← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 95

Sashe 43

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*********
Mama habee labarin gidan Ma'u da had'uwar sa da matsayin Wanda ta aura ya Zo Mata daga majiya Mai tushe duk hankalinta ya Gama tashi ta gama tsurewa Dan aduniya Tana son alak'a da Mai shi a matsayinta na marashi Dan ta Gama tunani da zataye dangin ta tace duk matsiyata ne Dan Haka ita da arziki sai dai su samu abokanen arziki a duniya Dan Haka burinta kullin ya za'ayi taci Karo da Mai arziki ya zama gatanta ya zame Mata jini da tsoka ,sai ga shi yanzu ta Sami labari da sanin asali na dangi da mahaifan Wanda Ma'u wacce tafi tsana a duniya yazo Mata ta tabbatar Kuma Dan Haka suka kullar suka shirya fito na fito da farin ciki da daular da Ma'u take ciki burin su yanzu ya za'ayi su datse ta ?
Mama habee tace ko zata yi yawo tsirara sai ta datse ma Ma'u da babanta farin cikin da suke ciki Dan Haka ya tabbatar Mata da kin nuna damuwar baban Ma'u Akan Auren Ashe yasan inda ya kaita shiyisa hankali shi ya kwanta .

Harri taga alamun Akwai Abin da ya faru ko yake son faruwa Dan ta jiyo magana da FU'AD yakeyi da mumcy duk da ba wani Abu taji ba Amman tasan tabbasa maganar nada alak'a da tambayar da FU'AD ya Mata Akan ma'un Dan Haka da hanzari ta tafi jikinta na rawa ta sanarma ma'un duk yadda sukayi da FU'AD har dabarar da barazanar da ya Mata Bata b'oye Mata komai ba ,Tana nuna rashin Jin dad'in Abin da ze farun ,jikinta duk yayi sanyi tanata ba Ma'u hak'uri Tana cewa karta zama silar faruwar wani Abu cikin Auren su .....sai ma'un ce tace babu komai ta kwantar da hankalin ta tayi tafiyar ta kawai , ma'un Bata nuna ta firgita da al'amarin ba sai Bayan harrin ta tafi sosai ta tsorata Tana sauraron Abin da kunuwanta zasuji.

