← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 95

Sashe 2

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

FU'AD bin wayar yayi da kallo ,Yana zargin ko Ran mumcy ya sosune ,Dan Haka atake yasake Kira ,sai d ya Kira so 3 yanajin _busy_ sai da ya sake Kira sanan ta d'aga .

Cikin ladabi kamar Yana Gabanta ,yace mumcy ta ALLAH ya hucci zuciyar uwa tagari banyi hakan don tab'a Ranki ba naji kinata Danna min bussy mumcy ta ?

Mumcy tace ba busy na dannama ba muna waya da yayanka ne akan maganar dawowan shi .

FU'AD yace ok mumcy barin kirashi mu Gama kashe boss d'in Dan tunjiya muka Fara mgn bamu k'arasa ba ya kashe wayar cike da kewar mahaifiyar shi.

Bayan Asma'u ta Kamala komai ,ta sanar ma mumcy ko Akwai wani Abu da zata Mata ?

Mumcy tace Babu, zaki iya tafiya Koda wani Aikin Da zakiyi agida ,nagode inji mumcy , Asma'u tace nice da godiya hajiyar Girma ,mumcy tayi murmushi tace har canjin suna na samu Kuna son lak'abamin sunaye kala_kala , Asma'u tace Ai kin cancanci hakan ne ,na Tafi sai ALLAH ya kaimu , mumcy tace ALLAH ya nuna Mana goben muna masu lpy Kuma Rayayu , Asma'u ta amsa da Ameen ta wuce gida cike da fargabar Abin da zata tarar na masifar mama habee.

Kafin Asma'u ta wuce gida sai da ta biya ta gidan su Hafeeza ta karbi number ta ,ta tafi wajen D'an Bala communication ta karbi waya ta kirashi Hafeeza ,Bata d'auki dogon lokaci ba aka d'aga ,cikin murna Asma'u tace Hafeeza y karatu ya 'yan uwanku nacan?

Hafeeza ta Gane me mgn ,tace "lpy kanwata ya gida y hak'uri da Rayuwa?

Asma'u tace "muna Kai ,Kar muja kud'i da yawa mgn Zan Miki Akan *RIK'ON KWARYAR* Da Kika bani dama ,wlh na fuskanci Akwai d'an rainin wayo agidan ke Kuma kince min gidan Babu matsala ta ko'ina kin nunamin basa kyamar talaka ,Naga hakan daga wajen hajia babba Amman wani d'anta Sam baze barni zaman gidan ba karkiji na ajiye Miki *RIK'ON KWARYAR* Da Kika bani kice ban kyauta ba ne yasa na Fara sanar Miki .

Tunda Asma'u ta Fara mgn sai d takai aya ta tsaya wai gudun Kar aci kud'i da yawa .

Hafeeza ce taja ajiyar zuciya sanan tace "k'anwata ki kwantar d hankalin ki yanzu mgn bazatayi ba Naga kina Sauri ki Bari anjima kije gidan mu Zan Kira mama nace inkinzo tamin flashing sai na kiraki muyi mgn kinji ?

Asma'u taji dad'i tace to ,ta kashe wayar ta mikama D'an Bala communication wayar akan taji nawa ya cajeta ?

Bayan y duba yace ,kudinki 150 ma'u ,ta ciro wata cikurkud'ad'iyar D'ari guda ta bashi tace zata ciko Mai Dan ALLAH ,duba d yanayin ta da zargin ukubar d takesha wajen kishiyar mamanta yasa shi cewa yabar Mata Babu damuwa ,Aiko tayita Mai godiya ta tafi ranta fes bame binta bashi .

Tana Shiga gida bakinta d'auke da sallama ,tozali d mahaifinta da tayi yasa bugawar zuciyarta ya ragu Dan Ana Rage wani Abu daga cikin kiyayar da ake nuna Mata agidan in Yana Nan .

Tana Shiga tace baba sannu da gida ,mama habee sannu da gida ,baba ne y Fara amsawa sanan mama habee ta amsa Babu yabo Babu falasa ,babane yace kinci Abinci ma'u ta?

