← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 95

Sashe 42

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya k'ara had'ata da bango Yana cewa bazaki fad'amin ba uwar masu taurin Kai ?
Tana Jin zafin Amman Taki fad'a ,sai da ya k'ara had'ata da bango ta fahimci mugunta yake Shirin mata ,sai tace oho nace maka mugu kawai Tana Shirin yin kuka ,yace waima ke wacece tukunna? Ki fad'a min Dan yanzu ya k'ara tabbatar da zargin shi Akan yasan me irin muryar da salon maganar

Ganin Bata da niyar yin magana ,ya cillata Kan kujera Dan Abin da yakeji Yana nema ya kasa controlling kanshi yace wallahi in Kika sake rufemin kofa sai ranki ya b'aci Ina dawowa yanzunan wajen mumcy zani .......fuuuuuu ya wugarda da ita kujera ,ya sauka wajen mumcy.

Yana sauka ya samu mumcy na d'aki ya Fara tambayar harri kitchen cikin rashin fara'a Yana cemata me ta sani game da Husna ? Tayi shiru sai da ya sake cemata nace me Kika sani Kan Rayuwar Husna Kuma wallahi in Kika fad'a min ba daidai na had'a da Wanda ta fad'amin na gaskiya zamu samu sab'anin da bamu tab'a samu dake ba ,Dan ta fad'amin gaskiya Kuma har tace na tambaye ki ,Jin Haka sai taji abun yazo Mata gidan da sauki tunda har Husna ce ta Fara gayamai tasan hajiya babba ma ta Gaya Mai Dan Dame bataga Amfani ko hikimar b'oyewa ba Dan Haka tace Mai " to ai Babu wani abun da zance maka tunda sun Gama bayani ,kawai dai itace wacce ka sani Ma'u wacce ta zauna anan kasan ,tun Bayan tafiyan ta Abuja bamu had'u ba sai da aka kawota gidan Nan a matsayin matarka wallahi kaji nama rantsuwar musulmi ....

