← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 95

Sashe 8

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna cikin Haka suka jiyo sallamar FU'AD ya shigo ,da fara'a ya shigo ya nufo inda mahaifiyar shi take ,Amman ganin Tana tab'a hannun Ma'u Tana Mata sannu sai y rage fara'a ...

Momcy ta dubeshi tace son andawo? Yace na dawo uwa tagari batare d y sake kalon inda suke ba ,yace abinci nake buk'ata momcy dafatan ya kammala ?

Y na Shirin zuwa inda aka tanada Dan can abinci , momcy tace eh Bari a taimakama da su plates d spoons,yace harmu nawane zamuci d naji kina jam'u momcy ...

Momcy tace ba sai ka zuba iya naka kabar sauran ba?

FU'AD yace "toh" momcy ta ,Amman Kar ki turo min wanan abun ta gabanki Dan Tana zuwa na hak'ura da abincin ...

Momcy ta Galla Mai wata uwar harara ,tace dallah ita hannun Tama ciwo yakeyi Bata da lokacin taimakama da Kai wani ne da ka taimaka musu suje adubata ...

FU'AD yayi saurin cewa "what"? Tab Ashe baza'a dubata ba momcy wanan abun? Momcy ta Harare shi tace "waye abun? Asma'u?

"Yace eh Mana momcy"

Momcy tace Kar na k'arajin kace Mata wanan abun acikin gidan Nan ,kaji menace?

FU'AD ya dago yasan Babu Wasa atare da momcy, yace "Amman Zan iya fad'a a wajen gidan Nan ,acikin gidan na bar fad'a sai a waje"

Momcy tace son kashiga hankalin kafa wlh ,umarni nake baka matukar na Isa a ko'ina karka k'ara kiranta da wanan abun kwata kwata na Hana ,kaji me nace?

FU'AD har mamaki Abin ya bashi sai d Yama momcy wani kallo na Anya momcy Baki rage Sona da k'aunata ba kuwa? Sanan y amsa d angama uwa ta gari ,Nima Kuma ta dinga kiyaye dokokina a gidan Nan ta Dena zuwa Inda abincina da Shana yake ...

Momcy tace kana nufin har gyaran saman ka ta Dena yimaka?

FU'AD yace aa wanan shine Aikin ta ma ai ,tafi dacewa d wankin _bathroom_ ta d'ora daga inda ta tsaya ,meye amfanin ta?

Momcy tace hmmmmm ,aikin kawai d sai kadin gayi da kanka ai Ashe tanada Rana ...

Momcy Bata k'ara sauraran FU'AD ba tace Harri kuje kinji duk abinda na Gaya Miki direba ya kaiku , ALLAH ya sawake Asma'u kinji kin d'auki ledar da nace ki d'auka? Ma'u ta girgiza Kai Alamar a'a sai momcy tace "Hari d'aukan Mata ki rik'e Mata , Harri ta amsa da to hajiya suka nufi kitchen Ma'u ta gama shiryawa ta cire birmemen hijab tasa karamin da taimakon Harri sanan suka dawo sukama momcy godiya da sallama suka fita ..

FU'AD Baki ya tab'e Yana cewa waya Bata aron Kaya ? _dirty girl_ kamar Ma'u ,Yana cin abinci yanajin haushin ma'u Akan yadda momcy take Mai a kanta Abin d ko a mafarki momcy Bata Mai fad'a Haka iya tsahon zaman su da mahaifiyar shi ,Dan gaka babu shi babu Ma'u ,shifa dole momcy ta gane jinin sune kawai be had'u ba .

Bayan Harri sun Isa wajen Mai gyara ,kafin Nan hanun Yama Ma'u tsami har kwalla tayi da ake gyarawa Ashe ta d'an samu matsala a hannun ,Bayan an Gama ta share hawayenta yasa Mata magani ,Harri ta rakata har gida da ledar ta har suka gaisa da baban ma'un ,Jin ma'un taji ciwo Abin har cikin ran baban ya dinga Mata sannu ,harrin ta k'ara jinjina so da k'auna irin na d'a da mahaifi ,sanan ta musu sallama tama ma'un ALLAH ya k'ara sauki sanan ta koma gidan momcy ..

