← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 95

Sashe 7

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan isowar su katafaren gidan ,horn FU'AD yayi baba Mai gadi ya bud'e musu Yana musu barka da zuwa ,ya samu waje yayi parking ,har bakin motar baba Mai gadin yazo Yana kwasan gaisuwa ga yayan FU'AD din da matar shi cikin girmamawa ,shima ya amsawa baban har yamai kyautan kud'i yanata GODIYA da murna ya dinga yima mahaifin su Addu'a kuwa da ALLAH yamai Rasuwa tun wasu shekaru da suka shud'e ,suka dinga amsawa da Amin ,Dan suna Jin dad'in ayima mahaifin su Addu'a...

Bayan shigan su falon momcy bakin FU'AD d'auke d sallama Yana tsokanan momcy ,momcy na hakince a kujera ,tozali da tayi da yayan FU'AD din sai murnar ta ta k'aru ,Amman ganin surikarta sai ta Fara cewa"Zo Nan surikar kirki taho kusa Dani kiyi masauki anan ,ta tafi kusa da
Momcy ta rungumota ta had'ata da jikinta Tana Mata oyoyo ,ita ko ta zauna ta Fara yaba karamci irin na surikar tata da nuna kulawa tun Bata Sami ko mintuna 5 ba acikin gidan .

Bayan sun gaisa ,momcy nata tmby y suka baro jama'ar can kasar da iyayayen sirukar tata, tanata nuna musu kulawa ,Bayan sun hutane momcy ta umarci da suje suci abinci kafin suyi masauki a sashin su don su huta ....

Jama'ar momcy ne suka halara gaba d'ayan su ,su hud'u awajen cin abincin surikarta na kusa da ita shima FU'AD na kusa da yayan shi sunata Hira Mai cike d nishad'i suna Hira suna raha mahaifiyar tasu na nuna musu kulawa ,ahaka har suka Kamala cin abincin kowa na yaba irin girkin d aka shirya musu Haka kala kala..

Bayan sun Gama momcy tace suje su huta a sashin su ,ta Kira Ma'u akan taje ta bud'e musu sashin Dan d'azu a hannun ta akabar makuli ...

Jin furucin momcy yasa FU'AD Jin wani iri wai Ma'u akaba makulin sashin yayan shi? Shi besan inda momcy takeson ajiye _dirty girl_ d'inan ba ,ya fad'a cikin zuciyar shi,Dan Haka ya maka Mata wata uwar harara Mai Tatare da gargad'i yace ta bashi makulin waya gayace ta sashin ma tukunna da har hannun ta ya samu ma'adanar makulin sashin?

Ta mik'o Mai kenan,jikinta a sabule, sai momcy tace "son kafita idona na rufe ,Ni na gayaceta na Bata umarni Kuma yanzun ma itace zata bude ta cika umarni na "abinda hukunci ya biyo baya kazo kamana nida ita ,wuce kije Asma'u ...

Abin da momcy tayi y kular da FU'AD ,itako matar Yaya murmushi tayi tace suna Mai dad'i shine akayi _short cut_ d'in shi wai Ma'u ,momcy tace ai Haka kowa yake kiranta Amman Banda Ni ,shidai yayan FU'AD d'in cewa yayi mu tafi nidai na gaji hutawa kawai nake bukata ,sai ko FU'AD y garoma Ma'u akwatin big bro d'in nashi wai gashi tunda momcy ta zab'ar maku abokiyar rakiya Ni bazan jera da ita ba Yana mita Yana kallon momcy ta gefen ido ...

Momcy kuwa cewa tayi ,sai me Abin da ba kaje kayi ba ,ma'un zata iya ai ,zuwanka d rashin zuwanka babu abin da zai k'ara kamar yadda babu abin da zai rage ,Ina dalilin wanan al'amarine ka aro Halin d ba nakaba ka k'ak'aba ma kanka ....

Yayan shine yace , gaskiya Kam Nima ban sanshi d wanan sabon halin ba ,maza kayi watsi dashi kabar halinka managarta Abin koyi ...

Momcy tace ka tayani dai tunda kaga zahiri yanzu kaima ....

