Sashe 38
Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
sallama yace sa'adiya tazo mami na kuka ,da sauri Aisha ta mik'e Tana cewa ayya my daughter Zo in ji dalilin kukan" sai ko Jameel yace ai Tana wajen mumcy " da gudu Aisha ta tafi d'aukan ta " Jameel d'in yabi bayanta ,sanan sa'adiya ma Tama sanaya sallama ta tashi ta tafi Tana cewa uwar Mami kamar tanada Abin Bata ,suka bar sanaya da Husna da mijin su . Sai Bayan sun fita Husna taji me ya hanata rigasu fita? Ji take kamar k'asa ta tsage ta nutse Dan kunya da nauyin FU'AD har sanayan ma ji tayi tana Jin kunyar ta ,sosai FU'AD ya Sami damar k'are musu kallo ,tun ma'un na d'ago ido su had'a ido har ta daina d'agowa ,shi kanshi yasan kalon yayi yawa Amman shi yabarma kanshi sanin dalilin kalon . Sanaya ce ta mik'e taji wayar ta na ringing ,ganin mufeeda ce take Kira da sauri ta d'aga tace ,sis nayi fushi dake dady be Gaya Miki ba? " Mufeeda Dace ayya double sorry blood sis ,dalilin Kiran kenan Dan na wanke kaina ma ,so ya kike ya 9ja ? Sai sanaya ta yamutsa fuska gata munata hak'uri har hak'urin namu na neman k'arewa , daga FU'AD har Husna sai da kowa ya saci kalon ta , itako ko ajikinta . "Mufeeda tace to ya mumcy yasu FU'AD ? " Sanaya gashi can " sai mufeeda tace Kai aunty Yana lafiya na tambayeki fa? Sai sanaya tace uwar tsari lafiya Mana yake tunda kikaji nace Haka" sai mufeeda tace Masha Allah" Ina Husna fa? Atsorace ta tambaya "sai ko sanaya tace gata Kar kice itama ban Baki amsar da ya Dace ba ki tambayeta lafiyan ta da kanki kin hutar Dani tafinta ,sai ta karama husna waya a kunne tace ga mufee na magana . Husna fara'a ta d'anyi tace mufee ya kike ya su dady da mamy? Cikin Jin dad'i da farinciki mufee tace lafiya suke wallahi. Husna tace ki gaishe min dasu Dan ALLAH . Mufee tace insha ALLAH. Husna ta ba sanaya wayar ta Tana Shirin tashi zata gudu sai FU'AD yace "Ina zuwa ? Da sauri tace wajen mumcy" sai yace barin raka ki ya taso yace ma sanaya Ina dawowa " hannu kawai ta d'aga Mai alamun toh saboda Tana waya . Tun lokacin da Husna take waya har Tana tambayan su dady sai yaji ta gama birge shi duk da har yanzu haushin dadyn yake ji ,sanan itama bawai Dan ALLAH yake son rakata ba Dan ya tambayeta inda tasan mufeeda har suka San juna Haka yake son ji daga gareta. Suna Fara tafiya yayi murmushi yace ya take sauri? Tace Babu komai " sai yace Husna a Ina Kika San mufeeda Haka har Naga kun zama 'yan uwa? Sai ko tambayar tazo Mata a bazata ,Amman ta dake "tace a Nan gidan Mana kasan mu Mata bamuda wuyan sabo " FU'AD yace hmmmm najima inajin wanan" cikin kwana kalilan har kuka Saba daga zuwanki gidan? Sai ko tace eh Mana Kuma ai na tab'a Jin labarinta wajen mumcy ,yace hmmmm ALLAH ko? "Husna taga alamun be yadda ba Dan Haka take sauri su Shiga falon mumcy ko ta huta da tambayoyin FU'AD. Gab da zasu Shiga ya cemata wai ma ya alak"arki da mumcy ne Asma'u ko Husna wanene na gaskiyan ne? Sai ko jikin Husna ya Fara rawa tambayar 2 zuwa Mata tayi , kafin ta bashi amsa sai ,Yaya Jameel ya fito ya tare shi Yana Mai magana ,da sauri sauri Husna ta samu ta gudu ,gudun Kar ya Kuma ritsata da tambayar shi ta zauna wajen mumcy tasan be Isa yaci gaba da tambayar ba . [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA*