Sashe 34
Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sanaya ma da masifar dady da na mamy ta samu tasaka leshin da mumcy ta d'inka musu ,ba wani kwaliya tayi ba Dan tace bataga Abin kwaliya a Auren ba ,dama ba gwanar kwaliya bace ,Amman kayan sun amsheta duk da dama tanada kyanta dadai nata .
Sosai gidan ya d'inke da jama'ar mumcy da ta gaytata ciki har da su hafeeza da kawayen su Ma'u da humaira da suka zage jiki suka dawo don aci uwar sabada da su ba tare da sanin humaira ba Dan da sai ta biyo su .
Sosai suka gwabji arziki sukaci suka Sha harda guziri suna k'ara yaba sa'a da Ma'u ta tabka .
Ma'u sai da ta canja Kaya kusan set 5 sanaya ko d'akyar ta canja 2 sai da mamy ta dinga had'ata da dadyn ta sanan.
FU'AD ma da taimakon su Ahmed da masifar da Yaya Jameel ya Mai yasa ya canja kala 3 ....
Sosai akasha taro da su gabatar wa har had'a ango da matansa sai da akayi fuskar Nan ta FU'AD Babu annuri Sam acikin ta ,sanaya ko fuskarta fes take kallon kowa duk da Babu ko alamun murmushi itama , Ma'u ko Babu Mai ganin fuskarta ma bare yacce idon ta k'iri da muzu Akan jama'a ,Dan Haka mutane suka dinga Mata shedar tafi amaryar kunya da kamun Kai ,karaf a kunnen mufeeda da mamy Dan Haka mama tayi saurin yima sanaya sakwan karta kwana a wayar ta Akan da bi al'ada ta rufe fuskar ta ,Amman Sana tayi burus da maganar mamyn ,sai magana mamyn take Mata da ido harda nuni da hannu ,sai ta mayar Mata da itafa zafi take ji weather Akwai dumi na 9ja bazata takura kanta ba ,Haka Dole mamy ta rabu da ita .
Sosai bikin yayi armashi don anyi nasiha anyi jawabi Akan zaman Aure da biyaya cikin Auren , mumcy tasa FU'AD yima mutane godiyar Dole na hallartan taron da sukayi na shi shida matan shi daga k'arshe ya musu fatan komawa gidajen su lpy badan yaso hakan ba sai Dan bin umarnin mumcy Dan yaga ranta ya baci sosai ne .
Sosai taro yayi armashi ar mutane suka Fara watsewa mumcy nata Basu Abin da ya sawak'a da musu fatan Isa gida lpy .
Su Kuma kowacce ta koma inda yake mallakin ta amatsayin ta na matar FU'AD .
Kowa ya watse gida ya rage daga 'yan ciki sai tsirarun bak'in mumcy .
K'arshen tika tik yau dai ta faru ta k'are ,yau ne FU'AD ya d'auki Al'k'awarin karb'an sanaya amatsayin matan shi ,Dan Haka ranshi yau yafi na Koda yaushe b'aci gashi babu gudu babu Jada baya ,Dan Haka tun wuri mumcy da Yaya Jameel suka Fara Mai tuni uwa uba Alhaji Yaya da Yamai magana shima ,sai ko FU'AD yace ya sani ....
Mamy ce taje tace ma sanaya y takeso a raba kwana? A Fara da ita ko afara da Husna kamar yadda taji suna Kiran ta? Sai ko sanaya tace suje can su k'arata Ni ko bezo ba daidai ne agareni sai ko mamy ta rufeta da fad'a Tana cewa ya zata dinga maida kanta ba duk Abin da ya biyo baya ita ta sani Kar tayi kuka dasu sunyi iya yin su wajen kwato Mata 'yanci Amman har yanzu tak'i ganewa ,Dan Haka saura ya rage nata ,ta fice taje tacema mumcy FU'AD ya Fara Shiga d'akin Husna kawai ,sai ko mumcy tace toh ,cikin ranta tace dama ai ita aka Fara d'aura mai Aure da ita Dan Haka daga kan uwar gida za'afara raba kwana ba Amarya ba Amman sai ta bita da toh kawai.
Mumcy ce tasa aka Kira Mata FU'AD ta gagauta bashi umarnin kaima uwargidan shi ziyara ,da gargad'i Mai zafi Akan kartaji Kar ta gani ya wulak'anta ta ko ya tozarta ta ,ya d'auketa matsayin umarnin ta ,bin umarnin ta gareshi Kuma biyayace da sakayyar da ze nuna Mata Akan reno da Tarbiyar da tamai tun haihuwa shi har kayau ,iya tukwicin daze Bata shine karb'an kyautar da takai na auramai Asma'u ,sosai tamai fad'a Akan yin adalci tsakanin su ,Yaya Jameel ma ya k'ara Mai da rarashi da ban Baki da nasihohi masu shiga jiki ,sanan ya tafi wajen sa'adiya .
