← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 95

Sashe 19

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ma'u cikin shirinta n zuwa wajen Aiki gidan mumcy ,wata zuciyar na karanto Mata rashin kyautuwa Abin d Tama FU'AD ,wata kuma na ganin dacewar hakan ,cikin kwarin gwuiwa dai ta k'arfafi zuciyarta tace itama ai ramawa tayi ,Dan Haka Haka tace ,ai Rama cuta ga macuci ibadane ,yanzu munyi 1,1 inya sake mun Nima sai na Rama , Ma'u d wanan tunanin ta siyi katin mtn na 200 ta nufi gidan manan hafeeza k'awarta da ta b'ata *RIK'ON KWARYA* Aikinta don ta saka a wayar mama su gaisa ,Tana Shiga ta korama mama bayani ,mama nata Mata dariya Tana cewa in Banda abinda har sai ta wani siyo Kati ,ai ko flashing akama hafeezar zata Kira , Ma'u dai tace babu komai mama so nake muyi Hira sosai mun kwana biyu bamu gaisa ba , Ma'u ta karbi wayar tasa katin ta Kira k'awarta ,sunjima suna Hira Tana Bata lbr gidan hajiya babba d karamcin ta har tafiyar da zasuyi d Yaya Jameel d matar shi , Ma'u na k'ara kozanta rashin kirkin FU'AD ,Amman hafeezar na kare shi ,Haka dai har ma'un tabarma mama sauran canjin a wayar ta Mata godiya d sallama ta tafi gidan mumcy don Aiki....

Cikin kwarin gwuiwa Ma'u ta Shiga falon ,musamman d taji alamun falon cike yake da mutane ,bakinta d'auke da sallama , mumcy d wasu tsiraru na falon ne suka amsa Banda FU'AD d ko samun darajar kallo batayi ba a gunsa ,dama itama batasa Rai ba ,Dan Haka wajen mumcy ta nufa har k'asa ta gaisheta sanan ta gaishe d Yaya Jameel sanan aunty sa'adiya ,sai FU'AD ,Yana Shan k'amshi ya amsa shima don mumcy ta jefeshi d kallon tuhumane ,Yana amsawa ,ta sake cemai ya k'arfin jiki? A dak'ile yace lpy ta qalau ko Baki gani ba? Mumcy ta katse Al'amarin d cewa "Asamu Kinga har Harri ta gyara falon ke jeki ki gyara saman FU'AD yanzu sai ki dawo dakina kinji?

Ma'u ta amsa d toh, ta mik'e zata tafi mumcy tace "Asma'u ko Zaki Fara karyawa? Bud'ar bakin Ma'u tace "laaa mumcy wlh Alhmd na karya ai baba baya barina na fito ban karya ba , FU'AD ko cewa yayi kamar gaske y d'auke wuta kamar bashi y furta hakan ba Kuma kowa yaji shi , mumcy tace jeki to anjima Kya k'ara, Ma'u ta haura Tana mita ai me Hali baya fasa Halin shi ,gwanda d nayi maganin ka ,aikin banza yasani asarar mage Haka kawai anbani ita Don nayi kiwo na kawo don na Rama Abin d yamin yasa anfitar min d ita ,Ni ba Abin nayi tmby ba na jama kaina Ruwa ,Dan rainin hammata kawai .....Tana tafiya Tana mita har ta Isa falon.

K'alk'al ta gyare Mai saman ,Yana zaune anata Mai sannu ,kowa na ji dashi awajen musamman Yaya Jameel ....

Bayan Ma'u ta gama gyaran ta sakko k'asa ,ta Shiga d'akin mumcy don gyare Mata shi ....

FU'AD ne yace ze haura sama don ya huta ,duk d mumcy da Yaya Jameel suna mgn tafiyan su ne ,Amman FU'AD sai yace duk Abin d aka tatauna a ajiye Mai inya tashi a bacci a gayamai , sa'adiya na tsokanan shi tace angama ,k'aramin megida *Na mage* lokacin da yayi daidai d fitowar Ma'u daga d'akin mumcy shi Kuma FU'AD Yana Hawa k'afar bene ,Aiko y juyo yace haka Kika samin ko matar Yaya? Tayi fari d ido tace "yes" Aiko yayi kwafa alamun sunan bemai dad'i ba ,itako Ma'u murmushi da Jin sunan d aka rad'a Mai ......

