Sashe 59
Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Turaren Husna ta d'auka ta dinga kallo Tana Kuka Tana kiranshi da bakin turare Wanda ya bakanta ran mutane da dama ,to ma meye acikin shi ? Mama habee kece kike Shirin tarwatsamin farin ciki? Wallahi Baki da gaskiya a turaren Nan ,har anan ma Baki barni ba? Sanin da na Miki bakya bin malaman tsubbu ko bokaye duk da bansan gaskiyar ki ba Kuma hankaka kike gabanki fari bayanki Baki ,yanzu in wani Abu ya Sami FU'AD fa ? Duk da badan shi kikayi ba kinyi ne Akaina Mara galihu da nayi Amfani dashi inajin da yanzu na sheka barzahu .........kuka ya ci k'arfin Husna Tana maimaita ALLAH ya Isa tsakani na dake nida yadda dake har gaban aba in Akwai kin kasheni da Raina wallahi badan baba ba sai na Toni asirinki makira nabar Miki gidan ma ban tsira ba ,sosai Husna take kuka a kujera ta kwana idonta fal hawaye idanun duk sun kumbura.
Ana Kiran assalatu ta farka a gigice ta d'auro alwala ta yi nafila sanan ta dinga Addu'a har aka Shiga sallah tayi sallah.
Bayan ta idan a dadumar bacci batawo ya saceta ta d'an runtsa,Tana cikin baccin ta farka a tsorace taba tashi bathroom kawai ta fad'a tayi wanka da zata tsaya gyaran d'aki sai taji Bata da k'arfi ko kuzarin da zata iya wani Aiki ,Dan haka wanka kawai tayi ta zura doguwar Riga ta zura hijab tayi kasa wajen mumcy.
Mumcy na Kan salaya Tana jira sai tayi sallah walha kafin ta mik'e sai taga Husna ,Husna har k'asa ta duk'a Tana gaishe da mumcy yayin da hawayen da take a adanawa yaki b'oyuwa sai da ya shatato kumatunta ,ganin ta cigaba da kukan mumcy ta rarasheta duk da Tana ayyana matuk'ar ta sameta da hannu cikin rashin lafiyan FU'AD tabbas zata ji babu dad'i.
Bayan mumcy tayi walhan ta Shiga band'aki tayi wanka ta saka doguwar rigar leshi ta d'auko hijab tasa da safar kafa ta riko carbinta ta d'auki Jakarta sai tace ma Husna tazo su koma asibiti hankalinta yak'i kwanciya kwana tayi cikin zulimi da fargaba,Husna ma cewa tayi wallahi Nima hajiya mu tafi Dan ALLAH.
Ko aunty sa'adiya sun manta basuma magana ba sai sako suka bayar abata ,ma'aikatan gidan nata musu Addu'a ALLAH yaba FU'AD lafiya Mai d'orewa,cikin kuka Husna take amsawa da Amin.
Suna Isa asibiti ,suka nufi d'akin da aka kwantar da FU'AD d'in Yaya Jameel y taso ya taresu , mumcy burinta taga FU'AD da sanin abinda yake ciki.
FU'AD ya dawo hayyacin shi yadan bud'e ido ,yanzuma kamar yaji muryar mumcy motsi sukaji a farayi Yana bud'e ido kad'an_kad'an har ya bud'e ido , mumcy kamo hannun shi tayi Tana Kiran sunan shi yayi shiru dai baya ko iya magana ,Husna nacan yanata kuka ,can FU'AD ya juyo sautin kukanta waigawa da zeyi ya hangota sai ya runtse idon Yana Mata nuni da hannu Akan ta fita a d'akin,sosai suka fahimci abinda yake nufi Yaya Jameel d mumcy ,Husna k'ara rushewa tayi da kuka Tana wallahi FU'AD banma komai ba wallahi ......Bata karansa ba FU'AD ya Kara runtse ido Yana dafe k'irjin shi Yana sake Mata nuni da ta fita kawai baya San ganin ta.
