← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 95

Sashe 91

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da kyar ta samu taci kadan ,Jin Yana taso Mata tayi saurin tashi tace zataje ta kwanta asama , mumcy tace toh ,Nan tabar aunty sa'adiya naba mumcy labarin dramar gidan mama habee.
Bayan tafiyar husna sama amai take ta kwarawa kamar zata amayar da yayan hanjin ta sai da tayi me isarta ta wanke fuska da Baki tafito ta fad'a gadon Tana dogon numfashi.
Bayan ta samu ya lafa Mata kamar bacci na Shirin d'aukanta ma sai tajiyo sallamar FU'AD kamar a matarki.
FU'AD kusa da ita yazo Yana Mata magana Akan ta tashi taci fruit din d ya kawo mata.
Badan taso ba ta bud'e fuska d Ido da kyar tamai sannu da zuwa ta karbi ledan ta ajiye.
Ganin baci zatayi alokacin ba sai FU'AD yace "kici Mana nasan kinyi Mayan Aman Nan ki samu kici".
Zatayi gardama , FU'AD ya bud'e ya d'auko banana ya Fara bare Mata Yana Miko Mata har sai da ya Bata kusan 3 ta cinye ya d'auko Apple shima sai da ta cinye 1 da Rabi lemu ma Tasha guda 1 Tana cikin Shan na 2 sai Amman ya dawo kafin ta Mike gaba d'aya ta wanke FU'AD da Aman sai sauran d ya mak'ale abakinta ta samu t rarafa d kyar tayi toilet.
FU'AD haushi d takaici nee Kama shi gani yayi kamar da gangan tayi Dan Haka kawai besan lokacin d ya Fara balbaleta da masifa ba har Yana cemata baze d'auki wanan kazantan ba da wawancin wallahi.
duk da ta fito a wahale a galabaice Yana gani Amman be fasa fad'an ba gashi Abin d ya Kara k'ular dashi Bata gyara Mai jikin shi take bama kwanciya tayi gashi ko hakuri Bata da niyar bashi sai wani Abu takeyi kamar me Shirin barin duniya,wani dogon tsaki ya ja Mata kafin ya saki ledar fruit din ya Mike Yana cewa sai ki karaci kazantan ki y fice daga d'akin ranshi babu d'adi yanata kyaman jikin shi.
Husna takaicine ya turniketa batasan lokacin d kuka ya kufce Mata ba tana cikin yine FU'AD ya shigo ya d'auki wayar shi d ya manta a wajen d ya zauna ,Jin gunjin kukan ta sai ya sake kuluwa Yana cewa"au keda lefi keda kuka Dan shagwaba? Ba amiki komai ba Amman Zaki zauna kina kukan santarta ? Wayar shi y d'auka yace kitayi har sarkin kukan yazo ya same ki ya sake ficewa yabar d'akin.
Husna sake gunjin kukan tayi Tana takaici Akan Halin FU'AD Ashe Yana Nan babu inda yaje ,yanzu hukuncin ta kenan baya lura da Halin da take ciki?.
Besan ya takeji dama yaudarace ya nuna kamar ya sakko? Har d wani siyomin kayan marmari Ashe ya siyone Dan ya cimin mutunci ta sanadin su?
Alwashi taci Akan bazata sake cin komai da ze Bata ba Kuma baze sake zama Mata a d'aki ba sanan baze gara ganinta ba a yau har sai gobe Dan Haka d kyar ta samu ta Mike ta saka key a d'akin ta gyara wajen d ya b'aci d kyar ta koma ta kwanta Tana tunanin rayuwa cikin Halin d take tunanin FU'AD ya canja Ashe be canja ba yaudarace kawai.

...........Bayan shigar FU'AD d'akin shi kayan y cire Yana wani ajiyesu a yamutse sai d y Gama ciresu yanata tsaki kafin ya samu ya fad'a bathroom ya fesa wanka y Gama jikinshi d turarukan wanka masu dad'in kamshi kafin ya fito ya janja Kaya y sake feshe jikin shi d turare Dan gaske.
