← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 95

Sashe 85

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

FU'AD kwanan wuya yayi kusan kasa bacci yayi sai d yajiyo Kiran sallah asubahi y samu yayi wanka ya dauro alwala sanan ya fito d niyar dosar d'akinta ko a tsiya ko a Dadi, har y nufi d'akinta sai yayi tozali da makulin dake center table d'in Rai a b'ace ya d'auka y nufi k'ofa ze zura sai yaga na jikin k'ofar k'wafa yayi ya bud'e kawai ya nufi masallaci.

Bayan y shigo gidan ya nufi sashin su mumcy sai ya tuna ai Basu bud'e ba har ze koma sashin sanaya sai yaji beki ace yabar sashin Bari na har abada ba Dan Haka dama d wayar shi ya fito sai ya Kira Husna a waya har ta katse Bata d'aga ba sai d ya sake Kira sanan ta d'aga cikin maganin bacci cikin murya Mai kamada rada Fu'ad ya umarci Husna d tazo ta bud'e Mai k'ofa Kar mumcy taji Kuma,zata Mai magana ya kashe wayar ,Husna d Ido tabi wayar da kallo.

Bayan husna ta bud'e Mai sai taga mutum ya Kama hannun ta ya cire daga k'ofan d take Shirin rufewa ya rufe ahankali ya sake kamota suka haura sama kamar mara gaskiya har sai da suka Shiga falo sanan y sake ta ,Yana raba jikin shi da nata yaji Abu ya dawo Mai sabo a take ya Kuma Shiga wani yanayi.

Husna na tambayan shi lafiya koroshi akayi?

FU'AD be samu damar Bata amsa ba ya wuce d'akin shi a zaton shi ko ze samu sasaucin Amman Ina abuma sai gaba_gaba yakeyi Dole ya d'aga waya ya Kira Husna ,Bayan ta d'aga umarnin zuwa d'akin shi y Bata be tsaya ta tambaye shi ba ya kashe wayar.

Husna da har tayi biris da umatnin nashi ,Amman sai ta mik'e da kayan bacci ta yafa siririn gyale ta Shiga d'akin bakinta d'auke da sallama , FU'AD kasa amsa sallamar yayi yanaya murkususu a gado alamu Akwai matsala.

Husna Jin shiru be amsa sallamar ba ,Abin har ya k'ular da ita ta fusata zata fice Tana cewa" shikenan dama Haka kawai aka Kira mutum babu dalili tunda sallama ma Babu damar a mansa maka har ta Kama k'ofa zata fita"

sai FU'AD yace "waalaiki sallam" cikin wata kasalaliyar murya Mai rauni da neman agaji ,Husna Abin tsoro ya Bata Dan Bata sanshi da irin muryar ba ,d sauri t dawo ganan gadon ta Kira sunan shi Tana tambayan shi "lafiya kuwa?

FU'AD nuni ya Mata da bedside d murya raunaniya "dubamin wani magani a ciki ki taima kamin d Ruwa"

D sauri Husna ta d'auko ruwan roba t lalubo wani magani Tana cewa" gashi tashi kasha"

FU'AD hannu y dinga Mika Mata ,itama mikamai ta dingayi ganin hanun su Taki kaiwa sai ta d'an hau gadon ,ruwan kawai ya karb'a Yana cemata "kamani na tashi"

Husna tsakani da ALLAH ta Fara kiciniyar kamashi ta bud'e| ruwan ta ballo maganin Tana Shirin samai a Baki Tana Shirin bud'e Ruwa FU'AD ya goce ya Fado kanta ,Husna kiciniyar kwacewa ta Shiga yi Amman Ina FU'AD ya mak'aleta ta ko Ina sai sambatu da kalamai yake zuba Mata ,tureshi ta dingayi Tana cewa" mugu Mara cika alk'awari Ni zakama dabara"

Duk yunk'urinta Husna kasa kwayan kanta tayi daga hannun FU'AD sai da ya cimma burin shi sanan ya Sami sukuni.