Mumcy ce ta ce ta fita Dan ALLAH hankalinta a tashe ,Husna taso Taki fita Amman yadda yaya Jameel ya hayayak'o Mata kamar zai turata Dole ta fita Tana shatayar hawaye.
Sai da mumcy ta dinga lalaba FU'AD da mishi tambayoyi Akan Husna Dan ta kafa hujja da kyau ,duk tambayoyin da take Mai amsa yake Bata kawai ko ya fahimta ko be fahimta ba ji yayi ya gaji da tambayoyin Aiko ran mumcy ya sosu fita tayi ta Sami Husna "kikace Baki da masaniya a matsalan FU'AD ?
Husna ta bud'e Baki Tana cewa "wallahi tallahi hajiya bansan..... mumcy tace "Asma'u Adana kalamanki kawai ki sani in FU'AD ya Sami matsala kin samu kema ya akayi baya son ganin ki? Kuma na tambayeshi kinada masaniya Akan samuwar matsalar sa yace min eh" Dan Haka Husna kije gida kawai har sai mun nemeki ,Husna zatayi magana mumcy ta d'aga Mata hannu kawai kiyi abinda nace muma barin k'asar zamuyi Dan Nemo lafiyan shi ta tafi tabar Husna a wajen tanata kuka.
Mumcy na komawa Yaya Jameel yace , mumcy husnace sanadin rashin lafiyan k'anina ,abinda yarinyar Nan zata Mana kenan? Mun suturtata mu zatama tsirara a kasuwa? Ki barni naje na hukuntata Kuma sai na mayar da ita gidansu a yau tare da kashedi Mai zafi da Zan Mata akan k'anina da mayakin Auren su fuuuuu Yaya Jameel yayi hanyar fita .......
Mumcy ce tayi saurin dakatar dashi "haba yayan aunta wanan da Mata yafi dacewa Kai da zaka seta nutsuwarka ,da hangen mafita ,ka rabu da ita Nima nace taje gidan su har sai muje India mun dawo kafin duk da banso hakan ba Amman Babu yadda zanyi ,yanzu mu fuskanci matsala da lafiyan son kawai kaje kaga Dr Khaner sai ku shirya komai Gobe a fita dashi kawai banason jira.
Jameel kwafa yayi ya fita , FU'AD ko shiru yayi gashi yanajin wasu abubuwa Amman baze iya mayarwa ba shi kad'ai yasan me yakeji duk da ba wani ciwo yakeji a jikin shi ko gabobin shi ba Amman jikin nashi Babu dad'i.
Husna Tana Kuka ta koma gida ,sashin aunty sa'adiya ta nufa Tana Kuka Tana gayamata yadda komai yake har cewar da hajiya tayi ta tafi gida ,sosai sa'adiya ta tausayama husnan har da tayata kukan Abin ya tab'a zuciyan ta ,shawara da hak'uri yaba Husna tace taje gidan komai zai daidaita insha ALLAH yanzu suna cikin Jin zafin faruwar lamarinne Amman zasu huce ,Amman karta tafi ta Bari sai zuwa gobe in zasu tafin in sun sake cewa tabar gidan sai ta tafi.
Aunty sa'adiya ta shirya ta tafi asibitin ta duba jikin shi sosai ta tausaya Mai ,taso tayi magana Akan abun gudun Kar tata tayi zafi sai ta fasa.
Husna wuni tayi a gidan su Harri na aikin rarashi ,har su mumcy suka dawo da FU'AD d yamma likis.
Yaya Jameel Yana tozali da Husna ya Fara cemata" me kikeyi ne har yanzu Baki tafi ba ?
Tsugunawa tayi zata bashi hak'uri ya juya baya Yana cewa baze saurareta ba kawai ta tafi gidan su sai yazo.
