← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 95

Sashe 90

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Su aunty huwaila ma sun shirya tsaf suna Shirin fita suka Kira Husna sukace su hadu acan.

FU'AD ne ya kaisu ganin su aunty huwaila Basu karaso ba Husna tace su Fara zuwa gidan su hafeeza sa gaisa da mama, FU'AD dai yace ma Husna kome ake ciki ta Kira shi ta kula da kanta Dan B2k ne yake ta takura Mai da Kira tunda FU'AD ya Kira shi yace zasuyi magana Kuma Daman Aisha ta Fara kyasa Mai zancen Dan itama ta Kira Husna tanata tsokanar ta.

Bayan su Husna sun gaisa da mama da hafeeza har Husna take gayama mama makasudin zuwansu ,Aiko mama tace "na kwana da sanin wanan ranar zatazo hafeeza ga amsar tambayar da na haneki da nanata min nasan wallahi tuggun habee ne yasa mamanki tabar gidan Dan ko a wajen wanka ba ita aka wanke ba Dan Ni ganauce ba kiyau ba ko sheda Zan iya bayarwa,hankalin Husna ne ya Kuma tashi da mamaki fal fuskar ta.

Kiran huwaila ne ya tsayar musu da komai ,Suma sun kataso ,fita Husna da sa'adiya sukayi har hafeeza mama ma tace gatanan biyo Bayan su.

A k'ofar gidan suka had'u da su Husna ,maman Husna fuskarta lilube da nikab suka Shiga gidan.

Suna Shiga suka dinga gaisawa da mutane masu zumden Husna nayi wai humaira ma ta samo nata Attajirin Kar amusu karyar azziki.

Mama habee na ganin Husna d su huwaila atunanin ta husna ta kawo Mata kabakin arziki ne tasan ta da hanun kyauta bare taga dangin su FU'AD sa'adiya wai sanan ga mutanen India.

Hakori ta dinga washe musu Tana musu sannu da zuwa ,Tana cewa Kai Amman kinma Yar uwarki kara ,itama kinji ta samo Attajirin miji ko gashi dai kunzama daya sai ku zauna lafiya agidajen mazajen kuyi yadon yabanya Mai kyau ta 'ya'ya.

Tir suka dingayi da Hali irin nata da baya boyuwa.

Gaishe su ta dingayi daya Bayan daya har tazo Kan maman Husna ,amsawar da taji har ta d'auki murya sai tace "wace wanan ku kuke ganin mu bamu muke ganin ku ba,Kya cire kodan Kisha iska ai kekuwa"

Tana fad'an Haka sai maman Husna ta cire nikabin ta kalli mama habee Ido cikin Ido Tana Mai karanto Addu'a neman tsari da mallam ya Bata.

Mama habee zabura tayi Tana cewa ke wacece wanan din? Banason lalata waya dawo min da abar Nan?

Mik'ewa tayi atake gumi ya Fara keto Mata ta tuge dankwalinta Tana firfita dashi.

Can maman Husna tace ,habee y taro?

Mama habee sake cewa tayi taron uban wa ke daga Ina sai mama habee ta Fara soshe_soshe Tana cewa ke dawowa kikayi? Waya dawo dake Daman seda akace Kar na Yar dake na Bari abirne ki nayi kardama nace nafison gawarki ta wulakanta a bola ko jeji Ashe hakan ze haifar min da gagarumar matsala wallah sai kingoma kabari Zo na birne ki......da gudu Tayo Kan maman Husna zata cakumota aka tareta Dan a lokacin hankalin mutane tuni ya dawo Kan mama habee d kalamanta Dan kamar Tama zare.

Yunkuri take zata Kama maman Husna Ana dakatar da ita ,mama habee dariya ta dingayi Tana cewa wallahi sai kin koma kabari Dan ban shirya mutuwa yanzu ba.

Sallati gidan bikin ya d'auka da gudu akasamu magulmacin da yaje ya sanarma baba da gudu har baba na tuntube sai gashi cikin Mata tsamo_tsamo.

Baba na tozali da maman Husna ya Fara godiya ga ALLAH da Addu'a girmamawa ga ALLAH Yana murnar yadda ALLAH ya karb'i Addu'a shi Dan ya Jima Yana mafarkin ta yasan Akwai boyayen Abu cikin mutuwar ta.

Mama habee Tana cikin wani Halli take tonama kanta asirin aikin da tayima maman Husna.

Malam ALLAH wadai da halinta ya dingayi ,Yana ya saketa muguwa macuciya.

Labari da yaje wajen humaira amakota sai kuka takeyi na Bata Mata show da mama habee tayi na bikinta wai me makon ta Bari sai ankaita sai ta haukacen ita wallahi zuwa gidan Alhaji babu fashi ta bita da Addu'a , amman bari taje ta ganta.

Humaira na zuwa taga Abin ya fi k'arfinta ,kuka ta dingayi Ana cikin Haka aka dinga cewa motocin d'aukan Amarya sunzo Ashe humaira da kawayenta ne suka Kira angwaye wai suzo akai Amarya kawai tun yanzu shine suka turo da motoci.

