← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 95

Sashe 69

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai Abba yace "toh ai sunso Ayi sulhu kikaki Basu fuska ta hanyar cewa bakisan inda take ba,Kika barsu haka"

Sai huwaila tace "wanan ai be wadatar ba Kuma ba wani neman kirki suka Mata ba da zasuso su gayamin Bata tayi ko Abin da ya faru ka fahimci zance na fa Abban su Affan"

Sai yace da gaskiyar ki Kuma Dan wanan Amman dai nasan zasu sake nemanki in Hali yayi Dan ALLAH karki wahalar da shari'a ki Basu ita ko yanzu nasan suna kewarta.

"To "kawai tace mai.

************
Sosai baban Ma'u yake ma su mama habee tijara duk sun zabura hankalin su atashe Musamman humaira da yasa ta fitar da miji da gagawa ko yayi kyautan ta, mama habee cewa tayi be Isa ba wallahi ,shiko yace zega Wanda ya Isa a gidan.

Mumcy da FU'AD hankalin su ko da yaushe nakan Husna ga komawar su india saura kwana 3 ita da FU'AD d'in kawai zasu koma Dan Yaya Jameel zasu je Abuja su d'an kwana biyu sai wata k'anwar mumcy da aurenta ya mutu tazo zata zauna agidan."

FU'AD ya kasa b'oye maganar husna har su B2k ya fad'ama , B2k ya dinga Mai dariya kafin yace komai,har FU'AD ya hassala yace "bana son iskanci fa Ina gayama Abu kamar na kawo ma wani Abin dariya ,matsalaka kenan na manta d'an adawa nake gayama ,har ya tashi ze bar office d'in sai B2k ya tashi ya kamo shi Yana cewa yi hak'uri abokina am so sorry ,I don't mean to hurt u,banji dad'in faruwar lamarin ba Amman ga shawara....

Sai FU'AD ya dawo ya zauna Yana cewa tame? Sai B2k yace Kun dubata ko Ina duk wani me alak'a da ita Kai har k'awa ma?

Sai FU'AD yace "duk anje duk da Bata da wasu 'yan uwa Kuna kawarta d'ayace Kuma munje babu wani labar har wajen wata aunty ta aka tambaya Amman tace bata ma da labarin ta kwana biyu ,bama tasan nemanta ake ba dake gaskiya badani sukayi wayar ba da mumcy sukayi."

Sai B2k yace "Ina ganin da Kun Mata bayani sosai Dan aji ko tanada shawara ko mafita,Amman ko anan ma ku tsanaita bincike batanta da ban mamaki Kuma ku ci gaba da tsorata marikiyar ta ko tanada Abin cewa ,Amman inama jaje gashi Naga kamar ka fad'a gaba d'ayan ka......sai Fu'ad ya Harare shi Yana cemai Ina na fad'a zaka Fara ko?

Sai B2k yace "wallahi love kanaso ko baka so ,shawara dai kawai kaci gaba da kishinta kamar yadda kakeyi dinan Dan Ni ganau ne ,sanan ka nuna Mata so na hak'ika in Kun had'u Dan kun mugun dacewa ba Zan maka Dole wajen gyara kuuren ka ba har sai in ka zauna Kama kanka karatun ta nutsu da kanka tunda kace zab'in mumcy ce."

Sosai Abin da B2k ya fad'ama FU'AD ya Shiga kanshi Amman Ina be yadda da kalaman ba saboda zuciyar shi ta karyata hakan in gangar jikin shi ta amsa,har suka rabu Yana dogon nazari.....

**********
Washe gari Affan ma be Bari suka had'u da Husna ba duk ya kasa gane ma kanshi da ak'ar shi da ita ,shin tsanar ta zeyi ko d'aukanta matsayin k'anwa, ko ya fita harkarta kwata_kwata? Be Gama shawara ba Dan Haka yake wasan b'uya da ita.

Husna ta so fahimtar kamar Akwai wata ak'asa Amman ganin ba'a sanar da ita ba Kuma batasan ko meye ba sai ta bar komai Amman ranta fal da tunanin su FU'AD.

