← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 95

Sashe 56

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan isa su wajen bikin aka dinga tarban su sanin wacece mumcy yasa suka Kara samun tarba Mai kyau wajen su day ban da irin abun da aka tarbesu dashi ba irin na wasu da dama bane ,aunty sa'adiya da Husna sun saki jiki da kowa Banda sanaya da taketa Shan kamshi wasu in sun tambaya akace musu a egy ta taso sai su Mata uziri wasu ko sadai ta Kara kular dasu ma su d'auketa matsayin Yar wulakanci ,su aunty sa'adiya ko kowa jansu yake da Hira da tsokana dama Basu taba had'uwa Haka ba a taro ayanzu mumcy ta dinga nuna musu kowa sosai suka Saba da, FU'AD sai da ya Kira Husna a waya Yana Mata gargad'in wai saura tayi rawa saboda Halin yarinta "Husna tace aa fad'i wani abun Amman ba wanan ba ,Ni ka tabaji ko nama Kama da Karishma? To fad'i wani abun Amman wanan be samu mahalli ba ,sai ko FU'AD ya fusata "ke Rashin kunyar ki Tana Nan ko? To Zan sauke Miki ita wallahi _dirty girl_ kawai ,kafin ya kashe yajiyo ta itama Tana cewa ,na mage kawai, har ya kashe ya sake Kira" ke me kikace? Husna tace "wa ni ba abinda nace ,sai ya kashe wayar Yana cewa zanyi maganin Mara kunya ai.

Sosai akasha hotuna da mumcy da jama'a Yan uwanda da abokanen arziki sai surukanta da akayi dasu Suma har wayar Husna aunty sa'adiya ta karb'a ta dinga musu hotuna da su mumcy da aunty sa'adiyan har sanaya duk nokewarta sai da aunty sa'adiya tasa sukayi da Husna ta janyota cikin su har da mumcy sai da sukayi mutane Bayan an Gama komai suka ma kowa sallama mumcy tasa su a gaba suka nufi gida anata Kiran sallah magriba.

FU'AD ya dawo gida duk yaji gidan babu Dadi ,wai Dan mumcy Bata Nan..........lol saura kuce😝

