Sashe 66
Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washe gari su Yaya Jameel da wuri suka fito Dan tafiya k'auyen da baba yake ,ko mumcy Basu sanar ma ba acewar su so suke su surprising nata.
Bayan sunzo sun d'auke shi Yana nuna musu hanya tirya_tiryan har k'auyen wajen neman gidan ma da kwatancen baban sun Sha wuya FU'AD nata b'acin Rai Yana ayyana akan wata dirty girl fa suke kwasan wanan ranar, har gajiya sukayi da tambaya sai abanza suka Sami inda baban yake ,aka kaisu Yana gindin bishiya yanata Hira da wasu cikin kwanciyan hankali da nishad'i.
Baba na ganin aminin shi da sauri ya mik'e Yana taro shi ko su FU'AD be sheda ba ma ,sai da aminin yace "tare muke da Baki fa surikin ka da wanshi"
Atake baba yaji mumunan fad'uwar gaba ,yace "sanun ku da zuwa bisimillah ya matsa musu sai abokanen nashi guda 2 suka gaisa da su Yaya Jameel sukace Bari a Nemo musu Ruwa irin na Yan birni wato ruwan leda (pure water) Bayan sun huta ankawo musu Ruwa da take ferare Mai kyau wankanke ga abinci shinkafa da wake da yaji da manta babu su salad Dan Basu damu dashi ba baban Ma'u nata cewa Dan ALLAH suci....
Bayan sun gaisa baba yace ALLAH yasa lafiya ba wani Abu bane ya Sami ma'uta ko wani abun tayi na laifi duk da ban taba samunta da hakan ba iya samunta da nayi a Rayuwarta?
Ajiyar zuciya Yaya Jameel yayi kafin yace "baba kana nufin bakwa tare da ita anan?
Sai baba ya zabira yace kamar Yaya?
Sai aminin baban yace "nemanta Suma sukeyi shine sukaje gida ankasa basu bayanin takamaimai inda take shine suketa nemanka kaima babu tartibin inda kake da kyar suka sameni da naso b'oye sirrinka kamar yadda mukayi da Kai ,Amman ganin Abin da ya shafi Ma'u ya shafeka shi yisa na sanar musu inda kake har suka nemi na rako su na rakosu sauran bayani kaji daga garesu.
Sai baba ya juya yace "Dan ALLAH kumin bayani Ina Ma'u ta Shiga?
Yaya Jameel ne yace "wallahi muma nemanta mukeyi Dan wani abune yad'an faru babu Abin da zamu b'oyema ,suka Mai bayanin komai Basu b'oye komai ba.
Sai baba yace "bawai son Ma'u bane ya rufe min Ido ,Amman kunyi kuskure kunmin ba daidai ba duk da ta wani fanin banga laifin ku Amman in hankali ya Bata tunani ke Nemo shi da kunyi Aiki da lura da Haka Bata faru ba ,Ni a iya nazari na da tunani na duk wanan Aiki baze wuce algungumar da ta raboni daga can bane ta shirya Kuma take Shirin cin nasara Dan zaman Nan da kukaga nayi anan gajiya nayi da mugun halinta da abubuwan da takemin ga wasu mafarkai da suka tasoni gaba Akan marigayiya mahaifiyar ma'un shine na bar Mata garin nazo Nan Dan na huta nasan inzan shekara bazata boyo Ni ba ,Kuma zaman da nake har Addu'a aketa min da tsari Akan sharrinta da ake bani,Amman yanzu komawa yazama min Dole kodan sanin inda bakin zaren yake Dan bazan fitar da komai ba sai naji daga gareta me yiwuwa tanada sa hanu a barin Ma'u gidan Dan yadda nasan Ma'u bazata taba tafiya ko Ina ba sai gida.
Sosai hankalin baba ya tashi ,sai da Yaya Jameel da aminin baba suka dinga kwantar Mai da hankali sanan ya samu ya hak'ura ya shiryo yayi sallama da mutanen akan ze dawo inya samu nutsuwa.