Sosai ammyn su Affan ta kula da d'auke wutar da FU'AD Yama Husna Dan Haka ta sake kiranshi tamai nasiha da nuna kulawa Akan damuwar shi da janshi ajiki da nuna Mai soyayya ta d'a da mahaifiya har take cemai mayar da Husna 'yar uwa agareshi kamar su muhibbat shine ze tabbatar Mata da ta Isa dashi Kuma ze iya Mata biyayya ko Bayan ranta,sosai Affan ya Bata hak'uri ya nuna Mata ze gyara Kuma ya hak'ura ya barma ALLAH komai daga yau Husna Bata da wani da ya wuce shi har ya rok'i ammin shi da Kar ta sanar Mata da Abin da ya faru Dan dama be tab'a Gaya Mata ba abar Abin a Haka kawai ,tamai Al'k'awarin bazata sanar Mata ba ta sama Rayuwar shi Albarka.

Komai ya koma normal tsakanin shi da Husna sosai yake Mata lesun tare da nuna Mata shi yayan tane k'ofa a bud'e take Akan duk wani damuwarta ko matsalar ta tagaya Mai sai inda k'arfin shi ya k'are,sanan ya dinga siyo Mata Kaya na kyale_ kyale gashi kusan kullin sai ya fita dasu Yana nuna Mata wajaje na wayayun mutane sosai Kan Husna ya k'ara bud'ewa ta waye dressing babu Wanda batayi daga name na hausa har na larabawa zuwa Kan turawa har indiyawa da take ganin su yanzu sari babu Wanda Bata sawa cikin lokaci k'an'kani ta k'aru da abubuwa sosai komai ta iya ci duk inda zaka ganta da su muhibbat zaka ganta hankalin ta a kwance ta k'ara cikowa komai nata yayi bul_bul tayi haske har wani shek'i takeyi gashi kowanne dressing tayi sai ya Dace da ita babu gatan da Bata samu Kama daga Aunty huwaila abban su Affan ,sadeeq Dan Haka takejin kamar tafi kowa gata a yanzu take k'arama ALLAH godiya Kan ni'imomin da ya Mata ,lokaci zuwa lokaci Tana Kiran maman hafeeza tana sawa wani k'anin su Yana dubo Mata baba da lafiyar shi Dan Haka takejin hankalinta na k'ara kwanciya.

*********
Yaune tafiyar su FU'AD bakuwar da zata zauna musu da a tun daren jiya ta is mumcy ta gama karanta Mata komai da nuna Mata ma'aikatan gidan itama ta gabatar musu da ita amatsayinta na kanwarta aunty karama suke ce Mata Amman sunan ta haule,sosai aka dinga musu fatan sauka lafiya ma'aikatan gidan,Yaya Jameel da sa'adiya ne suka rakasu har Airport dake su sai gobe zasu dawo,agoben Kuma sanaya zata duro itama......

Su FU'AD sun tashi lafiya har sun sauka lafiya cikin Aminci ALLAH.

Basu je asibitin ba sai washe gari wai in sun huta.

Washe gari kuwa da wuri sukaje sukaga likita,Bayan sun Gama ganin likitane ya duduba shi yaga jikin da sauki sai alamun tunani ko nazarin wani Abu dayaga kamar FU'AD d'in nayi ta hanyar tambayoyin da yamai ya gano hakan da ya tambaye shi damuwar shi sai yace "babu" Dr yace Mai Akwai ya fad'a Mai gaskiya ,sai Fu'ad yace "kawai sai dai ko damuwar wajen Aiki Bayan shi babu komai,sai Dr yace "ya Rage Dan Haka ba baze koma ba sai Bayan sati 1 amemako 4dys , FU'AD ze nemi Alfarma Dr yace dikace kawai yabi haka ya karb'a ya hak'ura kawai yace ya dawo Bayan kwana3 ya sake dubashi, suka wuce wajen cin abinci mumcy take cema FU'AD sai dai ya taho Mata da nata ,haka kuwa akayi ,

Husna da su muhibbat sun zama Yan Shan iskar gari har zumud'i fitar da akeyi dasu sukeyi sun k'ara shak'uwa da junan su.