Husna taci kuka tayi magiyar tayi ban hakuri Amman har sai d kuka ya rinjayi maganar ta.

Bayan FU'AD y dawo hayyacin shi ,Husna na ta kuka tana Shirin tafiya d'akinta FU'AD ya kamota daga rarashi da bada hak'uri sai ya sake nausawa birnin karaye sosai Husna da jigata , FU'AD nata aikin rarashi da magiya.

Husna taci kuka kamar ranta ze fita , FU'AD yayi rarashi kamar ze Ari Baki sosai yake rarashin ta Amman Ina ta zuciya gashi gari ya waye sai yanzu yake kunyar Kar mumcy ta ankara Yana sashin tayi zargin me ya kawo shi?

Jin kukan Husna ya mantar dashi tuhumar mumcy kawai ya koma d'akin Husna ya dinga Bata hakuri nuna Mata bada niya ko sa kanshi hakan ya faru ba ,Husna tsawa ta daka Mai Tana cewa" Daman ka Saba Haka ka fad'a kwanaki ma"

FU'AD d kyar y samu husna ta Dena kuka,da aka umarci me Aiki ta Kira Husna su karya da mumcy "FU'AD sai cewa yayi akawo Mata sama a had a harda shi yanzu y shigo a gayama mumcy,komawa akayi aka idar da sak'on oga FU'AD.

Mumcy mamaki ta dinga yi daga baya ganin cewar matar shice Kuma ya Fara damuwa da son ta duk da yaki yadda sai kawai ta share zancen.

Bayan ankawo musu ,d kyar FU'AD ya Shawo Kan Husna tad'an ci wani abun yanata ji kamar ze giyata Dan yasan yau ta taimake shi ayaune kawai ce iya cewa tamai hallaci a rayuwa Dan ya manta wacan lokacin.

Husna Abin har mamaki yake Bata ,Amman in ta lura da yadda yake Mata ayanzu Bayan ya cucewata sai taji ai badan ALLAH yake Mata hakan ba sai tayi watsi da Jin dad'in kulawa da tarairayar da yake Mata.

FU'AD ya Gama yanke shawarar yau ko Aiki baze fita ba ,har mumcy Kiran shi tayi awaya sai ya nuna Mata bayajin dad'in jikin shine ,ta umarci da yaje asibiti ko likita yazo ya duba shi ,sai yace Mata ai gajiyace kawai ya sani ze warke insha ALLAH kuma Yana samun kulawar husna, mumcy cewa tayi toh shikenan sai na ganku in bakuzo ba Ni nazo dubiya,sosai FU'AD yaji kunya Bayan ta amsa yabata fargabar Kar ta hauro din da gaske.

Husna ma Abin duk nauyi y Mata yau ta kasa sauka kasa ,ko tayi k'ok'arin sauka sai FU'AD ya hanata ta hanyar tambayar ta Abin da take bukata Abin har mamaki ya koma bata.

FU'AD d Husna Basu suka sakko ba sai azahar shima Dan FU'AD ze fita masallaci ne ya lalaba Husna suka sakko Kar mumcy ta tambaye ta Dan yasan Dole Ayi Haka....

Sanaya dai Abin duniya ya Fara isarta mamanta Tama waya Akan itafa zata taho Egypt ta gaji da auren d suka Mata naki Dan ......sai ta kasa fada Tana gudun Kar zargi ya biyo Bayan bayannan ta.

Maman ce tace"Dan mme fada min duk matsalolin ki inbaki fad'amin ba wa Zaki fad'ama a matsayina?

Sanaya cire kunya tayi tace ,Daman baya bani hakin Auren d kuka Mana ne jiya har neman shi nayi yaki kulani kuma ma.....

