← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 95

Sashe 39

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

```RUBUTAWA DA TSARAWA```
BY
*FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB*
( Maman shaheed)

💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥

Pg33

Bayan Yaya Jameel d FU'AD sun Gama hirar da zasuyi ,sai suka koma wajen mumcy gaba d'ayan su ,suka sami Husna sunata Hira , FU'AD yanata Satan kallon ta ,itako ko kalon inda yake Batayi ba sai Hira suke da mumcy.

Abin ya ishi FU'AD yaga mumcy taba Husna nutsuwar ta sunata Hira "sai FU'AD yace mumcy nifa bakimin bayanin Kan Asma'u uwa tagari da yadda muke alak'a ko nasaba ......be karasa ba , mumcy tace kaji daga baya Kai dai ka kula da matanka kasani amanace su agareka ,sai mumcy ta k'ara da yimai wa'azi Mai ratsa jiki da Haka ta bagarar da zancen ...

Sanaya ta zauna Tana ta latsa wayar ta , FU'AD ya shigo ya Mata sallama ,ta amsa sama sama ya zauna ganin hankalin Yana ga wayar ta ,ya tashi ya barta y koma d'akin shi .
Wasa Wasa sai da FU'AD ya shafe sati 2 shi a gida da matan shi tare da tursasawar mumcy .
Dan Haka yau da wuri ya shirya ya Fara Shirin tafiya office Dan har wani farin ciki yake yi ,Haka Bayan ya Gama shiri Yama sanaya sallama be jira amsawar ta ba ya nufi inda mumcy take ,ya gaishe ta yace ze tafi office da sauri da zumud'i ,har ya fita yayi hanyar waje mumcy ta dawo dashi da cewa yaje su gaisa da Asma'u ,a Dole yaje suka gaisa yake tambayar ta lafiyar da ,ta amsa da Babu matsala yanayi Yana Satan kalon ta har yabar dakin har yabar d'akin .
Bayan ya fita Asma'u ta koma wajen mumcy suka Sha hirar su .
FU'AD ya koma fita office yanata aikin shi hankali kwance ,matan Kuma ya raba musu kwana kowacce Yana Mata kwana 2 .
Aunty sa'adiya da Aisha suna yawan zuwa suyi Hira da Asma'u ,suna d'an lek'a sanaya ba sosai ba Dan har yanzu tak'i sakin jiki da su .
Da FU'AD yayi biris da son sanin wacece Asma'u ,Amman ayanzu da gaske yake son sanin asalin ta da alak'ar da ke tsakanin su musamman inya ga Tana Mai Kama da wacce ya tab'a gani a status d'in aunty sa'adiya ,Abin haushin shi ya Rasa dalilin da yasa be ajiye hoton ba da ya tantance ayanzu ,sanan Tana Mai kama da wata wacce be San kowace ba har yanzu .
Yau kwanan Husna ne Dan Haka kafin kowa yaje ya kwanta FU'AD ya Kira Husna yake tambayar ta asalinta da yadda suke da mumcy ,sosai Husna ta kasa Mai bayani ,da ya matsa Mata tace "yace ya tambayi mumcy ze samu amsoshin tambayoyin shi ,shi Kuma yace ai yasan da mumcy yake tambayar ta Dan hanka ya zama Dole ta fad'a mishi .
"Ita Kuma tace be zama Dole ba indai a bakin ta yake son sanin ko ita wacece ,ganin da gaske yake ta ci Alwashin ko me zai Mata bazeji komai a wajen ta ba ,badan Tana tsoron yasan ko ita wacece bane saboda ji take ayanzu ta Kuna Bata tsoron kauri Dan ji take ta shirya ma duk rigimar FU'AD ko Dame yazo itama tazo da nata zalon ,Haka suka Kai wajen 11 dare suna Abu d'aya tak'i gayamai shi Kuma ya nace sai ta Gaya Mai ,ganin bata da niyar fad'a yace in kin shirya zama Dani Dole ki fad'a min in ba Haka kuma.........sai ya kasa fad'a yayi shiru ..... Sai Husna tace inaki fad'a Kuma me? Barin je na sanar ma mumcy gwanda ka bayyana k'udirin ka tun yanzu tun zaman mu beyi nisa ba ta sani kowa ma ya sani na gidan .
