Sashe 27
Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sosai Ma'u ta saka batun Auren FU'AD a ranta da kyar take yaki da zuciyar ta wajen kawar da wasu tunanuka akai ,Amman Abu yaci tura ,ta Kuma kasa gane dalilin hakan . FU'AD Yana Jin d'aci da k'unar Rai inya tuna da auren sanaya da aka lik'amai ,da ya Kuma tuna Wanda mumcy tamai na huce takaici sai ya rasa inda zesa Kan shi ma ,har tambayan kanshi yake,wacce mumcy ta ke Shirin huce Mai haushi da ita ,inma makauniya ce ko kuturwa ko gurguwa ita dai mumcy ta jona Mai hankalinta kwance Bata tunanin Halin da ze Shiga ? Shidai yanzu har Yama rasa Abin yi..... Number B2k ya Kira ya Fara cemai Kai abokina nifa Ina Ruwa, B2k yace kamar ya ? "FU'AD yace hmmmm banma San ta Ina Zan Soma ba ,kawai dai Kar kuji Abu kamar saukar aradu shiyisa Zan sanar ma yanzu ,nifa angama Dani Dan Babu saurana , B2k yace abokina ninkeni kake baibai ,futo min a mutum pls"FU'AD yace ,hmmmmm anyi gunduwa gunduwa Dani an rabama wasu Mata Ni ,dayar ma ko sanin ta ban samu Halin yi ba dayar ma karkayi tunanin Dan na Santa ko da amincewa ta ne ko inaso ,kawai dai anbadani garesu ,in baka tab'ajin Auren gagawa ba to yau ga Auren katsaham ,wai ni za'ama Aure Kuma har Mata biyu ,pls Kaine mayen Auren kazo ka fanshe su a sadaka ma Ni dukan su har sadaki zanma wlh na maka Al'k'awari ...... B2k ya bushe da dariya ,yace abokina nasan baka Shan komai sai su easy da juice da su Ruwa nine ma sheda da sai nace ko kafara kurb'e kurb'e ne ko kana afa morijiwana da sauran su kasan me kake fad'a kuwa ? FU'AD tsaki yaja yace Kai fa wani lokaci kamar kaci Kai ,kawai ya kashe wayar shi . B2K ya Kuma bushewa da dariya sai da ya gama darawa sanan ya Kira abokin nashi yasan ranshi y b'aci ,kin d'agawa FU'AD yayi har sai d B2k ya tura Mai sak'on karta kwana na ban hak'uri sanan ya samu ya kirashi ya amsa wayar ,sosai FU'AD ya ma B2k bayanin komai , B2k ma ya fahimce shi ya Mai Al'k'awari zuwa gidan Kuma insha ALLAH. Mamy nata fama da sanaya itama Tana lalab'ata Dan taso bijirema Auren ta hurema sanayan kunne Kuma wata magana da dady ya fad'a Mata shine yasa ta d'an hak'ura har take ba sanayan Baki Kan ta bi umarnin dadyn ta shine biyaya da sakamakon gatan da ya nuna Mata Kuma yake Kan nuna Mata ,ita dai sanaya gidan tarbiya rashin kunya ta dinga yi har Tana cewa Suma Auren cushe aka musu? Ai na soyayya aka musu danme ita zasuci amanar ta Haka kamar siyota sukayi a kasuwa , mufeeda da haushi d takaici ya Gama cikata duk fitsarar yayar ta anrasa me fasa Mata Baki sai Kuma lalab'ata da sukeyi kamar tsoron ta sukeji ,ita wlh tafi tausayin mijin da za'a bata ma wlh ,Dan zega abubuwa ,har mamaki take ya akayi Halin su ya bambanta Dana yayar ta? Kuma iyaye guda ne suka haife su suka Basu tarbiya Kuma a hanun su suka taso tun k'uruciya har kayau ,lallai ta yadda da kalmar mlm bahaushe ta ALLAH d'aya gari bamban, halayar kowa Kuma daban Amman duk d Haka me Hali madai musamman yake , ALLAH ya shiryeta da gagawa inba hakaba za'asha fama a gidan miji . Mumcy ce taje wajen baban