← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 95

Sashe 47

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sai ko Husna tace banyi tunanin Dani kakeyi ba Dan banji sunan da baba yasa min ba sai shi yisa kaga ban tamka maka ba.

FU'AD wata muguwar harara ya wurga Mata yace hmmm yaro besan wuta ba sai ya taka da sannu Zan setaki _dirty girl_ zakisan waye FU'AD.

Babu Wanda ya sake magana sai da Husna taga ya Adana motar shi wani wajen da aka tanada Dan Adana motocin da sukazo siyaya wani katafaren wajen Saida wayoyi masu nunfashi ,Bayan ya adanata sai ya fito Yana Shan kamshi Yana bin Husna da wani mugun kallo ,Wanda yasa ta yunk'urin fitowa azaton ta magana yake Mata ta fito bakin be samu bud'uwa ba ,Tana Shirin fitowa taji muryar FU'AD na cewa "Ina Zaki ayawo? Waya kiraki ko kinyi ajiyane da zakije d'akowa?

Sosai ran Ma'u ya bacci ,sai cewa tayi banyi ajiya ba sai aike da nayi na gagawa Wanda ya zama Dole ga Wanda na aikan ,afusace FU'AD yace ke Ina Wasa dake ne? Na Miki kama da sa'an ki ? Me kike nufi?

Ganin kamar zai cakumo ta sai tace "Ni me nace , ALLAH ya baka hak'uri ban fad'a da wata manufa ba ,tsaki FU'AD yayi badan ya gamsu da Abin da ta fad'a ba ya nufi hanyar Shiga kata faren shagon siyar da wayoyin , iPhone 11 ya dankaro Mata ya biya ya had'o Mata da layi gud'a 2 ya fito a shagon batare da b'ata lokaci ba ,ko da ya dawo sai ce Mata yayi ke fito Nan yaci magani kamar me Shirin yin dambe ,Husna har ta Fara tunanin wanne irin tozarci ze Kuma yi Mata Kuma? Jikin ba kwari ta fito ,sai ya nuna Mata gaba yace ki zauna anan bawai Dan kin Isa ko Dan kin Kai ba Dan ma karki yaudari kanki ,sanan ga wayar da akasa na sai Miki ALLAH yasa kyauyancin ki ze barki ki iya Amfani da ita ya cillo Mata Kan cinyar ta ,sai ko tasa hannu ta d'auka zuciyar ta fal murna a zahiri Kuma Babu yabo Babu falasa sai dai godiya da Addu'a da ta Mai ,Tana cikin yimai godiya ne ya dakatar da ita yace kije kima wacce kikaci Albarkacin ta Amman bani ba Wanda d yinki da Bari duk 1 har gwanda ki Bari.
"Sai ko Ma'u tace wanan ai farilla ne Tata ta musammance ai ,sai yace ke Kika sani kidai tsaya iya Haka karki zarme Kuma wallahi kisan irin maganar da Zaki dinga mayarmin Inna Miki Abu inba Haka ba Zaki Gabe shayi daga Ruwa yake.

Husna Bata cemai uffan ba ta rabu dashi sai da suka kusa Isa gida yace Kuma aikwai sauran tamu dake Dan tsuguno be k'are ba sai kin amsa min wasu tambayoyi ,toh! Kawai tace Mai ta cigaba da kallon hanya har suka Isa gida wata magana Bata k'ara had'asu ba ,sai da y shigo harabar gidan ya ajiye mota a ma'ajiyar ta ya bud'e yayi ficewar shi yace Mata intaga wajen zama tayi ta zama shidai yayi gaba ,itama yunk'urawa tayi ta fito Tana cewa Bata min Kama da wajen zama ko yin wani abun nishad'i ba nida nakeda abinyi ,karaf akunnuwan FU'AD afusace ya juyo Yana tambayan ta Ni kike mayarma da martani tunda na Gama Miki komai na siya Miki wayar da ko mafarki Baki taba tunanin rik'ewa ba karshen ta har ki k'are rayuwarki ta gidan duniya Baki Isa rik'eta ba badan arzikin mumcy da ta had'ani dake ba ke kinsan karyar ki kice Zaki mallaketa shine zakimin rashin kunya a matsayin tukwicin wayar? Ganin Yana nufota sai tayi baya tayi nesa dashi Tana Shirin canja hanya ,shima k'ara nufota yayi ,sai ALLAH ya Aiko da aunty sa'adiya ta dawo daga wajen Mai yi musu guga ,sai ko tace ango da uwar gida outing Akan d'an fita ne?

