← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 95

Sashe 54

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan tafiyar husna fad'a mumcy ta dinga yima FU'AD har da nasiha Tana nuna Mai Jan matan shi a jikin shi ta yadda inya samu zuriya dasu zasuji dadin shi ,shi ko FU'AD cream yayi a zuciya tab wai zuriya a Ina Kar kima Sarai mumcy Dan Banga lokacin ba yara daga muna mace sai Mai over wayewa da nuna Isa Ina Mata a Nan dama_dama muna macen ma ita husunan Kai ko itan ma Ina abun yake Kai can ta gane Banga yadda za'ayi ba da har zanyi tunanin samun yara daga gareta ko ita sanayan.
Sai da mumcy ta sake maimaita magana sanan ya dawo daga duniyar tunani da ya lula.
Bayan Husna ta dawo tace "aunty sa'adiya ta gama shiryawa hanun ta d'auke da mamy tanata Mata Wasa"
FU'AD ido ya zuba musu Karo na farko da yaji yanason yaro sai Husna da mamyn suka bashi sha'awa Amman ya fizge ,sai mumcy ce tace sakwarata Zo mu gaisa.
Sai husna ta mik'a Mata Tana cemata hajiyar mu sakwara fa kikace takwara dai ko kice namcyn ki kawai zamufi understand ,sai ko FU'AD ya juyo ya kalli Husna Yana tunanin dama tasan wani Abu daga cikin harufan turanci?
Sosai mumcy takema mamy Wasa itako tanata dariya dama Akwai fara'a musamman in taga Husna Dan ta saba da ita sosai.
FU'AD tun Yana basarwa akan birgewar da Husna da mamy suka Mai sai da takai yace kawo min me sunan uwa tagari mu gaisa ,har ta yunk'ura zata kawo Mai sai yace Bari ma nazo na d'auketa ,sai ya k'arasa yasa hannu ze d'aketa sai hanun su ya gauraya Dana Husna sai da wani kyakyawan sak'o ya samu matsuguni a illahirin jikin su ,ita dai Husna ta fassara shi da oho koma meye,shiko FU'AD fassara Yamai kala_kala Dan sai da Yama Husna wani kallo da shi kad'ai yasan ma'anar shi ,da yaga mumcy na kalon su sai yaji wani iri sai ya d'auki mamyn ya Fara Mata wasa Yana cemata dadyn ta ya kusa dawowa ,itako many Taki Mai dariya kamar tasan be Saba d'aukanta ba ,sai ya sake canja salon wasan nashi Yana ce mata yarinya me fiskar mamanta me kyawun babanta Dan sauran abubuwan duk namune ,mamy sai ta Fara keb'e Baki alamun kuka ,sai ya lakato Mata kumatu Yana cewa bazakimin dariya ba kodan Kinga bana samun lokacin renon ki ingaya Miki babanki tare da mumcy sukayi renina Nima naso yin renon ki Dan dai ba anan aka haife ki bane yanzu Kuma da kukazo Mana naso yin hakan Aiki NE baya bani dama ,bazakimin dariyar da Naga kinama su mumcy da aunty Nan Taki ba? Sai ki mamy ta rushe da kuka kamar wacce aka bigeta sai Fu'ad ya hau salati Yana cema Husna "ungo rik'eta jijigata Dan ALLAH kiji yarinya"

Husna na karbanta ta jijigata ta Fara Mata Wasa sai tayi shiru , mumcy nata mai dariya ,shiko cewa yake mumcy ko kyuya ta Fara?
Be Gama tambayar shi ba yaga ta Fara bangalama Husna dariya sai ya dawo kusa dasu Yana cewa laaa kuji yarinya Ni zakima Haka? Yana tab'a kumatunta ,sai ko mumcy tace "kaga banbancin salon wasan mace Dana namiji ko?
Kai duk a wasanka baka Kama hanyar da zata ma dariyar ba sai kanayi kamar labari kake Bata ,itako Husna tsokanar ta takeyi Tana sata nishad'i zauna kayi course indai kanaso ta Saba dakai nidai barinje nayi sallah walha inkayi biyaya Husna ta koyama yadda ake Reno kafin naku yazo.