Ma'u ita da Yaya Jameel batare da sanin FU'AD ba ,sun tafi Kan maganar Auren FU'AD da Ma'u ,sosai baba yaji dad'in maganar Auren Ma'u ,inda matsalar take beyi maraba da Abin ba ,da akace FU'AD ne ze aureta hamshakin matashin Mai kud'i kamar FU'AD Sam be shirya siyama yarsa wulak'anci da cin mutunci ba ,talaucin shi be Kai Haka ba Dan Haka baba fir yace be amince ba Sam , mumcy d yaya jameel suka kad'a suka Raya Sam yak'i ,sai da mumcy ta dinga bashi Baki tace Mai Kar ya musu Haka Mana suda suka dogara da ALLAH da Kuma shi wajen samun amincewar Ma'un don shine tal zai taimaka musu da taimakon shi ,don shi yisa Basu sanar Mata ba don su bashi ikon shi da k'arfin shi da ALLAH ya bashi a matsayin shi na uba ga Asma'u ,Kuma sunmai Al'k'awari rik'e Asma'u da Amana Kuma Babu wulak'anci ko tozarci tsakanin su fa Asma'u, Kuma basuyi Haka don nuna ikon arzikin su Akan su ba ,basu yi haka don Raina talaucin su ba ,hasali ma sunyi hakan ne don girmamawa da ganin mutuncin juna da yabawa da tarbiya da Halin datako na gidan nashi . Sosai maganganun mumcy suka Shiga baba ,Amman duk d Haka Yana dogon nazari ,ya Kuma yaba Hali irin nasu na d'aukan duniya sannu ahankali Basu d'auki kansu maysayin da wasu masu arzikin suke Kai kansu ba ,yaji Dadi sosoi ya amince musu yace Amman da sharad'in bazema Asma'u dole ba wanan shine sharad'in . Babu ja'in ja suka Amince suka Mai godia , Yaya Jameel ze Mai wata dunk'ulaliyar kyauta don Jin dad'in Abin da ya musu , mumcy ta yi gagawan hanashi da ido da Mai nuni da hannu ,ya fasa suka Mai godiya suka tafi ,amota mumcy take sanar Mai ai zaka sa kwab'ar mu tayi ruwa ,wanan d kake ganin shi jajirtacen datijo ne Mai kudin duniya ,ai duk wani kyautatawa da bajinta da zamu Mai abari sai Bayan bikin FU'AD da Asma'u wanan shine ze zama tukwuicin yaba kyauta ,Amman ba yanzu ba gudun Kar abata rawar da tsalle ,Ina fatan ka fahimta ko ? Sosai jameel ya fahimci manufar mahaifiyar tashi . Baba Yana Shiga y kasa sanar ma da mama habee maganar gudun maganganun da zata jefi Ma'un tasa dasu ,shima Kuma be tsira ba ,dama kulin cikin jifan ma'un da jafa'i take wai ita da dawowa sai ta kawo musu tsarabar yawon ta zubar wato d'an shege take nufi ,baba saidai ya nema wa ma'un tsarin ubangiji yace bakinta ya sari tulun Kashi ,y fasa fad'a ya bar gidan ma . Barin Kashi aciki baya maganin yunwa ,Haka baba yayi shahada yasa audiga ya toshe kunnen shi ya fad'ama mama habee Amman be bayana Mata Wanda ze auri ma'un ba ,masifa da bala'i da mugayen maganganun da take jefo musu ya Hana baba bayyana Mata ko waye mijin da Ma'un zata aura atunanin ta wani Sha katafin ta samu a Abujan ,shiko baba Jin masifar na neman harzuk'ashi ya fice ya bar Mata gidan cikin daren gashi ya gaji Yana son hutawa don Haka baba yace dole shima ya k'ara aure ya gaji da masifa d bala'in habee tin tanayi a b'oye yanzu a bayyane take yi,in yayi Auren ma raba musu gida zeyi ALLAH yagani baze Rasa yadda zeyi ba sai ya samo ko wacce Bata haihuwa ne ko datijuwa Mai Halin kirki ko ya mutu cikin sutura ta mutunci . Da