Kiran Yaya Jameel ne ya shigo wayar shi yace yazo Yana part d'in shi suyi wata Yar magana.
Yawa amsawa ya ajiye wayar ya tafi Kiran d yamai,a falon mumcy y bar mumcy d aunty sa'adiya kafin y nufi Kiran Yaya Jameel din.
Bayan yayi sallama y shiga y sameshi a zaune Yana kallo daga bisani ya dawo d nutsuwar shi Kan k'anin nashi y Fara Mai bayani Akan hakuri d zaman Aure d hakuri da me ciki Dan zuciyoyin su a kusa yake b'acin Rai baya musu wuya gasu d kayan takaici wasun su Amman Dole Ayi hakuri Ayi k'ok'arin Basu farinciki har ya bigamai misali da aunty sa'adiya har yaji ta tabayi akan tamai amai ajiki ya Mata fada ba karamin wuya yaciba kafin ya samo kanta tundaga Nan ya kiyaye ya Fara lalab'ata ba Kuma yadda zata sangarce ba haka sukata hakuri da juna suna renon kyautan da ALLAH ya Basu har ya Isa haihuwa Dan haka Yana shawartan shi da yayi hak'uri ya ajiye zuciyar Nan tashi har zuwa Husna ta haihu lafiya ya ninka kulawar da yake Bata Kuma".
Tunda Yaya Jameel y Fara magana FU'AD ya nausa duniyar tunani sai yaga kamar ya fahimci meya faru ma badan yasan Husna bazata gayamai ba da sai yace itace ta sanar Mai.
Jin yayi shiru Yaya Jameel din y cigaba d bugs Mai misalai d yanayin ciki ga wasu matan d ya samu labarin su a wajen abokanen sa wasu Abin tausayi wasu Abin dariya akarshe dai ya nuna Mai tsananin buk'atuwar kulawar d ya Dace aba masu dauke d juna biyu Dan samu su haife lafiya cikin kishin lafiya batare d uwa ko Dan ya fad'a cikin gararin matsala ba.
Sosai kalaman Yaya Jameel suka ratsa FU'AD ya samu sauyi a lokaci guda so da k'aunar Abin da za'a Haifa Mai tun besan meye bama atake yaji nadamar Abin d ya aikata ma Husna dazu Dan ji yayi harma ya kosa da tunasarwar Yaya Jameel din.
Bayan sun Gama magana suka tatauna akan sanaya Yaya Jameel din Yana Mai fad'a Akan ya dinga Bata hakkin ta , FU'AD y amsa d Yana iya k'ok'arin shi yarinyar ce Akwai wuyar sha'ani Amman ze Kara k'ok'arin wajen kulawa d itan.
Atare suka koma Fallon mumcy Yaya Jameel ya zauna Ana hirar dashi FU'AD Kam ba'a bashi zama ba haurawa yayi wajen Husna.
D'akinta ya nufa yaji ansa key ,yayi mamaki Amman sai yayi tunanin ko bacci take har ya Fara bugawa sai ya fasa y koma d'akin shi Dan ya rage wani aikin.
Bayan kusan awa daya y sake dawowa buga k'ofan ya farayi Amman Babu niyar budewa Dan Haka ya d'auki waya ya kirata kusan so 3 kafin ta d'aga bisani ta d'aga cikin muryar tausayi.
Ji yayi tausayinta d wata kaunarta ya Kama shi sai yace "Zo ki bud'e min k'ofa".
Sai tace "me zakama kamaza?.
Ko zakazo ne tsautsayi yasa na maka amai ka sake cin zarafina?
"Kayi zamanka tunda babu tausayi da jinkai a tsakanina da Kai ko ganinka banason yi Kuma barma gidanka zanyi Inna haihu na kawo ma danka Amman na Gama Rayuwar wulak'anci bazan sake jure Mata ba ta fashe da kuka"
FU'AD yanajin kukan har ranshi yanata Kiran sunan ta Amman Ina kuka yaci k'arfinta maganar duniya da magiya Taki amsawa.

