← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 95

Sashe 87

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan jirgin su ya d'aga zuwa Ghana,Suma su Aisha Ana can anata faman Shirin tarban jama'ar ta Dan ta Gama musu tanadi.

Su humaira anata ahagali Aure wani satin angama tsara komai mama habee taso aje aga gidan angon yace ba sai sun wahala ba sudai Amarya kawai zasu kawo Akwai komai,mama habee aka buga shewa da guda aka Fara sakar ma baba habaici Ana cemai ya rik'e gadon bonon da yake shirin tozarta humaira dashi kamar yadda aka Kai Husna zikau ta dangwali arziki itama humaira haka zata tarar Dan haka basa buk'atar komai nashi.

Baba murmushi ya sakar musu Mai Kama da gargadi ,kafin yace ,ba girin girin ba dai tayi Mai,kuyi yadda kuke so habee ALLAH ze nuna Miki aikin ki tun aduniya kafin ki shude.

Mama habee d masifa d tsiwa tace ,zatayi Mai har da naso bakinka ya sarin bangon gidan ka, Kuma wlh babu wani aikina da zangani.

Baba bar Mata gidan yayi Yana Mata fatan shiriya.

*INDIA*........
Aunty huwaila ta Gama shiri tsaf akan yayar ta ga wani shak'uwa da yake Kara Shiga tsakanin su har suna Jin kamar Kar su rabu gashi sunaso su had'asu da Husna yarta kodan samun farinciki Husna d yayar ,Dan jiya d Husna ta kirasu zata musu sallama tafiyar su Ghana sai da sujaji kamar su Gaya Mata Amman aunty huwaila ta fasa Dan tafison tayi tozali da ita har baba da tafiyar iya Affan da sadeeq ne Amman yanzu tafiyar har aunty huwaila d su muhibbat d Husna Dan ba zuwa sukeyi ba Dan Haka zuwan nasu ya Kara Nisa Amman Nan d sati 1 zasuzo daidai da bikin humaira.

Matafiya sun sauka lafiya sun Sami tarba na girma,Aisha sai sunkuyar da Kai takeyi na kunya aunty sa'adiya kuwa ta saki jiki sai murna ganin iyaye da Yan uwa takeyi.

Bayan sunci sun Sha aka Basu masaukin da zasu huta har kwana kafin suyi abin da ya kawo su.

Sosai suka dinga Jan Husna Akan ta saki jiki dasu,sun sanar ma mumcy saukan su lafiya ta musu fatan huta gajiya.

Bayan sun huta aka musu iso zuwa gun baban su aunty sa'adiya suka gaisa yanata farinciki da zuwan su kafin FU'AD da B2k suka ba Yaya Jameel d baban nasu waje Dan isar da sak'on abokin FU'AD din.

FU'AD ne ya umarci Husna d ta kirama abokin nashi sahibar shi,Husna har Fallon Tama Aisha iso suna ganawa da masoyin nata shima FU'AD acan nesa da su Yana hirar Dole da Husna Dan gani yake kamar antakura shi gashi kwanan Nan sai ya dingajin wani Abu game da husnar sai yayi kamar ze bayyana Mata tsagwaron son ta sai zuciyar shi ta Hana shi ta nuna Mai faduwar mutuncin shi da darajar shi ne ze billo baya sai ya Adana zuwa lokacin da Hali zeyi.

Husna ko sosai ta saki jikinta Tana Jan shi da Hira Yana amsawa Yana Mata tambaya Tana bashi amsa itama sunayi suna kallon dacewar da B2k da Aisha da sukayi ,can Husna take ba FU'AD labarin zuwan su aunty huwaila 9ja da ahalin ta har matar da ta bashi labari Mara lafiyar Nan Amman yanzu ta Sami sauki ,sai Fu'ad yace "Amman zasu kwana biyu har zamu koma mu same su ko?

Husna "eh" tace Mai.

Husna fata Fara Gane Fu'ad Yana son ta ya damu da ita ba sai da ta nuna Mai rashin Jin dadinta na halartan bikin yayarta humaira da bazatayi ba.