Ya wurga Mata wani mugun kalo ,ta kawar da idon ta ,daga baya ma ta mik'e zata sauka k'asa alamun gayama mumcy zatayi ,da sauri yace "Ina Zaki? "
"Tace wajen mumcy in sanar Mata Abin da kace tayi gaba abinta ,yaga da gaske take zata tafi ,da sauri yasha gabanta "yace Kar ta sake ta sauka ko da Wasa ,yaga Bata da niyar komawa ta tsaya Yana ta Mata magana Tana Jin shi ,yasa hannu ya kamo kafad'un ta yayi kujera da ita yace ta zauna ko taje ta kwanta ,da ya rik'eta sai da wani spark ya shige shi bayare da yayi aune ba da sauri ya dagwarar da ita Yana tunanin al'amarin .
Itako Yana zaunar da ita ta tashi ta sakeyin hanyar barin falon da niyar tafiya Tana cemai kabari naje na sanar Mata Mana .....da zafin sa da nuna Isa ya daka Mata tsawa ,ta tsorata amman ta ki Bari ya gane ,yayi sauri ya saka Mata k'arfi ya kamota ,yana ji wani Abu na ysirga Mai Amman be sake ta ba sai da ya tabbatar ya kaita d'akinta ya zaunar da ita abakin gadon ta "yace wlh inta sake ta sauka a yau d'inan wallahi ranta zai mugun b'aci zata San waye FU'AD ,Yana tafiya Yana magana ,cikin k'aramar muryar da batayi zaton zeji ba tace "waye Kai Banda mugu kawai" da sauri ya juyo don Yana son tabatarwa itace tayi furucin ko kunnen sa ne Yamai k'arya ? Sai yaga bakinta kamar ba ita tayi maganar ba ,duk da Haka be yadda ba sai da ya ce mata "me naji kince"?
"Tayi mursisi tace Ni? Babu Abin da nace ,ko kaji nace wani Abu?
"Kwafa yayi ya fice ya rifo Mata k'ofar zuciyar sa fal da tunanin furucin da yaji kamar tayi sai ya tuna da Ma'u _dirty girl_ sosai abubuwan ta suka dinga dawo Mai har yake neman gaskata cewa tabbas muryar ta yaji Babu shakka ,ya Jima Yana tunanin yadda zai bullo ma da mumcy maganar son sanin wacece Asma'u? Amman Yana tunanin Kar ya balloma kanshi Ruwa .
Washe gari da safe Ma'u ta rigashi tashi Dan ya makara ,ta kwankwasa Mai k'ofan d'akin shi ,Bata jira fitowar shi ba ko amsawar shi ta tafi k'asa Taya su Harri aikin break ,tashi yayi ya Shiga bathroom yasan itace ta tashe shi ko magana beyi ba ,sai Bayan ya watsa Ruwa ya shirya tsaf don tafiya office ya fito yanata zuba kamshi Mai dad'in ji ,ya sauka ya gaishe da mumcy itako dama yasan Tana k'asa ,Dan Haka a k'asa suka had'u ta kasa Mai magana sai Satan kalon shi da takeyi shima Yana Satan kalon ta Yana Mata kalon gargad'i ,itako so take ta gaishe shi Amman Tana tsoro Kar mumcy tace meya hanasu gaisawa duk asama sai yanzu ,shima Dan Kar mumcy tayi zargin wani Abu yasa ya kasa Mata gargad'in da yakeso ya Mata ,Haka mumcy ta saka su a gaba har dining don suyi breakfast tare har ita ,ta aika a Kira sanaya ,sai aikowa tayi da cewa ita ba yanzu zata karya ba , FU'AD har ya tashi zeje ya Mata magana mumcy ta Hana shi ,badan yaso ba ya zauna ya rabu da ita Yana mita aranshi .
Tsakanin FU'AD da Husna sai kalon kalon sukema junan su duk mumcy Bata sani ba har FU'AD ya Gama ya ma mumcy sallama ya ma Husna sallama itama tamai Addu'a wacce ba mumcy ba har shi yaji dad'in Addu'a,ya amsa da Amin ya fice mumcy na cemai Kar ya sake ya fita be lek'a yaga lafiyar sanaya ba ,yace to ya tafiyar shi ko bi takan sanayan beyi ba Dan ta k'ular dashi akan kin zuwan da mumcy tasa Ayi Mata Taki zuwa wato ta Raina Mai uwa tagari Dan Haka yaki zuwa inda take shima .