Jin anmai yawa y haura sama ranshi Babu dad'i Yana mita ,Yana Kara Jin haushin Akan wata kazama aka Mai Haka? Ya zama dole yayi maganin ta wlh.

Ma'u tabi umarnin momcy ta rakasu har sashin su ta bud'e musu kofar ,ta Kira me yima momcy wanki da guga ya dibi akwatunan su ya Kai musu sashin su , momcy ta umarci Ma'u da takai musu wani abinci da ko tabawa ba'ayi ba atunanin ta ko kunya surikar tata takeji ...

FU'AD tunda y haura sama be sako ba sai da ya samu Kiran gagawa daga office ,Dan yau dama yace ranar ta yayan shi ce ,gashi Ma'u ta Shiga Mai cikin ranar ta b'ata Mai Dan Haka y sakko ,yana ma momcy sallama yace ya samu Kiran gagawa ne , momcy atunanin ta duk fishin ne yasa zebar gidan ,Dan haka Taki kulashi bare rarashi ,sai Addu'a sauka lpy d tamai....

Bayan ya fita ,ya samu ma'u naba baba Mai gadi abinci ,sai FU'AD ya shirya Mata mugunta Bayan ta gama bashi ta juyo Tana tafiyar ta hankalin ta kwance batasan ma ya fito ba kawai , FU'AD yayi kanta da mota ze kad'eta gadan gadan k'iris ya rage be tab'ata ba badan tasa ihu ta koma bayaba ,Aiko ta bugi gate d'in gidan sai da hanun ta yayi wani irin k'ara kanta ya bugu alamun kamar taji ciwo ,hatta baba Mai gadi sai da Abin y tsorata shi ,itako ajiyar zuciya kawai takeyi atunanin ta FU'AD besan me ya aikata ba,sai kawai taga Yana ba baba Mai gadi Umar nin bud'e Mai gate ,ita Kuma Yana Mata wani mugun kallo na irin kad'an Kika gani d'inan ....

Bayan an bude Mai ya Cinna hancin motar y tafiyar sa batare da y saurari Abin d y aikata na yunk'urin kisan Kai ba ,yasa ta dinga ajiyar zuciya d k'ara yadda tsanar d y Mata har ya Kai ze iya kashe ta?

To aikuwa ko tabarmai gidan su kafin yayi ajalinta ko tayi damarar fafatawa dashi a filin daga, matukar karfin ta yakai na rike makaman yakin da zata iya yak'ar shi .....

Maman shaheed ce👌🏻
[4/23, 4:00 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA*

_RUBUTAWA DA TSARAWA_
BY
*Fatima Abubakar Shu'aib*
(Maman shaheed)

_shafi na 9_

_Dedicate to oll Rik'on kwarya fanc_
❤❤❤❤❤❤
🥰🥰🥰🥰🥰🥰
😍😍😍😍😍😍

Bayan baba Mai gadi ya Gama jajantama Ma'u ,jikinta a salub'e ta koma ciki Amman Tana Dan Jin zafi a kanta da hanun ta inda ta bige ta had'u da gate d'in ...

Haka ta koma ciki suka d'an tab'a Hira da su Harri sukaci Abinci ,..

Yaya da matar shi suna sashin su sunata huta gajiya .

*************
Kici Abinci inzakici ke kulin sai ansha fama dake wajen cin abinci ,kici Kisha magani in Kuma kukan kikafi so to in kin Gama na dawo na Baki maganin ....

Wanan furucin na fitowane daga bakin wata ma'aikaciyar jinya ta masu tabuwar kwakwalwa ( mahaukata) Tana ta tursasa wata baiwar ALLAH Akan taci abinci Tasha magani ....