FU'AD da mumcy sukan Dan fita ganin gari so 2 mumcy nacema FU'AD su kaima aunty huwaila Husna ziyara daga Nan sa sanar Mata da Halin da ake ciki sai Fu'ad yace "aa Dan ALLAH base ta sani ba shi baya son gani wani na Husna har sai ta bayyana agaresu,sai mumcy ta hak'ura.

Yauma sun koma asibitin ,likita ya duba jikinshi yace "da sauki sosai" daga can suka wuce gidan wani abokin FU'AD acan ma suka had'u da sadeeq yaje wajen shi shima Ashe abokin shine awajen Aiki Amman ya girme shi sosai suka gaisa suka mutunta juna har aka d'an Saba daga baya sadeeq ya tafi yabar su a gidan.

Ana sauran kwana 2 su FU'AD su koma ,sun tafi siyayya wani k'aton supper market Mai kyau da girma , FU'AD na saman bene ta window kamar ance Mai ya l'ek'a yayi tozali da wasu Mata 3 biyun kansu d'aya sai karamar su da bata kaisu ba,a zuciyar shi yake cewa wad'an Nan matan sunyi kama da 'yan 9jan mu ,kamar ance su juyo yayi Tozali da wata zankad'ed'iyar budurwa komai nata gwanin birgewa Koda ya k'ure Mata kallo sai idon shi yake tambayar zuciyarshi da kwanyar shi "wai baka gane fuskar ba?

Sai da yayi gajeren tinan da nazari sai ya bada amsa da cewa "Kai kamar Husna ta? Sai zuciyar shi ta tambayi kwanyar shi "husnar ka? Waya baka? Kai da take cewa Auren mumcy ce?

Da sauri ya Kori wanan sakaran tinanin ta hanyar gaskata idanun shi da suka Fara tsegunta Mai ,eh wallahi itace ,Kai Aiko sai cema mumcy yayi Ina zuwa mumcy yanzu Zan dawo cigaba da zab'an abin da kikeso , mumcy na tambayar shi Ina bejira me zatace ba ya d'au hanyar sauka har Yana had'a steps......

Wajen dai ya k'araso Yana cewa "Ina kukayi Kuma? Wallahi ba gizo bane ,Dan ya gaskata wani Mai sai da Ice_cream ya tambaya bega wasu Mata 3 ba yanzu hannun su da bag?

Mutumin ya sheda Mai ai tare suke da wani Yama d'auke su suntafi har Yana nuna Mai inda suka bi har da Mai bayanin kayan da suka sa Nan FU'AD ya gaskata itace ,da sauri ya koma wajen mumcy yace "ta taho su tafi ganin yanata Abu wuta_wuta ta fara tambayan shi sai cewa yayi ta taho ze Mata bayani,Bayan an cajesu Abin da suka siya ya biya sai suka nufi masaukin su."

Ganin ya kasa samun nutsuwa sai mumcy take tambayar shi ,sai yake Gaya Mata yaga Husna fa a k'asar Nan Dan Haka ta taso suje gidan aunty ta kawai."

Mumcy sai cewa "tayi bana son Wasa da shashanci karya zatama da ta nuna Bata gidan ta?

Kuma ma Babu inda zamu Dan so kusan3 inacema muje ko gaisheta muyi ka hanani zuwa Ni kuma Dan banaso na barka na hak'ura sai yanzu da mafarkin ka ya gayama k'arya zaka tasheni a tsaye kace muje Babu inda zani."

Magiya FU'AD ya farama mumcy ,atake mumcy tace wallahi yau d'inan Babu inda zata Dan ya sani,sai cewa yayi "to bani address d'inta Ni nace.....be rufe Baki ba ta sake cewa wallahi kaima ba inda zaka ka zauna ka huta kamar yadda Dr yace."
Chapter 69 · 0% Book details