← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 95

Sashe 5

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin kufula FU'AD ya tafi Yana mita dama nasan kin Dena ji dani momcy Akan wata kucaka har kina barina da yunwa , ALLAH y kawo min yayana lpy y haura sama Ranshi a b'ace tsakanin shi d ALLAH .

"Cikin Ranshi yanata hak'aito irin abinda zema ma'u Koda zesa tabar gidan ne kuwa"

Maman shaheed ce dai👌🏻
[4/23, 4:00 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA*

_RUBUTAWA DA TSARAWA_
BY
*F.A.S*......

_Shafi na 5_

Mumcy na barin parlour ta Shiga d'akinta , FU'AD y haura yin hukunci .

Koda y Tura K'ofan Ya Shiga Babu Sallama wai Bata Kai yamata sallama ba, shida parlour shi a irin Rainin d yake ganin abin .

Y sameta tanata Had'amai Kan Takardun shi d y watsar ,ko kallon inda yake batayi ba bare tasan ya shigo .

Yaje ze giftata y kamo kunenta da yake cikin hijab da hanun hagu Dan mugunta Yana cewa uban wa kike murgud'ama baki dazu? Waya Miki Kama d sa'anki duk gidanan ?Yana wani hucci d zare mata idanu .

Sai d tasaki 'yar k'ara tace , ALLAH y baka hak'uri Ni konayi ma bansan Nayi ba Tana turo Baki .

Yace Aljanune dake ko me da zakiyi Rashin kunya kice bakisan kinyi ba ?

Ta samu ta fizgi kunnen ta da kyar ta shek'a d gudu tayi hanyar fita ,tace "eh sune Dani masu gyarama mutum zamansa wanda be so azauna lpy ba , ta bugo Mai k'ofar parlour ta seta benen atamanin Tana hucci.

Shiko FU'AD mamaki yake yaushe ta samu dama d saken mayar Mai d martani Haka? Tab! Lailai Dole y gyara Mata zama yarinya 'yar ficiciya ta iya Rashin kunya haka ,oo no duk mumcy ce taja min yarinya har cikin gida har parlour na tamin Rashin kunya ,tab ! Yarinya kin Tab'o Zaki,hmmmm dirty girl ko gyaran Bata Gama ba tayi Rashin kunyarta ta gudu .

Itako Tana sauka taga mumcy tayi saurin gyara nutsuwar ta ,tazo tace hajiya na Kamala d saman saura parlour , mumcy tace Zo ki gyara barin Shiga d'aki inkin Gama ki kirani na dawo parlour Dan mu karya d Son , Asma'u tace to hajiya .

Asma'u gudu gudu sauri sauri take Kar FU'AD y sako tayi saurin shara tayi morphine Tana Kan goge goge FU'AD y sakko ganin ita kad'ai ce a parlour gashi sai wani hucci yakeyi yana sake b'ata Rai yaci magani kamar be tab'a dariya ba ,ya nufota d niyar zalintar ta ' Aiko Tana ganin niyarsa d gudu ta saki Abin goge TV ta Ruga D'akin mumcy ,kafin ta Shiga t seta nutsuwar ta ,ta Shiga d sallama tace mumcy na kammala .

Shiko FU'AD kwafa yayi da Tamai gudun wuce sa'a ,Amman zasu gauraya ne ,Dan Haka dining y nufa Yana jiran mumcy shi .

Tare suka fito d Hajiya ,wani mugun kallon gargard'i y wurga Mata ,itako ta k'ara murgud'a Mai Baki Karo na biyu ,Abin ya tsaya Mai A zuciya shikenan kucakar 'yar Nan ta Raina shi?

Yama Rasa meze Mata Dan ya bak'anta Mata ,Sai y Tuna Bata K'arasa Gyara Mai takardun Parlour ba ya zaburo ta, ta gudo ,Dan Haka cikin izza yace Wuce kije ki Gama Aikin ki na sama da Baki Gama ba .

Mumcy tace ,au Bata Gama ba Daman?

Asma'u tayi karfin halin cewa , mumcy na gama komai shima sheda ne ,muje da wani agani inbangyara komai ba .