Kafin ta bashi amsa ,haidar karamin D'an mama habee yace gashican akicin barin d'auko Miki Yaya ma'u dake jinin su ya had'u da shi ,mama habee Babu bakin mgn Haka ta zuba Ido taga Wanda ze d'auko Mata Dan Bata zuba Mata ba Sam ,nata n tunkunya asandare.

Aiko na Yar gwal ya d'auko ,humaira ya ajiye gaban ma'u ,takaici y rufe mama habee tayi mgn baba yace Babu banbanci tsakanin ma'u da humaira Dan Haka ta had'iyi bak'in ciki da takaicin haidar .

*Muje zuwa Ruwan comments Ruwan typing*💋💋
[4/23, 4:00 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA*

_RUBUTAWA DA TSARAWA_
BY
*F.A.S*

_Shafi Na 3_

{Nafi son Ruwan comments ba heart,da stikers ba guys ,duk d Ina godiya d hakan ma}

Bayan ma'u ta kammala cin Abincin ta rage taje ta ajiye a kitchen ta wanke hanun ta ,ta wuce tsohon d'akin mahaifiyar ta da ta shud'e .

Bayan humaira ta dawo daga gantalin asarar ta ,wuf ta afka kitchen da niyar neman Abinci in Yar Aiki ta, ta gama wato mama habee sbd tsabar tausayi da imani irin na humaira .

Ko da ta shiga bataga sakayayen abinci ba kamar yadda aka Saba killace Mata sai ragowar d Ma'u ta Rage sai sandarare na tukunya ,Dan Haka a fusace taje take tmby mama habee Abincin ta?

Mama habee dama a sama take yau tace Yana gidan uwarki Dan ubanki gantalaliya Mara aikin fari bare na Baki ,inkinga dama ki duba tukunya in yamiki sanyi Kya d'umama .

Humaira ta tab'e Baki tace mama habee y ba'a zubamin an boye min ba Dan ALLAH ?

Mama habee tace Mai kafar yawo ,Wanda n Adana miki ya zamo Rabon kanwarki ma'u Dan ita ta cinye .......fuuuuu humaira zata tafi hukunci .......mama ta dawo d ita d cewa to Alkaliya sarkin hukunci kyaji yadda akayi kafin ki d'auki hukuncin ai de ko?

K'aninki nee ya d'auko Mata y Bata tacinye ,kinsan haidar d imanin d bansan inda ya gado shiba , kamar kaninta uwa 1 uba 1 D'an bantan uban yaro .

Humaira aka furzar d hucin takaici akace "wlh taci sa'a ,shi Kuma ze dawo naji Dani d Ma'u waye ahak'un shi sokon yaro kawai t fice ta tafi cin sandarare dan lalaci baze barta ta d'umama ba .

Bayan ma'u ta huta ta share gidan ,baba y shigo tace Mai zata gidan su Hafeeza Kai sak'on da hajiya babba tabata takaima maman su hafeezar ,baba yace sai ta dawo Amman Kar ta Jima ,tace "toh ta fice zuwa gidan mamar Hafeeza Dan yin waya da hafeezar"

Tana shiga bakinta d'auke d sallama ,ta tsuguna ta gaishe d mama .

Mama ta amsa cikin sakin fuska ,tace "kinzo?

Ma'u tayi murmushi tace "eh mama"

Mama tama Hafeeza flashing ,ba'a Jima ba Hafeeza ta Kira mama taba Asma'u wayar ta fice ta Basu guri .

Hafeeza d Asma'u,anata Hira akan FU'AD Asma'u ta dage barin Aikin zatayi sbd wulak'ancin FU'AD tun ba'aje ko Ina ba ,Hafeeza nata Bata hak'uri Tana nuna Mata Ribar Aikin da Kuma cewa shi Haka yake Amman Kuma yanada kirki duk Wanda ta tmby ze fad'a Mata kyawawan d'abi'u da halayar FU'AD ta gwada tmby wasu ma'aikatan gidan Kuma taji ,sosai Hafeeza ta kwantar Mata d hankali ta Bata hak'uri da dabarun yadda zasu zauna lpy da FU'AD Amman ta koya Mata dabara in yazo Mata a Wuta ita Kuma ta fito Mai a Ruwa Dan ta kashe shi Dan cin zarafi da tozarci bashi da dad'i ba kowane ze iya jurewa ba , Asma'u ta gamsu da shawarwarin Hafeeza ta Mata godiya sukayi sallama ta kashe wayar , Asma'u Tama mama sallama mama tace "ta gaishe da mutanen gidan"

