← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 95

Sashe 18

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ma'u na hango tayi 'yar shewa da k'wafa ,daga bisani tsoro da rawar jiki ya kawo Mata ziyarar bazata yayin da ta doshi wajen kwalin d ta shigo dashi gidan ,ta Jima Tana shawara d zuciyar ta Akan Abin da take Shirin aikatawa ,tsoro nata yawo a k'irjin ta ,tunawa da suman d ya tab'a sata tayi Wanda taci Alwashin ,bazata yafe Mai ba har sai tamai kwatankwacin Abin da ya aikata Mata sanan zata yafe Mai shima sai taga irin Halin d ya Shiga sanan ,Dan Haka a fusace ta bud'e kwalin ta fito da kuliyar (mage) dake ciki wata me gashi kamar na yaron Kura ,ta sid'ad'a gabanta na fad'uwa tasan indai ya ganta aikin ta tabbas yazo k'arshe Amman tayi shahada Taki hak'ura ta sunkuya ta Isa bakin motan ta k'ofar baya ta saki kuliyar a cikin motar ,jikinta na rawa ta lalab'a ta koma har k'ofan falon hajiya baba da rarafe sai d ta Isa bakin k'ofan sanan ta mik'e ta Shiga bakinta d'auke da sallama ,Babu kowa a falon sai motsin mutane d tajiyo a kitchen,Bata k'arasa ba sai d ta tataro nutsuwar ta ta dasa a jikinta da zuciyarta tukunna ta doshi su Hari ,ta gagaishe su ,suka amsa cikin sakin fuska har ta Kama wani aikin kafin ta Fara nata na falon ..

Shiko FU'AD hankalin shi kwance yake Yana duba takar dun shi ,Aiko kuliyar Nan ta kamo seatbelt ta d'ane kujerar da FU'AD yake Kai Tana dube dube can ta saki wani kuka irin na maguna ....

Jin kukan a kunen FU'AD besan lokacin da ya kusan sakin fitsari a 3kwatan shi ba ,a sukwane ya juyo don ya tabatar ba wani bane yake tsokanan shi?

Aiko suka k'ara 4eyes da kuliyar Nan ,beyi aune ba ta fad'o jikin shi ,dabara ko azacin nutsuwa yayi yunk'urin tureta duk basu zoma FU'AD ba sai ma da ta sa faratan ta tanason haurawa fuskar shi ,anan yasa ihun da be tab'ayi ba a Rayuwar shi sai gashi a sume cikin mota kuliyar Kuma Tana jikin shi ...

Baba Mai gadine ya jiyo ihun y taho a razane Yana cewa yallab'ai lafiya? Sai tozali yayi d yallab'ai a sume ga kuliya a jikin shi ,da sauri y talabo shi Yana Mai mgn ganin Babu numfashi atare dashi yasa shi rikicewa ya nufi falon hajiya babba a rikice ,Yana Shiga y Fara Kiran hajiya ! Hajiya!! Yallab'ai fa Babu lfy kizo ...

Da sauri mumcy ta fito daga kitchen har su harin ma ganin yadda me gadi ya shigo musu , mumcy ce tace wane yallab'an?

Murya na rawa me gadi yace auta dai naki Yana farfajiyar gidan acikin mota baya numfashi ........kafin y karasa mumcy ta fice a zuwa wajen motar Tana Ina zeje shida yau baida zuwa office ,yaushe ma ya sako k'asan?