Sai Bayan sun Gama har Asma'u ta koma saman ta ta gyara Rana ta farayi Bayan su aunty sa'adiya sunzo sun gaishe da mumcy sun tafi sanan sanaya tazo kwasan Tata gaisuwar wajen mumcy , mumcy nata janta da Hira don ta nuna Mata kulawa da son nuna Mata itama Yar tace ,Amman sanaya sai Shan kamshi take Tana nuna ba hirar takeso ba daga baya ma ta nuna k'osawar ta da hirar da mumcy take Mata har tace zata tafi don ta huta in ta gama karyawa ,har mumcy take Mata fad'an Akan ta daina Bari Rana Tana Mata Bata karya ba saboda ulcer ,sanayan tace to kawai bawai Dan ta gansu da bayanin mumcy ba ta koma sashin ta .
Da Rana ma su aunty sa'adiya da su Husna a wajen mumcy suka wuni Amman sanaya ko ta lek'o har FU'AD ya dawo da yamma duk Husna na tare da mumcy da su Aisha ,ganin Husna Bata da niyar haurawa ta Sami FU'AD ,sai aunty sa'adiya tace Mata ta tashi taje tamai sannu da zuwa Mana ta rubuta Mata a wayar ta ta turo Mata Tana cewa Kinga hoton d nake Miki magana Husna ,sai Husna ta karb'a ta karanta ta kalli aunty sa'adiya Tana murmushi alamun ta gamsu Kuma zata ,sai ko mumcy tace"ya kamata a canja Miki waya kema Asma'u Bari zamuyi magana da FU'AD d'in .
Sai Husna tashi Tana ce musu Tana zuwa sai ko mumcy tace "in FU'AD d'in ya huta kice Mai Ina neman shi ,da girmamawa Husna tace "to hajiya"ta haura saman bakinta d'auke da sallama ta Shiga ta same shi ya baje a kujera alamun hutawa yakeyi .
Ta Mai sannu da zuwa "ya amsa Babu yabo Babu fallasa ,ita Kuma ta d'auko Mai Ruwa Mai sanyi ta bashi ,ya karb'a Yana cikin Sha tace mumcy nason ganin ka Inka Gama hutawar .
Har Yana Shirin kwarewa yace me? Tace hajiya nason ganin ka ,yace me kikaje Kika ce mata ? Wani abun Kika Gaya Mata ya Mata kalon tuhuma ,itako tayi mirsisi ,ya taso kamar zai damk'eta yace ba magana nake Miki ba?taga da gaske yake sai ta seta hanyar fita Tana cewa in kasan ka firta wani Abu kazo da Shirin amsa tambaya in kasan baka shirya ba Kuma kazo hankalinka kwance ta fice ko jiran Abin da zece Mata batayi ba ta fice ta sauka k'asa wajen su mumcy .
Kwafa yayi kawai Yana mamakin rainin da take Shirin Shiga tsakanin shi da yarinyar Nan ,Bayan ya canja Kaya da zeje masallaci ya sauka k'asa yace ma mumcy ya wuce masallaci yaji kiranta Yana Nan dawowa cike da fargaban Abin da akaje akace ma mumcy Dan Yana zargin kamar Husna ta furta Mata wani abune .
Bayan ya dawo har ze haura sama dake mumcy Bata wajen sai Husna sai aunty sa'adiya Dan Haka yakeson gujema Kiran mumcy , sai Husna tace "ba dai ka manta Kiran mumcy ba? Yadda kowa zeji lokacin da yayi daidai da fitowar mumcy daga kitchen wajen su Harri ,sai ko FU'AD "yace oh na na manta uwa tagari gani ,Yana nufan inda take Yana hararar Husna da gargad'i Mai zafi akan Abin da tamai ,itako cikin ranta Tana Mai dariyar mugunta .
Koda mumcy tace muje ta nufi d'akin ta ,sai ya saddakar yana cewa yarinyar Nan badai ta sanar da mumcy Abin da mukayi jiya ba ,har suka Isa d'akin Yana tunani .
Bayan sun Shiga yaji mumcy namai magana Akan yabi sanaya ahankali ya bi komai sannu a hankali sanan ya Kama ya siyama Husna waya Mai kyau ta zamani kodan ta dinga gaisawa da mutan gidan su ,da yaji inda bayanan mumcy suka dosa sai yace to zeyi yadda take so Insha ALLAH,yaso Mata maga Akan Husna da labarin ta Amman ya kasa Kar ya b'allo ma kanshi Ruwa sai ya fasa suka d'anyi Hira da mumcy ya tashi ya fice ya tafi wajen Yaya Jameel don zasuyi magana Akan komawar shi Abuja shi kad'ai Dan aunty sa'adiya tace ba yanzu zata koma ba abarta a Nan yaje ya dawo weekend .
[4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA*
Chapter 39 · 0% Book details