← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 95

Sashe 33

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Bayan ya dawo gida ,sukayi magana da su mumcy Akan tafiya wajen matan sa ,yin duniya yace shi fa sai satin da mumcy tace zatayi gagarumin taro Akan bikin sanar shima ze ziyarci d'akin matan , mumcy masifa ta Fara Balbale shi dashi sai da Yaya Jameel ya Bata hak'uri yace abarshi zuwa ranar ai duk takusa kare wa duk abinta ,yanzu ya kakeso ayi tukunna a ina zaka kwana ma? Jameel yake tambayan shi ,sai ko yace a part d'in ku tunda kun koreni yau a sama ,Jameel yace toh jeka kwanta ganinan zuwa , FU'AD ya tashi ya fita , mumcy Dan haushi ko kallon shi batayi ba,sai Bayan ya fita ta rufe Jameel da fad'a Akan Yana sangarta FU'AD da nuna mai sai dai subishi badai shi ya bisu ba? Jameel Bayan mumcy ta gama yace "ba binshi muke ba ,kowa ya kamata abashi hakkin shi ne uwa ta gari ,kin bashi umarni ya bi kin tursasashi ya amince bafa Dan baze iya bijire Miki ba ,kawai biyaya ce tasa Haka ,to Damme kema bazaki iya Mai wasu alfarmomi ba da Basu Gaza ikon ki ba? Ki tuna fa abu biyu kike d'auka Akan mu nida shi kece uwar mu kece uban mu ,shi ko FU'AD Ina Mai hakane don in dinga tuna Mai da gata da yanayin k'aunar da Alhajin mu yake nuna Mana kafin k'asa ta rufe idon shi ,kinsan duk Abin da mukeso shi yake Mana hatta Abin da zamuci sai mun zab'a in ban manta ba munsha zab'an Miki kayan da zakisa ajikin ki don yagani yaji dad'i muna yara ,duk wanan besa mun lalace ko zama sangartatu ba saboda gata ,to damne bazamu dinga tunashu ba? Da yin d'abi'u irin nashi ba,shima fa Yana kewar shi kamar yadda ni dake mukeyi ,Kuma Yana buk'atar Kulawar mu ,yamana biyaya iya biyayya ,da wanan zamu saka Mai muma ,sai ko mumcy tace shi kenan na fahimce ka , ALLAH ya nuna Mana ranar lpy ....

Kwayen Ma'u da humaira sun koma gida da su hafeeza da mamanta ,kawayen su humaira sun korama humaira labarin gad'uwar gidan Ma'u da irin daular da ta samu ,sai ko mama habee da humaira suka tsure mama habee ba'cin Rai ne ya turnuk'eta Amman Tana sake Mata Addu'a ALLAH yasa d'an mafiya ne ,tun da suka tafi humaira take zirgilon son zuwa ,gashi Basu sanar Mata da gagarumin taron da hajiya babba zatayi ba ,sai k'arya da sukama humairan ma sukace "Akwai manya manyan karnuka agidan ,Kuma in Basu tab'a ganin mutum ba yagalgalashi sukeyi Suma sai da aka nuna Mai susanan suka Shiga ,ga sojoji marasa mutunci har pant dinki sai sun caje Kuma gate 4 a gidan ,ke gidan fa Abin tsoro ne duk suka tsorata humaira Dan sun gano hassada karasa atare da ita da Babar ta da sukema ha'un ,Aiko sosai humaira ta tsorata mama habee ta sake tabbatar wa Dan yankankai akaba Ma'u
[4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA*

_RUBUTAWA DA TSARAWA_
BY
*FATIMA ABUBAKAR SHU'AB*
(Maman shaheed)

💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥

Pg 29

Sosai humaira ta tsorata da gidan Ma'u dama gata kura ga tsoro ga ban tsoro ,Amman tanaso taga shin da gaske ne Ma'u ce tayi Dace Haka?