Sai FU'AD ya harari Husna ,Bayan mumcy ta shige d'akinta sai Fu'ad yace ke ya kike Mata take dariya ? Ina magana kina sauraron mutum.
Sai Husna tace kunuwana fa abud'e suke ba atoshe ba ,sai Fu'ad yace "rashin kunyar Zaki min?
Ya dungureta Yana cewa ,Zo mamy na ,sai ko ta manne ajikin Husna, FU'AD yace Kai kuji sai kace itace mamanki, sai Husna tayi wani fari da Ido tace to Ni d'in da ba mamanta nake ba? Yatace halak malak aunty da Yaya sun bani ,sai ko FU'AD yace matsani Mara kunya kidai haifi naki wanan ta mutane ce sai Husna tace kaide ka haifo naka Ni ai Rai dai ,Kuma ko ayanzu an haifo min ,sai Fu'ad yace fitsarariya sai a haifan Miki Kam Dan ke Babu Abin da Zaki iya akace Miki yara iriki ne zasu iya haifan yara masu kyau Haka? Dallah bani Yar mutane ya kwakwumeta a jikin Husna Yana cewa nine babanki yarinya Zo kiji inkin girma Ni Zan d'auki dawainiyar ki ,Yana karbanta ta Fara kuka da sauri yace ma Husna Zo kimata Wasa Dan tayi shiru ,Husna na Fara Mata wasa tayi shiru har da dariya ,suna Haka sai ga aunty sa'adiya ta shigo hanun ta d'auke da hulan mamy ,sai tace inyeee iyayen mamy Ana Shan luv ne da Yar taku?
Sai a yanzu FU'AD ya lura yaga yadda sukayi daf da juna shida Husna har kayansu na gogan na juna sai kunya ta kama shi ,sai ya ajiye mamy a cinyan Husna batare da tayi aune ba Yana kamo hannun t Yana cewa rik'eta da kyau barin ma sanayan magana ta fito mu tafi.
Dariya aunty sa'adiya ta dinga Mai Dan ta gano shi .

Bayan sun taho dashi da sanaya tanata rangaji kamar iska na kad'a bishiya ,sai ta fashe su lokaci na farko da bakinta ya Fara gaishe su ,har d'aki ta Shiga ta ma mumcy sallama ,tare suka fito da mumcy Tana Mata fatan sauka lafiya Bayan ta cikata da tsaraba ,uwar iyayi harda cewa ta barshi sai da mumcy tace ai ba ita taba ba su mufeedan ta zata kaiwa ,sai ko sanaya tace hmm mufy ta kowa da kowa kenan ,sai aunty sa'adiya ta mayar Mata da martani ai halinta daban yake awaye take kowa natane ta iya mu'amala ,sai jikin sanaya yayi sanyi Amman taso mayarma da sa'adiya martani sai Fu'ad ya taho Yana cewa kufa nake jira Ina mota .

Sai sukama mumcy sallama ,har bakin mota mumcy ta rakasu suka fice daga harabar gidan.

Isar airport jirgin su ya kusa tashi ta musu sallama suka Mata fatan sauka lafiya sukayi bankwana ta shige ,shiko FU'AD ko nuna Mata wata irin kulawa irin ta miji da Mata be tsaya yi ba sai kawai cewa da yayi sai munyi waya ya wuce mota abinshi, su Husna sukabi Bayan shi Husna na gaba da mamy sai Wasa sukeyi aunty sa'adiya na baya.

Bayan isarsu gida duk wajen mumcy suka tsaya kafin lokacin tafiyan su biki yayi su koma Dan yauma zasu sake komawa.

