← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 95

Sashe 50

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Husna ko tinani ta dingayi Akan kalaman FU'AD ,taso ta gaskata ya Fara kishinta duba da Abin da ya faru tsakanin ta da B2k ga yanzu ma da taji wasu kalamai daga gare shi duk da ba afili ya furta ba Kuma sanaya ce ta sashi yin hakan amatsayin ta na me kishi akan FU'AD d'in,Amman Tana karyata kanta wani lokaci na cewa FU'AD baya sonta Kuma baze sota ba Tama sani.

Sanaya sosai taci kukanta ta k'oshi kafin ta samu tayi waya da mamynta ta tsara Mata yadda zata billomai ,taji ta d'auka tace zuwa gobe zata aikata sai taji daga gareta.

Sosai charting da aunty huwaila ya gusar ma da Husna duk wani tunani Mai kyau da Mara kyau da yake cunkushe a kwanyar ta ,taji dad'in hirar tasu har aunty huwaila take nuna Mata yadda zata zauna da su mama habee ta Kuma sheda Mata jibi zata koma indiya bazata Sami Daman dawowa ba saboda Akwai Abu Mai mahimmanci da zata gabatar Gobe ,sosai Husna ta Mata fatan Alkhairi tace ALLAH ya dafa Mata akan Abun da tasa a gaban.

Aunty huwaila Bayan ta wuce a mota ta koma gida kwana tayi Tana wasu mafarkai Akan matar da take cewa su Taimaka Mata Tana Kuka ,da safe da ta tashi cewa tayi Dole seta je taga matar Haka kawai taji Tana son Taimaka Mata inda Hali hakan atare da ita Dan Haka taje har gidan mahaukatan ba tare da kowa ya San taje ba daga gidan hajiyar su ,ta Jima Tana kwatance da dogon bayani kafin suka gano matar ,sai da Tasha Tambayoyi Tana basu amsa da Alkhawarin Taimaka mata kafin aka Bari zata gana da maralafiyar Mai rangwamen hankali."

Tun da aka Taho da maralafiyar k'irjin aunty huwaila yake luguden bugu har aka kawota gabanta be Dena ba ,sosai aunty huwaila ta kad'u hantar cikinta ta kad'a da tayi tozali da da maralafiyar Dan sai da ta zabura ,ma'aikatan sukace ko ta Santa ne wani lokita (Dr Junaid)da wata mace ?

Da kyar aunty huwaila ta seta nutsuwar ta tace "A kawai tausayi matar ta Bata har ta karajin Tana so ta taimaka Mata."

Sukace kuma matsalar ta ba babba bace sai dai Akwai tsanani cikin matsalar ta gami da sark'ak'iya saboda ba hauka takeyi tuburan ba ga kuka da take yawan yi maganin akeyi babu fashi Amman sai aga ta Fara samun lafiya sai aga Abin ya dawo har daga waje Ana kawo Mata magani Ana Mata afmani dasu Amman har yanzu sauki be Gama zuwa ba ga wani hamshakin Mai Arziki da yake Taimaka Mata Yana k'ok'ari da Aljihun shi da jajircewar shi duk Akan ganin lafiyar ta Amman har yanzu.

Sai aunty huwailan tace "ya suke da Wanda yake Taimaka matan?

Sai likitan da yake kula da ita yace "babu wata alak'a tsakanin su shima bigeta ya kusayi da mota ALLAH ya rufa Asiri shine yaji Yana son ya Taimaka Mata ,shine yake Mata magani da dukiyar shi har yanzu da kina Nan ma jibi zai Zo akan maganar maganin ta......likitan be Gama magana ba wayar shi ta d'auki k'ara ya fita Dan Amsawa."

Sai Aunty huwaila takai dubamta wajen matar da suke tare da Dr ma'aikaciyar gidan da take Bata labarin har daga waje Ana kawo Mata magani da sa hanun babban su na gidan ,sai ko aunty huwailan tace"Nima Zan iya kawo nawa maganin abata?

Sai ko matar Tace ,ai baza abari a Bata ba ,sai aunty huwaila tace saboda me?

Sai matar Tace "saboda dokar gidan ,Aunty huwaila sai cewa Tayi keko ki Taimaka min daga india Zan Aiko dashi ko ta hanun ki kinsan Haka kawai bazan cutar da ita ba me tasani ma da wanne zata ji da har zanyi mumunan kudiri akanta?

Sai matar Tace badaga mu bane Haka dokar gidan take Kinga Kuma a hakan suna haukan wasu sunada mumunan kudiri akansu saboda tsabar son duniya anyi case a gidan Nan har so ba adadi ,wasu ne suke kashe wasu inda da Hali kiyi hak'uri kawai duk da na yadda dake.

Sai aunty huwaila ta Fara Bata Baki Tana Mata Al'k'awarin kyauta mafi tsoka ,har ta Shawo kanta Akan in ta koma zata Aiko da magani daga india adinga Bata insha ALLAH zata samu lafiya.

Matar Taji kyauta ta Amince ,har sukayi exchanging na number waya su matar tace sunan ta hindatu ,aunty huwaila ma tace sunan ta huwaila a India take Aure zata Mata magana idan zata Aiko da maganin sai taje Airport ta karbo ta Mata Amfani dashi.

Sosai aunty huwaila ta sake kurama Mara lafiyan ido duk son ta da tagano Abin da takeson ganowa ta kasa Dole ta hak'ura ta tafi Bayan Tama hindatu d'an ihsani.

Washe gari FU'AD da wuri ya bar sashin sanaya ya koma nasu mumcy Dan hukunta Husna ,Koda yaje sai mumcy ya samu ze haura mumcy tace Dan ALLAH ya kyaleta ta samu isashen bacci tunda ta kwana da ciwon Kai jiya yanzu Haka bacci ta samu inajin kawai ka Mata waya anjima."