Jin Haka mumcy ta gano kodan 'akwai 'yar tsama ne tsakanin su d ta Rasa Dalilin tsana da tsangwamar da FU'AD yakema Asma'u ,Dan Haka tace to jeki ki karya sai kije ki Taya su harri Aikin part d'in yayan FU'AD .

Asma'u tamai wani irin kallo sanan ta tafi zuciyar ta fesss.

Cikin kad'uwa da Tsarin part d'in ta dinga k'arema komai kallo ,ta Shiga cikin su Tana tayasu Aikin sunata hirar yayan FU'AD d'in da Bata sanshi ba ,sai yau d Tasha lbr shi harma d wasu kyawawan d'abi'u da halayar FU'AD d hajiya ,ita dai ta yadda d halayen hajiya managarta Amman FU'AD Kam Babu abinda zata d'orar sai kinjinin marashi a tunanin ta,shiko yayan sai yazo zata d'orar da nashi salon.

Bayan sun kammala gyaran komai yayi k'alk'al suka turare ko 'ina da turaren wuta d na freshner sanan suka Rufo suka dawo part d'in mumcy .

Kusan wuni Ranar Asma'u tayi agidan Dan har kasuwa ta Raka hajiya babba sukayi siyayan kayan d za'a tari bak'in gobe sanan suka Shiga store ta siyama Asma'u ,dogayen Riguna kala 5 da k'ananan hijabai daidai kafad'a masu flawowi da stones ajikin su kala 5 Suma sai flate shoe 3 sai atamfa kala 3 sanan tasai Abinda take buk'ata suka koma gida da taimakon driver d ya kaisu ,shi y d'auko kayan gaba d'aya y shigoma d hajiya babba da taimakon Asma'u .

Bayan ankammala komai na gidan ,hajiya babba taba Asma'u umarnin tafiya gida d yamma lis ,ta d'auko ledar dogayen Rigunan ta Bata tace natane t Bata kyauta ,Aiko Asma'u anmata kyautar d tun zuwanta duniya Babu Wanda ya tab'a Bata ,Aiko ta Dinga yima hajiya Addu'a da godiya d Addu'a ALLAH yajikan iyayenta ,hakan ba k'aramin faranta Ran mumcy yayi ba duniya tanason ayima iyayenta d suka Rasu Addu'a har sadaka takeyi Don hakan .

Asma'u zuciyarta fes ta Isa gida Bata samu kowa tsakar gida ba ,tanata sallama mama habee na d'aki tanaji tak'i ko kulata ,Dan Haka taje ta Adana kayanta d niyar sai anjima zata bude ta gwadasu in ta nunama mahaifinta .

Asma'u muryar mama habee ta jiyo tanata kiranta wai tazo ta kwashe tuwo tunda baiwarta ta gama miyar .

Asama'u ta fito ta nufi kitchen d'in ta had'o kwanuka ta duba taga tuwon be Isa a kwashe ba ma gashi Babu wuta sosai ,Dan inda sabo ansaba musu d'anyen tuwo agidan ,sai ta gyara with ta rufe tuwon Dan ya k'ara silala kafin ta kwashe kodan cikin mahaifinta ta gyara tuwon badan su humaira ba .

Tana cikin kwasa baba y shigo hanun shi Rik'e d na auta haidar ,d gudu haidar y shigo kitchen d'in Yana cewa yau zamuci tuwo Mai dad'i tuwon Yaya ma'u ,Aiko mama habee ta danno Mai Ashar tace sai ka fad'i Wanda Babu dad'in Dan uwarka Dan nema samamme kawai ,Aiko baba y Fara Mata fad'an zagin d takema haidar ta d'inga gunguni kamar zata zageshi ,sanin Hali yafi sanin kama yace ALLAH ya shiryeta .

