← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 95

Sashe 92

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Kafin ta turo k'ofa batayi aune ba sai ganin FU'AD tayi kawai aciki ya harde hannayen shi biyu a k'irjin shi Yana kare Mata kallo.
Haushi Abin ya Bata sai kawai ta juya zata fita ya rikota Yana Shirin had'ata da k'irjin shi,kwacewa tayi Tana cewa" mekake Shirin yi?
FU'AD cewa yayi "zanji dumin baby na da ko hallita ba'agama Mai ba sanan ki nutsu ki fahimce Ni nasan fishi kikeyi Dani ko?
Batare da ta kalli inda yake ba tace "sai ka Bari inyazo duniya kaji dumin nashi inyaso ka had'a harda sanyin shi kaji ba dumi kawai ba,ka Gama kwance min zani a kasuwa yanzu mun dawo gida zakace zaka daura min bazan yadda da milkin Kama karya ba wallahi ayanzu ko ada na hakurane saboda wasu dalilai yanzu kuwa bazan iya d'auka ba gara nabar gidan naje inda ake nemana"
FU'AD d sauri yace "nine na kwance Miki zanin ? Kuma nine me miki mulkin kama karyan? Shin a Ina ake nemankin wane buk'atar ki ahalin yanzu da ya wuce Ni?
Batare da ta d'ago ta kalle shi ba tace"eh duk Kaine kake min ,Akwai mayaifinta ahalin yanzu d su aunty huwaila sunfi kowa buk'ata ta"
FU'AD d sauri ya tuno d hirar su d aunty sa'adiya sai yace "na sani Nima Ina tayaki murna da son Jin dumin ta da bakiyi ba shekaru masu tsayi Amman kibi komai ahankali ki nutsu ki fahimce Ni Zan tayaki yakin Nemo kuri'a da lashe zaben kaunarta gareki Wanda Kika Rasa a shekarun baya da suka shude Amman inaso ki bani Aron lokaci d nutsuwarki kiji da Abin da nazo Miki.
Kalaman FU'AD sun Fara karya lagon Husna sai ta kwad'aitu da son Jin manufar sa Amman duk da Haka Tana tunanin bazata yafe cin zarafin d ya Mata ba,sai tace inajinka ai kunne ne yake sauraro mezaka gayamin d ban sani ba?
FU'AD Rasa yadda zeyi yayi Dan yama Rasa ta inda ze Fara Amman sai yayi shahada kawai yace "husna ki cire komai aranki Yana Mai kamo hannun ta Yana murzawa ahankali Dan bayanan shi Sufi saurin ratsa zuciyar da illahirin jikinta,yaci gaba da cewa"ki manta duk wani Abu da ya faru abaya kawai mu fuskanci gaba.........be dire maganar shi ba Husna tace "kana nufin duk abubuwan Nan sun tafi abanza?
FU'AD sake kamo hannun ta yayi yaci gaba da cewa "haba ya kike maida gaba baya ne? Ko sai nace kiyi hak'uri haka kikeso? Toh kiyi hak'uri Akan abinda ya faru Dan ALLAH?
Husna d'agowa tayi tana kallon FU'AD Tana mamakin shine yau yake Bata hak'uri? Y kamata ta saurareshi taji Dame yazo zaman lafiya ko yafiyar abubuwan da ya aikata Mata a baya Dan Haka sosai ta maida nutsuwarta gareshi tace inajinka me kakeson sanar Dani Wanda ban sani ba?
Cikin kwarewa da salo FU'AD ya dinga bama Husna hakuri har ya Fara tuno Mata da abubuwan da suka faru baya Akan jarabawace wacce bazasu iya tsalake Mata ba Musamman shi da ya dinga Mata abubuwa Wanda faduwar su yanzu bata lokaci ne Abin da gaba zata haifar kawai ya kamata su fuskanta wato kula da Abin da yake tare da ita nadaga jinin shi.
Husna Baki sake take cewa "kana nufin ka aminta d Auren mumcy ? Ka janye daga jingina shi da mumcy da kakeyi?
*FU'AD da sauri yace eh Auren shine bana mumcy ba Kuma wallahi zata sameshi me Bata kulawa da tatalin da babu wani miji da ya tab'a mafarkin bama matarshi bare a farke kawai ta tayashi kula da cikin dake jikinta Dan ALLAH!
Husna farinciki ya lulubeta Tama Rasa me zatayi murna ko mamaki yau ga FU'AD Yana Mata magiya Yana rokonta yafiya Akan Abin da ya gabata ya Kuma shirya zaman Aure da ita matsayin matar shi d ya aminta da ita? Yau tafi kowa farinciki aduniya Amman bazata tabbatar da hakan ba sai tagani a zahiri da aikace sanan zata gaskata zancen shi da nadamar shi.