Sosai FU'AD ya fusata yana hucci yabar kitchen d'in ya tafi a fusace .........
[4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA*

```RUBUTAWA DA TSARAWA```
BY
*FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB*
( Maman shaheed)

💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥

Pg35

Sosai FU'AD ya fusata yana hucci kitchen d'in ya tafi a fusace ya doshi wajen mumcy fuskar Nan ko annuri babu.

Yana zuwa k'ofar d'akin ya buga kafin ta bashi izini ya Shiga Yana Shiga mumcy ta ga yanayin shi da hanzari da nuna kulawa ta Fara tambayan shi ko lafiya ta ganshi Haka?

FU'AD shiru ya Mata sai goron numfashi da yake saukewa gami da hucin takaici.

Sai da mumcy ta sake Mai magana ,sanan yace "mumcy ya za Amin Haka Dan ALLAH Dan Annabi ,wanne laifi na aikata mafi girma da hukuncin shi yayi daidai da Abin da akamin irin Haka batare da Yana kallon idon mumcy ba bare ya ji shayin amayar da Abin da yake cin shi Aran shi.

Mumcy d'agowa tayi Tana cewa ,son lafiya meya faru ko ince me akayi? Ban fahimci inda kasa gaba ba.

FU'AD sai da yayi wata doguwar ajiyar zuciya sanan yace "mumcy Dan ALLAH karki ce min Baki fahimce Ni ba uwata gari me share hawayena ,Dan ALLAH me na Miki Kika hukuntani da Abin da nafi ki wane laifi mafi Muni na aikata Miki Haka uwa ta gari?
"Mumcy cewa tayi nifa ban fahimci inda kasa gaba ba ,in bazaka min magana da yaren da Zan fahimta ba ka Adana kalaman ka inajin zasu maka Amfani wajen warwarewar matsalar ka ,tama tashi Tana niyar ficewa a d'akin ,maganar da FU'AD yayi ne ta dawo da ita.
Mumcy kin San wacce Kika had'ani Aure da ita kuwa? Kina sani kikamin Haka uwa abar Alfaharin 'ya'yanta ko kema a rufe aka baki kamar yadda aka bani?
Sai da mumcy taji k'irjin ta ya mumunan bugawa sai da tayi da gaske ta iya aro mazantaka ta d'aura a zuciyar ta ta Sha mur Babu alamun Wasa ko sasauci tace "wafa kake nufi ?
FU'AD yace mumcy wanan _dirty girl_ d'in da Kika manna min take neman zamemin kaska rabi me jini Asma take ko wa da kuka canja Mata sunan ta kuka zamanan ta da shi wai husuna ko me su matar Yaya suke ce Mata , mumcy yanzu Ni aka hada Aure da kazamar Nan mumcy kuma house girl d'inki fisa illilahi mumcy an kyauta min ? Da ita Kika min huce takaici Yana fad'a idon shi a gefe bayason ko hada ido da mumcy don Kar ya kasa amayar da ta cikin shi ,Dan Haka Yana fad'a Yana bayyanar da rashin Jin dad'in shi da lamarin.
Fad'a da gaskiya tsoro ne Inji wasu masu iya maganar Dan Haka tayi ta maza tace "son duk Abin da zakace kace Amman kasani banyi ko ban taba wani Abu Dan na cutar da Kai ba sai Dan neman maka masalaha da samun nutsuwa da kyakyawan nufi Akan Auren akan Auren da na maka Wanda kamai suna da auren huce takaici tunda baka d'auki Abin da nama da hannu bibiyu ba da kyakyawan nufi ba,son kasani banyi Dan na cutar da Kai ba ......... FU'AD ne yace katse ta da cewa mumcy meyasa Baki tambayi raayi na ba Kika aura min wanan yarinyar? Mumcy...........ce ta karbi maganar da cewa meye illar ta ko aibun ta ko Kuma tsanar ce kawai ka Mata ba tare da tarin hujoji ba?

Ran FU'AD a b'ace yace mumcy yarinyar da take Miki Aiki fa mara kunyar Nan fa wacce kike goyon bayanta idan tamin rashin kunya da har ta Fara Shirin rainani Kuma kike goyon bayanta haba ? Mumcy Dan kun barni da Zan Nemo wacce Zan aura Nan da wani lokaci ai ,Amman har arufe min sanin wacce aka bani a matsayin Mata fisabillilahi ki duba fa mumcy kiga wanan lamarin andakeni Kuma ace bazanyi kuka ba? Hakan anyimin adalci kuwa mumcy ?

Mumcy ce tace ,ahangen da nayi wanan shine adalci aganina ,Amman in Kai kana ganin hakan a rashin adalci to ,yarinyar Nan har yanzu baka fad'amin illar ta ko aibun ta ba ,ko kana ganin kafin k'arfin aurenta ne? Dan suna talakawa? A iya tunani na bansanka da izgilanci ko kyama ga talaka ko talauci ba ,ldan kasa hak'uri a Rayuwar Auren ku da yarinyar Nan zakaji dadinta da yadda ALLAH ,kusan jihadi kayi Akan Auren Asma'u ........ mumcy Bata rufe Baki ba .......... FU'AD yace Ni ai jihadin nawa yafi na kowa ga wacan Abin da Alhaji ya k'ak'aba min ga naki na wanan yarinyar da kuka rufe min ita duk Kuma har yanzu bakiga anmin rashin daidai ba ...........fuuuu ya mik'e ze tafi ranshi a b'acce sai wani fitar huci yake , mumcy ce tace Zo ka zauna tunda aka Fara da Kai sai an Kai k'arshe ,yanzu ya kake so Ayi ? Ina sauraron ka.

Ana cikin Haka sai ga Yaya Jameel ya shigo ,yatana kwankwasa musu k'ofa basuji ba sai muryar su mumcy da take jiyo wa ,sai ya bud'e ya Shiga Baga bakin shi d'auke da sallama Yana cewa uwa da d'an ta me ake tataunawa ne?

Sai ko FU'AD ya wurgo Masa uwar harara da Jan ido ,sai ko Yaya Jameel yace k'anina me akayi ne? Me ya faru naganka a wani yanayi?

FU'AD kasa magana yayi ,sai mumcy ce tayi ma yayan bayanin Abin da FU'AD yake kalubalantar ta akai .
Yaya Jameel yayi ajiyar zuciya ya dafa kafad'ar FU'AD yace "k'anina kasani duk duniya bamu da kamar mumcy Kuma itama Bata da kamar mu bana mafarki ko tunanin yanzu ko Nan gaba Akwai Abin da mumcy zatayi Dan ta cutar damu ba ,ba'ayi maka hakan ba sai Dan maye maka gurbin b'acin ranka da Abin da ze iya zama farin ciki a gareka , FU'AD k'anina d'an uwa ta gari ,ka yadda ka karb'i auren ka da Husna matsayin k'addara Mai kyau duk Abin da baba ya hango yaro baze hango shi ba ....... FU'AD ne a fusace ya Fara cema Yaya Jameel ai har da Kai akamin Abin da akayi Yaya nayi imani da kasan komai Amin Auren cushe na nuna k'ina kun had'u kun bani Baki kunganni k'arami kamar Mara 'yanci sanan kukazo ban Gama da wancan b'acin ranba kuka sake turani cikin wani da auren da babu shawara ta ko sanin asali ko nasabarta da mumcy banyi ba na karb'a kuka sake harbani cikin wani yanzu ,ya kukeso nayi da Raina ? Ya za'amin haka Dan ALLAH ,yarinyar Nan ma Kuma Dan ALLAH arasa wacce zata zama Mata ga FU'AD sai kazamar yarinyar Nan ? Har ma a b'oyemin Abu daga gareta Alhalin na Santa ,haba mumcy haba Yaya Dame kukeso naji? Auren cushe ko Auren huce haushin ko b'oye nasaba ko asali ?
FU'AD mik'ewa yayi Yana hucci ranshi a b'ace Yana cewa Ni gaskiya Abin da akamin anunamin kamar ba d'an gidan bane da Alhaji na, na raye da ba'amin Haka ba nasani Kuma Kai Yaya har da Kai akamin Haka Kai ai matar da kakeso ka aura duk da a k'uraren lokaci ka samota amman ai Kai ka nemota da son ranka ,Nima ku saka acikin ranku Dole na Nemo wacce nakeso wacce zanyi Auren ra'ayi da it's wacce nake so take Sona Dan shafe Abin da akamin bada ra'ayina ba fuuuuuu ya nufi k'ofa zai fita ranshi a b'ace ..........har Yaya Jameel ya bud'e Baki zai Mai magana sai mumcy ta dakatar dashi .

Sosai ran mumcy ya b'aci duk da Tana hango gaskiyar FU'AD akan lamarin ,Amman hakan be Isa yasa ya samu lasisin fad'an magana son ranshi ba ,ganin ranta ya b'aci sai Yaya Jameel ya Fara tausar ta Yana nuna Mata irin Halin da FU'AD yake ciki Dole sumai uziri yaro Mai hakuri da kawaici kamar FU'AD ya dinga magana irin Haka Dole su bashi damar shi yayi yadda yakeso shima tunda sun Mai yadda suke so, mumcy dai Jin shi kawai takeyi Amman kalaman Basu Gama Isa kwanyar ta ba.
Chapter 42 · 0% Book details