← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 95

Sashe 6

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Can ya tuno da wani wulak'anci da ze Mata ,sai ya d'au phone nashi ya dailing numb momcy shi ,Bayan ta d'auka ranta har ya d'an Mata wasai ,tayi shiru tace ya akayi son?

Yayi ajiyar zuciya ba yadda momcyn zata jiyo ba ,yace "momcy yau ko Arzikin gyaran samana ban samu ba kinata big bro kin barni cikin dirty ?

Murmushi tayi ,kamar Yana kalon ta ,tace barin turo Ma'u ta gyara ma , _if u like it?_ Da izza d mugunta a ranshi yace toh ! Turo wawiyar ....ya kashe Kiran.

Jin furucin shi na karshe yasa momcy _deciding_ inta bar Ma'u zuwa Mai gyara ita kad'ai _definitely something must be happing wihch is embarrassing_ da ze fito from FU'AD to Ma'u Dan Haka atunani da sanin ya kamata irin na momcy sai ta deciding sake Kiran shi don ta bashi umarnin sakowa kasa Don ma'un taji dad'in Aikin ta hankali kwance ...

Koda momcy tace y sako ,sai cewa yayi tazo tayi aikin ta shi Yana wani abune a sama _which is important_ yanzu sai ya Kamala zai sakko .

Momcy tace toh ,gata Nan ,yayi kwafa ya cigaba da duba wata tablet dake hanun shi .

Momcy Kiran Harri tayi da ma'u tace suje su gyarama Son sama Dan ALLAH tare in sun kammala su sakko su cigaba da Abin da sukeyi ,babu musu ko shayin komai Amman dai Ma'u ba Haka taso ba ,Amman ganin harda Hari Kuma babu mutsu ko gardama tsakanin ta da hajiya babba sai kawai ta amsa suka nufi saman nashi ..

Suna zuwa ,ma'u tayi sallama ,harri Kuma ta kwankwasa ,Jin muryar Ma'u yace " _dirty girl_ asamu shigowa Dan nasan ba wani _come in_ ma Kika sani ba yadda kike _empty head_ d'inan ....

Suko Jin furucin shi beba kowa daga cikin su dama Shiga falon ba sai kallon kallo da sukema junan su kowa na tunanin dashi ake ,ita dai ma'un tasan da ita yake Dan har ranta taji zafin furucin nashi amman sannu Bata Hana zuwa sai dai adade ba'aje ba ,Bataso ta Fara mayar Mai da martani a matsayin yadda take a gidan su .

Jin shiru yayi yawa ,ya wani daka Mata tsawa dallah in bakiga Daman wanke toilet d'in bane ki koma ki sanar ma wacce ta turo ki ,kina taremin hanyar kofan falon ...

Ganin ze cinye su d'anye babu shawara kawai Harri ta Fara Shiga Bayan ta bud'e falon bakinta d'auke da sallama ,sanan ma'u ta Rufa Mata baya ,kafin ma'un ta taho yimai Aikin sai da ta kirma wani yabud'odon hijabin ta mara galihu ta cire k'aramin Mai kyau ta ajiye sanan ta kirma wanan hijabin da ya b'oye kwaliyar ta .

Ganin Harri sai beji dad'in furucin d ya musu ba Kuma yaji haushin zuwan harrin Dan ta tare Mai wani mugun wulakancin d ya tanadarma Ma'u ...

Harri ce ta Fara gaishe shi ,sanan ma'u Yana hararta ma ya amsa tare da kwafa ,fuskar Nan kamar besan meye _smile_ ba arayuwan shi .

Ma'u har tayi hanyar _toilet_ Harri tace Bari na wanke Mai karki b'ata rigan ki Ma'u ,sai ma'un ta dawo Tana murna cikin ranta ,ga fargaban irin harara d mugun kallon da FU'AD yake Mata lokaci zuwa lokaci.