FU'AD badan yaso ba ya hak'ura ranshi Babu dad'i ,Harri ya Kira yace ta kawo Mai break din shi Nan ta kaima sanaya nata anjima shi da wuri ze fita ,har aka kawo Mai sunaci suna Hira har ya Gama yanata Saran ko Husna zata sako shiru har Yama mumcy salama tamai fatan dawowa lafiya ya fita."

Husna Bata sakoba sai da ta tabatar FU'AD yabar gidan ,har k'asa ta durk'usa ta gaishe da mumcy , mumcy ta amsa Tana tambayan ta jikin ta?

Husna ta amsa da "da sauki"
Mumcy tasa tayi break tare da nuna Kulawar ta ga husnan tasa aka kaima sanaya nata kamar yadda FU'AD ya Basu umarni.

Bayan Husna ta koma sama tayi wanka ,sai ga aunty sa'adiya da Aisha da sauri Husna ta karbi Mami Tana Mata Wasa ,sai Aisha take cewa kifin Rijiya kizo ki Rakamu store yanzu zamu dawo Amman in man d'in ki ya barki."

Sai Husna tace dama duk na gaji da zama waje Dayan kamar kin Sami ,sai aunty sa'adiya tace kizo muje je ki Tambayo k'anin nawa ,sai Husna tace "ai ya tafi office"

Sai Aunty sa'adiya tace meye amfanin phone d'inki?
Sai Husna tace toh barin Kira naji bataso Susan Akwai wani Abu tsakanin su Dan Haka kirjinta na lugude a zahiri shahada kawai zatayi sai ta kirashi Tana Addu'a cikin Ranta."

Yana D'agawa yace "Uwar Marasa kunya inajinki?
Sai Husna tayi ta maza tace "Dama Dan ALLAH aunty sa'adiya ce tace na Rakasu store......Bata Gama fad'a ba ya katse ta da cewa bazaki ba me kafar yawo zaman gida Baki Fara Shiba ma tukunna.......Husna d'auke wuta tayi na wani lokaci sai ta wayence da tari Mara sauti .....sai aunty sa'adiya tace bani k'anin nawa Naga ke soyayya zaku gabza Mana bani mu kashe boss d'in ta karb'i wayar ....

Sallama Tama FU'AD ,jin muryar ta FU'AD ya saki fara'ar Dole yace maman mami kun Gama shiryawa ne?

Aunty sa'adiya tace eh kanina ,Husna kawai muke jira idan ka amince in baka amince ba ta zauna muje mu dawo.

FU'AD yasan da kunya ya Hana Rakiyar sai yace To kuje Mana Babu damuwa na Baki amanarta sai kun dawo."

Aunty sa'adiya tace "insha ALLAH na d'auka ,nagode sai mun dawo.

Sosai Husna tayi farinciki ta karb'e wayar ta katse Kiran.

Atare suka fita Bayan Husna ta gyare baby Mami ta feshe ta da turare masu sanyin kamshi ta rik'eta sukaje yima mumcy sallama dama ashirye take fad'uwa tazo daidai da zama.

Mumcy ma fatan dawowa lafiya ta musu , mumcy nata ma Mami takwarar ta Wasa itako tanata bangala dariya ,har suka fita Mami na hannun Husna.

Sosai suka siyoma Aisha kayan tsara da zata tafi Ghana dasu Dan saura 3days ta tafi ,a store d'in Aisha ta had'u da wani Gaye Mai Aji da kwarjini da kyar ya samu ta kula shi har wasu siyayan ya Kara mata ,cikin girma ya gaishe da su Husna da aunty sa'adiya duk ya kirasu da Aunty's.

Bayan sun dawo gida sukaba mumcy Abin da suka siyo Mata na tsaraba a falon mumcy suka baje anata cin kayan kwad'ayi da suka siyo sukaba Harri takaima sanaya nata tunda batason Shiga cikin su sunjata Taki Shiga cikin su har sun Rabu da ita.

Husna nata tsokanar Aisha Mai new catch."

[4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA*

```RUBUTAWA DA TSARAWA```
BY
*FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB*
( Maman shaheed)

*ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*

Pg41

Sosai suka Sha Hira da mumcy kafin suka ci abinci aka Kira sanaya Taki zuwa ,sukaci nasu aka Kai Mata nata ,sanan su aunty sa'adiya suka koma part d'in su Husna ma ta haura saman ta.

wajen yamma lis sanaya tazo wajen mumcy kamar tazo Hira da itane Ashe tatace ta kawo ta.

Sanaya ce ta dubi mumcy "tace Dan ALLAH tasa Baki akan matsalanta da FU'AD na cewa bazataje Egypt ba Kuma da ya amince har Yana cewa ita da zuwa sai Nan da shekara da shekaru Dan tsabar ya kuntata Mata har da cewa Kam gidan Nan babu Wanda ya Isa ya sashi ko ya hanashi Akan maganar tafiyar ta ,har inace Mai har mumcy? Ya budi bake zece eh ,na dakatar da shi nace karyayi kuskure Dan uwa uwace ,sai sanaya ta barke da kuka irin na tausayi sai da ta tabatar su Husna da Aunty sa'adiya basa nan.

Sosai ran mumcy yad'an sosu a kalaman Husna na k'arshe ,wani bangaren Kuma Tana zargin FU'AD baze furta hakan a gareta ba ,Amman intayi tunanin yadda bayason Auren har yanzu biyaya kawai yakeyi sai taga ze iya firta hakan ko cikin fushine.
Chapter 50 · 0% Book details