FU'AD ko zuwa yayi yad'an kwanta ya k'ara hutawa kafin ya tashi.

Da yamma lis ya d'auki su mumcy bisa ga umarnin mumcy ya kaisu wajen biki.
Da dare yayi ma shi ya koma ya d'auki su ya dawo dasu gida.

Yau kwana biyu da tafiyar sanaya , FU'AD ya dawo d'akin Husna har zuwa dawowar sanaya ,sai Husna take cemai Dan ALLAH tanaso taje ta gaishe da mahaifinta Dan tayi kewar shi ya Mata Alfarma Dan ALLAH .
Sai yace toh zeyi tunani akai.
Shiru shiru har kwana biyu da maganar bece Mata komai ba sai ko ta sake tuna Mai "sai yace ya manta amman ze Mata magana ,Husna tace Dan ALLAH ya fad'a Mata a lokacin ta Matsu da son ganin shi ,ganin inya hanata be kyauta ba inya barta taje da Rana ma shima duk be lamunta ba sai yace ta shirya yau ze kaita amnan bazata wuce minti 30 ba inta yadda to in Bata yadda ba shikenan.
Husna tace ya zanyi samu yafi iyawa ,zani ,amman Dan ALLAH zanje ATM indan Ciro sak'on da aunty huwaila ta turo tace na bashi ,sai ko FU'AD yace Babu inda zata indai sak'on kud'ine ze Bata ta bashi Amman ita da k'ara zuwa bank ko ATM babu Rana indai agidan take Dan shi yasan darajar Aure .
Sai Husna tace to duk da bataso hakan ba.

Husna murna ta wuni tanayi ,har dare yayi dama FU'AD ya sanarma mumcy husnan ma ta Gaya Mata , mumcy taji dad'in hakan sosai.

Suna Isa baba na dawowa daga sallah sosai baba yaji dad'in ganin ma'un shi cikin farinciki abi da yake Mata fata kulin ,tun da tazo su mama habee da humaira aketa zumburar Baki haidar kuwa sai murna yakeyi sosai ma'un tamai tsaraba ko su humairan Bata barsu a baya ba sunsha nasu tsarabar da FU'AD ya Bata ta Basu .

Bayan ta musu sallama ,ta dunkulle wasu kud'i da FU'AD ya Bata ko kirgawa batayi ba tace gashi yayi Amfani dasu kodan bunkasa sana'ar awon shi ,sai ko baba ya bud'e Baki Yana mamakin yawan kud'in sai yace ma'uta Bata sana'a na turaki ba zaman Aure na kaiki ko rok'on su kikayi? Duk da nasan sunada arziki kija takaucin mu yadda ya Dace Kar kijawo Mana Gori kinji ?
Husna tace baba wlh Ina kiyaye duk umarnin da kamin Kuma Ina Nan a yadda nake ban canja ba daga ma'un ka ,kayi Amfani da kudin Nan hankalinka kwance aunty huwaila da FU'AD su suka bani Ni Kuma na baka Dan ALLAH baba Kar ka sake cewa komai in har ka yadda Dani.
Sai ki baba yace to shikenan ,muje na gaisa da FU'AD din kamar yadda kikace ai basai ya shigo ba .
FU'AD na hango futowar baba da Ma'u ya bud'e mota ya fito yazo ya d'an duk'a ya gaishe shi gaisuwa na girmamawa ,baba yanata shimai Albarka da Addu'a,Bayan sun Gama suka wuce shi da Husna baba nata sha'awar zaman nasu.

Mama habee kuwa bakin ciki kamar ta mutu inda takema humaira data ace Ma'u ce aciki? Aiko da sake anba me kaza Kai Sam Dole tasan abinyi kafin ta mutu da bakin ciki tunani ta farayi kafin wani lalausan murmushi ya bayanna a fuskarta Mai ma'anoni da yawa.
Chapter 54 · 0% Book details