FU'AD ko takan wasu matan shi be bi ba ya Shirin kwanciyar bacci ,sai yaya Jameel ne yaje yayi sallama dasu , Ma'u da aunty sa'adiya da Aishat zasu kwana kamar yadda mumcy tayi umarni , Ma'u har kunyar had'a ido take da mumcy ga godiya da takeson Mata na rashin kyama da ta nuna Mata ta had'ata Aure da d'anta mafi soyuwa a gareta ,duk da ita Ma'u tanajin zaman su bazeyi armashi ba Dan har yanzu kallon mugu azzalumi take Mai ,sanan Kuma Tana ganin intayi ma mumcy godiya kowa ze zata Tana farin ciki ne da aka Bata FU'AD matsayin miji zasuga kamar nunawa take tafi kowacce macce sa'a a duniya ,dad'i ne yasa ta fito har take godiyar ma ,Dan Haka ta Adana godiyar ta zuwa lokacin da ya Dace .
Su Harri Aiki ya musu yawa sunata d'auki zuwa ganin Ma'u matsayin surika cikin gidan hajiya baba Abu kamar a mafarki ,tunda labari ya same su suketa jijuya lamarin har me gadi da masu wankin gidan da duk wani ma'aikacin gidan .
Ko da Harri ta kawo musu abinci sukayi tozali da Ma'u sai murna take yima ma'un da ,itako Ma'u har tallabo Harri takeyi Tana tambayan ta sauran ma'aikatan gidan ,duk Harri tace suna Nan lafiya suna tayata murna zama surikar mumcy ,murmushi ma'un kawai tayi ,suka d'an tab'a Hira da Harri kafin Harri ta koma aikin ta.
Sosai su aunty sa'adiya suke d'ora Ma'u Kan hanyar samo Kan FU'AD ,suna nuna Mata k'iyaya ko gani Bata Isa zama matar shi ba duk ta ajiye tayi biyayar Aure kawai , inhar tayi da sannu zataga ribar Abin ,tunda abune Babu Wanda ya kwana da sanin shi ,ko ita mumcy bawai ta had'a don dama can da Abin Aranta bane ,zuwa yayi kawai batare da kowa ya sani ba ,Dan Haka Dole ku d'auki na anabawa hak'uri ,kubi umarnin Wanda suka had'a Abin ,sosai Ma'u take sauraron aunty sa'adiya wani abun Tana ganin zata iya wani ko Tana ganin Ina badai ita ma'un ba ,Haka har bacci yayi gaba dasu .

FU'AD dai ya tare wajen yayan shi kamar yadda mumcy ta maida sa'adiya wajen ma'u Haka mufeeda take Taya sanaya kwana a part d'in ta Dan dama Akwai komai gyara wasu abubuwan akayi ,kwanaki sunata tafiya har gobe ake Shirin gagarumin taron biki da mumcy ta had'a don Taya d'anta Aure duk da ba Haka taso bikin yazo Mata ba yadda taci burika a Auren autan nata ,Amman Babu yadda ta iya yanzu ma Dole ta nuna farin ciki ta Dan tabada umarni Kuma ambi ,Dan Haka ta gayyaci mutane sosai ,duk wani Abu da za'aci ko asha ko na kyauta ta gama dasu Dan order ta bayar .

Washe gari da safe ranar taron ,Wanda FU'AD d sanaya har ma'un ba wani matsanaicin farin ciki ,kowa yak'e yakeyi .
Tun safe aunty sa'adiya tasa Husna tayi wanka ta turare ta da turaren wuta na jiki Mai dad'in kamshi dazo ta turare Mata kayan da zata saka wani leshi da mumcy ta siya musu har sanaya Amman Akwai bambancin kala sanan ,ta Bata wasu turaruka Dana jiki Dana Kaya tace ta feshe jikinta dasu sanan tasa kayan ,d'an kwalin kuwa ta Bari Aisha tazo ta nad'a mata,sosai Aisha ta gyara Husna ta fito cas da ita ,sukaje suka kwashi gaisuwa wajen mumcy ,Sana da rakiyar Aisha sukaje gaishe da mamyn sanaya har wajen sanayan sukaje batare da sanaya taga fuskar Ma'u ba ta amsa gaisuwar a wulak'ance suka koma part d'in su Yaya Jameel don gaishe su ,Yaya jameel kawai suka gaisar FU'AD ko tashi abbaci beyi ba Dan Haka suka koma saman da suka baro .
Biki yayi biki FU'AD Dan Dole ya shirya da taimakon su B2k ya saka wani arnen yadin shi Mai tsada da laushi yamasa kyau kamar danshi akayi yadin ga hular shi da ya kafa tangaran ta had'u da yad'in sai basarwa yake irin bikin ba akanshi yake ba da Ayi da Kar ayi duk 1 gara ma Kar ayin badan mumcy ta dage ba .
Chapter 33 · 0% Book details