FU'AD futitikewa yayi Yana Mata fad'an rashin sanin ciwon kanta mutanen da suke son ganin bayanta da zasuga ranta da zasu d'auka Amman ita Tana damuwa dasu,ganin yadda yake bilhakki da gaskiya yasa ta fahimci sai ka damu da mutum kake tatalin lafiyar shi Dan Haka yace ko sun koma babu inda zata zeje har gida Yana baba hak'uri da uzirin yin hakan.

Suko su B2k da Aisha anata zuba luv ,sai da aunty sa'adiya da Yaya Jameel suka shigo suka raba tsakanin masoyan hudu.

Aunty sa'adiya ce ta shawarce su da fita Sudan ga gari ,ta had'asu da wani k'anin ta saurayi Amaduu su sai gobe sai su fita gaba d'ayan su suyi ziyara gaba dayan su.

Basu dawo ba sai gab da magrib ,su Husna anata hirar soyayya da Aisha.

Bayan sunje masallaci sunyi sallah dawo aka kawo musu abincin suka Dan taba Hira gaba d'ayan su zuwa Bayan Isha kowa ya nufi masaukin da aka bashi Dan kwana.

FU'AD ko Abu zai tambayi Husna sai ya kirata a awaya su Aisha sunata tsokanar ta wai ta zama rik'e wuyan Fu'ad Amman ya dinga basarwa Bayan mun sani.

Kusan kwana sukayi suna Hira.

Washe gari da safe har d Husna aka Shiga kitchen aka shirya girki maman su Aisha nata yabon kirki irin na Husna har suka kammala suka kaima su Yaya Jameel nasu Suma sukaci nasu kafin sukayi wanka suka shirya Dan ziyara zasu yau da ganin gari.

Bayan sun fito cikin Shirin driver ya d'auki mota Yaya Jameel ne agaba dai matan na baya su FU'AD na tsakiya suka nufi gidan yayan mahaifin su aunty sa'adiya,isar su aka tarba Mai kyau da girmamawa.

Bayan sun fito suka nufi gidan kakanin su aunty sa'adiya ,kusan ziyarar Nan Tama sa'adiya da Yaya Jameel Dadi Dan be tab'a wanan ziyarar ba sai sanadin neman ma B2k Aure,kusan hakanne ga Aisha Dan ko yanzu dangin ta sunsan wa zata aura.

Sosai sukayi ziyara suka zaga gari sunga gari daga k'arshe sukaje wani wajen shakatawa kowa da wyfin shi Husna ma da FU'AD har bakin Ruwa sukaje gab da bakin ruwan ne wani irin jiri ya dibi Husna tatafi luuuu kamar zata afka ruwan badan Fu'ad yayi sarin rikota Yana tambaya ta lafiya ba da ta fada.

Runtse ido tayi d sauri hankalin su aunty sa'adiya d su Aisha y dawo kansu FU'AD da Husna, gefen ruwan ya zaunar da ita Kan wata kujerar da ika yita ta gini Mai ban shaawa yayi Yana tambayar ta meya sameta?

Bud'e Ido tayi d kyar tace "babu komai ji tayi jiri ya dibeta kawai Amman lafiya Lau take"

Duk sun gamsu da bayanan ta sai Sanu! Sannu!! Suke Mata Bayan sun Dan taba Hira Awajen ganin walwala ta Dan kaura daga fuskar Husna sai Fu'ad ya nemi da su koma gida kawai,sai Yaya jameel yace "toh muje mudan Sha ko juice ne sanan sai mu tafi,duk acikin wajen ne dai ,da taimakon aunty sa'adiya sukaje wajen.

Wani abokin Yaya Jameel ne ya kirashi a waya Wanda ta sanadin shi suka had'u da aunty sa'adiya har ya aureta yake sanar Mai ya dawo gari insun shigo su nemeshi Dan ALLAH.