FU'AD ya tashi zai fita jikin shi duk Babu kwari Kuma ya kasa tofa ko ufan ,har ya fita falo ,besan mumcy Tana biye dashi ba taga yayi hanyar waje alamun ze fita cikin dare ,sai ko mumcy tace Ina zuwa Kuma? Cikin alamun na rashin gaskiya yace "zanyi waya da su B2k ne ,sai ko mumcy tace dawo Nan kayi wayar dasu sanan ka haura sama ina gani in Kuma sallama zakaje kayima sanaya to ? Da muryar takaici yace ai na Mata sallama , mumcy tace "ka kyauta " ba shi da zab'i Dole ya d'aga waya ya Kira B2k Yana lek'awa yaga ko mumcy ta koma yaga Bata da niyar tafiya ,sai ko B2k ya Fara cemai Kai abokina yaufa ranar kace sai inda ka zab'a meye na kirana Ni ban dameka ba Kai zaka dameni Kar kasa matanka su Fara tsana ta fa suce na Shiga hakkin su "FU'AD ne ya katse shi da cewa dalla mallam Ni ka kawo min sak'on Nan Ina jiranka yanzunan ,sai ya kashe wayar ,shi kanshi besan wanne sak'o B2k ze kawo Mai ba ,Haka shima B2k tunanin duniya ya Rasa wanne sak'o ze kawo ma FU'AD d'in can dai yace Dan iskan abokina kodai k'unshin da ango yake shigar ma Amarya dashi yake nufi Dan tun d'azu nake Mai magana Yana basarwa to yanzu ya kasa shigane inaga ,barin juya mota na taimaka ma Daren angon cin shi Dan ALLAH da Amarya badan shi ba ,mutumin kawai ,abaka Mata biyu zuk'a zuk'a asauk'ake Amman ka tsaya kana yawa kana waskewa ,mutumin kawai .
Cikin sauri B2k ya faka motar shi inda ake Gaza dakwalen kaji masu kyau da tsada ga dumi komai yaji atare da su ya siyi gud'a 2 ya hada musu da fresh milk Mai sanyi sanan ya nufo gidan su FU'AD" mumcy dai ta kafa ta tsare Tana jiran sak'on FU'AD ko zuwa ya karb'o Bata yadda da hakan ba Tana jira B2k ya shigo har ciki ya kawo Masa ya juya shima ya nufi wajen baccin shi ,sun d'an Sha jira ba laifi sai ga B2k shima be wahalar da kanshi ba wajen tsayawa Kiran FU'AD cikin gidan ya shigo kawai yayi sallama mumcy ta amsa sai B2k yaji kunyar ta da nauyin ta ya har'iye tsiyar da zema FU'AD d'in ,ya k'ara gaishe da mumcy yaba FU'AD sak'on yace shi ze wuce sai sunyi waya ko? FU'AD Yamai godiya duk da besan me B2k ya kawo Mai a matsayin sak'on k'aryan da yayi ba .
Sai ko mumcy tace "maza ka haura sai da safe , ALLAH ya tashe mu lafiya ,bashi da zab'i Dole yaja Leda ya tafi saman ledar da yaso barinta ma a wajen Dan Kar yasake jama kanshi magana ne yasa ya tafi da ita duk da baya tunanin Akwai amfanin da zata Mai .
Sai da mumcy taga ya bacema ganin ta har tajiyo k'arar bud'e kofa sanan ta koma nata d'akin .
Koda FU'AD ya Shiga da sallama Dan Al'adar shice ko Babu mutum ciki yakanyi sallama in ze Shiga ,yaji ba'a amsa ba yasa Kai ,yaga Babu mutum a falon Dan Haka yasa Kai zuwa d'akin shi ya ajiye ledar ya fad'a gado cike da tarin tinani kala kala ,sai can ta d'an shafo ledar da B2k ya kawo Mai sai yaji dumi ,sai yace "baringa Abin da Dan rainin hankalin Nan ya kawo min ,Koda ya duba yaga dakwalen kaji namai disko ,sai ya ja gajeren tsaki ,yace "Dan iskan banza Abin dai Yana ranshi ya Gama nacin naki kulashi shine da tsautsayi yasa na kirashi shine ya aiwatar da manufar shi?
Jan ledar yayi ya nufi kitchen ya d'auki 1 kazar yasa a plate y d'auki fresh milk 1 yabar sauran a ledar ya nufi inda yake hasashen anan amaryar mumcy take ,ko da yayi sallama cikin wata zazak'ar murya yaji an amsa ,har ga ALLAH muryar ta d'aki kunnen shi har zuciyar shi ,Kuma Yana tunanin kamar ya tab'a Jin irin muryar ,Amman gajartan lokaci be bashi damar tuna inda yasan ko ya tab'ajin muryar ba kawai ya Shiga ,yace kina lafiya amaryar mumcy?
Ma'u ta jinjina Abin Aranta ,amaryar mumcy Kuma? Shine sunan da kamin d'an rainin wayo? Hmmmm sai tace "lafiya Lau nake mijin Mata biyu ,shima sosai ya Jin jina sunan ,zece wani Abu Amman lokacin bana tatauna wani Abu bane balle su kaiga sa'insa Dan Haka ya mik'a Mata leda yace gashinan sai da safe ,har yace bakin k'ofa ta ce "ALLAH ya bamu Alkhairi ya Kuma kaimu muna masu kosashiyar lafiya, hankalinta kwance ,sai muryar ta dinga Mai gizo yaso ace yaga fuskarta kafin yabar d'akin ,Amman in ya tuna da yadda akayi Auren sai ya fasa ,ya fice kawai zuciyar shi fal tunani .....
Maman shaheed dinku ce👌🏻
[4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA*
```RUBUTAWA DA TSARAWA```
BY
*FATIMA ABUBAKAR SHU'AB*
( Maman shaheed)
💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥
Pg 30
Sosai muryar Ma'u Ta Dinga dawoma FU'AD adodon kunen shi ,gashi ya k'aryata kinen shi da cewa muryar zak'i tamai ,sai ma neman kushewa da yayi Kuma cike da son ganin fuskar mama lakiyar fuskar ,da kyar ya samu yayi watsi da tunanin da yake neman addabar zuciyar shi ,ya samu ya kwanta.