← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 95

Sashe 25

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan sun yi sallama da mufeeda ,suka wuce zuwa mota mufeeda nata d'ago musu hannu ,Jameel ma Yama dady sallama da mamy da mufeeda ko takan sanaya da uzaifa be bi ba ya wuce ,sanaya ta wurge shi da harara tace "Kai ka sani ,uzaifa ma hararar ya Kai Mai suka tafi .....

Bayan su Jameel y dawo dasu gida ,suka koma d'aki suna yaba halaya irin ta mufeeda suna kushe Halin sanaya da uzaifa.....

Isar su dady keda wuya ,ya Kira mumcy Akan sun Isa azo a d'auke su, mumcy da gagawa ta umarci driver yaje ya d'auko su ,ta dinga Kiran FU'AD a waya Tana Mai gargad''in Kar ya Bari Alhaji Yaya ya rigashi shigowa gidan ,sosai FU'AD ya k'ulu da maganar mumcy y Rasa dalilin da yasa take Abu kamar Tana tsoron mutumin Nan Bayan Babu abun da ya Isa ya Mata sai Abin da ALLAH ya Mata ,in anyi magana tace gudun magana ,kwana da lafiya yafi kwana da kud'i ,yadai tabatar Mata da zai dawo Yana hanya ,al'halin ko hanyar be gau ba ,har akaje aka d'auko su suka shigo main parlour......

Sosai mumcy ta sa aka shirya musu lafiyyayen abinci kala kusan 6 da juice kala kala da snacks ......

Alhaji Yaya FU'AD ya Fara tambaya don yayi mamakin da bashine yaje d'auko su ba ...

Mumcy murya na rawa tace "baya gidan ne ,Amman ta same shi a waya gashinan zuwa " shiru kawai yayi Mata sai mamy da suke ta gaisawa da mumcy ,sai sanaya da uzaifa da suka gaishe da mumcy ,sai mufeeda a k'arshe har take ba mumcy sakon gaisuwar Ma'u ,mumcy sosai ta tuba da Asma'u taji dad'in sak'on Kuma ,hakan ya bak'anta ran sanaya sai tab'e Baki da tayi ....

Suna zaune gaba d'ayan su su 3 uzaifa ya tafi masaukin su da aka sauke su ,sanaya ma da mufeeda sun tafi nasu ,su Kuma sunata magana Kan matar d FU'AD d'in ze aura , mumcy tace ya Bari in FU'AD d'in yazo yaji daga bakin sa .......sai ga FU'AD ya shigo ....

FU'AD da yayi tozali da Alhaji Yaya ji yayi kamar ya koma ,Amman Ina ya Riga ya shigo sunyi ido 4 dashi ,kawai karasawa yayi ya kwashi gaisuwa ...

Nan Alhaji ya Fara Mai maraba da tambayoyi zafafa Akan maganar matar da ya fitar ze aura ,da kyar FU'AD ya iya furta Babu ,Bayan gumin da yake shirin keto Mai yau ya tabbatar da gaske ake maganar ga wani mugun kwarjini da yayan mahaifin nashi yau ya Masa ji yake baze iya musu da duk Abin da ya yanke Masa ba a yau gani yake bashi da tacewa ,barawo a hanun Mata ya gamar sadak'arwa da duk wani zabi ko hukuncin da ya zartar Mai don Haka ya San cewa yau sunan shi ,sai yadda ALLAH yayi ....

Alhajin ne ya dawo dashi hayyacin shi ,da bashi minti 2 kacal ya Gama tunani da Nazari Akan matar Aure in ba hakaba yau zemai Mata gobe atashi da d'aurin Aure a gidan .....ba mumcy ba FU'AD d'in kanshi sai da hankalin shi ya tashi .....

Kusan mintuna 4 FU'AD Babu labari mumcy nata Mai magana da ido ,Akan ko adangi ne ya zaba amma Ina FU'AD tunani ya tsaya cak ya Gama sadak'arwa ....

Afusace Alhaji Yaya yace to ya shirya Gobe ze d'aura Mai Aure Ana sakowa daga masalacin juma'a Babu fashi matuk'ar numfashin su yakai Gobe gaba d'ayan su ....

FU'AD kasa d'agowa yayi ,sai mumcy da ta iya tambayar Yaya wa zaka aura Mai Ni da inada shawara .......dakatar da ita FU'AD yayi Akan tayi shiru ,sai ko Alhajin yace ko baka dakatar da ita ba ,Bata da hurumin yin magana Akan wanan batun Mara kunya fitsarare ,ko babanka ALLAH yayi Mai rahama na fad'a baya tankawa kasani kaima Kuma ko Yana Raye Zan iya zartar da Abin da nake shirin zartarwa kasani itama ta sani ,gyada Kai mumcy tayi Alamar hakane ,Bata hak'ura ba ta sake tambayar to wa zaka aura Mai kenan?

Cikin nuna Isa da gadara da Gaya Mata Dan kowa ya sani Yana hura hanci kamar botorami yace " *SANAYA* k'anwar shi ................mumcy da mamy atare sukace *SANAYA KUMA*? ...........

Shiko FU'AD ba'asan a duniyar da yake bama ...........