Da sauri suka nufi motar tashi ,ganin FU'AD Babu alamun numfashi a tare dashi yasa , mumcy rabza salati da salalami Tana Akira Mata jameel yazo y tayata ganin bak'ar Rana yau ,da sauri Ma'u ta tafi jikinta sai rawa yake kuka kuwa tuni ya kwace Mata da take isar ma da Jameel sak'on mumcy tsabar tausayi da nadamar Abin da ta aikata da ba kowa ne ya sani ba ,sosai take kuka tsakanin ta da ALLAH ta ,da gudu Jameel d sa'adiya suka Zo ,suka bar Ma'u a baya Tana kukan nadama , Jameel ne y karb'i FU'AD a hannu mumcy da ta takabo shi Yana jijigaji Yana Mai mgn ,Bayan yayi Yan gwaje _gwajen shi ya razana can Kuma yace Ina k'anina baze mutu yanzu ba ,baze mutu ba mumcy ,Ina driver yazo muje asibiti d gagawa ,Aiko Mai gadi yace Bari amai waya dazu ya tafi gida wai kanshi namai ciwo ....

Jameel a fusace y d'auki key d'in motan FU'AD din d ya gani a k'asa ya ma mumcy umarnin Shiga motan gidan gaba ,ya mayar d FU'AD baya ya kwantar dashi ,suka doshi asibiti........

Suna Isa aka Fara ,ba FU'AD taimakon gagawa jikin mumcy sai rawa yake tanata jarumtakar jero adu'o'i Kar autan ta ya mutu ,shima jameel sai kai komo yakeyi Yana buga hannu....

Ma'u kamar tabisu taji Amman Ina Babu Hali ,tunanin ta in FU'AD mutuwa yayi fa? Shi kenan ta Shiga uku itakam tasan sai ankama dangin ta Kam yadda su mumcy sukeda masu fad'a aji (kud'i) Nan ,can kuma tace to ai Babu Wanda ya sani ,sai ta sake cewa kisan Kai fa ,wlh fad'a zanyi na gwamaci kunyar duniya da na lahira ,sai ji su sa'adiya d su Hari sukaji ta k'ara wani uban kuka Mai ratsa zuciya kamar wacce akama mutuwa ,kowadai a tsorace yake ,Amman na Ma'u daban ne da na kowa ,sbd suna cikin Alhini shiyisa Basu tsaya tunanin dalilin tsananta kukan ta ba ,sai danganta abun d sukayi da yarinta ko tsantsar tausayi d Babu Abin d baya sawa .....

Sa'adiya d Hari NE suka dinga ratashin ta ....

Asibiti......da kyar FU'AD y farfad'o da Addu'a y farfad'o Yana neman tsari da kuliyar ,Yana runtse ido Yana cewa su d'auke Mai ita ,sai a lokacin mumcy da Yaya Jameel suka dawo d tunanin su kan kuliyar d Yaya Jameel din d hannun shi ya fitar da ita a motar d zasu taho asibiti ,don suna cikin tashin hankali ne yasa Basu tmby meya kawo kuliya gidan ba har Kuma motar FU'AD ,sai a lokacin mumcy ta tuna ai tayi manakin ganin kuliyar ,yanzu ta sake tabatar d itace sanadin shigan autan ta Halin da yake ciki a yanzu ,Amman burin su yanzu lpy FU'AD ....

Mumcy tace Dr yayi duk Mai yiwuwa y dawo Mata d nutsuwar d'anta sanan tanaso abar shi y huta yad'an samu bacci ,Bataso y cigaba d surutun da yayi yanzu ....

Dr yace insha ALLAH komai yazo da sauki ,kawai zamu samai ruwane sakamakon firgita da yayi sanan Wanda ze zauna tare dashi yayi k'ok'arin faranta ransa muma zamuyi namu k'ok'arin wajen kawar da razani da tsoran dake zuciyar sa ....

Mumcy ce tace Jameel yaje gida ita zata zauna da shi ,Jameel yace aa shi zai zauna ita ta tafi ,ganin zasuyi ja'in ja dai ,sai mumcy tace to Bari Naga yanayin jikin sai na tafi ,Jameel yace to ...

Sa'adiya ce ta Kira Jameel Tana tmby jikin FU'AD ,ya sheda Mata d sauki Yama farfad'o Amman a razane d alamun kuliyar Nan ce ta firgita shi ,acema baba Mai gadi yayi gagawan fitar da ita daga gidan , sa'adiya tace to ,ta aika aka sanar ma da Mai gadin ...