Bayan sunyi sallah suka dau hanya sosai aka musu tsararbar rake aka gyara aka zuba musu a mota suka d'au hanya FU'AD ya kasa cewa komai.
Bayan sun Isa gidan baba suka tsaya baba ya Shiga gida da gudu haidar ya taho yamai oyoyo yanata murna ,mama habee ko a razane take Mai magana sai cewa ma tayi "shine dawowa babu bayani ?
Harara baban ya wurga Mata yace" ba wanan ba ma'u tazo gidanan ko Bata Zo ba?
Mama habee tace "batazo ba"
Sai ko haidar yace wallahi naji kuna magana da humaira kunce tazo Kun koreta ai naji ku wallahi Kuma abokina me kanti yace ya ganta danaje siyo biscuits da wata aunty ta bani kud'i na siya.
Sai ko baba ranshi ya b'aci Yana huci yayi kutufoli da roban da mama habee take diban kulin Dan wake Tana wurgawa cikin tukunya akan wuta da sauri mama habee ta mik'e Tana cewa "malam k'onani zakayi ne?
Humaira ko da sauri ta saki turmin da take daka yajin da zasuci Dan waken taja haidar d'aki Tana zagin shi Tana cemai munafiki.
Baba wuyan mama habee ya shak'o Yana cemata ,bazaki fad'amin gaskiya ba ?
Da mama habee taji shak'a sai tace "wallahi ba laifi na bane mijinta ne ya Fara korota sai ta dawo Tana tambayar ka nace bansan inda kakake ba inta damu da son ganin ka taje ta Nemo ka shine tun da ta fita Bata dawo ba atunani na ta koma gidan mijinta ne Bayan Haka bansan komai ba.
Sai baba yace "k'arya kike wallahi ki rubuta ki ajiye watan tashin hankali da rashin kwanciyan lafiyan ki ya kana wallahi inhar banga Ma'u ba ki saka aranki komai ze iya faruwa innace komai Ina nufin koma meye yanzu ba da bane" har yayi hanyar fita ya koma wajen su FU'AD sai ya jiyo kukan haidar da magana k'asa_k'asa cikin d'aki ya dawo ya nufi d'akin yaga humaira ta kama kunen haidar,haidar nata matsar kwallah ......
A fusace baba yayi kanta ya d'auketa da gigitacen Mari Bata Gama fahimtar ya shigo ba ya sake aika Mata da wani a sukwane ta fito Tana ihu ya biyota ya rufeta da duk'a Yana masifa Akan ya fad'i aika_aikan da kukayi shine kike Mai hukunci ku Abin da kukayi in hukunta ku za'ayi da duka ai ko k'ashin ku baza'a gani bama sosai idon baba ya rufe yake dukan humaira da wata igiyar Taya labceciya da haidar ya shigo da ita Yana wasa da ita ,sai ko ta gudu wajen mama habee ,sai mama habee tace Dan ubanki ki gudu kafin ya illata min ke Dan Naga a haukace ya dawo bazan iya tare Miki ba babanki yau babu sauki ,da gudu humaira tayi hanyar waje ta sheka makota Tana hawaye su FU'AD nata binta da kallo suna mamakin meya korota ko gyale babu sai gunjin kuka Haka?
Baba sai cewa yayi haukar da nazo da ita bakuga komai ba ma ku jira na dawo na koma kanki,yayi waje wajen su FU'AD....
Yana fita aminin shi yace "ya dai lafiya Naga Yar wajenka a guje kamar wacce mayunwacin Zaki ya biyota?
Sai baba yayi tsaki da furzar da iska Mai zafi yace "hmmmm da nine wallahi Basu da imani suna da sa hannu a barin Ma'u gidan Nan ita da uwarta su fad'amin gaskiya Kuma sunki su min magana d'aya.
