← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 95

Sashe 15

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan baba sun Gama gaisawa ,ta d'auko kud'i taba baba yak'i karb'a sai da ta dinga had'ashi da ALLAH sanan ya karb'a mama habee Ashe Ana lab'e sai ji sukayi tace asara yawun bacci ,girma ya fad'i Rak'umi ya shanye Ruwan 'yan tsaki ,Dan Haka aka dawo ai ,duk sun jita Kuma sun gane manufarta ,itako azuciyar ta haushi taji anba baba Abin da ta dinga sa rai ita ta samu sai gashi ya tsalaketa ,baba ya mata godiya da fatan Alkhairi yace zai wuce kasuwa ALLAH ya maida ita gida lpy ,Amman duk d Haka ta rok'i baban Kan Ma'u ta kaima hajiyan su ziyarar bazata ko ta Rana 1 ce ,inta karb'eta a jika to inbata k'arbe ta ba sai su fawalama ubangiji su barta da halinta , da kyar baba y amince Akan wata Rana Ma'u zata insha ALLAH ,sosai huwaila taji dad'i don Tana son farfad'o da zumuncin su ,taso ace a k'asar take Aure da tafi kula da Ma'u .

Bayan tafiyar baba ,aunty huwaila ta dinga ma Ma'u tmby Akan karatun ta da matsayinta yanzu duk ma'un ta Gaya Mata tunda ta gama junior section Bata samu taci gaba ba ,islamiya ma kud'in term ne ya hanata zuwa har na term 2 sai ta magriba da take zuwa tunda ita kud'in laraba kawai ake biya .

Aunty huwaila ta d'auko kud'i ta Bata har da wata jaka Mai d'an girma tace situru ne aciki harda gyale da hijabai ta k'ara ta dinga Amfani dasu ...

Sun d'auko jakar sun bud'e Ana dudu ba kayan ,sukaga alamun Ana musu lek'e ,har aunty tace ko abari sai ta tafi ta duba ,ma'un tace ai ko kin tafi innatafi Aiki za'azo Amin bincike gwanda yanzu a Gama gani afi kyaleni na huta ,sanan suka Gama bud'e kayan gaba d'aya ,Kaya basuji jiki ba masu kyau da tsari har da takalma set 5 masu kyau ,ma'un nata godiya Tana Mata Addu'a.

Sun Jima aunty huwaila na Mata nasiha da ta kula da kanta ,aikin nata ma ta rik'eshi da daraja ta rike mutuncin ta Kuma ,karatu kuma ta dage ko da kud'in aikin ne ta dinga taimakon kanta ,duk ta d'auka tamata godiya Kuma taso ace ciki d'aya aunty huwaila suka fito da mahaifiyar ta tasan da batayi maraici ba ,Amman ahakan ma ta godema ALLAH.

Sai daga baya aunty huwaila tace zata tafi , Ma'u badan Taso ba ,ta tafi rakata har bakin hanya sanan ta dawo kud'in da ta Bata Yana soke ajikin ta.

Koda Ma'u ta koma da sauri taga an Shiga d'akin ta ,koda ta Shiga humaira ta gani Tana d'ad'aga kayan da aka Bata , sai ta zuba Mata ido kawai ,da sauri humaira ta juyo Jin motsi a Bayan ta ,suna ido hud'i da Ma'u sai ta saki kayan Tana inda inda , ma'un tace ya akayi Yaya humaira ?

Sai humaira tace ,dama murna nazo tayaki kayan sunada kyau wlh ,ki bani aron wanan doguwan rigan naci bikin afifa baby dashi Dan kinsan doguwan Riga za'asa a Arabia night din ,Ma'u tace d'auki Yaya humaira kima ajiye a wajen ki kafin jibin ,humaira gwuiwa Babu kwari ta karb'a ta fice ,itako Ma'u ta Mata hakane don ta saurara karkuma ta sake zuwa Mata bincike don ta Mata Abin d in itace bazata iya mata ba ..