FU'AD wani irin yanayi ya Shiga Mara misaltuwa Yana cikin wanan Halin B2k ya kirashi a wayar shi d kamar baze d'auka ba sai ya d'auka de.
Bayan sun gaisa sai suka Fara maganar company sai FU'AD yace "ka Bari anjina mayi magana"
Sai B2k yace "mutumina lafiya kuwa najika kamar a wani yanayi fa?.
FU'AD yaso b'oye Mai Amman B2k d magiya d lalami har sai d FU'AD y bashi labarin komai tundaga samuwar cikin Husna d abun d ya faru yau,atake B2k yaba yaba FU'AD rashin gaskiya y nuna Mai inhar yanasin gaskiya d son zaman lafiya d happy family sai ya zubar da makaman shi na baya ya fuskanci Rayuwar Aure Mai cike da tatali da nuna kulawa ga iyalin shi ya manta komai ya fuskanci gaba yasan cewa Husna wata kyautace Kuma tsarin ALLAH a gareshi Dan su tsara rayuwa Mai inganci ,duk yadda FU'AD ya bullowa B2k sai B2k ya toshe ya Gina Mai hujja Mai k'arfi Wanda Dole ya yadda Haka har B2k yaci galaba akan FU'AD ya yadda bashi da abar so da kauna samada _dirty girl_ sunan da bayason ko tunawa yayi yanzu , B2k be kashe wayar ba sai d Yama FU'AD tunin kyautan da zezo karb'a na maganar su ta baya da yake cemai kamar me duba ,sai ko FU'AD ya dinga dariya Yana cewa maye me gani har hanji sai kazo Ni barinje in gyara Abin da na Bata.
B2K cemai yayi ako kayi sauri Dan inba hakaba a haifo ma d'a da tabon b'acin Rai ajikin shi Yana cewa sai nazo karb'a.
FU'AD da kakarfar zuciyar shi ya sake komawa wajen Husna yin duniya Taki bud'e k'ofan y sake kiranta Yana mata dabara Akan ta fito taci abinci tace "Bata ci" Abin duniya Yama FU'AD zafi ,Dole sai da yaje ya nemi taimakon aunty sa'adiya batare da mumcy ta gano ba.
Tun zuwan aunty sa'adiya da Husna ta fito take ALLAH...... ALLAH....ta tafi kafin FU'AD ya hauro Tana cikin tunanin hakan FU'AD yayi sallama ya shigo auwar harara Husna ta wurga Mai ya gani Amman yayi kamar be gani ba ,aunty sa'adiya cewa tayi Bari tatafi tunda ga FU'AD dama tazo ta d'ebe Mata kewa ne taga jikinta Kuma,Husna godiya ta mata.
Bayan tafiyar aunty sa'adiya Husna har ta dau hanyar komawa d'aki FU'AD yasha gabanta Yana cewa" wai Ina zakine haka?
Husna cemai tayi "inda na fito ko Akwai Abin da zanma ne? Ko kauanka da na batama Zan wanke ma?
FU'AD cemata yayi "eh shi Zaki wanke Ayi mutum Mai gardama anaso afahimtar dake Abu kin kasa bada lokaci ki fahimta"
"Wani irin kallo ta wurgamai sanan tace "mezan fahimta ka fahimtar Dani din malamin fahimta"
"Dariyace taso kubcema FU'AD Yana cewa hmmmm gafa aikin masu cikin duk ya Fara bayyana atatare da yarinyar Nan dama Akwai gaddama Amman kamar ta Kara ninkawa Amman Bari na bisa ahankali Albarkacin jinina dake damfare ajikinta ko na samu ta fahimce ni,Afili Kuma sai yace "me kike da buk'ata yanzu love me zakiyi?
Cemai tayi "Ni bana buk'atan komai daga gareka nagode ka rik'e komai naka na barka lafiya ta karasa kulewa d'aki,......
Chapter 91 · 0% Book details