Sai aminin baba da Yaya Jameel sukace "ka bisu a hankali har su fad'a fushin fari ba naka bane Kar ka biye musu"
Sai baba yace "anamiman sunki fad'a ai Kuma Zan iya fito na fito da kowa akan gudan jinina Ma'u na Rasa uwarta macce 'yar halak me biyaya itana nazo na Rasa ta wallahi baze yiwu ba bada son Raina nabar gari ba da Haka bazata faru ba inda Ana ganin idona Abin da yasa ban kawo komai a Raina ba nasan Ma'u ba zuwa Nan take yi ba Dan tasan bamasu sonta bane su da nasan Akwai Rana irin ta yau da ko da Wasa bazan tafi na barta dasu ba,baba Yana fad'a fuskar sa na nuna matuk'ar b'acin rai.
Tun da aka Fara FU'AD bece uffan ba sai yanzu "kawai in Basu fad'i inda take ba ku barni dasu da inspector sani gume Zan had'a su ya dealing dinsu Dole su magantu suyi bayani.
Sai aminin baba da Yaya Jameel sukace basai takai ga Haka bama zasu fada asaukake.
Sai baba yace "hmmmm bakusan taurin kansu bane kamar mutanen farko suke sai sunji wuya zasu fad'a ,sai Fu'ad yace ku barni dasu nace Gobe Nan zamuzo dashi in sun sassauta ma kansu suyi bayani a Nan gida inko sunyi taurin Kai muyi gidan kwalawa dasu. .....haka dai aka tsaida magana su FU'AD suka nufi gida baba da aminin shi aka barsu anan.
********
Husna Tana Kiran maman su hafeeza a waya su gaisa ta tambayeta labarin babanta sai tace Bata da labarin shi Amman tasan Yana Halin lafiya insha ALLAH.
Affan ko yacigaba da nunama Husna kulawa fiye da tada har sadeeq ya Fara fahimtar shi su muhibbat ko Basu fahimta ba sun zata irin son da suke matane Suma Dan kullin cikin k'ara sonta da shak'uwa da ita suke.
Abin ya Fara damun aunty huwaila Dan ta Gama harbo jirgin Affan ta Rasa Abin yi ta Kuma kasa gayama Abban su ,sai ta yanke shawarar Kiran Affan tamai magana Akan Kar zarginta ya zama gaskiya.
Koda ta kirashi ta Gaya Mai ,yaso b'oye Mata sosai ya nuna ba haka bane da yaga ta fututuke Mai sai yace "eh sonta yake Kuma da Aure shi yaga mata.....
Sosai hankalin aunty huwaila ta tashi ,Amman ta daure ta bashi hak'uri ta nuna Mai tun dare be Mai ba ya cireta a ranshi Dan Akwai matsala Kuma bataso ya tsananta tambaya bataso taci gaba da ganin alakar da a tsakanin su ,ze Mata magana ta koreshi.
Sosai Affan ya zurfafa a tunani da son gano matsalar da ammin tashi take fad'a Sam ya kasa ganowa ,Dan Haka yaci gaba da neman zabin ALLAH ,Abin na damun shi har hirar sukayi da sadeeq , sadeeq yace "tunda ammin su tace Haka yayi hak'urin tanada huja Dan Kar ka manta tanason duk wani Abu da muke so uwa uba mu kammu ji take babu kamarta a duniya da tayi sa'ar samun yara kamar mu ,muma Haka muke gani babu Mai sa'ar uwa kamar mu kaga ko tun tasowar mu ahaka muka ginu Aiko Dole mu karbi Abin da duk tazo Mana dashi indai mun sheda bazata cutar damu ba Dan Haka Ina shawartan ka kayi yadda takeso Akwai fa'ida ko hujjar yiu hakan bayyah au d'an uwana sai ko Affan ya kawo Mai duka ya goce Yana dariya.