← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 95

Sashe 51

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ana Haka sai ga ,mamyn sanaya ta Kira mumcy daga Egypt d'in, mumcy D'agawa tayi suka gaisa kowa na girmama kowa ,sanaya na sauraron su ta gane mamyn take ta kira,sai mamy ta gama Dora mumcy Akan maganar zuwan sanaya Egypt ta gama zazago Mata k'arya da gaskiya ,wani mumcy taji Bata yadda ba wani kuma tayi ta kokwanto akai ,akarshe dai taga masalaha kawai sanayar taje Egypt d'in taga uwar da zatayo insun rik'eta ma sun hanata dawowa shi kenan huta roro waken gizo yaki 'ya'aya ,Amman saboda mumcy ta nuna musu ba umarni suka Bata ba Kuma shawaraga da iko na wajen ta ,tace zatayi tunani akai zata Kira inta yanke shawara su jira wayar ta ,sanan mamy tace sai Taji daga gareta ta katse wayar ta.

Sanayan ma da guntun hawayen ta ta mik'e Tana Kara cema mumcy ,nidai tafiyana Yana hanun ki hajiya , mumcy tace to sai kin jini Zan nrmeki Akan maganar ,sanaya tace to ta fita Tana goge hawayen ta na makirci Dan kukan a iya idon ta ya tsaya ba har ranta ba Dan ta Gama tsara tafiya Koda yadda FU'AD ko babu sai tatafi Koda zaduyi baram_batam da dadyn ta kuwa.

Gab da magriba FU'AD ya dawo gida ,wajen mumcy ya Fara zuwa tamai barka da dawowa sanan ya koma wajen sanaya yaga tanata cika Tana batsewa ya fita harkar ta tunda yaga lafiyar ta ,sai ya haura saman husna yaga Tana Shirin fitowa ta sauka wajen mumcy da hannu ya maida ita Yana Mata muzurai ta juya zata koma ciki da sauri ya figota har Tana fadowa jikin shi yace "gidan uban wa Zaki? Wa Kika rains? Keda Mara mutunci Nan da ya kiraki 'yar uwarsu ,to in ma 'yar ubansu ce nayi mahanin shi yau saura ke ,Dan yau yasan yayi da d'an halak FU'AD Mai nasara Dan wallahi ko agidan Nan na k'ara ganin shi sai anmana shara' a Haka kema ko a filin arfa Kika hadu dashi ko ta cikin mafarki Dan nasan Baki da ranar zuwa bare shekara ,Kika sake Kika ko Kali inda yake bare kimai magana sai kin gane kuren ki walahi na Gaya Miki .

Kuma in Kika sake magana da wani ma bashi ba irin maganar da Kika Mai sai kin sani wallahi ,ke ko bako akayi ma namiji a gidan Nan Kika k'ara gigin kawo Mai Ruwa sai na barar daku keda Abin da Kika kawo Mai d'in ,ai ba aikin ki bane ki rik'e aikin ki .....be rufe Baki ba ta kwace daga Rik'on d ya Mata tace.

To Ni ka kyale Ni meye damuwarka da Ni ,Dan ya Fara min magana na amsa Mai ,wai Kai to meye hakan kakeyi? Ni sunan Abin nakeson sani? Ka fad'amin da bakinka ?

Bata rife Baki ba ya matse Mata Baki Yana cewa ke Ni sa'an kine ? Ina fada kina bani amsa? Har wacece ke acikin mata da zaki titsiye Ni kina min tambaya ? Ke martabar Aure fa kawai nake karewa da barin ki zanyi ki tafi sakaka kamar tunkiya ,Dan bakya gabana dake da oho duk daya kuke a wajena ,sai ko Husna tace bakai zaka Fadi hakaba lokacine ze nuna.

Sai ko FU'AD ya k'ara matse ta yace da wa kike? Lokaci ne ze nuna me? Me kike nufi? Yana matse Mata Baki da k'arfi ,yasa d'an k'ara tace eh Mana Inna bar hanun ka ko nabarma gidanku ai lokaci ya nuna kanshi na huta da zalincin ka ,sai FU'AD ya tureta da yaji manufarta yace ,sai me inkin bar gidan daidai ma kenan dirty girl kawai Yana dosan d'akin shi.