Bayan komawar ma'u gida ta samu humaira na cin zalin haidar ,sai take tmby dalili ,Aiko humaira ta dawo kanta d masifa,mama ta Shiga mak'ota tsegumin d ta Saba ,Tana shigowa tajiyo hayaniya ganin Ma'u ake tsigalewa yasa da bazatayi mgn ba sai ta hango haidar autanta Yana rusar kuka shine fa ta magantu ,Ma'u tace haka kawai take cin zalin karamin yaro Dan an tmby dalili shine ta dawo Kan mutum ita d Bata k'unar zaman lpy Sam.

Aiko mama tace Dan ubanki me y Miki ? Humaira t turo Baki ai zagina yayi d rashin kunya ,sai baba y shigo shima y samu Ana tmby ba'asin dukan haidar d humaira tayi .

Shiko haidar Yana kuka yace k'arya ne wlh wai Dan dazu n d'auko Abincin d aka ajiye Mata naba Yaya ma'u shine take dukana yanzu .

Anan mama ta gano dalilin duka ,shima baba Ranshi y b'aci ya Fara yi ma humaira fad'a Yana nuna Mata d ita d Ma'u duk 1 suke a wajen shi kuma karta sake dukan Mai autan shi ,mama ma taji haushin dukan haidar d'in ta dinga zazagama humaira Ruwan fad'a har sai d tayi nadamar hukuncin d tayi .

***********
Washe Gari ma'u tayi wanke wanke ta share gidan Bata tsaya jiran dumamen tuwon mama habee ba ta yima baba sallama Kan zata tafi gidan Aikinta ,ya Mata nasiha kamar kulin to ma'uta ki kula da kanki na Baki amanar kanki da kanki ALLAH ya Shiga cikin Al'amarinki ako Ina kike .

Asma'u tace Ameen baba , insha ALLAH sanan ta fice Tana cema mama habee Sai na dawo mama ,ko ci kanki batace ba sai tabe Baki da tayi inda sabo ta Saba gwanda a tab'e Mata Baki ma d ace Mata wani Abu Dan cin mutunci d zagin mahaifiyar tane ze biyo baya .

Yauma kamar kulin d ta Shiga harabar Gidan motar Nan me sata fad'uwar gaba tafara tozali da ita ,ta wuce tayi sallama a part d'in hajiya babba cikin ladabi da biyaya Babu kowa a parlour sai FU'AD da yake tsaye Alamar wani Abu yake jira .

Da ya juyo d niyar Amsa sallamar Dan yaji sautin muryar har kwanyar shi y juyo d niyar ganin balarabiyar da tayi sallama kawai yayi tozali da wacce yafi Tsana a yanzu cikin Rayuwar gidan mumcyn shi ,kawai yayi tsaki batare da ya amsa sallamar ba ,har sai d ta Kara Bayan tasan yajita kawai baze amsa Mata bane ,sai ga Hari Mai Aikin su ta fito dg kitchen sai yace yauwa Hari Zo ki amsa sallama anayi ,ta taho d niyar bin umarnin uban gidan nata ,Abin Yama ma'u ciwo .

Hari d sakin fuskarta tace , waalaiki sallam Asma'u kamar yadda sukaji mumcy na fad'a ,Aiko ma'u tace Ita dai sallama ta kowa d kowa ce kuma Lada mutum yake samu inya amsa ta .

FU'AD ya juyo afusace yace " ke dawa kike"? Mema Kika ce? Sai ga mumcyn ta fito Tana ma FU'AD mgn .

Ma'u ganin yadda y taho azafafe Kar Taci bugu sai tace mekaji nace ? Yalabai? Ganin mumcy ta fito sai ta juya itama tace gaishe kafa nake tayi yafi so 5 kak'i amsawa .
Chapter 2 · 0% Book details