Ma'u da d'aya hannun ta fito da su abincin da kayan cincin d'in d momcy ta cika Mata leda dasu taba babanta tace yaci ,yace" ta Fara ci ,tamai k'aryar ai ita taci kad'an zata k'ara ,sanan ya karb'a ya Fara tmby garin Yaya taji ciwo ,ta sake labarta Mai yadda ta tsara ba ainahin Abin da ya faru ba ....baba y Mata sannu yace taje ta huta ,tace "toh ta tafi da sauran Abin dake cikin ledar ta nufi tsohon d'akin d take kwantar d hak'ark'arinta ...

Bayan ta d'iban ma mama habee Abin d tazo dashi ta tafi Kai Mata ,koda tayi sallama ta Shiga ta Bata ,sai tabe Baki mama habeen tayi tace batacin Abin d Bata da tabas akanshi ,ko satowa akayi ko me akayi aka samu Bata sani ba ,Abin Yama Ma'u ciwo Amman inda sabo ta Saba ,ta mik'e zata tafi haidar ya shigo d gudu Yana cewa Yaya Ma'u Ashe ciwo kikaji? Wayoo ALLAH sannu Yaya Ma'u ,mama habee tace agarin satar ne inajin aka kwad'eta wata ranama ajalinki Zaki sato indai Baki canja Hali ba ....

Haidar yace ,wlh Yaya Ma'u Bata sata Yana turo Baki ,Aiko mama habee ta makomai duka d Kofi ya kauce k'iris ta fama ma Ma'u ciwon ta ,tayi saurin barin d'akin kafin ta mayar Mata d Abu sabo ...

Bayan Ma'u ta koma d'akinta ,kwanciya tayi Akan yaloluwar katifar ta ,Tana ta tunani da Jin rad'ad'in Abin d FU'AD ya Mata ,gashi ko abincin kirki ta kasa CI , gashi yanzu ya barta da ciwo Mai tab'a zuciya Dan har ranta take Jin ciwon harfa kuka tayi ......

Haidar ne yazo y katse Mata tunani d cewa ,Yaya Ma'u humaira tace kibani abinda Kika ba mama habee Taki karb'a ,Amman tace Kar bace ita ta turo Ni wlh sai d ta murd'emin kunne ,karki Gaya Mata kinji Yaya Ma'u ? Ma'u ta saki murmushin dole tace "kuda wajen kwad'ayi za'a mutu" ta dib'o ta bashi tace shima yaci da yawa fa ,ya tafi Yana murna Yana cewa kad'an Zan Bata ,Ma'u tayi murmushi ta koma tunanin ta ..

Cikin ranta Tana cewa Anya zata sake komawa gidan su FU'AD kuwa ,yaufa d yazo d tsautsayi d y kashe ta ,Kuma Taji ciwo ta dalilin abinda y mata Amman Yana sake binta da sharri , gaskia y Kanata tabarmai gidan su ....

Washe gari Ma'u Bata samu Taya mama have aikin gidan ba ,Aiko ta dinga sababi harda cewa Dan kartayi Aiki yasa taji ciwon ,yanzu haka ma ciwon karya ne, sai d baba ya ma mama habee da gaske sanan ta saurara kad'an ,Amman duk d haka mama habee sai d tace Bari nagani ko zataje aikin boyi boyin d ta Saba shine ze tabatar d k'aryar ciwon , bud'ar bakin Ma'u tace wlh babu inda zani Ina gida har gobe har jibi har ......d sauri baba y dakatar d Ma'u da cewa sbd Ma'u ta?

Ma'u tace wlh baba hanun namin ciwo Kuma kaga Aiki zanjeyi Kuma karfin aikin da hannu ne ,Kuma kaga yadda hanun ya zama .