Maman shaheed ce dai💃🏼
[4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA*

_RUBUTAWA DA TSARAWA_
BY
*FATIMA ABUBAKAR SHU'AB*
(Maman shaheed)

💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥

Pg 24

*NA GODE DA ADDU'O'EN KU*👏🏼
*Shi Kuma mamaci Allah ya Haskaka kabarin sa ya Raya Abin da ya Bari ,Allah ya shafe lefukan shi ,da mamatan da suka Rasu nacikin motar Baki daya,Allah ya lulub'e su da Rahamar say yasa Aljannah ta zama makoma agare su ,intamu tazo Allah kasa mu cika da imani*😭👏🏼👏🏼

Jameel be Bari wata damuwa ta cigaba da baibaiye FU'AD ba duk inda yayi Yana tare dashi har mumcy da ta ji su shiru saman ta haura don ganin Halin da suke ciki ,Tana zuwa ta gansu kamar wani Abu na rashin Jin dad'i baya Shirin faruwa a gidan musamman yadda ya sama d'an uwan nasa farin ciki ,sosai tayi Hira dasu ta jadada musu yin biyaya
Ga ummarni shi .
Yara masu biyaya sun amsa ,Amman FU'AD ji yake bana fa kamar ze kauce ,kawai dai ALLAH ya tsare .

Sanaya tanata dambarwar akan Auren da dadyn ta ya kirkirar Mata Tana cewa bazata auri FU'AD ba ,Dan Babu ruwanta da Abin da zuciyarta ta Fara hango mata na nagartan shi bere har ta yaudari kanta ta amince dashi maysayin zabin dady kamar wata Yar k'auye ko Almajira Dan kusan sadakanta yayi ko za'ayi biki na kece raini ma kuwa ,ganin wanan duk ba mafita bane ta d'auki wayanta ta Fara Kiran dadyn nata ,sai da takai Kira 5 sanan ya d'aga ,kafin tace komai ya katse ta da Yana tare da abokin shi ,yakusa dawowa gidan ,Dan yasan tatsuniyar gizo baya wuce na kok'i ,akufule ta jefar da wayar ,mufeeda Tace "sorry big aunty sai an had'a da hak'uri shi biyaya ga iyaye ALLAH ne ya bada umarni ,bin iyaye Kuma wajibine don mutum zega daidai arayuwar shi .......Bata k'arasa ba ,sanaya ta wulo Mata wani takalmi dake kusa da ita ,Tana cewa "Dan ubanki ke ai sai ki Aure shi laraba imani ayi canji dake uwar biyaya munafuka ,in kin haufu Dan ALLAH ki bigi kirji kice ya mayar da auren kanki ,karyar banza harni zakima wa'azin k'adangaru ,Tana yunk'urin tasowa ta duketa Dan ta kufula sosai .
mufeeda cew tayi , ALLAH ya Baki hak'uri ban furta hakan Dan Bata ranki ba , yi yadda kikeso ,Amman fa ki tuna daga k'in gaskiya sai kauce hanya tabar musu d'akin ,a zafafe sanaya take Shirin bin mufeeda ,Amman mamy ta Hana ta hanyar kamota ,Aiko sanaya aka saki kukan takaici ,mamy kinaji tanamin rashin kunya da wa'azin k'arya Amman Baki hanata ba sai Ni da zan Mata hukunci?
Mamy ,toh inbanda sanaya meye ta fad'a Wanda ba gaske ba duk cikin maganganun ta? Kiyi hak'uri ki Bari dadyn ku yazo muyi magana ta fahimta ,sanan sanaya taji sanyi na wucin gadi ya ziyarci zuciyar ta ,

Alhaji Yaya ,Yana dawowa ya Fara da Kiran sanaya ,Tana fitowa ta fad'a jikin shi ,Rayuwar turai Tana tabara da shagwaba ,sai kuwa ya cireta a jikin shi don yasan yanzu zasuyi bataciya don ya Gama yanke hukunci ba tare da amincewar ta b.
Sanaya "dady wai tatsuniyar naji ne ko GASKIYAR labari? Cikin himma da dabaru ya Fara Shirin birneta ta hanyar rarashin ta ,Yana Mata bayani Akan zumunci yakeson su k'arfafa gudun Kar rasuwan k'anin shi yasa zumuncin ya lalace ,Aiko Bayan ya Gama yimata bayani sanaya ta dire tace ita Sam bada ita za'ayi wanan zumuncin ba ,ya be Gaya Mata manufar shi ba tun kafin su bar Egypt sai yanzu kawai Dan yaga anzo ? Atake ta saka Mai kuka ,ganin tanata surutu bakinta har Yana Shirin furta zafafan kalamai ga dadyn nata ,yayi saurin tsawatar Mata da nuna Mata cewa Aure fa Babu fashi ta rungumi k'addara kawai ,Mara kunya tace "ita Bata Santa ba Dan ko hanya Basu had'a da k'addara ba ,Dan haka......Bata k'arasa ba mufeeda Tace haba bis aunty kisan kalaman da Zaki dinga firtama mahaifinki Mana?
Sanaya harara ta doka Mata ,sai shi dadyn ne yace "barta mufeedan dady so take taga b'acin Raina ,Kuma ba Abu Mai wuya bane ,mamy sai yanzu ta sako musu Baki , gaskiya hukuncin Nan anyanke batare da dogon nazari ba fa ,ya kamata aduba fa ,Ni yarinya ta ......Bata idar ba dady yace "dallah rufema mutane Baki bazaki yayafama wuta Ruwa ba sai K'ara izata ,in Baki da Abin cewa kimana shiru Akan Auren Nan Zan iya batawa da kowa wlh ,in nace kowa Ina nufin ke,ko ita ,ku kowa ma kawai ,Dan Haka kowa ya karb'i Abin hannu bibiyu kawai ,Dan Haka Gobe Akwai meeting misalin goma na safe ba Akan kowa bane Akan Auren ne zansa date kad'an Kuma Zan sa ,ya fice ya bar su ....
Chapter 25 · 0% Book details