Husna ta juyo tayi hanyar nata d'akin tace ,Nima Haka nakeso ai na mage kawai ,ya biyota a sukwane ta afka nata d'akin ta rufo Tana haki da ajiyar zuciya.

D'akin shi ya koma Yana k'wafa da y kamata da ta Mai bayani ,Yana Shiga yaga gyaran da akama d'akin Yana Mai oyoyo sosai tsari da k'amshin d'akin suka d'auke shi Amman halaya ta mazantaka ko Halin wasu mazan sai be yaba ba Yama tab'e Baki ya d'auki hakan matsayin Dole tayi ai aikinta tunda dama tanan tafi kwarewa da rashin kunya ma Naga yanzu har dgree take Shirin yi Akan fitsarar tata,toh yarinya kin had'u da me hukunta ki.

Husna Bata fito ba sai da Aisha ta hauro saman taga FU'AD ta tambaye su yace Tana d'aki dama taji shigowa Aisha sanan husnan ta fito kamar ba buya tayi ba ,suka sauka kasa FU'AD nata jifanta da hararar gargadi ,daga Nan ma part d'in aunty sa'adiya suka tafi suna Taya Aisha had a kayanta na barin gari,sosai suka Sha Hira kafin Husna tabaro part d'in ta dawo nasu ,a kasa wajen mumcy ta had'u da FU'AD ,Tama mumcy sannu ,sai mumcy ta tambayi Husna "Ina Aisha me zumudin barin gari? Sai murna take ,sai FU'AD yace .

Aisha tafiyar tazo ne? Sai Husna tayi saurin cewa eh Mana bana gayama ba? Sai mumcy tamai wani irin kallo tace zaka Fara Halin naka na mantuwa ko? Sai FU'AD ya wayance yace kinsan abubuwanne da yawa mumcy ita Kuma Bata tunamin ba ,Yana mamakin yarinya karama tasashi yin karya yanzun Nan tasa ya sake kwai na karya ,sai Husna tace kad'ai manta Amman na tuna ma ,sai mumcy tace kyale shi Asma'u nasan Halin kayana fa.

Yauwa FU'AD bikin gidan Alkali za'ayi wanan satin Dan Haka dakai da matanka duk zamuje har sa'adiya ma Dan Haka ka shirya zamuje _mother's day zamu dinner_ karkace ban fada maka ba.

Yauwa aunty huwailan Nan ta India k'anwar mahaifiyar Asma'u ta Rokeni Alfarmar ka Taimakama Husna ta bud'e account zata Aiko Mata da sako taba babanta Kar naji wani magana kuma Dan nasan baze gagara ba ko zuwa gobe ne ka d'auketa kuje Ayi a wuce wajen , ALLAH yayi Albarka kaji.

FU'AD dai kallon mumcy ya tsaya yanayi ,Yana ayyana ta dakeshi ta hanashi kuka ,ta sharemai hawaye da Addu'a,ya ya iya Haka ze cika umarni kodan wanan Addu'a,iyakaci in yarinya tamai kauyanci ya bibigeta.

FU'AD be Mike ba mumcy ta Dora Mai da cewa ,yauwa son muyi magana ta fahimta ka bani aron nutsuwarka Nan ,kabar sanaya taje taga iyayenta kaji zeyi magana yaji mumcy nacewa inda rabon Taki dawowa ma kaga shikenan ,Jin haja yasa FU'AD cewa "Toh" Amman yarinyar naso sai na ladabtar da ita kafin Dan har nuna Mata nayi baza'ayi tafiyar ba ko meze faru,sai ko mumcy tace "au Ashe dai gaskiya ta fad'a har nake karyatata"

Sai FU'AD yace wani Abu tace Miki ? Me Dame tace Miki mumcy ? Sai mumcy tace "abar wani tashin tashina tunda ka maimaita yanzu a gabana kace komai ze faru baza'ayi tafiyar ba daidai yake da kalmar da ta furtamin, FU'AD yace "wacce kalma mumcy?