Bara k'arasa ba maman tace,sanaya me Kika zama har ke kike neman shi ? Ai ban taba tunanin lalacewan da kikayi a Nan yakai ki nemi namiji ba haka, wayace ki nemeshi bakisan komai ze iya faruwa ba? Ko yace Baki da tarbiya ko yace kin saba bin maza....

Sanaya kuka tasa Abin da take gudu ya afku Amman tasan Mama bazata Bari maganan ya fita ba zata kashe shi Dan Haka ta sake cewa "haba mum kekika ce na fad'a Miki kuma gaskiya na nafada Miki kinsan dai Ni ba dutse bace tun kawo da kuka girke be tab'a kulani bafa maganan da nakeson ki Gane ace banki tonamai asiri tuni ba sai yanzu Dan na fad'a har kema zakiga nayi laifi?

Mum cewa tayi ehtoh kema kince wani Abu kinyi daidai kinyi ba daidai ba koma dai meye kawai wanan maganar kartaje ga dadyn ki Amman Akwai ta inda Zan billoma lamari sanan Kar ki Kara nuna buk'atan ki gareshi kina mace Mai class Haka Dan kin banbanta da wawiyar da suka Kara aura Mai din can kinji ko?

Sanan zamuyi magana kinji ki barmin komai a hanuna.

Sanaya tace "toh sukayi sallama"

Bayan Husna ta sakko suna Hira da mumcy FU'AD har yaje yayi sallah ya dawo ya shige cikin su Yana tayasu hirar sama_sama Husna inta kalle shi suka had'a ido sai ta Harare shi , FU'AD sai ya dauke Kai,kusan so biyu Husna na hararar shi d alamu haushin shi takeji ,sai ya fito da dabarar da ze goge haushin shi da takeji sai ya d'aga waya ya Kira B2k suna hirar office sai B2k ya sako hirar Aisha ,sai ko Abin Yama FU'AD dad'i suka dinga magana har FU'AD na Kama sunan Aisha Ghana yanayi Yana Satan kallon Husna tanajin sunan tayi wani iri har kusan tsare Fu'ad tayi da kallo batare da ta sani ba fal tambaya a tare da ita ,har FU'AD ya ajiye wayar Husna neman Karin bayani take daga FU'AD din Dan tanason gaskata bayanan dake fita daga bakin FU'AD Akan Aishar da take zargi.

Bayan FU'AD sun Gama wayar sai yafara cewa"hmmmmm kunsan mutumin nawa ya kusa zama ango Yar gida zamuyi insha ALLAH.

Sai mumcy tace wakenan? Kuma dawa za'ayi Yar gidan?

Itako Husna da Ido take tuhumar shi idon ta kir akanshi Taki daukewa Dadi hakan yamai ko banza ya samu attention d'inta yanzu sai yace"B2k ne soyayya ta kullu tsakanin shi da Aisha k'anwar matar Yaya Jameel wacce ta zauna da ita d'inan ko nace kawar Husna Dan kufi ganewa wacce sukayi rayuwa tare a Abuja.

Husna mamaki tayi har batasan lokacin da tace Aishan? Da B2k naka?

Mumcy ko cewa tayi "Masha ALLAH" ALLAH yasa yin na ALLAH ne Abu yayi Dadi ai tanada hankali gwanda ta dawo kusa da Yar uwarta.

FU'AD sai da ya amsa Addu'a mumcy kafin ya amsa tambayar Husna da cewa sudai Kinga kawar ki zata dawo kusa daku sai kawancen ku ya Dora.

Husna murmushi Mai kayatarwa tayi da ya sake bayyanar da kyanta yayi gagawar korar haushin Fu'ad , FU'AD ma Dadi yaji yayi hamdala da dabarar Nan d yayi na sanyata cikin Nishad'i.

Kiran wayane ya shigo wayar mumcy ,Bayan ta d'aga sai take cewa ai na shafa'a da maganar taron Nan Amman insha ALLAH zanzo ko ba Akan lokaci ba zuwa anjima Kar ku damu ai aikin mune munsaba.
Chapter 85 · 0% Book details