Sanan baba yace eh ba fahimce ki ,sannu kinji ALLAH y k'ara sauki d lpy.

Ma'u tace Ameen baba ,ngd.....

Mama habee d humaira sukace uhummmmm munafurcin dodo dai ,sai d baba y harari humaira sanan ta shiga hankalin ta tayi shiru ,itako rasa'u Bata fasa jifan Ma'u da miyagun kalamai ba .

Maman Shaheed ce👌🏻
[4/23, 4:00 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA*

_RUBUTAWA DA TSARAWA_
BY
*Fatima Abubakar Shu'aib*
(Maman shaheed)

_shafi na 10_

*FU'AD kaga ta Kanka da makaranta ,ku fahimce shi Mana jinin sune kawai bai had'u ba da ma'u*👌🏻👌🏻🤷🏼‍♀

Gari har ya K'ara wayewa Rana ta fito Ma'u babu niya bare haramar tafiya gidan momcy ,Kuma tanata fama d Shan bak'ar magana daga mama habee Abin karayar ta na safe ma a wulak'ance aka Bata shi ,dama Bata Gama cinye Abin cin da momcy ta jido Mata ba ,Dan Haka Babu d'umame ta Kama cin abincin ta Dan jiya dama zafin abinda FU'AD da Rad'ad'in ciwon ne yasa Taki cin abincin,yau ko yunwa ta sa ta kama ci haidar na tayata .....

Momcy ganin lokacin zuwan ma'un ya wuce, yasa ta Fara tunanin ALLAH yasa lpy tajita shiru ko Kuma hannun ne y hanata zuwa ? Tun Tana mgn da zuciyar ta har sai d ta fito fili ta farayi da ma'aikatan duk sukace ALLAH dai yasa lpy ,momcy tace "Ameen"

Bayan wasu Awanni matar big bro ta shigo ta gaishe da momcy ,momcy cikin kulawa da yabawa ta amsa shima big bro d'in ya gaishe ta ,Bayan sun gaisa yake tmby FU'AD ! Momcy tace Yana sama Yana baccin lalaci dake yau Asabar CE Babu Aiki ,da azama yayan nashi y haura sama y same shi yanata bacci hankali kwance , bubuga bayanshi yayi ,FU'AD ya d'an bud'e ido tozali da yayan shi da yayi ya saki wani murmushi Mai k'ayatarwa yace " morning big bro" big bro d'in yace "morning junior " hw was ur night? Yace fine big Yaya ,Ashe har kun tashi ? Ina aunty tawa na kwashi gaisuwa kafin n Kuma Mata laifi ,Dan tace ranar d kuka diro k'asar Nan na Fara Mata laifi ,yayan yayi murmushi y d'an daki kafad'un shi yace Tana k'asa tare d surikar ta ,nasan ko break bakayi ba so ka tashi ka gyara kazo kayi break ji room d'inka ma gyara yake buk'ata Yana k'arema ko Ina kallo .

FU'AD y yatsine fuska yace eh _dirty girl_ d'inan d momcy ta rakibo zatazo ta gyara Dan amfanin ta kenan ,yayan nashi yace wa kenan? FU'AD yace wata me Kama da mayya ko Ma'u ko me'u sunan ta oho naji momcy dai na cemata ko Asama ohon Ni dai ,yayan nashi yayi dariya yace K'anina ka fa canza daga yadda na barka na Kuma Sanka _why_? FU'AD yace kaima ka Fara yadda d mgn momcy wlh Ina Nan kamar yadda nake kawai fahimta fuskane bansan meyasa momcy takemin lak'abi da canja Hali ba ,Ni har mamaki nakeyi , yayan nashi yace ko ma dai meye Zan gani Nima kafin muje Abuja Dan Akwai wani aki da zamuje muyi na 6months da Zan bar madam anan ita da surikarta Amman tace gwanda mu tafi tare ,so nake muyi shawara d momcy Abin da tace shi za'ayi ....
Chapter 8 · 0% Book details