Bayan Asma'u ta Kamala taci nata ita d haidar ta kaima baba nashi ,ta yi hanyar d'akinta ta d'auko kayan d Hajiya ta siyo Mata ta nunama baba agaban mama habee ,baba yasa Mata Albarka y k'ara yi Mata nisiha da tuni Akan halal d bin Rayuwa sannu a hankali ,sanan t Mike t nufi mama habee zata nuna Mata d sauri mama habee ta dakatar d ita Tana cewa "me Zan gani akayan sata baze wuce satowa kikayi ba anyo gado har Gyatuma ta kwanta dama ai sana'ar ta kenan ,Abin ya Sosa Ran Asma'u idon ta ya ciciko da Ruwa.

baba yace tashi ma'uta kije Abinki nine Wanda zanbada sheda Akan mahaifiyar ki ko tsinke Bata tab'a d'auka d sunan sata ba ,a cikin gida ko mak'ota Kuma ita ta huta don tata tayi kyau yanzu mu ta Bari cikin cakwakiyar duniya shi Kuma iya Ruwa ai fidda Kaine .

Mana habee ta Fara masifa Tana cewa "waye kakema fatan tasa kartayi kyau Ni ,to walh saidai bakin ka y fad'ama tsohon gidan Nan naka d k'iris yake jira y Rugurguje muga ta fad'i sauro y kada cizo Tana jaraba kamar adamar kamaye ta cikin dadin kowa .

Baba yace sede kiyi d wani habee kulin Addu'a shiriya nake Miki ,bazan fasa ba .

Asama'u ta koma d'akinta d kayanta ranta fess Dan baba y yaye Mata k'uncin d mama habee ta k'unsa Mata ,zama tayi tanata gwada kayanta Tana juyi Tana murna Tana ganin kyawun da kayan suka Mata gashi kamar an gwada ta ba k'aramin dad'i taji ba ta ware Wanda zata sa Gobe Dan ta fuskanci goben ta musammance ga kowa na gidan hajiya baba harsu masu Aikin ba'a barsu baya ba ,Dan Haka itama zata k'ure adakarta gobe tafito Shar d ita .

*F.A.S*..........
[4/23, 4:00 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA*

_RUBUTAWA DA TSARAWA_
BY
*FATIMA ABUBAKA SHU'AIB*
( Maman Shaheed)

_shafi na 7_

```Comments Dinku Na Bani Karfin Gwuiwar Yi Muku Typing ,Dafatan Ana tsintar Darusan Dake Tatare Da ilimintarwa Dake cikin labarin```👌🏻👌🏻

Bayan haurawan FU'AD Sama ,mumcy badan Taso ko taji dad'i Aranta ba Son D'in nata yayi zuciya da break ba ,sai Dan tayi Adalici kawai, Bata rufe Ido ta goyi Bayan karya Alhalin ga gaskia Tana kallo muraran ba,Dan haka ta yi kokarin danne Abin cikin zuciyarta.

Bayan ta kammala ,Ma'u tazo ta k'arasa gyara komai na falon ta Kuna turaren wuta masu dad'in Kamshi suka baibaye falon ta ko Ina .

FU'AD wayar sa ya d'auka ya Fara latsawa Yana kale kale ,can ya buga uban tsaki yayi kwafa ,sanan ya Mike ya Shiga bathroom d'in shi ya feso wankan kwalisa irin na 'yan bana7 ya fito sai kamshin turarukan wanka yake Yana goge Kan shi da towel.

Gaban dressing mirror ya nufa Dan shafe jikin shi da cream din shi Mai kamshi ,Bayan ya janyo stool ya zauna ya Fara shafe jikin shi da Mai ahankali kamar Mai tausayin jikin nashi ko wata macen Bata lalab'a jikinta haka ,ya feshe jikin shi d body spray Mai kamshi ya Gama ya nufi cllothset ya ciro wasu k'ananun kaya masu tsada da kyau Yana sawa Yana bad'e kayan da jikin shi da turaruka kusan kala 3 har su Bayan kunen shi seda ya samu rabon kamshi ,Dan FU'AD Akwai sani lungu da sakon da ya kamata ace turare ya ziyarta Dan har yafi wata macen sanin Haka .

Ganin _Time be_ k'arasa ba na zuwa d'auko big bro d'in shi dg _Airport_ yasa ,ya zauna ya Shiga _thinking to what he do to Ma'u_ _dirty girl_ da har zata ji zafi tabar gidan _before her big bro_ jirgin su ya landing....
Chapter 5 · 0% Book details