Mumcy tace "kawai magana ta wuce ,taje inta dawo falillahil hamdu in ata dawo ba shikenan.

FU'AD yace ALLAH yasa ma karta dawo cikin zuciyar shi besan maganar ta fito ba ,sai ko mumcy tace "ba Amin ba" ta d'auke kanta kamar ba itace ta bashi amsa ba ,sai Fu'ad ya juyo yace "wai kinji ne? Sai mumcy tamai wani irin kallon tace as cikin k'irjin ka nashiga na tsaga zuciyarka na jiyo abun da kace,sai Fu'ad ya Sosa k'eya yasan bak'a mumcy ta Gaya Mai ,sai ya haura saman kawai.

Bayan anfama cin abincin dare ,Husna ta haura zata kwanta FU'AD ya rutsata ,Yana kalubalantar ta Akan cewa ita tace a bud'e Mata account ko? Da Taki kulashi Kuma ita ta had'a Abin da mumcy Dan Abin yafi tafiya bisa umarnin mumcy ,ganin ya dinfarota ze bige kamar sauro sai ta magantu ,Tana Shirin ja da baya Tana cewa "Ni to Ni ko zancen ma ban sani ba sai yanzu a bakinka , FU'AD ya harareta Yana cewa mak'aryaciya rantse ? Sai Husna tayi fari da Ido tace "na rantse " yace "Haka ake rantsuwa a kauyen ku? Sai tace "ai Dan babu kyau rantsuwane Dan ita rantsuwa icen kabarice Amman da na rantse ,Amman Ni bansan maganar ba ma ,sai ya dungure Mara Kai har ya wuce ya dawo ya Fara cewa saura Kiki shiryawa gobe da wuri Dan zankaiki bisa umarnin uwa tagari ki bud'e na dawo dake saura kimin kyauyanci walahi tun acan Zaki gane kurenki.

Husna dai azuciya ta dinga Mai dariya Tana Dole akaini a dawo Dani driver.

Washe gari Bayan sun breakfast ,Husna tashirya cikin wani material Mai matuk'ar kyau d'inkin buba yaji adon duwatsu masu kyau da d'aukan ido tayi simple makeup abinta ,ta fito da mayafinta kalan flat shoe d'inta Mai kyau farare masu d'aukan ido shi Kuma material d'in Orange ne da fari ,ko da ta sauko ya harareta Bayan ya had'u da mumunan fad'uwa gaba adadai lokacin da ya kalli Husna kalon farko , mumcy ma husnar ta Mata kyau tace "Asma'u anfito zoki karya sai ku wuce ko?

Husna cikin girmama a taje ta zauna kusa da mumcy tasa FU'AD a gefenta ,har mumcy ta gama tabar FU'AD awajen Tana cemai yayi sauri su tafi shida ze wuce office.

Bayan FU'AD yanata jifan Husna da wani kallo da ya Rasa dalilin yinshi sai can yace "ke malama ko Baki gamaba ki tashi mu tafi Dan ba yaron gidanku bane Ni.

Sai Husna tace toh ,nama Gama ,yasa Kai dak'in mumcy Yana cemata mumcy asa wani ya gyara sama Dan ALLAH kafin mu dawo ,sai ko Husna na Bayan shi zatama mumcy sallama itama sai tace ai na kammala da komai babu abinda ban gyara ba har d'akin ka ,sai mumcy tace sannu uwar k'ok'ari ALLAH ya bada zuriya d'ayiba ALLAH ya Baki me Miki ,Husna rufe fuska tayi Tana amsawa Dan ita sai yau ta tuna ko hankalinta ya tab'a tunano Mata Ashe fa wata Rana zata Sami yaro na k'ashin kanta? To yaushe ne? Tab! Shekarun Amman ai da yawa ,da tunanin a ya Fara haurawa Kan to dawa zata samu yaron? Sai tayi saurin gusar da tunanin ta Dan har ta Fara Jin kartayi sab'o .....da sauri ta bar d'akin.
Chapter 51 · 0% Book details