Maman shaheed dinku na godiya da comments
[4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA*

```RUBTAWA DA TSARAWA```
BY
*FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB*
( Maman shaheed)

💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥

Pg36

Mama habee da humaira sosai suke shiri akan zuwa gidan Ma'u Dan ganin ra'ayil ayn Akan Abin da sukeji na wai wai ,suna son zuwa humaira na tsoro ,sai da mama habee ta zazage ta tayi Mata tas tukunna humaira ta Fara tunanin zuwa ganin irin gidan da Ma'u take ciki.

Ma'u dai jikin ta sai rawa yake gashi tanata k'ok'arin ta aro dakiya da rashin tsoro ko shayi ta dasa ma zuciyar ta ko ta iya fuskantar FU'AD da barazana ko hargitsin da yake Shirin tinkarota Dan tasan tabas Yana Nan gabato ta.

FU'AD ko sai da yaje part d'in sanaya ya shige d'akin shi batare da yace Mata komai ba Amman ran Nan nashi adagule ,ko da sanaya ta ganshi sai cewa tayi can da yawar ka inkaso ma ka fashe muga karshen kumbiri can da yawar ka.

FU'AD ko ya dawo part d'in sanaya ne ko ze samu sukuni yadda yakeji cikin ranshi Dan yadda ranshi ya dugunzuma ji yake ze iya aikata komai ,Amman duk da hakan sai yaji kamar ran nashi ma Kara baci yakeyi Dan Haka ya fusata ya bar d'akin ya nufi inda Husna take Yana tafiya Yana fitar da hucin d'acin Rai har ya Isa k'ofar falon ko sallama be samu damar yi ba har sai da ya tabbatar Yana cikin falon Aiko ranan a bacce yake furta ke _dirty girl_ zonan ,yaji shiru Bata fito ba da alamu Kuma Tana d'akinta ne ,Husna ko da Tana falo tanajin motsin k'ofa ta rufta d'akinta da sauri sauri ,Jin Yana kiranta da sunan da tafi tsana har kusan so 3 sai ta fito gwiwa a salub'e batace Mai komai ba Tana Shirin zama a kujera.

Gigitaciyar tsawar da FU'AD ya Mata ne ta dakatar da ita daga zama a kujerar da take Shirin yi ,Yana cewa ke wai har dake za'a yaudare Ni? Arasa Abin auramin sai ke a matsayin huce takaici ? Basusan yin hakan daidai yake da ilata rayuwata ba? Ke Kuma Kika amince?
"Husna ta girgiza Kai alamun aa"
"FU'AD yace to ke kikace kina son aurena Amman tun da haka kawai ba'a k'ak'abamin ke ba wait matsayin Mata wacce zanyi Rayuwar Aure da ita ,tir da wanan had'i wallahi ,ke inaso yanzunan ba anjima ba kije kicema mumcy wallah ajanye wanan tarayyar Taki Dani Sam bamu Dace ba Kuma wallahi ya matso ya kamo kunnen ta Yana cewa ba shawartan ki nake ba umarni na Baki yarinya ,sanan ya sake Mata kunne ,tayi hanyar Shiga d'akin ta d sauri ya damk'ota Yana cewa gidan wa Zaki ? Bakiji karatun da na biya Miki bane?
"Tayi yunk'urin kwacewa daga rik'on da yayi Mata Amman Ina komai na babba yafi na yaro ta kasa ,sai cewa tayi eh to ka sakemin hannu naje na idar da sak'on ka Kuma yadda ka biyamin Haka Zan boyama Wanda kakeso sak'on ya Isa garesu ,Kuma Ni d'in akace ma na tab'a mafarki ko tunanin zama matar mugun mutum Wanda besan hakin Dan Adam ba kamar ka? Ko tinani ko sha'awa bantab'a d'aya daga cikin su ba ,Ni in kanaso ka birgeni muje ka maimaita kalaman ka a gaban hajiya inkamin Haka ka Gama min komai sarki zalimu kawai ta murgud'a Mai Baki .......Aiko FU'AD ya saki hannun ta ya kamo bakin zai murd'e ta zille ya sake cakumo ta Yana laluben bakin har hannun shi yayi karambanin zuwa inda be shirya ko tab'a zuwa ba a Rayuwar sa da sauri ta bige hannun Tana cemai Allah ya isana mugu kawai sarkin cin zali kawai ,shiko da sauri ya d'auke hanun shi ya mayar Kan bakinta ya matse Yana cewa Mara kunyar banza me zanyi dake Baki isheni sakace ba bare k'oshi wata kazama dake fitsarariya kawai ke har kina sa kanki sahun Mata ?
Ta kwace bakinta daga rik'on da yayi Mai ,tace ai Ni har nafi wasu matan da kake ganin su cikakun matan lokaci shi ze tabatar ma Kuma wallahi in baka Dena kirana da kazama ba bazan Dena kiranka na mage ba mamugunci kawai muryar ta na rawa Dan k'arfin Halin mayar Mai da martani kawai takeyi ,Dan ta Sha matsa a wajen shi ,Aiko FU'AD ya sake had'ata da jikin shi ya matse ta Yana cewa bazaki bar min rashin kunya ba ko yarinya wallahi da rabon asibiti suyi bak'i Dan wallahi inna Miki wani abun sai dai asibiti inda rabo su ceto ki.

Husna tace ohooo kafin ka kaini Ni na Fara kaika ai ,sai ko FU'AD ya kamo bakin ya k'ara murd'ewa Karo na 3 yace me kike nufi uwar fitsararu ? Yimin bayani ko ki kwashi kashin ki a hannu yanzu ,sai ko tace ohooo Ni ka sakeni Tana k'ok'arin waskewa Kar yasan ita tayi sanadin zuwanshi asibiti da gasken kamar yadda sub'utar Baki ya kaita furtawa batayi tunanin Abin da zaije yazo ba ,ganin da gaske yake son Jin Abin da take nufi da bayanan ta sai ko taga sai ta Fara had'awa da kirsa a tsakanin ta da FU'AD Dan Haka da ya k'ara matse Mata Baki ta Fara Shirin kuka muryar ta ta raunana Tana fitar da sautin azabtuwa daga cutarwar FU'AD d'in.

FU'AD cigaba yayi da Mata tambaya Yana sake matseta da bango sai kawai ta Fara kuka Tana cewa ,mugu ka sakeni muje wajen hajiya na fad'a Mata sak'on ka Nima na gaji da muguntar ka mugu kawai ,tanata yunk'urin kwacewa daga rik'on da yayi Mata Aiko sai FU'AD ya tsaya cak Yana cema to tayi sauri ta kwace in zata iya ,yin duniya Husna ta kasa kwacewa daga rik'on FU'AD,sai ko FU'AD yace kin Gama sai ya saketa Dan kanshi da gudu ta zuba zata sauka kasa Tana Shirin cewa wani Abu yayi saurin shak'ota yace wallahi idan kikaje Kika maimaita Abin da nace a wajen mumcy ba tare da kince ke Kika ga dacewar hakan ba wallahi sai kin fuskanci Abin da yafi na yanzu in kin Musa kije ki fad'a ,ya tureta har ta kusa fad'uwa.
Sai da taga takai bakin k'ofan fita tace sarki zalimu kawai Kuma sai na fad'a inyaso ka kasheni abirne gawata mugu ,tsoratata yayi kamar ze biyota da gudu ta sauka Tana haki ALLAH yasa babu Kowa a falon ,sai d ta zauna ta huta ta goge fuskarta numfashinta ya dawo kafin ta nufi kitchen ta Sami su Harri ta Fara tayasu Aiki suna hanata Tana cewa babu komai ai d'aya suke zuciyarta fal tunanin yadda zata kaya tsakanin ta da FU'AD gashi yau a d'akinta yake har mumcy ta shigo ta same su taga Asma'u tsamotsamo a cikin su tanata Aiki mumcy ta musu sannu ta Kira Asma'u zuwa falo.

Sun jima suna Hira tsakanin mumcy da Asma'u , mumcy nata tausan zuciyar Asma'u akan FU'AD Tana rok'on ta da tayi hak'uri dashi na wani gajeren lokaci sanan babu hallacin d zata Mata kamar na rufe sirinta ko tsakanin ta da FU'AD shine iya sakayyar da zata Mata a rayuwa batan ta biyata Alkhairin da tamata arayuwa ba ,sosai maganganun mumcy suka ratsa zuciyar Husna ta Mata Al'k'awarin insha ALLAH zatayi iya Abin da zata iya ,so 2 FU'AD na niyar sakowa daga sama sai ya koma a tunanin shi ko Husna na gayama mumcy Abin da takeson sanar Mata ne daga baya dayaga Abin yaki ci yaki cinyewa kamar cin Kwan makauniya sai ya fito da k'arfin gwiwar komai ma ya faru Dan ya shirya b'ata ran kowa akan Husna ayanzu ba sanaya bace matsalar shi Husna ce damuwar shi Dan itace abar fafatawar shi Dan sanaya baya sata a lissafi ayanzu.
Chapter 43 · 0% Book details