Mama habee hauka ta kankama anata yage yagen zani Tana tonama kanta asiri Abin yazamar ma su Husna wani irin Dan mamaki sun Rasa mema zasuyi ,maman hafeeza d shigowar ta kenan sai cewa tayi ALLAH ya Toni asirin ki , ALLAH y shirya masu Hali irin naki.

Gidan biki ya koma gidan gulma da tsugudidi anata gulmar uwar Amarya ta haukacen asirin da Tama kishiyarta ya koma Mata.

Baba ko ji yake kamar ya rungume maman Husna macen rufin asirin shi.

Humaira ko sai cema wata kanwar mama habee tayi su rik'eta su kaita d'aki da ta Isa gidanta zata Fara Shirin samo kudin da za'a Mata magani ,itama aunty hafsun dake uwar son Abin duniyace tace ai Tana Nan har ta warke taji abun samun kud'i.

Aunty huwaila had'a Kan su Husna ta dingayi Tana cewa su tafi tunda kaikayi ya koma Kan mashekiya Kai Kuma mijin Yaya in kanason magana da ita ka biyomu gidan hajiyar mu ,baba d maman Husna har seda sukaji kunya gashi Basu samu sunyi magana ba.

Humaira Kam ita ta dinga tataro Kan mutane Tana cewa suje su Shiga mota su tafi kar angwayen su fahimci me ake ciki ,mutane nata mamakin yadda matsalan uwarta baya gabanta.

Husna d sa'adiya wucewa gida sukayi cike da murna da farin ciki.

Mama habee Kam an sata a d'aki anata bunka Mata hayaki wai na temako sai suritai takeyi.

Su aunty huwaila Suma gidan bawan ALLAH Nan da ya dinga taimakawa maman Husna suka nufa Dan kaimai ita yaga Halin da take ciki na samun lafiya daga can sunifi gidan hajiyar mu suka wuce cike da murnar tonuwar asirin mama habee ayau.

Sanaya ta fahimci cikine da Husna ganin yadda aketa Mata sannu da jiki Kuma mumcy ma ta Mata magana Akan ta Mata ya jiki Dan bataji Dadi ba ,hankalin sanaya inyayi dubu ya tashi wato itace FU'AD baya kulawa?

Tana Kuka ta Kira mamanta take Gaya Mata sai ko dady ya kwace wayar ya dinga zaginta Yana cewa itama inbatayi ciki a satin ba ze yafeta daga yaranshi sokuwa wacce batasan Abin da ake nufi da itaba, Yana ajiye wayar gumi ya dinga keto Mai Yana tunanin meye abinyi akan FU'AD komeye ma zeyi Dan cikar burin shi.

*Saura fejin k'arshe insha ALLAH*😍😍
[4/23, 4:01 PM] Hayat: **RIKON KWARYA*

```RUBUTAWA DA TSARAWA```
BY
*FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB*
( Maman shaheed)

_The last page_.............The end_👌🏻

*Special Thanks to All my Fanc I really appreciate your caring,ddu'ah, support,nd follow m bomba to Bamba*👌🏻😀😍😍

Pg70........🔚🔚🔚🔚

Bayan sanaya ta ajiye waya ,ta rabza ihu Tana mitan y dady zece sai ta samu ciki d mutumin da kamar besan meye Aure ba akanta Ashe munafuki Yana can Yana Abin da yakeso ko Dole uwarshi take Mai Amman ai yayi din ai Dan Haka itama Dole ta tirsasa Mai.

Tun Bayan isar su aunty huwaila gidan Mai taimakama maman Husna yayi matuk'ar farinciki ganinta cikin sahun masu gamsashiyar lafiya har iyalin shi sosai sukayi murnar ganin ta da lafiya.

Itama godiya tamai sosai ,har aunty huwaila ma ta tayata yimai godiya daga bisani suka wuce gidan hajiyar mu.

Su Husna na Shiga gida FU'AD ya kirata Yana tambayan ta komai lafiya dai ko?

Cemai tayi "lafiya sun koma gida ma"

Hakan Dadi Yama FU'AD kafin yace "toh ta zauna ta huta shima ya kusa dawowa"

Husna Bata samu bakin amsawa ba sai samun sararin mamakin canjawar FU'AD farad d'aya Haka ,kodan Yana tunanin Akwai jinin shi a jikinta? In ta fahimce shi badan ALLAH ya canja ba kenan?

Sashin zuciyar ta cemata yayi "nd so what? Hakan ma ai yanadaga cikin so da nuna damuwa Kuma sai kanada kima mutum zai hada jini dakai har ya baka lokacin shi nawane ake had'a jini dasu din Amman Babu wani nuna kulawa ko damuwa da Halin da suke ciki?
Kawai kobada Kai bori ya hau kema"

Bayan sun huta mumcy ta tirsasama Husna cin abinci Dan ji tayi batason cin komai gudun Kar tayi amai a gaban mumcy.
Chapter 90 · 0% Book details