Humaira na Shiga ta cillar d doguwan rigan a gadon mama habee da yaketa neman agajin a gyara shi ko yayi hankali,mama habee tace kyauta ta Baki? Humaira tace aro dai kamani tayi fa Ina Mata bincike ,shine na wayance da aron rigar ,Kuma wlh Akwai kayan d sukafi doguwan rigan kyau Amman na tsaya a ita ,shegiya wlh ta samu Kaya masu kyau da tsada ,mama habee tace Yar banza ba Dole ta Baki wasu ai Naga wata Riga da wando ma cikin d'akin jiya zasufi dacewa dake ,kice ta Baki intak'i kimin mgn sai na tursasa shegiya ,humaira tace toh ,mama habee tace kema kece Mai tsinannen Baki duk wani kud'inki ciki yake tafiya acici mala'ikun tauna kinba kwad'ayi da had'ama dama ,shiyisa Baki da Abin arziki sai na tsaiya , humaira ta turo Baki tace "Zaki Fara Kuma ko mama? Mama habee tace ai gaskiya na fad'a ...

Ma'u ta gama kaiwa k'arshe akan tunanin Abin da zata ma FU'AD da zaiji har ransa kamar yadda taji itama ,sai tsoron abinda zai je yazo da takeyi ,Amman t k'udiri aniyar aiwatar da niyar ta inba Haka ba bazata huce ba ......

*Maman shaheed ce*👌🏻
[4/23, 4:00 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA*

_RUBUTAWA DA TSARAWA_
BY
*Fatima Abubakar Shu'aib*
(Maman shaheed)

_shafi na 16_

*AFUWAN INADA EXAMS GOBE DA JIBI SO BAZAKU GA POST NA RIK'ON KWARYA BA SAI MONDAY ZAKUJINI INSHA ALLAH*

*INA BUK'ATAR ADDU'A KU AKAN EXAMS DIN DA ZANYI ABIN ALFAHARINA FANC*👏🏼👏🏼

Washe gari Ma'u ta saka wata doguwan Rigar atamfa ya d'an Mata yawa Amman ba sosai ba ,ta zabo hijabi cikin kayan dai da aunty huwaila ta Bata ,ta zura ,ta Adana kayanta a jaka tasa kwad'o ta rufe ta tafi da can akulin ta saboda tsaro badan tsoro ba ,dama ta gama ragema mm habee wani aikin,sanan tayima baba sallama ,ya mata fatan samun nasara atafiyar ta da dawowar ta ,sanan Tama mm habee ,Aiko tace "ba ya Miki Addu'a ba shi Wanda kike zaman shi ? To ai ba sai na Bata Baki ba absnza da wofi ,ajuri dai zuwa Rafi wata Rana tulu zai fashe ,Ma'u Bata ce komai ba ta ficewar ta haidar na Mata baibai Yana jikin baba .

Bayan fitar Ma'u fad'a baba y Fara yima mm habee ,Amman ta Fara tsagalgale shi ,dake tace ne sai yayi Mata shiru danma yanada addini yasa wani aikin intayi baya Kama shi ,shida yarsa Ma'u da ta tsole musu ido ,Amman mama habee ba a zaune take ba ..

Ana d'an kunge kunge ,Dan ko mahaifiyar Ma'u Tasha fama sosai .

Ma'u cikin Kamala ta d'au hanyar zuwa gidan momcy ,Koda tayi tozali da motar FU'AD taji fad'uwar gaba matuk'a Amman Haka ta k'arasa falon cikin sallama da nutsuwa ,Babu kowa sai motsi d tajiyo a kitchen nasu Hari Dan Haka kawai sai ta nufesu don su gaisa .

Bayan sun gaisa Tana ta tayasu d wani aikin ,can sai ta jiyo motsin momcy a falon ta fito sai ta tafi Dan kwasan gaisuwa ,har k'asa tsuguna ta gaishe da hajiya ,hajiya ta amsa fuska asake Tana tmby y jikin ta ,sai ga FU'AD sakko cikin Shirin tafiya office Yana ma momcy mgn cikin sakin fuska da Kamala .

