← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 95

Sashe 21

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

FU'AD ya kwana biyu baya ganin Ma'u Yana so ya tambayi mumcy Kuma sai ya tuna meye hujja shi na tambayan meya had'a da ita ,shi d ya rabu da ganin kazama ma ALLAH ya taimake shi meye zeyi da ganin ta ,Dan Haka ya share ko bi takanta be sake ba sai ma sabgogin shi daya fuskanta tunda Tana gyara Mai saman shi ai shikenan , mumcy ko Jameel ko aunty sa'adiya Babu Wanda ya sanar Mai Ma'u Tana tare dasu .....

Itama ma'un hankalin ta kwance kamar Bata tab'a gamuwa da mugu FU'AD ba ......

Mumcy na zaune sunata Hira da FU'AD sai yayan dadyn su ya Kira ,Tun da yaji mumcy tace "ASSALAMU ALAIKUM" Alhaji Yaya ,sai FU'AD yasan me Kiran Wanda ayanzu Babu Wanda ya tsana kamar shi ,Bayan sun gaisa sai yace Mata Yana Nan zuwa k'arshen wata Nan Kuma in yazo da maganar bikin FU'AD zezo asanar Mai kafin yazo Kuma da iyalin shi zasu Zo ,be jira cewar mumcy ba ya kashe wayar shi .

FU'AD tuni ya kufula , musamman da mumcy ke Kora Mai jawabi Abin da yace , FU'AD ko magana beyi sai had'e gurar sama da ta k'asa da yayi ,mumcy ce ta dinga Mai nashiha da tausar sa da bashi shawara Akan inyanada wacce yake so ya kawo in Babu ya Nemo ko adangi ne har ta dinga lisafo Masa matan da suka dinga nunawa suna sonshi Amman ko 1 be tab'a kulawa ba ,Amman FU'AD ko ufan be ce Mata ba sai ma tashi da yayi ya Fara Hawa bene ze tafi d'akin shi ,Yana cewa in yazo yaga Babu matar ya hak'ura ya barni ai , mumcy sai ajiyar zuciya tayi Tana Addu'a akan zabin ALLAH ,ta Kira Yaya Jameel ta sanar Mai Akan ya Kira FU'AD ya tataushe shi y bashi Baki ......

Kwanci tashi Babu wuya saura kwana 10 zuwan Alhaji yayan baban su FU'AD ,hankalin FU'AD a kwance Amman na mumcy atashe da Yaya Jameel Dan har sun Rasa yadda zasuyi da taurin Kan FU'AD sun zuba Mai ido .....

Ma'u ta samu an samo Mata number baban ta da ta hafeeza k'awarta ,don sa'adiya ta Bata wata Nokia wacce Babu number kowa sai ta mumcy da babanta da hafeeza da aunty sa'adiya kawai ......

Tanata karatun ta ta k'ara kyau ,cikin aunty sa'adiya ya fito dodar don ta Shiga watan haihuwar ta ma .............

[4/23, 4:00 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA*

_RUBUTAWA DA TSARAWA_
BY
*FATIMA ABUBAKAR SHU'AB*
(Maman shaheed)

💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥

Pg 21

*SADAUKARWA GA MASOYAN MA'U MUSSAMAN NAME SAKE UMMU QASEEM*😍🥰

Mumcy ,Yaya Jameel suna cikin fargaban zuwan Alhj Yaya ,shiko FU'AD ko ajikin shi an tsikari kakausa ....

FU'AD Yana zaune a d'akin shi Yana latsa wayar sa ya Shiga IG ,ya fita y koma WhatsApp sai ya Fara viewing status na fanc can y ga na aunty sa'adiya be fiye viewing status na kowa da kowa ba ciki harda na matar yayan shi ,Amman yanzu sai y tsinci kanshi da bud'ewa yayi tozali da pic d'in ta da ita d wata matashiyar budurwa d'anya sharaf Mai asirtacen kyau ,azahiri tamai kwarjini Amman ji da Isa da tak'ama ya Hana ya gazgata zuciyar shi bare shed'an yamai wasiwasi a tunanin shi,Dan Haka y banzatar da Abin ,Bayan y Gama viewing status d'in har k'arawa yayi ,gudun Kar zuciyar shi ta bijiro Mai d wani Abu kawai ya fita ya koma duba sak'onin da suke ta shigo Mai .

Yaune Ma'u da sa'adiya sun fita suna tataki Tana d'an tatakawa saboda ance ta dinga motsawa Dan haihuwa zata iya zuwa Mata koda yaushe ,shine suke fita da Asma'u ,sun fita lpy a hanyar su ta dawowa kafan aunty sa'adiya ta rik'e d'akyar ta samu ta d'aga sun Fara tafiya k'afan ta sake rigewa ko d'agata ta kasa yi sai zama da tayi Kan wani kwalbati dake bakin wani link d'in unguwan su ,Jin abun na kamari gashi Ma'u sai subo Mata ruwan sannu take tun Tana amsawa har ta gagara ,da Ma'u ta rikice har cewa tayi ko ta goya ta? ,Ita dai sa'adiya waya ta mik'a ma ma'un tace ta Kira Mata Yaya Jameel ,cikin sauri da himma Ma'u ta lalubo number d taimakon sunan d sa'adiya ta fad'ama ma'un kamar yadda tayi saving sunan dashi ,bugu 1 ya d'aga ya Fara tsokanan ta wai sai yaushe zata haihune suci hanji ,Jin Haka Abin Yama ma'un banbanrakwai taji nauyin mayarmai da amsa sai tasama sa'adiya wayar a kunne ,sai sa'adiya ta Fara Mai mgn Tana cicijewa ,yanajin Haka yace "Bata da lpy ne ? Tace eh yazo suje asibiti kawai ,da sauri ya tambaye su inda suke ,suka kwatanta Mai Basu da nisa da gida sosai Dan Haka yace gashi Nan zuwa shima yanzu ya Shiga gida Dan Haka zai taho da baby bag din da suka had'a na haihuwar ya kashe waya y tafi a tamanin ....