Duko sunji dad'in farfad'owar FU'AD musamman Ma'u harda doguwar ajiyar zuciya tayi ......

Su Hari ne sukaje suka shirya lafiyayen abinci aka ba Mai Aiki takai musu ,sai suka taho da mumcy gida ....

Mumcy duk Bayan minti talatin sai ta Kira Jameel taji jikin FU'AD ,shiko Jameel Yana kwantar Mata da hankali ...

FU'AD dai ya samu kansa da kyar Amman har yau inya tuna da kuliyar Nan sai yaji Babu Dadi ,sanan ya Kara tsananta tsana da kyamar kuliya yanzu ,sosai ya Rasa kuzarin sa ,da taimakon Jameel y samu yaci abinci ya Sha magani yayi sallah ,har ya samu yayi waya da mumcy Dan hankalinta ya kwanta sosai ,taji dad'in Jin ya samu lpy kuwa sosai ...

Ma'u dai jiki Babu kwari ranar ta gama aikinta har yabar gidan sai ma momcy ce take cemata ta saki jikinta ai ya samu sauki ,Tana alakanta firgitar Asama'un da Mai tausayice shiyisa duk tashiga wani Hali ,Amman shi FU'AD ya tsani yarinya Haka kawai ,gata ita Tana tausaya ma Halin da ka Shiga ,kaiko lokacin d ka tsoratata ko d'igon tausayinta bakaji ba , ALLAH dai ya cirema tsanar yarinyar Nan son .....

FU'AD dai a asibiti y kwana shida Yaya Jameel , mumcy kusan kwana tayi Tana waya dasu,shima jameel Yana Kiran sa'adiya akai akai Don yaji lpy ta ....

Ma'u kwana tayi Tana tausayin FU'AD Tana mamakin kamar FU'AD Yana tsorata har d Suma Haka? Wani sashin zuciyar ta kuma yace kema Haka ai yasa ki ,kawai sai ta samu kwarin gwuiwar itama ta Rama yanzu abun ya wuce a zuciyar ta ,Amman duk da Haka Tana Jin babun dad'i Aranta .....

Washe gari Ma'u batazo Aiki d wuri ba ,har mumcy ta fita asibity ita d sa'adiya sukaje wajen FU'AD don ganin shi d Kuma in an sallame shi su dawo gida ...

Bayan Ma'u tazo ta kammala duk wani Aiki d tasan natane har saman FU'AD sai d tamai k'alk'al ,Bayan ta gama ta Shiga kitchen Tana tayasu suna hiran rashin lpy FU'AD ,itadai Ma'u tayi shiru Tana jinsu ,sai mumcy ta Kira wayar Hari wata k'arama da mumcy t siyamata don Kira irin Haka ,take tambayar ta Asma'u tazo kuwa? "Tace "eh" mumcy tace ta gyara ko Ina ? Harri "tace eh Mumcy "tace bani ita" Harri ta mik'ama ma'un waya,ma'u ta k'arba ta gaishe da mumcy , mumcy tace tayi k'ok'ari ta gyara saman FU'AD yanzu ,sai Ma'u "tace ai na gyara tun d'azu ,sai mumcy tace to ,Suma gasunan dawowa an bashi sallama ,sai cikin Ma'u y d'uri ruwa ji take kamar ya gano ta ,ta Rasa dalilin d yasa ta tsorata take tunanin gamuwar su al'halin Babu Wanda yasan shirinta .......
[4/23, 4:00 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA*

_RUBUTAWA DA TSARAWA_
BY
*Fatima Abubakar Shu'aib*
(Maman shaheed)

_shafi na 19_

*Wanan page din sadaukarwa ne ga duk wata Mai suna ASAMA'U ,Ko Ma'u ko Asmy ,Duk dai* kawayen ga fejin kunan kuyi yadda kuke so dashi🥰😍❤

Ansallami FU'AD dg asibiti har sun dawo gida ....
Chapter 18 · 0% Book details