Ita dai wanan matar Bayan wasu shekaru da suka shud'e ne wani atajiri ya bigeta da mota sakamakon ganinta d yayi a yanayin hauka yasa yaayi gidan mahaukata da ita Don yanada Halin talafama Rayuwar ta Dan Haka ake kuka da ita da maganin ta da Abin da take ci ,maganin ake Mata Amman fa kullin jiya iyau Abin kamar zeyi sauki sai ya Kara tashi ,yayi cigiyar Yan uwanta har ya gaji ,matar shi da mahaifiyar shi sun shawarce Alh malan akan agwada Mata na gargajiya yace Sam ba zeyiba asibiti ma sunayin komai shi irin Yan asibiti akida d'inan Nan gidan shi ba'a Shan jik'e jik'en gargajiya ko wasu abubuwan da ya shafi malamai a cewar sa duk 'yan tsubbu sunfi yawa yanzu da masu maganin karya ,kowa ka gani shine Mai gaskia Mai bada maganin kowacce cuta Karin Abin takaici su fito kafafen sadarwa kamar su ,gidan rediyo,talabijin,suta talata kansu ,da wanan ya kafa hujja yasa duk ya musu kud'in goro baya harka dasu Sam Kuma iyalan shima Basu Isa ko ab'oye suje ba bare azahiri ,Dan ganin yadda bayaso yasa hajiya Ramatu ta hak'ura hatta hajajju makkatu wato mahaifiyar sa ta sallama dake gidan su d'aya ya dawo da ita kusa dashi sashinta da ban ,zaman su kadaran kada han da surikar ta da jikokin ta ,shidai Yana matsanaicin kula da mahaifiyar shi ...

Bayan ma'aikaciyar jinyar ta gama ma matar sababi taje ta dawo ta Bata abincin ta karba ta Bata maganin kamar yadda suka Saba kullin sai sunkai Ruwa Rana kafin Tasha maganin inda sabo har sun Saba ....

****************

Momcy ce ta umarci Ma'u da taje sashin su yayan FU'AD ta fito da kayan Abincin da suka kammala ,cikin girmamawa da bin umarni Ma'u taje bakinta d'auke d sallama har ta k'ara yi musu ban gajiya ,suka amsa d gajiya tabi lpy taga matar yayan ta Kara canja Kaya daga Wanda tazo dasu zuwa wasu masu masifar kyau Dan sai d ta birge Ma'u ....

Wani Abu ,da kyar Ma'u ta d'ibo kayan Abincin zuwa kitchen din mumcy Tana Gama ajiyewa ta dinga shafa hannun ta Tana "wash ALLAH"! Haka ta sake komawa ta d'ebo sauran dauriya kawai takeyi Amman hanun ta na Mata zafi tabas kawai dauriya takeyi ...

Bayan wasu awanni da yamma sosai Bayan an Kamala girkin dare , momcy ta umarci Ma'u da ta kaima su yayan FU'AD nasu sashin su harda tacacen lemukan da aka hada musu don Susa a firinji don yayi sanyi kafin su buk'ata ...

Koda Ma'u ta d'auki jug din don Fara Kai musu hanun ta kasa d'auka yayi jug din tintsirewa yayi ya zube ,momcy da Harri sukace lpy Ma'u kalau kike?

Ma'u yatsina fuska tayi tace wlh hanun tane taji baze iya d'aukan jug din ba .

Momcy tace meya Sami hannun ,Hari tayi saurin cewa badai tun dazu ba d kikace kin bige ? Ma'u tace tun shi wlh kawai daurewa nakeyi .

Momcy tace kufito min a mutum? Meya samu hanun?

Nan Ma'u ta saya Mata abinda ya faru ,kawai tace bigewa tayi da taje kaima me gadi abinci dazu shine hanun yaketa ciwo har yanzu ga zafi da nauyi ko motsa hanun banason yi sai dole ....

Momcy ta tab'a hannu Ma'u tace "wash ALLAH na da zafi" momcy tace sannu Harri babu inda ake gyara d Kika sani kuje aduba kafin ta tafi gida inyaso inkunje daga can sai ta wuce gida ta huta nasan Ma'u da son ganin babanta da bin umarnin shi tun dazu na fuskanci son tafiya gida takeyi ,ko ba Haka bane Asma'u? Inji momcy.

Ma'u tace hakane babu kunya Dan duk ta k'osa ta tafi gidan taga baban ta da haidar autan su .
Chapter 7 · 0% Book details