai wata aunty k'awana inason Kai Mata ziyara ma a Nan take ko ita sai insa ta Nemo min"

Mumcy "toh ai shikenan babu matsi ko takura dai ga ahalin gidan Nan kema sheda ce"

Sanaya "no banfa ce kin matsa min ba wallahi na fahimce ki Nima ki fahimce Ni Dan ALLAH?

Mumcy "nasani yo Kya Fara cewa na matsa Miki ma? Kawai dai Ina tuna Miki Abin da Kika sani ne.

Sanaya "eh hakane nagode barinje ,Kinga ko yanzu ma mun d'an tab'a Hira ai natafi bye.

Mumcy binta tayi da kallo Tana murmushi.

Baban Ma'u ,tun dawowar shi mama habee ta Dena ganin walwalar shi da fara'ar shi ,Kuma da ta Fara hayayak'o Mai ze juye Mata kwandon fad'a har sai ta rusina ,Abin na matuk'ar Bata mamaki Akan yadda ya samu dama yake Mata haka.

Humaira kuwa cikin samarin ta tanata laluben Wanda zata shak'e amusu Aure kafin abata kwashikwaraf d'in da baba yace kowa ya samu tasan ze aikata tunda mama habee ta Fara laushi Dole itama tayi laushi ,Dan Haka taketa lalube Kuma wai me d'an kyau ko k'asa da FU'AD d'in Ma'u ne ,sanan med'an abinyi na rufin asiri Dan itama Auren zefi Mata ta gaji da soyayar shafi muleran da takeyi (soyayyar Shan minti) gwanda taje taji d'an gasken shafi muleran......

Maman hafeeza nata murna yau hafeeza zata dawo daga karatun da tatafi wajen k'anin ta a manbila ,Dan Haka har Dan girke_girke tamata da toye_toye tanata jiran saukarta,

Bayan awa 1da Rabi kuwa hafeeza ta sauka, Bayan ta huta sunyi Hira da mamanta take tambayan ta ina kuwa Ma'u zun kwana biyun basuyi waya ba ko ta kirata ma Bata samunta Dan Haka takeso inta huta taje gidan hajiya babba taji ko lafiya?

Maman hafeeza Bata labarin duk abun da yafaru tayi tace Kuma "Taki sanar matane saboda Kar ta batama Ma'u shiri na barin k'asar Dan tasan halinta zata iya Bata hak'uri tace ta hak'ura ,ita Kuma tanason yin nesa dasu Musamman ma da zata bar musu k'asar ,har zuwan su baba gidan neman Ma'u sai da mama taba hafeeza labari.

Hafeeza ajiyar zuciya tayi tace , ALLAH sarki k'awata ta ga tashin hankali ,Amman da yadda ALLAH komai yazo k'arshe ,zanje gidan baba kuwa Dan jin labarin ko yasan inda take innaga tashin hankalin shi a bayyane gaskiya Zan sanar Mai inko Naga ya dangana Zan kyale shi ,sanan har gidan hajiya baban zani naji ko sun Sami labarinta ,hmmmm maman humaira fz Daman kamar Babu ALLAH aranta wallahi Bata da imani mama Akwai abubuwan da takema ma'un idan na tuna Abin tsoro da mamaki suke bani.....

Mamace tace "hmmmmm ke Wanda Kika sani kenan ,Ni Akwai wani zargi ma da nake Mata Akan mutuwar mahaifiyar ma'un bantaba gayama kowa ba kema ki barta anan inhar zargina gaskiyane komai Nisan dare gari ze waye Kar dad'in Hira ya debeki ki gayama Ma'u nasan surutun ki......

Hafeeza murmushi tayi Tana cewa "haba mama babu meji , ALLAH ya shiryeta.

"Amin" Inji mama,

Washe gari hafeeza taje gidan su ma'un ta gaishe da baba,humaira da mama habee nata hararar ta, Jin baba bece Mata komai ba sai ita tace Mai "baba har yanzu shiru labarin Ma'u ko?

Sai baba yace "eh hafiza Amman da yadda ALLAH jikina na bani nakusa tozali da ita insha ALLAH tana hannu nagari yadda zuciyata take min shakku akanta yanzu Sam na samu nutsuwa,
Chapter 74 · 0% Book details