Karema rigan kallo yake ita Bata sani ba ,rigan d ake cewa karta Bata ,Bayan shigan Harri _toilet_ yace jari bola kenan wai karkiyi datti ,to meye marabar ki da dattin shi kanshi ? Ki Fara Abin d yake gaban ki ba abubuwan munafukai d kikeyimin Shiba yanzu ...

Ma'u babu musu ranta ab'ace ta Fara gyara falon ta kasa furta ko uffan Dan fargaba daga ita sai shi a falo...

Tanata aikin ta ,ta jiyo shi Yana waya d wani abokin shi cikin nutsuwa d Kamala kamar wata macce ,Yana cewa shi ai babu abin d ya tsana a duniya sama da *kuliya* Sam beson ko ganin ta acikin dabobi ita yafi tsana shi yasa ko inda take baya nufa itama Bata zuwa Dan ze iya kirga iya ganin shi d ita a duniya ...

Ma'u duk Tana jin shi ,tanata kisima wani Abu cikin ranta da koni bansan meye ba ,har suka Gama hirar d abokin shi ya kashe wayar .

Aikin ta yazo inda yake zaune Dan ,Haka cikin girmamawa tace yallab'ai Zan gyara wajen kanta a k'asa ..

Ya wani bita d kallon tuhuma ,waye yallab'an naki ? Me ? Yallab'ai , barin Miki gargad'i na farko Kuma na k'arshe ko a wawan mafarkin ki karki sake tsautsayi yasa ki k'ara gigin kirana d wanan sunan ,only ma'aikata nane kawai suke kirana da shi ,keko Ina Kika Kai matsayin yimin Aiki bare ki kirani da sunan ? Baki Kai ba bazaki Kai ba Kuma ,Ni wlh bansan meyasa momcy ta
_accepting d'in ki as_ Mai taimaka Mata ta wani b'angaren ba wlh , kawai kiyi aikin ki, ki fice min da gani Yana wani jifanta d wawan kallo....ya Mike y Shiga bedroom d'in shi hannun shi rige d _phone da tablet_ d'in shi .

Ma'u taji zafin kalaman shi ,ta sake k'aryata maganar hafeeza da tace wai yanada saukin Kai da kirki da iya mu'amala ,atake tace wlh ko 1 baida shi _totaly_ ma beyiba a Rayuwa besan hakkin d'an Adam ba sam ,ahakan yakeda ilimin addini sosai? Aiko indai yasan ayar da ALLAH yake cewa ya karama bani adama ko almajirin gidan Nan beze wulakanta ba bare ita d ba bara tazo ba Dan ta wuce bara duk da tasan ita ba wata bace ,Dan Haka ilimin shi baya amfanar shi Kuma ma itafa aikin Nan *RIK'ON KWARYA* Ne agareta Da Mai shi ta dawo zata sakar Mata abinta ta koma zaman ukubar gidan mama habee, can Kuma ta tuno da azabtuwar d tijarar mama habi sai Taji Rana zafi inuwa Kuna kenan duk d Haka gwanda gidan hajiya babba matsalan ta FU'AD ne kawai ,can ko harda su humaira ,sai d idon ta yayi yunkurin zubar da Ruwa ,sai Jin mgn harri tayi Tana cewa yi maza mu k'arasa mu sauka Ma'u ,da sauri ta mayar d kwalar ta amsa Mata suka Kama aikin hanu bibiyu kafin kace me sun gyare Mai ko Ina sai kamshi ne yake safa da marwa a falon d ko Ina ,besan sun sauka bama Yana bedroom d'in shi .

Ko da suka sakko Kan aikin su suka fad'a kad'an y rage a Kamala girkin ma Dan fin Rabin ya kammala .

FU'AD sak'on kamshine ya kaimai yasa shi fitowa falon yaga duk babu su y tabatar sun Gama ne ,Dan Haka ya zari makulin mota ya nufo k'asa batare d ya yabi gyaran ba ,acewar sa baze yabi gyaran ta ba Dan Bata Kai ba ,Yana sakkowa ya nufi inda momcy take zaune ya zauna Yana ce Mata saukan su Yaya kawai yake jira Amman kamar zuwa zeyi kawai jirgin y landing a gaban shi Dan Haka ya tafi d'auko Mata _first son_ d'inta ta musu fatan dawowa lpy ,cikin murmushi d iya zama da kowa da bama kowa hakkin shi tace adawo lpy ALLAH ya kaika lpy, su Kuma ALLAH ya kawo su lpy ku iso min gida cikin Aminci , FU'AD yace Ammen uwa tagari ya fice zuwa inda motar shi take ....

Maman shaheed ce dai👌🏻
[4/23, 4:00 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA*

_RUBUTAWA DA TSARAWA_
BY
*FATIMA ABUBAKA SHU'AIB*
(Maman Shaheed)

Pg 8

*Shafin Nan nakune masoyan RIK'ON KWARYA Ina mugun yinku kamar yadda kuke mugun yin RIKON KWARYA*❤❤👌🏻

FU'AD bai tsaya ko Ina ba sai _Airport_ befi minti 15 da zuwa ba jirgin su big bro ya sauka a makeken filin jirgin Aminu Kano .

Su Ma'u dasu Hari suna Kamala aikin komai sai Abin d ba'a Rasa ba na shirya wajen da za'a kwashi garar girkin ,hatta sashin da su big bro d'in zasu zauna an sake gyarawa an bade shi da turaruka masu dad'in Kamshi aka rufo musu .

Mutane nata sakowa daga jikin jirgi wasu turawa ,wasu bakar fata Amman da ka gansu kasan hutu d Jin dad'i ya ratsa su ,kamar yadda na hango big bro d'in FU'AD da hutu da Jin dad'i ya Gama canja Mai fatan shi,shida matar shi Mai kyau hanun su cikin na juna suna sakowa suna Hira cikin nishad'i da birgewa da salon soyayya Mai k'ayatarwa ...

Bayan sun karasa sakowa ,ya ciro waya da alamun yin Kira kenan yaga k'anin shi FU'AD yazo fuskar shi d'auke da fara'a da Jin dad'in Yana cewa gani Ina ta jiranku ai ,da sauri suka rungumi juna suna sakin wani murmushi na matsanaicin zumunci da ganin su kasan suna son junan su matuk'a.

FU'AD ne ya kalli matar big bro d'in yayi murmushi yace matar Yaya sannu da isowa kasarmu ta gado ,dafatan bakiyi fushi ba da na Fara kula big bro d'ina kafin ke?

Murmushi ta Mai ,sanan tace "ai wata kusan tafi wata kusan ,wariyar launin fata ka nunamin tun a Airport Tana kallon mijinta Tana wani narkewa kamar zatayi Mai kuka , kafin mijinta yayi mgn FU'AD yace "tuba nake banyi Haka don son Kai ba kema ai Tamuce munma fi ji dake Dan kamar canji akayi kece tamu, tace ba wanin Nan zakamin dad'in Baki ko?

Cewa yayi " yanzu aimin afuwa Yana had'e hanun sa a kirjin shi Alamar ban hakuri .

Ita dai cewa tayi ,naki wayon ,sai da Mijin ta yasa Baki sanan ta hak'ura , FU'AD yace aunty rigima kenan Yaya Haka kake fama? Yayan nashi yace Mata ai sai da rarashi , FU'AD yace hmmmm musamman taka ba ,yayan yad'an daki kafad'un FU'AD yace Kai wayasan Abin da zakayi ma , FU'AD yace hmmmm Babu Ni cikin wanan aikin wahalar da Kan gaskia ,yayan nashi y dinga yimai dariya da matar tashi suna cewa irin ku sunfi kowa ma..

Kayan jakankunan su aka Gama zuba musu a motar FU'AD sanan FU'AD ya jasu sai katafaren gidan momcy.

Hari da ma'u sun Kamala had'a wajen da za'aci abincin sun jere komai sun gyara ga kamshi Mai nishad'antarwa dake yawo a wajen ...
Chapter 6 · 0% Book details