Su Ma'u basuyi aune ba sai ganin Yaya Jameel sukayi a gaban su ,da sauri yazo ya Suri sa'adiya Tana cijewa yasa ta a mota Ma'u ma ta Shiga sai asibiti ....

Suna Isa aka Shiga d ita labour room aka gwada cm dinta akaga har ya Kai 5 ,Nan da Nan kuwa ciwon ya tashi da gaske ,su Jameel d ma'un nata Mata Addu'a sauka lpy had'e da Kai komo ...

Bayan kusan awa 1 da rabi ,aka sanar musu ta haihu ta Sami yarta mace ,murna harda bada goron Albishir Yaya Jameel yayi ,ya nemi ya ganta akace ya Bari a Gama gyara baby itama a canja Mata d'aki ,Ana Gama wa aka fito da ita har wani runguma ya Kai Mata ,sai d ta ture shi tace "zai balla ta ita Bata d kwari ,ya manna Mata kiss a goshi Yana Mata sannu ,sanan suka tafi d'akin da aka kaisu Dan ta huta ,Ana Shiga ya karbi babyn ya Mata huduba da Ameena suna mumcy ,murna fal cikin Ma'u da Jameel ,da sauri y d'ako wayar shi ya sanarma FU'AD ,sanan mumcy ,Suma sunata murna da Addu'a samun lpy ita da baby ....

Ma'u ma sai murna tanata yi Mata sannu ,Bayan 24hr aka sallame su ,suka tafi gida .....

Aranar mumcy d FU'AD suka Kira sa'adiya suka Mata barka, shiko FU'AD cewa yayi a d'auki pic d'in babyn atura Mai ,Aiko Yaya jameel y tutura Mai kusan 10 harda Wanda na Ma'u ta rik'e babyn fuskarta Bata fito sosai ba saboda Tana murmushi Tana kalon baby Tana sanye da wata marun din doguwar Riga ta yane kanta da gyalen shi tayi kyau Dan koni ban ganeta ba ,har a lokacin da yaga pic d'in sai yaji kamar yace ta juyo yaga fuskarta Dan ya gane wacce ya gani ne a status d'in aunty sa'adiya ,Amman ya basar girman Kai ya cuso cikin lamarin shi na har yanzu bega maccen da ze ma kallo 2 ba daga 1 ya Gama duk had'uwarta ko mulkinta kuwa ....

Washe gari k'anwar sa'adiya tazo daga Ghana Dan asalin su su 'yan Ghana NE sunan ta Aishat ,tazo don ta dinga Taya Ma'u Aiki Kar aikin ya Mata yawa ,Aiko Ma'u taji dad'in zuwanta ta samu abokiyar Aiki Kuma abokiyar Hira don Haka tare suke komai Nan da Nan suka Saba da junan su ,suna Aiki suna Hira ,Ana suna saura kwana 3 mumcy ta biyo jirgin yamma tazo Abuja ganin baby da nik'i nikin kayan arziki na baby da uwar baby ,ranar murna wajen ma'u kamar tayi me har Yaya Jameel d sa'adiya ma sunyi murnar ganin ta ,ranar mumcy tare suka kwana room d'aya da Ma'u da Aisha ,Ma'u nata jinjina rashin girman Kai d Isa da nuna Halin arziki irin na mumcy har ta yadda suka iya kwana d'aki d'aya badan Babu wani d'akin ba a gidan sai don tanason tana son su kwana tare kawai ,sun Sha Hira kuwa har mejego kafin ta tafi ta barsu Dan da wuri zata tafi gobe ,kowa sai cewa yake meya Hana FU'AD biyota su taho ,sai cewa tayi "yace ze Zo Amman ga kayansa su Fara isowa kafin shima yazo ganin mamin shi don shi ya zabi lak'anin sunan d za'a dinga kiranta Dan Yaya Jameel shi yaba zab'i kowa yayi naam d hakan kuwa ...

Ma'u da Aisha kace sun shekara ne sunyi mugun sabo har Aisha naba Ma'u wayarta ta Kali hotuna ko video irin na chats har ta dinga chat a gabanta Tana Bata labarin media ,har take cewa ya kamata ace tanada waya don yanzu duniya Kan kowa a waye yake kodan saurayi ka rik'e babbar waya ,dake Aisha tafi Ma'u wayewa da d'an rawar Kai ,Ma'u dai sai cewa tayi Ni 'yar gidan saurayi ,rufamin asiri ban Isa ba saurayina karatuna ,sosai Aisha ta dinga yima Ma'u dariya harda rik'e ciki ,sai ta Mata uziri da ta gano rashin wayewa ta duniya atare d Ma'u ,sai cewa tayi "lokaci ne ,Zaki ce na fad'a Miki rashin bakisan waye ke bane bakisan me duniya take ciki bane bare kisan waye namiji suwa so da k'auna da ALLAH yake sawa tsakanin mace da namiji ,kema na tabata Dan Baki bada had'in Kai bane ga mazaje Dan baxakice Babu Wanda ya tab'a Yana kyanki ko Miki tayin soyayya bane da kin samu Wanda ra'ayin ku yazo d'aya da duk wanan furucin bazakiyi shi ba ,Amman Bari ki fad'a tafkin son wani kiga yadda labarin zai canja ki rubuta ki ajiye ,Nan gaba kibani labari.....
Chapter 21 · 0% Book details