Sai FU'AD ya sakar Mata fara'ar Dole ,a aunty daga Ina kike Haka? Sai ta sanar Mai daga wajen Mai guga take ,sai FU'AD ya gaishe ta ,sai Husna ma ta gaishe ta Tana cemata wlh wai munje siyan waya ne Kinga wayar da akamin kyautan ta kitayani godiya aunty na ta mik'a Mata tanayi Tana kallon FU'AD ta wutsiyar ido ,shiko ya d'auke Kan shi har ya Fara tafiya ya tsinkayo muryar aunty sa'adiya ,lalai angwangwaje k'anwar tawa godiya mara'adadi angon Husna da sanaya Sha alwashi kabada kanka asare kaje gida kace ya fad'i na sanaya da Asma'u bada mamaki ,murmushi yak'e yayi yayi gaba kawai ya rabu dasu ,itako Husna har part d'in aunty sa'adiya ta k'arasa suka gaisa da Aisha ta d'auki baby Mimi dake Aiahan ta kusa komawa k'asar su ta ghana saura sati2 ba wani jimawa yayi ba ta koma part d'in mumcy Dan nuna Mata wayar da d'anta ya siya Mata bisa umarnin ta ,Tana Shiga ta sameta ita kad'ai FU'AD har ya haura sama,Husna na Shiga ta ma mumcy barka da gida ta mik'a Mata kwalin wayar Tana ce mata hajiya wayar Nan tayi kud'i da yawa Ni da me k'aramin kud'i ya siyamin ma ta ishe Ni amsa Kira dai ba wani Abu ba hajiya ? Sai mumcy tayi murmushi tace "Banda abinki Asma'u shi yaga ze iya tunda ita ya shiya Miki kema sai ki Shiga yayi kawai , ALLAH ya Baki ikon Aiki da ita ta hanyoyin da suka Dace ALLAH yasa Alkhairinta ya rinjayi sharinta agareki ,Dan ita wayar Nan da kike gani Akwai sharuka atare da ita Akwai Alkhairi yadanganta game sarafata ,Akwai Amfani Akwai akasin shi atatare da wayar zamanin Nan sai dai mu daure mudinga Abin da ya Dace da ita ba sab'anin Abin da ya Dace ba ,jeki abinki kinji Yar Albarka ,sai ko Husna tayi Tama mumcy godiya da Addu'a ALLAH ya jik'an mahaifan hajiyan da mijinta baban su FU'AD ,sosai mumcy taji dad'in Addu'a ,Dan Haka take k'ara son Asma'u Akwai nutsuwa da sanin ya kamata .