Sai Yaya Jameel yace "sun shigo har suna Shirin komawa jibi Amman gone zasu kawo Mai ziyara dafatan yanada masaukin bataliyar Baki Dan sun kusa su d'ari,dariya Abdulmalik yasa yace "ko su million ne yanada masaukin su ko shekara zasuyi Yana maraba dasu shida me d'akin shi" Yaya Jameel yace toh gobe zasu Zo insha ALLAH,sanan y kashe wayar.

Bayan sun koma gida Husna duk jinta take wani iri Taki gayama kowane sai k'arfin Hali da takeyi kawai.

Ranar aunty sa'adiya da Aisha kusan kwana sukayi suna Hira Amman Husna tuni tayi bacci Dan ko wayanta a silent tasa FU'AD ya kirata kusan so 3 Amman bataji ba bare ta d'aga,Dan yad'an kula da yanayin ta ba kamar yadda sukazo ba ,Amman ganin ba ita tafad'a Mai da bakin ta ba sai ya kyaleta shima.

Washe gari suka dunguma sai gidan su Abdulmalik sunga tarba daga gareshi da Matar shi anty ayna sun Sha Hira sosai Husna ko sai yake kawai takeyi.

Basu bar gidan ba sai yamma lis sunso kowama a washe gari Dan adaren ranar Jameel ya nemarma B2k izinin neman Aisha aka tsaida magana da niyar manya zasuzo asaka ranar bikin Nan bada jimawa ba Amman anbashi Aisha Albarkacin Jameel ,da kyar mahaifin su aunty sa'adiya suka ce su Bari sai jibi sai sutafi ,ganin sun gaji tarbiya Basu Saba jayaya da manya ba suka hak'ura zuwa jibin.

Washe gari wuni sukayi a gida sai su aunty sa'adiya d Husna d Aisha da suka Shiga kasuwa suiayi siyaya,Bayan sun koma gida maman su aunty sa'adiya taba Husna kyautan setin tukunyar Ghana Mai kyau da tsada da Kaya kirar Yan Ghana har da takalman su masu Aminci har mazan akaba har da tsarabar mumcy ,adaren ranar suka Gama had a komai nasu da niyar zasu wuce gida gobe.

Sosai alamun gajiya suka baytana ajikin Husna in antambayeta sai tace gajiyane kawai sai amata uziri Dan ansan Bata Saba zirga_zirga irin hakaba rabanta d irin wanan zirga_zirgan tun kafin ta samu yancin zama matar Dan mumcy wato Fu'ad Dan Haka ta wahala sosai aganin su.

Yauma da wuri ta kwanta Bayan sunyi waya da FU'AD taje ta karbi kayan shi tazo ta had'a musu cikin akwatin da sukazo da kayan aciki, B2k ma Hira akasha da Aisha ta bankwana Bayan sun rabu ya koma wajen Fu'ad yake cemai shifa anan zasu barshi Dan yaga waje inze tafi yabar Rabin ranshi a Ghana?

FU'AD dukan kafadan shi yayi Yana cewa "baban soyayya to kace adaura kawai ka wuce da ita mana Naga har kana nema kafi masu Auren ma sanin makamar aikin"

B2K "bance ba komai lokacine Suma masu Auren asirin su insha ALLAH ya kusa tonuwa munafircin banza sukeyi sunaso suna kawaiwa kasuwa Bayan anyi walkiya mungano komai Sanu sannu Bata Hana zuwa sai dai adade ba'aje ba,da sannu haske zai haska,Inji b2k.

FU'AD sai cewa yayi "kaji dashi munafiki hasken inya haska har kyauta zanmaka ka tunanin Inna manta Kai zakasha kunya yaro"

B2K dariya yasa yace, Zan tunama kuwa Dan kaikeda Jin kunya Dan nasan ba dutse bane Kai........Yaya Jameel ne ya shigo cikin su suka bar maganar suka koma wata hirar daban.

Washe gari kowa na dokin kowa Musamman Husna da takejinta wani iri Amman aunty sa'adiya ji takeyi kamar su barta anan tasan ma jameel baze yadda ba Dan Haka Bata Fara tambaya bama.
Chapter 87 · 0% Book details