Washe gari su Affan, sadeeq , muhibbat,Husna suka kawoma Husna ziyara sosai mumcy tasa aka shirya musu lafiyayen girki na saukar Baki masu mahimmanci a saman husna aka baje musu kolin abincin FU'AD Yana Nan sukazo yakan saki jiki da sadeeq Amman har yanzu Akwai takun saka tsakanin shi da Affan duk yadda yaso ya goge Abin ya nuna Mai babu komai aranshi Amman ya kasa sai ma ji da yakeyi yanzu ya Fara kishi da duk Wanda ze ketare Mai ta gona.
Husna sunsha Hira sosai da Yan uwanta kamar bazasu rabu ba daga baya su Affan d sadeeq suka tafi suka bar su muhibbat zuwa dare FU'AD yace ze maida dasu ko yasa amayar dasu sosai hakan ya faranta ran Husna Dan wata sabuwar walwalace da Jin Dadi suka sake mamaye ran huana.

Humaira dai yadda Alhajin birni ya zugaga Mata labari harda cewa gidanta daban Tana zuba Ido a jibgeta a hadaden gida Mai yalwa da kayatuwa sai taga an direta a family house Bata sake dorar wa ba sai da aka ajiyeta aka Shiga k'aton gidan kafin ta Fara cewa wani Abu sai taga anyi wani waje da ita wajen yafi na kowa tsaruwa a gidan sai wata tafara cewa ba Nan bane ciki zakuyi da ita daga cikin matan gidan,sai dayar wata Mai tsiwa ta Fara cewa a ki Bari ta lasa kamar yadda aka Saba Mana canne sashinta ku direta acan sannun ku da k'ok'ari kudai d kirsa d makircin matar aka dire humaira a sashin komai Akwai tunanin da yake zuwama kowa arai shine Nan fa yafi kama da sashin megidan Amman Babu Wanda ya firta.
Bayan an dire humaira dama taron kwado da hamane suka kawota ba Wanda yayi tunanin kaita wajen iyayen gidanta Dan abada amanarta Dan Haka Nan sukazo aka gagaisa ,Bayan ansaukesu d kaji da lemuka Basu Gama ci ba aka Fara cewa su fito Dan ajuya dasu Aiko wasu suka dinga guziri suna diba suna fita da sauri Dan Akwai tazara tsakanin gidan su mama habee d gidan humaira Dan sabuwar unguwace gashi ance har yanke Kan mutane anayi indare yayi Dan Haka kowace hantar cikinta ta Gama kadawa kowa ya watse akabar Amarya ba kowane ma ya samu zarafin Mata sallama ba.
Itama Daman babu Wanda take buk'atar gani sama da Alhajinta Dan yace kyautar ta ta farko motace adaren ze mallaka Mata Kuma Dan Haka ta daukaki Daren.
Babu jimawa Alhaji ya shigo d ledar shi yanata baza hanci kamar gajeren wando yanata fadin Rai ,yaso nuna Mata mazauninta tun adaren Amman dokin kwasan amarci da zeyi yasa y kasa sai yace Bari ya Bari sai gobe Dan Haka dama Akwai karancin sani sallah d ake gabatarwa ma shi ya yafeta Dan Haka ya cillo Mata ledar kazarta su humaira kamar jira ake ta hauta da yaga tanaci Tana korawa da drink shiko goga yana gefe Yana jiran mayinwaciyar kaza ,Tana ganawa kuwa ya ajiye babbar rigarshi y umarceta da takaimai d'aki Tana Shiga yabi sawunta.
Bayan wasu mintoci kamar 40 sai tashin Zaki da cin mutunci tsakanin ango da Amarya Yana ALLAH y Isa ancuce shi yayi asarar kudinshi ya banzatar dasu abanza wallahi bazata Sabu ba Dan Haka adaren zata barmai d'aki kafin washe gari ta koma gidan me dattin hula da dankwalinta.
Humaira kuka ta saki Tana bashi hak'uri Tana ya rufa Mata asiri ya Mata aikin gafara ya tuna da kauna ya barta ko zuwa wani lokaci kokai ze dedeta wallahi batasan ya akayi Haka ta kasance ba.
Alhaji masifa y Shiga surfa Mata Yana wlh zati 1 kacan ze Bata shima Dan Baki su Gama komawa ne Amman Dole ta koma gida Dan besan asara y d'auka ba,humaira magiya d kuka harda majina Tana bashi hak'uri d kyar y hak'ura Amman da Al'k'awarin gobe d asuba zata barmai sashin shi t karasa kwana 6 da suka rage Mata acan.
Chapter 92 · 0% Book details