Ma'u ce ta gaishe shi ,Amman sai yayi kamar beji ba Kuma yaji ,sai momcy tace "haba son bakaji ne Ana gaishe ka ko ta daina ne ? Sai y yatsuna fuska yace "Ni banji bama attention d'ina Yana ga uwa ta gari ,lpy shike Nan Yana kallon wajen da aka jere Mai break d'in shi ,sai ya doshi wajen Yana cewa momcy kizo muyi breakfast pls Kar na makara ,itako momcy mamaki ne ya Kama ta sai d tace "son" yace "naam? Sai tace "Zo" da yazo ta nuna Ma'u tace haba kamar ba d'an musulmi ba Kuma Dan hajiya ko ka tmby yarinyar Nan jikin ta? Bayan kaine ummul'aba isin sakata cikin yanayin Koda bada son ranka bane ai ta cancanci ka Mata sannu duk d ta samu sauki .

Sai yace ,ayya n manta ne ,Zan kiyaye gaba momcy ,sai ko yasa Kai zai tafi ,momcy tace "son wlh inbaka ma yarin Yar Nan sannu da jiki ba wlh sai ranka ya bacci ya Ina nunama annabi kana runtse ido ,musulmai muke fa ba kafirai ba ,haba ne ? Banason wanan Halin beyi daidai da naka ba Sam ka sake ,kabi umarni Kuma ko kaga Aiki d cikawa yanzun Nan.....itako Ma'u kanta a k'asa tanajin dad'in yadda ake tursasa FU'AD akanta .

Ganin momcy da gaske take ,sai y Bata Rai yace "ke sannu ,y kinji sauki ai ko? KO tsayawa yaji amsar da zata bashi beyi ba ya wuce zai haura saman shi .

Ma'u tace , Alhmd naji sauki ,Tana Mai dariya cikin ranta ..

Momcy ce tace son Ina zaka? Yace sama Zan d'auko jakana ne ,sai momcy tace "oh Dan nama gyara shine kayi fushi da breakfast? Sai y Kama inda inda zai wayance ,sai momcy tace "Zo nan mu karya in kaci ka fita ka amayar dashi kaji ko ? Zo ka wuce ,Dole ya dawo ya wuce wajen kayen abincin ,momcy tace "ma'u taje ta gyara Mata d'aki ,da sauri Ma'u tabi umarni .

Momcy ce ta dinga lalab'a FU'AD Tana Kuma k'ara Gaya Mai gaskiya ,sai cewa yayi "shifa Abin d y sa shi Jin Babu dad'i fad'an d ta dinga Mai gaban kazamar Nan ,kamar wani yaro menakon abayan idon ta ? Ai sai ta rainani momcy ,momcy tace yo to raini na nawa tunda baka Jan girman ka Kuma Tana baka girman ka ,kabi ka tsaneta Kuma ta sani ,sanan tsautsayi yasa ka sumar da ita kace Mata ya jiki kawai bazaka iyaba ,bansanka d wanan Halin ba wlh ,indai baka gyara ba zamu dinga kwasan 'yan kalo gaskiyar mgn .

FU'AD yace ,to Zan gyara ,Amman duk kuskuren da zanyi Kar ki min fad'a agaban ta Dan ALLAH ,Ni dake sai kimin fad'an ,Amman .....momcy tace "meze Hana ka kiyaye duk Abin d zesa namaka fad'an ? Yace "Zan kiyaye ,itama ta daina Shiga sha'ani na ta dinga bin umarni na ,momcy tace "Ana jika dai , ALLAH ya kyauta ,kayi sauri ka Gama ka tafi ,yace ,Ni nama Gama ,kice ta gyara min sama Kar na Mata mgn kice nayi wani abun ba daidai ba ,barin d'auko jakana .....

Ma'u cikin lokaci k'ank'ani ta kammala komai ta dawo falo ,shima ta gyara ,momcy tace ta gyara saman FU'AD ,shima ta tafi ta gyara ..

Sa'adiya ce to shigo ta gaishe da momcy ta umarci Ma'u tazo ta tayata gyaran sashin ta ,momcy tace to Asma'u Babu komai Zaki iya ko Harri taje? Sai Ma'u tayi murmushi tace Zan iya hajiya ,sanan suka tafi .
Chapter 15 · 0% Book details