← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 95

Sashe 58

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Husna Bata Gama tunani ba mumcy ta tsayar Mata dashi ,ta hanyar cewa ki kaisu Sana ko sai Harri ta biyo su da Ruwa ,Husna tace to hajiya Mama have kuzo muje ,zungwi_zingwi suka bita , mumcy na dogon nazari akansu.

Husna bataso kaisu saman ba Amman dai ta kaisu bisa umarnin da Amincewar mumcy.

Mama habee kamar ansamu cenima kallo kawai takeyi na k'auyanci ,can tayi narai_narai da ido Tana Shirin fitar da kwalla Tana cewa "Ma'u ki d'auki komai ba komai ba duk Abin da ya faru ki barshi a baya ki kalli gaba ,ki zauna lafiya a gidanki ki rik'e mijinki da surikar ki ,abun da ya faru baya kiyi afuwa nasan ke me afuwace sai mama habee aka Fara kwalla har Tana zubowa har Ana cewa "ALLAH yajikan mahaifiyar ki" mahaifinki Kuma ALLAH ya barku tare ,ga 'yar uwarki kisata Addu'a ki ALLAH ya fito Mata da nata mijin ko kwatan_kwatan nakine ma'ana ko Wanda bekai naki ba gata Nan ki dinga Mata fad'a Naga kinfita nutsuwa da hankali .....sai ko humaira ta juyo a zabire ,mama ma'unce ta fini hankali da bakinki kike fad'a?
Itako Husna abun sunata Mata yawo a kwanya shin gaskene ko ba gaske bane? Kai gaskene harda hawaye fa ALLAH sarki mama habee ta dawo hanya,humara tana cewa nidai wallahi wata Ma'u bance tasani a addut ba Kuma banga hankalinta ba da har zata fini,sai ko mama habee tace ta fiki sai dai Kiki ALLAH ,humaira aka sunkuci Baki.

Mama habee ta inda ake Shiga Bata Nan ake fitaba ta gama cikama Husna Kai da karatun ta ,sunayi suna taba Abin da aka cika musu gaba dashi har da kaji Dan takansu ma suka fara, cikin hirar mama habee Tama Husna dabara Dan suji inda company d'in su FU'AD yake ,har da office d'in shi inda yake ,Husna tace Ni dai wallahi ban sani ba Amman naji suna cewa a sultan road yake office d'in ko a second floor ne ko 3rd ne nadai manta ,mama habee Bayan ta gama ji tace to shikenan ma barshi ba buk'atar sani nakeyi ba,sosai suka ci suka k'oshi harda guziri da zasu tafi mama habee taba Ma'u want turare Mai kanshi wai tayi Amfani dashi har humaira zata fesa Mata mama habee ta daka Mata tsawa Tana cewa uwar azarbabi da rawar Kai ce miki tayi bata iya fesawa ba? Dallah bani ungo jiki ki Adana abinki,Husna karb'a tayi ta tafi Tana murnar canjawar mama habee lokaci d'aya haka.