ma'un ta Kira babanta suka gaisa Yana son sanar Mata Yana tunani ya Kuma yadda kamar yadda sukace Bata sani ba yaga alamun hakanne ,don Haka yace Mata ,ze Mata wani Abu amatsayin shi na mahaifi agareta dafatan zata karb'i abun hannu bibiyu bazata bashi kunya ba saboda tasan baze cutar da ita ba inko tak'i karb'an abun to ta d'auka tamkar ta tozartashi gaban mutanen dake cikin duniya ne ,ya samu k'arfin gwuiwar furta hakanne sakamon munanan kalaman habee da nuna bak'in ciki k'arara Akan lamarin shi yisa ya amince yakeson yima ma'un umarni da amincewa itama ,sosai hankalin ma'un ya tashi burin ta baba ya fad'i buk'atar shi tamai ko menene Dan tamai Alk'awarin hakan ,baba dai kasa fad'a yayi sai cewa yayi ze sake kiranta Amman kartasa komai cikin ranta ,Yana diya da irin yarinyar da ALLAH yamai kyauta da ita ,sosai Ma'u ta gano baban najin nauyinta ne ko nauyin fad'an maganan ,Dan Haka ma'un tabashi hak'uri ta k'arfafa Mai zuciya har ya fad'a Mata maganar ,Amman ya nuna Mata Akan wanine yakeson aurenta Kuma iyayen shi sun Zo ,ya Kuma yi bincike akansu sunada nagarta da datako ,sosai Ma'u taji abun kamar saukar aradu Amman bin ummarnin da Tama baba Al'k'awari ya zama dole Bata da zabi ko neman shawara atake ta amsa da sanyayiyar zuciya tanata danne damuwarta Kar baban ya fuskanta ,Jin ta amsa sai Addu'a yake Mata da shi Mata Albarka ,sanan yace ta kashe wayar shima ze kirata yaji ko Tana lpy ,Bata iya amsawa ba ta kashe wayar jikinta a macce sai kuka ya kwace Mata Kuma ...... Aisha ce ta shigo ta sameta Tana rabza kukan sosai take rarashinta Tana tambayan ta ,ganin Taki shiru Kuma tak'i fad'a Mata kawai Aisha ta kwalama aunty sa'adiya Kira ta shigo suka Fara tambayanta gaba d'ayan su .... Sosai ma'un take kuka ta Gaya Mata duk yadda sukayi da baban ta Bata b'oye musu komai ba ,sosai Suma suka tausaya Mata ,aunty sa'adiya Tana cewa "oh keda FU'AD irin k'addarar da ta fad'o muku kenan? Gaban ma'un ne yayi mumunan fad'uwa k'irjin ta na bugawa da k'arfi da k'arfi ,batare da tasan manufar hakan ba ....... Kukane ya sake kwace Mata ,sai su sa'adiya da Aisha suka koma rarashin ta da Mata umarni da bin mahaifinta in ALLAH ya yadda zataga daidai arayuwar ta ,tayi hak'uri da yadda rayuwa tazo Mata da sannu zata cinye jarabawar ubangiji ,sosai ta samu hankalinta ya kwanta da taimakon nasihohin su ga wani kulawa ta musamman da suke Bata tamkar ciki guda suka fito . Sa'adiya Kiran Jameel tayi ta sanar Mai tashin hankalin da ma'un ma take ciki Bata rufe Mai komai ba murmushi Jin dad'i yayi Amman sai ya nunama sa'adiya ya tausaya Mata ,Amman su cigaba da rarashin ta da nuna Mata bin iyaye wajibine da sannu zataga sakamako Mai kyau,shi Kuma ze zame Mata uban d'aki nagari a cikin Auren insha ALLAH,sosai sa'adiya tamai godiya ta kashe wayar tanajin dad'i har ranta ,ta sanar ma husna yadda sukayi da jameel ,taji dad'i sosai don dama shine fargabanta na farko inda za'a Sami kud'in da za'a Mata Abin da ya samu na Auren , Aisha ma tayi k'ok'arin kawar Mata da damuwa ta hanyar d'ebe Mata kewa da