← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 95

Sashe 53

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Bayan FU'AD ya dawo gida sosai ya titsiye Husna Yana surfa Mata ruwan masifa da dikoki Akan mazan waje ,Husna ta dinga turo Baki Tana cewa to Inka sakeni ai acikin sune wani ze aureni ko ka manta kace jona maka Ni akayi inkaga Dana zaka Kara min wuta NE naje na karata kaima ka d'auko 'yar luv wacce take type d'inka ka manta da wanan batun naka? In kamanta Ni na adanashi a kundun Adana mahimman baya naina Kuma Akwai Randa mumcy zata Mana Alkalanci akai.......Bata karasa ba taji saukar wayar hanun FU'AD Akan bakin nata atake ta tsuguna saboda wani azabar zafi da ya ziyarci bakin ,Tana bud'e hannu Tana jini ,shima yazo d'aukan wayar shi Yana Shirin rufeta da masifa yaga aikin da ya Mata sai yayi saroro ,Husna tasa kuka tayi hanyar sauka Tana cewa wallahi tun yau d'inan ma mumcy zata Fara Mana alkalancin ba sai mun d'auki dogon lokaci ba har ka Fara Shirin illatani ?
Cikin kakausar murya FU'AD yace ke karki sake ki sauka k'asa.
Husna tace sai na saukan so kake nayi mushe a saman ?
Tana Shirin sa kafarta a kofar FU'AD yace "bakiji ba wallahi in Kika fita ......be k'arasa ba Husna tace wallahi ko me zakamin sai na fita Haka kawai ka dakeni ka hanani kuka.....tasa Kai ta fice sai Fu'ad ya bita da sauri saurin ba d'aya ba ya kamota yayi_yayi ta dawo tace wallahi bazata dawo ba ,ganin Bata da niyar komawa d'akin ga jini na zuba a bakinta ga hawaye da takeyi sai Fu'ad ya sungumeta kamar jaririya Tana dukan shi ta kirji ta kanshi Amman bema San tanayi ba sosai ya rik'eta ya had'a da k'irjin shi be ajiyeta ko Ina ba sai d'akin shi ya direta a gadon shi ,Tana tureshu Tana cewa Ina zaka kaini Ni ka rabu Dani wallahi.
Ganin ta a gadon da sai dai hanun da su Kai yau itace a kwance male_male ga k'ato a kusa da ita yasa k'arfin zakin shi ya danneta Yana Shirin Ciro Abu a karkashin gadon sai kokuwa cirowa yakeyi da hannu 1 sai ko Husna tace "ka rabu Dani wai me zakamin wallahi in ja cutar Dani ALLAH baze barka ba me kake Shirin yimun ne a banzan gadin Nan mugu Mai Shirin aikata .........sai ya toshe Mata bakin ya sako first aid box Kan gadon ,Tana gani tadan samu sukuni daga Abin da take Shirin firtawa ga FU'AD ,Tana tirjewa Yana saka k'arfin da ALLAH ya bashi Yana sarafata har ya Gama gige Mata ya sa mata magani inda taji ciwon ma kad'an nne ba kamar yanda yayi zato ba shi yisa hankalin shi ya tashi shima ,sai ce mata yayi uwar raki ji dan Abin ,Mai arahar jini kawai tashi kiban waje Ni ,sai alokacin ya sake ta daga Rik'on da ya Mata ya bar kusa da ita gaba d'aya ma ,sai ko borin kunya ya Hana Husna tashi sai cewa tayi,ai kawoni akayi sai a mayar Dani inda aka d'aukoni .....
FU'AD gadan_gadan ya taho Yana cewa Bari na nuna Miki karyar rashin kunya fitsarariyar yarinya kinji gado Mai taushi Zaki more to Baki Isa ba Baki da mahali acikin shi ,Yana Shirin tab'ata ,ta gice da sauri tace zanma tashi muguntar da kamin ma ya Isa ,ta Mike jiki Babu kwari ga tarin kunya da taji duk ta lulubeta ,da sauri ta fita Tana cewa , ALLAH dai Yana kallon ka , FU'AD yace ke baya kallon ki kin buya a gidan mumcy Yana Shirin Shiga bathroom din d'akin shi.