........ loading.........🖊
[4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA*

```RUBUTAWA DA TSARAWA```
BY
*FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB*
( Maman shaheed)

💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥

Pg47

Wani uban k'ara Husna ta sake lokacin da taji FU'AD ya fad'o jikinta rigijib ,badan taimakon kujera Mai laushi da suka fad'a Kai ba da zeyi wuya wanin su beji ciwo ba,Husna ce a kasa FU'AD a samanta ya sakar Mata nauyin shi da ALLAH ya bashi,gashi ba ahayyacin shi yake ba ,sai da kyar ta iya karanto salati da su hailala Tana Shirin kuka Tana neman agajin Wanda ze kawo Mata doki wajen daga Mata Fu'ad ta samu ta mik'e.

Da kyar Husna ta samu ta jirkitar da FU'AD ,ta dinga jijiga shi shiru ,sai ta sake sakin uwar k'ara a firgice Tana na Shiga uku FU'AD ka tashi Dan girman ALLAH meya sameka ?
Kafin kace kwabo idanu da kumatun Husna sun Gama jikewa da ruwan hawaye ,maganar duniya FU'AD ko numfashi bayayi,da gudu Husna ta bud'e k'ofan falo tayi k'asa wajen mumcy, a firgice mumcy ta ganta tace" lafiya Asma'u ,waye ya mutu?
Husna babu Baki ,nuna saman su kawai takeyi Tana cewa FU'AD ne ,sai mumcy ta saki wayar hanun ta Tana cewa shine ya mutun? Arazane sai ga Yaya Jameel ya shigo falon ,sai mumcy tace "Jameel Zo Nan" muje Asma'u ,da sasarfa suka haura Saman Suna Shiga sukaga FU'AD wanwar a kujera kafafun shi a kasa ,sai ko mumcy d Yaya Jameel sukayi kanshi a firgice ,suna jijigashi suna Kiran sunan shi.

Ganin baya motsi , mumcy ta juyo tace Asma'u me Kika Mai? Husna ta kasa furta uffan Dan ita har tunani da maganar ta sun d'auke gaba daya Tama Rasa meye abinyi yanzu in FU'AD ya mutu ,Tana wanan nazarin Yaya Jameel ya daka Mata tsawa "ke meya Sami d'an uwana ,me Kika Mai?

Husna sai fanfon hawaye takeyi Tana nuna turaren da ya fesa ,a fusace da k'unar Rai Yaya Jameel yace "wai ba akiyi magana ba musan abinyi? Wanan duk baze kaimu ba kina ganin ko numfashi bayayi sai , mumcy tace Jameel mu tafi dashi asibiti da gagawa aunta be mutuba Yana Raye ya za'ayi ya tafi ya barni a cikin duniyar Nan?

Sai a lokacin bakin Husna ya bud'u tace "in ALLAH ya yadda be mutu ba Kuma baze mutu ba Dan ALLAH mu kaishi asibiti.

Yaya Jameel ne ya d'auke shi ya yo kasa dashi da sauri Husna ta Suri hijab jikinta na rawa idon ta nata ambaliyar hawaye take bin Bayan mumcy da Jameel , mumcy ma hijab ta samu ta d'auko da wayarta suka nufi wajen Adana motocin gidan.

Jameel ya manta da matar shi ma sai da ya ganta ta fito tajiyo hayaniyar ma'aikatan gidan suna tambayar meya same shi ,babu Wanda ya samu damar Basu amsa sai mumcy da tace "ku kula da komai zamu asibiti Dan sanin meke faruwa muma bamu sani ba ,sai aunty sa'adiya tace "toh ALLAH yasa muji Alkhairi Dan ALLAH da kunje ku kiramu Dan zaku barmu a Rud'ani ,Yaya Jameel yace to insha ALLAH sudai tayasu da Addu'a ,shi yasa FU'AD a mota , mumcy da Husna suka Shiga sai Asibiti ......

Suna Shiga aka Fara ba FU'AD taimakon gagawa sosai wani likita ba indiye ya tsaya akanshi yanata bincike ,yanatama Yaya Jameel tambayoyi akan Abin da ya faru har ya Shiga wanan yanayin ,ganin baida amsar su sai suka Kira Husna sukace tayi bayani.

Husna cikin kukan da ta Rasa me rarashinta ta Fara cewa ,wlh nidai lafiya Lau yake ze fita Bayan ya Gama Shirin tafiya sai Mike d'an takkadama Akan wanan turaren Dana nuna muku ,ya karb'a ya fesa Yana fesawa ko minti 2 ba'ayi ba Naga ya Fara wani Abu sai ya fad'i Naga idon shi nata wani Abu ,shine nazo na Gaya Miki daga Haka wallahi bansan komai ba.