Suko su mumcy dariya sukayi ,sukace sunan ya Dace da Kai , gashi har y kaika ga kwanciya a asibiti .....

Har ma'un tayi hanyar Shiga kitchen wajen su Hari ta jiyo hirar su ,Aiko sai Yaya Jameel yace "Ma'u kike ko Asma'u kin Gama shiryawa ko don tafiyar mu ta kusa Ana bani update Nima Zan sanar Miki don anrage lokacin ....

Ma'u Kai ta gyad'a Mai Alamar eh ,sai mumcy tace "magana zakiyi Asma'u " sanan tace "eh insha ALLAH" sanan sukace taje sai taji kira,tace "toh"...

Ma'u Tana murna da tafiyar wani b'angaren Kuma tanajin Babu dad'i zata zauna na wani lokaci d mutanen d Bata Saba dasu ba ,zata bar babanta Abin share kukanta gatanta na duk duniya tunda ta Rasa mahaifiyar ta ,dg baya ma tayi watsi d tunanin tace "Rayuwa dama ai ta gaji Haka , ALLAH y tabbatar Mata d abin da zefi zama Mata Alkhairi a Rayuwar ta ....

B2k ne da wasu daga cikin abokanen su FU'AD sukazo duba shi ,Bayan sun Gama cacafkewar su zasu tafi sunaya tsokanar shi wai ya zama *na mage* Yana ce musu sunyi biyu Haka ma wifyn Bros tace Mai ,wlh ze karta musu RM in Basu Bari ba ,Aiko suka sa dariya suna cewa kabada maza wlh ,yace "eh yaji d'in don Basu San meya faru dashi bane a zahiri su yanzu bar'ini suke ji ,har zasu fita a falon ,B2k yace "ya Ina bara gurbin kamun da kace kamin ne d'an iskan abokina? FU'AD be furta komai ba sai ga mumcy d Ma'u na biye d ita ,sai ko mumcy tace "aah badai kunfito ba ? B2k ne yace "eh wlh zamu koma wajen Aiki mumcy munga jikin d sauki ma mutumin namu ya fito daga tarkon kuliya ,sai wani a cikin su yace "hhhhh dakyar Nasha yafi dakyar aka kamani ,Amman Kai baka Sha ba don kamuwa kayi wlh ,Aiko sai aka dinga darawa Ana dariya har mumcy , Ma'u ma batasan lokacin d murmushi Mai sauti ya kwace Mata ba ,Aiko sai a idon FU'AD ya had'e Rai yace _dirty girl_ waye sa'anki anan?

Da har Ana
magana kike k'ok'arin ......... mumcy ce tace "bana so son" ba ruwanka d ita ,sanan B2k yace oh itace Yama FU'AD alamu d ido ,sai ko FU'AD y Harare shi ,shi ko B2k yace ,Abin yayi fa FU'AD yaushe zamuyi magana? Sai ko FU'AD y Harare shi y d'aure fuska y fahimci me yake nufi ,y fice y barsu a falon irin in bazaku fito ba kuta zama d'inan ,sai ko sukace mumcy mun tafi ALLAH y k'ara sauki ,suka fice ......

B2k na son tsokanar FU'AD ,Amman yaga yaci magani ,sai y kyale kawai ,suka Mai ALLAH y k'ara sauki suka tafi ......