Husna batayi tunanin fita ba yanzu ,d'akinta ta nufa Dan taga yadda aka Mata da Baki Dan taji yad'an canja Mata , dressing mirrow ta duba taga Ashe fashewar Babu yawa kamar yadda Wanda yayi aikin ya fad'a Amman jini ya zuba ,sai ta canja hijab ta nufi kasan mumcy Gam taji alamun FU'AD ya rufe ya kuma tafi da makullin ,k'wafa tayi da tsaki ta koma d'akinta Tana tunanin muguntar FU'AD har take auna yama zece Yana kishin ta ko zuciyar ta zata karanta Mata k'arya wanan Sam ba gaskiya bane .
[4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA*

```RUBUTAWA DA TSARAWA```
BY
*FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB*
( Maman shaheed)

💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥

Pg44

Bayan dawowan su mumcy kowacce tayi part d'in ta Bayan mumcy ta yad'a FU'AD da sanaya ta yi musu nasiha d togaciya ,shi Akan kula da hakkinta ko d Tana can irin su kiranta yaji lafiyan ta ,itama irin tasan tanada Aure tabar mijinta ta kula da kanta duk sunji sun d'auka kamar gaske daga baya ta musu Addu'a akan sai goben su aunty sa'adiya sa rakata Airport d'in Kuma har da FU'AD d'in za'aje.

Yau FU'AD a d'akin sanaya yake yayi k'ok'arin zama a falonta Yana kalo Yana Amfani da wayan shi sama_sama Yana Hira da ita ,itama Tana bashi amsa sama_sama Har yake cemata yaushe Zaki dawo ?
Ta yatsuna fuska tace "za muyi waya kasan tafiya itace da Kai ba Kaine da ita ba"
FU'AD kalon ta kawai yayi yace "hmmm"
Sai Tana tashi tace "Bari taje ta k'arasa had'a kayanta.
Shiru_shiru Bata fito ba kusan awa 1 Dan said kawai ya tashi ya wuce d'akin shi.

FU'AD kwana yayi Yana tunanin wasu abubuwa game da Husna sanan ya dawo da tunanin shi Kan sanaya a tunanin shi tasan meye Aure tunda ta girmi Husna Kuma idonta yafi na Husna bud'ewa Amman tayi buris da komai kamar yadda yakeso shidai har Rasa yadda ze Kira Auren shi yake,ya Jima Yana tunani da dogon nazari kafin ya ajiye komai ya kwanta.

Washe gari da asuba ya tashi sanaya akan tayi sallah ya wuce masalaci ,Amman har ya dawo Bata tashi ba sai da ya tsaya akanta sanan ya samu tayi alwala tayi sallah.

Bayan sund'an koma bacci Basu tashi ba sai da Harri ta kawo musu break d'in su ,Bayan FU'AD yaci ya barma sanaya nata Dan so 2 kacal suka tab'a Break tare ,ya tafi Dan ya samu yayi wanka.

Bayan ya fito yace ta gama shiryawa Kar azo Ana jiranta Dan babu yaron ta a duk gidan be jira amsawar taba ya fice yayi part d'in mumcy.

Tare da Husna ya same su suna breakfast suna Hira ta surika da surika ,shi kanshi Abin ya birge shi Amman be nuna ba, a fili sai ya gaishe da mumcy har k'asa ,ita kuma Husna ta gaishe shi cikin girmamawa da Ladabi ,sai Fu'ad yace kun shirya ko? Dan bazan jira kowa ba nasan matar bro Bata da case ,sai ko mumcy tace "itama Asma'u ai Haka Akwai cika Al'k'awari yadda na Santa,sai ko Husna ta keb'e Mai Baki irin yauwa kaji? D'inan taji an yabeta"
Sai FU'AD yace "Kai mumcy kamar kece lawyer ta" sai mumcy tace waya sani baka da wata maganar ta Isa daga Haka? Inci gaba da kareta.
Husna har murmushi tamai gami da fari da Ido ,abun Yama FU'AD wani iri Amman yaki yadda yadda yadda kirashi da kyau Kuma har ji yake kamar ta Kara yi Dan ya gani.
Husna ya harara yace tashi kije ki cema ammyn mamy ta gama shiryawa?
Sai ko mumcy tace "haba son meyasa kake hakane? Bata da suna ne? Sai kayi gaba sai ka dingayin baya ,yau ka canja gobe ka koma Ruwa.
Sai yace "Kai uwa ta gari toh husuna take ko Asuma'uu tashi kije ki Tambayo Ina magana kunata bin mutum da Ido.
Jin ya dai Kira sunan ko Yaya sai Husna ta mik'e ta tafi fad'a mata.
Chapter 53 · 0% Book details