Husna mikewa tayi tace su Mata alfarmar magana da FU'AD ko so d'aya ne Dan ALLAH.......Basu Bata izini ba ta tashi taje gaban FU'AD tace Dan ALLAH FU'AD kayi hak'uri ko kiyashi bantaba cutarwa ba bare Kai kayyada Dani wallahi Nina kaina a daure yake kabud'e Baki kayi magana ka fitar Dani daga zargin da su mumcy sukemin inkamin Haka kagama min komai sai na tafi nabarma gidan ku ,kayi magana FU'AD Dan ALLAH Tana had'a hannun ta biyu a goshinta tanata rabza kuka, sanan kaima ka amince na tafi? FU'AD d'aga Kai yayi Yana kawar da Kai gefe ,zaro Ido Husna tayi ,tace nagode da katamcin ku gareni bazanmanta wanan ba ko zanbar duniya dashi Zan tafi acikin Raina.....
Sai mumcy tace tashi kije driver ya kaiki je ki d'auki kayanki ,Husna cewa ta sakeyi na tafi ko FU'AD? Da hannu ya Mata nuni da eh ta tafi baya son ganinta,husna na kuka ta tashi ta haura sama ,aunty sa'adiya ta bita tanata Bata hak'uri suka rungumu junan su ,aunty sa'adiya ce ta tayata had'a kayanta a wani akwati me kyau da tsada ,har ta d'auko wani kud'i ta Bata har bakin mota rakata Tana cemata zasuyi waya ,Husna na kuka tabar gidan duk da mumcy Tana Jin babu Dadi a ranta Amman Babu yadda zatayi lafiyar FU'AD yafi Mata komai ayanzu.
Husna Bata gane Tana cikin matsanaicin tashin hankali ba sai da taga anfaka a gidan da take farinciki lokacin da ta barshi yau gashi ta dawo Mai inta tuna da cewa da babanta zatayi rayuwa a gidan sai tad'an samu nutsuwa ta fito a mota ta ja akwatin ta da sasanyar sallama ta Shiga gidan jiki Babu kwari.
Mama habee na ganin ta tace ,me ya dawo dake Nan keda kike cikin aljannar duniya har kina hurama mutane hanci? Husna kukane yaso kwace Mata ta nufi d'akin da ta Bari ,sai ko humaira Tasha gabanta ke Baki da matsuguni a gidan Nan mun yafe ki Nan dakina ne waje road ........Tana nuna Mata hanyar waje Husna ajiye akwatin tayi tace Ina babana?
Mama habee tace uban wa Kikaba ajiyar gyatumin naki?
Husna cikin kuka ta fice a gidan ta nufi wajen sana'ar shi ta awo ,tun kafin ta k'arasa taga shagon a rufe ,da zata juyo ganin ko zama anyanatayi a gidan ubanta sai ta k'arasa wajen mak'ocin shi taga ma ba Wanda ta sani bane ,duk da Haka tamai sallama ta gaishe shi ta tambayeshi babanta ,yace wallahi Suma cigiyar shi suke yau satin shi kusan na 3 kenan be bud'e shagon ba sun aika gidan ance wai ba'asan inda yake ba ,salati Husna tasa yayinda kuka yaci k'arfinta ta nufi gida.
Tana Shiga ta sake tambayan su Ina babanta ne wai ,mama habee tayi shewa tace ya bacce Suma neman shi suke in ta ganshi ta turo musu shi humaira nata taunar cingam.
Husna kuka tasa Tana ta Shiga uku ,mama habee tace ko d'aya back shiga ba sai kin ganni a titi Zaki kwana karti sunyo kanki Nan Zaki San cewa kin Shiga uku dumu_dumu Dan wallahi bazaki kwana cikin gidanan ba in Kuma kina musu zauna kisha mamaki ,Husna kuka tasa Tana ba mama habee hak'uri Amman ta turo Mata d'an kwali ma alamu babu sani babu sabo rashin mutunci zallah.
Husna d'ankwalin ta ta shimfida zata zauna sai humaira ta tare wajen ta nad'e Mata d'an kwalin ,sosai duniya Tama Husna zafi Nan ta sake tabatar da cewa Akwai mugun k'ulli da sukayi cikin turaren Nan Dan Haka ta taho dashi.
Haka suka Gama abincin Rana suka cinye a gaban Husna ,sai da suka Shiga d'aki ta d'auki buta ta kama Ruwa tayi alwala ta shimfida d'ankwalin ta tayi sallah ta dinga rok'on ubangijinta.