Sai likitan yace ko yanada Asma ne? Da sauri mumcy tace ko d'aya ,sai likitan ya sake cewa baida wani ciwo bayananne da yake tashi Mai?

Atare da Yaya Jameel suka had'a Baki "sukace babu"

Likitan sosai ya Gama gwaje_gwajen shi kafin yace da ranshi Amman inaganin ya shaki turaren nne over har Yana nema Yama huhunshi illah ,zamu Mai scanning Bayan mun samai Ruwa min Mai wasu allurori sai muga abun da za mu iya Akan matsalar shi.

Sosai hankalin mumcy d yaya Jameel ya dugunzuma ya Kara tashi ,har Husna da take cewa nice sila inya mutu na Shiga uku afili take fad'a batare da tasan Tana fad'a ba ,sai ko mumcy ta juyo tace "me kike cewa Asma'u?
Da sauri Husna ta toshe bakinta azaton ta a fili ta fad'a har mumcy Taji?
D sauri tace "mumcy FU'AD baze mutuba insha ALLAH Zaki rayu da d'anki bazan zamo silar rabaki da jininki ba Kuma wallahi ki yadda Dani bansan komai ba.......
Bata rufe Baki ba mumcy tace "kin San komai Asma'u ,ki kuka dakanki matuk'ar wani Abu ya Sami auntana ki fad'amin Abin da Kika sani ko kike b'oye min? A Ina aka samo turaren da ya fesan? Siyowa kikayi ko nashine ? Ko Baki akayi?

Husna mumunan bugawa kirjinta yayi ta kasa fad'an inda turaren ya fito gani take inta fada har babanta zasu shiga uku ba mama habee da humaira ba kawai ita Kuma da babanta ya Shiga mummunan yanayi gwanda ta mutu cikin mumunan yanayi indai babanta ze tsira.

Mumcy ce ta sake cewa "Asma'u duk lokacin d Nagano kinada hannu a faruwar matsalar FU'AD ,saki fuskanci fushi na Mai tsanani agareki fa ,Dan kin nunamin ke Yar Adam ce ,tun wuri ki gayamin musan abinyi.

Sai Husna tace "turare nane na kayan lefe na Amman yau na Fara Amfani dashi"

Mumcy cewa tayi "hmmmmm ALLAH ka dawo min da d'ana hayacin shi.

Yaya Jameel Yana ta waya da aunty sa'adiya Yana ce mata ankusa Shawo Kan matsalan su cigaba da musu Addu'a ,Yana Raye ya kashe wayar.

FU'AD har dare besan waye akanshi ba ,har abokanen aikin shi d sakatariyar shi suka dinga Kiran wayar shi sai dai Yaya Jameel ya d'aga yace bashi da lafiya Yana asibita Amman jikin da sauki har wasu sukace zasuzo asibitin ya basu address ,ya hanasu ta hanyar kwantar musu da hankali wai su jira jikin nashi da sauki ,Dole suka hak'ura badan sun so ba.

Dare yayi anma FU'AD scanning sun kasa gane ainahin matsalar ko Abin dake damun shi ,ganin zasu Sha wuya kuma maybe suta kashe kud'i abanza ,sai likitan yace su Bari agama Mai iya taimakon da zasu bashi in ba'a samu Abin da ake so ba sai ya musu transfer zuwa India ya had'asu da wani kwararen likita a asibitin kwararu na Delhi a India zuwa jibi a fita dashi Dan Shawo Kan matsalar da gagawa.

Ranar Husna wunin kuka tayi , mumcy dai jira take kawai ta sani da sa hanun Husna a rashin lafiyar FU'AD ko babu kafin ta d'auki mataki.

Bayan isha'i su mumy da Husna suka tafi tare da aunty sa'adiya dake ita ta kawo musu abincin dare ita da driver.

Bayan komawar su gida Husna ta kasa aikata Abin kirki sai ma mumcy ce take karfafa Mata gwiwa sanan ta samu tayi sallah tasata ta had'a lafiyayen tea da yaji had'i ta sata gaba ta shanye kamar magani Haka Taki tea din.

Husna a falon mumcy ta kusan kwana sai da mumcy ta fito ta ganta sanan ta tasheta ta koma saman su ,duk sai mumcy ta Fara Jin tajsayinta.

Bayan Husna ta koma tanaso ta sanarma aunty huwaila Tana tsoro Kuma sai kawai ta fasa.
Chapter 58 · 0% Book details