Maman shaheed
Comments dinku na karamin karfi💃🏼💃🏼
Stikers na sani murmushi🥰
Addu'o'inku na sani nishadi😍
Acigaba da *kaftawa*👌🏻🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀
[4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA*

```RUBUTAWA DA TSARAWA```
BY
*FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB*
( Maman shaheed)

💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥

Pg46

Bayan su mama habee sun tafi Husna ta Adana turaren a d'akinta tanata murnar canjawar mama habee.

FU'AD Bayan ya dawo gida yaci abinci ya fita wai zashi wata unguwa ,tunda ya tafi be dawo ba sai around 9:30pm by d time d'in Husna ma ta Shiga d'aki ta kwanta har bacci yayi awon gaba da ita Dan har sai da ya lek'ata yaga tanata bacci sosai wani Abu ya dinga Mai yawo a kwanyar shi ahaka ya rufe Mata k'ofa ya koma d'akin shi.

Washe gari FU'AD be fita Aiki da wuri ba sai da yasha bacci kafin ya shirya Kuma yace da wuri ze dawo Dan yau Yaya Jameel ze dawo da yamma zai je ya d'ako shi a airport.

Sosai aunty sa'adiya ta dage ta Shiga kitchen Ana shiryama abban mamy girki lafiyaye na taryar shi Husna na tayata da ma'aikata Akwai kitchen a part d'inta Amman tafi so tayi anan saboda Akwai masu tayata ,cikin kwarewa da birgewa suka kammala komai aka Adana Ana jiran me ci.

Mamy kusan yau a hannun Husna ta wuni har da FU'AD ya dawo gida ya k'ara shiryawa ya tafi d'akko Yaya Jameel yanata ma mamy Wasa ya fita wai so yake Dole ta Saba dashi.
Bayan ya dauko Yaya Jameel su dawo ,Yaya Jameel sai da ya Fara zuwa yaga mumcy har rugumarya yayi na kewarta da yayi sanan suka gaisa da ma'akatan gidan sai Husna da ta sakko suka gaisa hannunta rik'e da mamy ,Yaya Jameel ya mikamata hannu Yana murna ze d'auketa Taki zuwa wajen shi mumcy da FU'AD sunata Mai dariya wai ta manta shi Dan Haka sai yayi sabon shiri wajen sabawa da ita ,Dole ya hak'ura da d'aukan ta ya tafi wajen Aunty sa'adiya.

FU'AD karb'an mamy yayi ya haura sama Yana Mata Wasa ,husna kuma Tana k'asa ,mamy ta Fara gajiya ga FU'AD be iya wasan da takeso ba sai ta fara Shirin kuka ,sai ya d'aga waya ya Kira Husna Tana D'agawa yace Zo ki karbeta kin koyamata kin mutane ya kashe wayar be jira me zata ce ba.

Husna dariya ta dingayi har mumcy ma da Husna ta Gaya mata Abin da FU'AD yace ,Tana haurawa ta Sami yanata rarashin ta ,sai Husna tace kawota sai ta karb'eta ta Fara mata Wasa Tana rarashinta har tayi shiru ta Fara ma dariya , FU'AD yazo kanta Yana lakace mata hanci Yana cewa an koya Miki kin mutane ko mamyna,sai Husna ta kalleshi ,sai Fu'ad yace "ya da kallo ko da magana ne? Ko karya nayi Baki koya Mata ba?

Husna dai kincemai komai tayi ,sai murmushi da ta sakar mai.
Sai FU'AD yace "Rashin kunya tayi sanyi kenan"

Washe gari Bayan FU'AD ya tafi office ,Yana zaune Yana Aiki sai yaga sakatariyar sa tazo tace yanada bak'uwa ,Koda yabada izini Akan bakuwar ta shigo ,ba wata bace bak'uwar sai humaira ,tana shigowa ta Fara karema office din kallo ,shiko FU'AD ko d'agowa beyi ba bare yasan wace bak'uwar Dan yasan baida appointment da kowacce mace,Bayan ta gama kalon ta seta nutsuwarta tace "Assalamu Alaikum ina gajiya ya Aiki?

FU'AD d'agowa yayi yace , waalaiki sallam,sai wacce ya kamata na amsa ?

FU'AD cewa yayi "daga Ina?
Humaira fari tayi da Ido kafin tace "nasan bazaka ganeni ba tunda ba'a maka bayanin wacece Ni ba Dan Haka nakeson sanar maka da kaina ,Ni yayar matarka ce baiwar ALLAH Ma'u ,Husna ba ,nice yauarta ita take Bina nazo mu gaisa ne Dan ita ta bani address d'inka tace wata Rana na leko mu gaisa idan nayi hanyar bama so nake ba ta dinga had'ani da ALLAH ,shine fa na samu na leko mu gaisa.

FU'AD kare Mata kallo yayi ,azuciyar shi yace to kaza kanki da motsi, afili kuma yace "sannu yayar Ma'u kinyi k'ok'ari nagode yanzu na sheda ki.

Humaira sai cewa tayi Bari na tafi Dan so nake dan napep d'in da ya ajiye mu ya wuce damu nida mama kasan Tana waje ko zakazo ku gaisa?
Sai FU'AD yace wacce mama Kuma?
Sai humaira tace "laaa mama habeen maman tamu nida Husna ko kazata watace?
Sai FU'AD ya wayance yace oho na fahimta duk ya gaji da gani da sauraron humairan sai Fu'ad yace ok muje na gaisheta ,tare da humaira FU'AD ya sakko duk inda ya gifta sai an girmama shi Ana barka dai oga Ana Mai jinjina wanna abun sai ya karama humaira girman Kai taji kanta yayi girma Tana ji kamar ma ita ake girmamawa har suka sauka k'asa ,har suka fito wajen company din ,acikin adaidaita ya hango mama habee anata Hira da Mai adaidaita ,sai ko ta fito daga ganin humaira da FU'AD ,ita ta Fara gaishe da FU'AD duk da humaira bataso ba ,taso mama habeen ta Bari a bata girmanta Amman Taki sai can tace toh zamu wuce sai wani lokacin ,sai Fu'ad yace "au Zaki Kara dawowa kenan ,sai yace mata a fili to ku gaida baba Dan ALLAH,ngd ya mik'ama humaira wasu kud'i masu kauri yace sa biya Mai adaidaita ,sosai mama habee ta wage Baki tanata godiya kamar me neman dad'i ,itako humaira ji take kamar ta toshe bakin mama habeen ,sai cewa tayi mungode FU'AD Mai adaidaita ja mutafi ,awajen suka bar FU'AD yanata mamakin abun kamar a mafarki....

Yana tunanin har yaushe Husna tasan wajen aikin shi da har zata turo yayarta? Kai Akwai ayar tambaya a lamarin Naga kamar Akwai bambancin tarbiya tsakanin su first ya kamata nasan ya suke kafin nasan Abin yi ......

*********
Mamy dai da kyar ta Sha Kan dady har yabar sanaya ta d'an zauna Dan said da suka Kai Ruwa Rana dashi da ita kafin itama sanaya sai da ta dinga kuka da rok'o da magiya kafin ,chart Kuma a waya sai Fu'ad ya Mata magana sai taga dama take amsa Mai shima sai ya fita harkan ta in Bata amsa ba.

Bayan FU'AD ya komo gida be cema Husna komai ba sai da suka kammala komai suka hauro sama zasu kwanta har zata tafi d'aki sai ya kirata ta Zo.

Sai yace ke wace humaira ma ya kuke da ita ?
Sai Husna tace "yayata ce"
"Sai ya sake cewa dukanku mama habee ce ta haife ki?
Sai husna tace "eh " agajarce alamun ta Fara k'osawa da tambayoyin shi ,sai Fu'ad ya sake cewa karki b'oye min komai tambayar da na Miki tanada mahimmanci agareki inkika min karya Zan had'a da Abin da mumcy ta gayamin kin gane ai ko?
Sai ko Husna tace hakane ,barin gayamai gaskiya Dan bazan karyata mumcy ba ,sai tace mama habee ita ta haifi yaya humaira Ni mamana ta Rasu tun Bayan da ta haifeni ,wani abune?

Sai FU'AD yace "hmmmm biri yayi Kama da mutum ,da zakimin karya" Amman Baki da matsala dasu ko? Husna tace eh babu duk ta b'oye mai,sai yace to jeki ...

Sosai FU'AD ya Fara hassaso wani Abu.

FU'AD yaki fad'ama Husna ne saboda ganowa da yayi Bata da masaniya da zuwansu ,Dan Haka yabar zancen.

Washe gari ,Haka ya tafi office tare suka fita ma da Yaya jameel Dan Akwai aikin da zeyi a company dinsu suna Hira ta d'an uwa da d'an uwa har suka Isa.
Chapter 56 · 0% Book details