Bayan FU'AD y dawo daga rakiyar su ,sai y Sami Ma'u a falon ita kad'ai y k'arasa wajen ta y zuba Mata rankwashi akanta Mai lulub'e da hijab ,batare d tasan y shigo ba atsorace tace ,mena maka? Yace "tambayata ma kike? Bakisan Shiga sha'anin mutane da kikayi ba dazu sai kace dake ake? Tayi nesa dashi Tana Jin zafin rankwashin Tana sosawa tace au to ,Ni din Aljanace da bazan Shiga sha'anin mutane ba? Yayi yunk'urin k'arasowa inda take ,sai ko ta k'ara nesa dashi tace ,Naga dai Nima mutum ce kamar kowa ,afusace FU'AD y biyo ta, ta afka kitchen d sauri ganin Kar taci bulus be hukuntata b y bita kitchen din Yana Shiga yaga harri sai y wayance d cewa ke kawo min Ruwa d juice yanzu Nan ,sai ko Harri tace yi maza Ma'u ki kaima yallab'ai ruwa juice Yana Miki magana ,jiki Babu kwari tace to ,ya harareta sanan ya fice Yana jiranta a falo , Ma'u nata nuk'u nuk'u ta kasa Kai Mai ganin Harri Kar ta gane tsoron fita takeyi sai kawai tayi shahada ta fita ,ta Kai Mai jiki na rawa zata ajiye Mai ta gudu yacce in ta ajiye wlh sai y hukuntata ,sai ta mik'a Mai tace "toh gashi ,sai yasa hanu y d'auki juice d'in ya bud'e bakin ,zata ajiye Mai Kan center table ta gudu kenan duk'awar ta keda wuya ya watso Mata juice d'in ajikinta har fuska yace "ko Dan gaba da glass cup ake hadoma da mutum ba a bashi Haka ba ,Kuma acikin minti 2 ki gyara wajen wlh ko hukunci ya biyo baya _dirty girl_ kawai ,wani k'ululun bak'in ciki ne ya turnike Ma'u gashi duk y Bata Mata hijab ,tace "toh ai nata ko su turawan na kasashen duniya ma bana k'asata 9ja ba ,suna Shan Ruwa da bakin roban da shi lemon ba hadisi bane ko aya da za'ace lalai sai anzuba a Kofi kafin ya Shiga Baki ba ,su da sukafi mutum wayewa kenan .......Tana Shirin guduwa y kamo gefen hijabin ta ,ta kusa fad'uwa ya Kama kunnen ta acikin hijabin yace Ina gargad'an ki da ki guji mayar min d amsa ayayin da na Miki magana ,wlh don mumcy na barki a gidan Nan d tuni na k'ara Miki wuta wlh ,Naga alama Baki da kunya wuyanki y fara kauri ko?

Ya sake Mata kunne kenan ze rankwashe ta sai ta gudu Tana cewa "ai dama ko a lahira wani nacin Albarkacin wani kaima wataran bakasan ko nawa zakaci ba "ta shige da gudu Tana cewa *na mage* kawai FU'AD kasa gaskatawa yayi furucin daga bakinta ya fito ko ba daga bakinta ba ,cikin Isa da izza yayi k'ok'arin binta har kitchen d'in domin tabatarwa , mumcy ce ta fito ta dakatar dashi ta hanyar yimai magana Akan tafiyar yayan shi Jameel ,sai ya had'iyi hak'uri Akan Abin d y k'udiri aniyar yi ,ya zauna Yana huci suna Hira d mumcy Amman be Bari ta fahimci Halin d yake ciki ba ,....

Ranar Ma'u har tabar gidan Bata Bari sun had'u d FU'AD ba .

Washe gari , Ma'u batazo Aiki ba ,sbd babanta ba lpy ,sai washe gari taje ,koda mumcy ta tambayeta sai ta fad'a musu dalilin rashin zuwantan ,suka Mata ALLAH ya bashi lpy,ta amsa d Amin. .

Tafiyar su sa'adiya d ma'u tazo , mumcy har ta Fara kewar ta don mumcy na yabawa da aikin ma'un d'ari bisa d'ari ,Amman ya zatayi tunda sa'adiya d lalura Haka zata hak'ura , mumcy d kanta ta fad'ama ma'un ,sanan Jameel y d'auki sa'adiya sukaje suka sanar ma da baban ma'un har da ranar da zasu tafin ,suka Mai Alkhairi da kyar baban Ma'u y karb'a sai da sukata bashi Baki sanan ....
Chapter 19 · 0% Book details