**********
Mama habee na zaune taji anyi sallama da kamar bazata amsa ba sai dai ta amsa ,sai sukayi ido biyu da wata mata da tatab'a zuwa wajen ma'u tace ita 'yar uwar mahaifiyar ma'un ce wacce take Aure a India ,ganin ta da maik'o yasa mama habee fad'ad'a fara'ar ta kamar mayyar da taga nama, Tana Mata iso zuwa shifid'ar da tayi na wata tsohuwar tabarmar da kamar gadon ta taciyo wajen kakar kakar ta tsabar datti da tsufa ,sai ko ta kundumo ma humaira uwar ashar kamar wacce ta had'a nasaba da matuzawa wai ta kawo Mata dadumar baban su wacce yake zuwa sallar juma'a ,ganin rawar jikin mama habeen yasa humaira sauri ta d'ako ta shin fida Mata har ta Fara zama ma aka dakatar da ita ,Bayan sun gaisa take Kara Mata bayanin kanta inta aunty huwailan Dan da mama habee Bata Gama gano ta ba tadai sheda fuskar ,Jin wacce ake nema ya sa tad'an rage fara'a tace ta zab'i Aure ai Akan zaman gidan mahaifinta Tana can tabi namiji tabar babanta yanata fama da bak'in talauci ,sai ko aunty huwailan tace Aure ma'un? Humaira tace sosai ma kuwa Tana can da wani Wanda ko sanin asalin shi ba'ayi ba ko d'an mafiyane ko waye ohon Mata ita tace Taji ta gani ,sosai aunty huwailan ta fahimce zancen su akwa shagube da son Rai gami da hassada aciki ,Amman bazata tabbatar ba har sai taje sunyi magana da Ma'u Dan Haka tace a rakata gidan Ma'u , humaira har ta kusa sub'utar Baki tace Suma Basu San gidan ba ,sai mama habee ta Mata magana da Ido tace Basu sake zuwa gidan ba tun kaita da sukayi itace ta k'ular dasu har yau batazo ta gaishe da mahaifin taba har Yana gab da yafeta ,sai ko aunty huwailan tace ba'ayi Haka ba ,yanzu dai ya za'ayi nace wajen ma'un na Mata tasa Dan tayi Aure har ta Fara wofantar da mahaifinta Haka ya zama Dole na Mata wankin babban bargo Tana musu dabara Dan su kaita gidan ,sai ko sokwayen sukaji Dadi mama habee tace ki Bari Gobe sai a rakaki ,sai aunty huwaila tace ALLAH ya kaimu goben barin tafi ,mama habee tace sai goben inkinzo ,sai ta zaro 5k taba mama habeen ta karb'a hannu na rawa ,ta Mata godiya ,Bayan ta fita aka zageta wai matsiyaciya ta Rasa Abin bayarwa sa dubu biyar kacal sai kace wacce ta d'aurawa tsiya zani ,sai ko mama habee tace meyasa ma na karb'a ne ,ungo mayar Mata da kayanta ko ruwan leda tasa shegiya ,sai ko humaira ta karbi kud'i zata Mike ta Kai Mata ,sai Mama habee ta wafce ta bige hannun humaira ,ke bakisan gatse ba Dan ubanki memakon ki hakurtar Dani kin barni sai balok'ok'o nakeyi har da karbanki Zaki Kai Mata tunda Baki da tunani Dan jakar uwarki ,Yar kundun uba Banda bashin da iliya Mai kanti yake bin mu da kin mayar Mata da kyaci bantan ubanki muga ko ubanki zamu siyar mu biya Dan kinsan uban ki ba biya zeyi ba zece ai ba'ayi shawara dashi ba wajen ciyowa ,sai ko humaira ta keb'e Baki tace "bake kikace na mayar ba ai da Amfani zanyi dashi Dan bazanga samu Naga Rashi ba mama ,sai ko mama habee tace macuciya to bazakici sisi ciki ba tashi ki kaima iliya dubu uku ciki mu Fara rage Mai ta wurga Mata tace wanan ma biyan bashi zanyi ,humaira ta Suri kud'i ta fice Tana cewa wallahi 2500 Zan bashi Dan said naci wani Abu Nima ,sai mama habee take me kike cewa Dan ubanki kike magana ciki ciki meye Kuma wani tufayin? Fadi da hausa Dan kanuwar ubanki ? Humaira tayi waje tanama ta dariyar wai tufayin matsalar kyauye kenan......
[4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA*

```RUBUTAWA DA TSARAWA```
BY
*FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB*
( Maman shaheed)

💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥

Pg39

Mumcy Bata falon ganin Husna Bata samu mafaka ba tanajin motsi a kitchen sai ta fad'a."

FU'AD biyota yayi yaga Babu kowa a falon yayi zaton wajen mumcy ta shige Dan Haka be tsaya bi takanta ba yayi part d'in sanaya Dan tun d'azu tace tanason magana dashi, be Bata dama ba sai yanzu ya tuna shine ze je."
Chapter 47 · 0% Book details