← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 95

Sashe 49

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana shigowa falo ya Fara muzuran inda zai gano Husna kawai yake ,ganin babu halamum ta a falo ya haura sama a zafafe ,saman ma Bata Nan ko Ina ya duba Dan Haka ya sakko har kitchen ya duba sai su Hari da ma'aikata.

Zama yayi a falo Yana fitar da iskar takaici Yana cewa "munafukar yarinyar Nan Tana wajen mumcy atunaninta ta tsira batasan karama kanta lefi tayi ba ,Dan Banga me hanani hukuntata ba wanan karon.

FU'AD Yana zaune har mumcy ta fito Husna jiki na rawa yadda mumcy bazata gane ba ta biyo bayanta , mumcy ce ta Fara cema FU'AD.

"Dama kana zaune Son ?

FU'AD cewa yayi "eh mumcy"

Mumcy cemai ta k'arayi "ya Ina B2k ya fitar ko kun fasa ne?

"Ko d'agowa ya kalli mumcy beyi ba sai ma wayancewa da yayi da latsa wayar shi Yana ce Mata "eh mun bar fitar zuwa gobe ne"

Mumcy daga Haka Bata k'ara cemai danme ba ,sai tace "ALLAH ya kaimu"

Ciki ciki yace "Ameen"

Husna ta kasa katab'us ,Amman ko yadda ta had'a ido da FU'AD batayi ,a zahiri Tana nuna Mai batayi lefin ba a cikin ranta Tana tsoron Abin da ze biyo baya."

Har aka Kira magriba duk suna zaune sai Hira jefi jefi da yake Shiga tsakanin mumcy da Husna FU'AD Kam ya d'inke bakin shi sai ma'aikata dake Kara k'aina a tsakanin su."

Ganin FU'AD kamar baida niyar zuwa masalaci sai da mumcy tamai maga sanan ya tafi Yana jifan Husna da harara Mai cike da gargad'i Mai zafi ,itako tasan za'a rina ,ko kalon shi takiyi burinta ya kauce inta haura samanta sai safe ita da sakowa Dan da biyu tamai haka tasan ba a d'akinta yake ba."

Husna cema mumcy tayi Bari ta d'ibi abincinta ta haura Dan kanta ciwo yake da tayi sallah isha'i magani zata Sha ta kwanta."

Mumcy tace Mata" to Allah ya sawake ki tabata kinsha maganin in bai saukaba ki sanar Dani da wuri inyaso ko asibiti FU'AD ya kaiki"

Husna zaro ido tayi a hanzarce tace" Asibiti da FU'AD? Batasan maganar ta fito ba har mumcy tajiyo ta.

Sai mumcy tace "eh meye Naga kin razana? Ko da matsala ne? Inda matsala ki sanar Dani Asma'u kinji?

Da hanzari "Husna tace "a mumcy babu matsala Razana nayi da Kika Kira asibiti saboda tsoron Allura nakeyi,Amman Babu komai hajiya."

Murmushi mumcy tayi kafin tace "toh ai in Banda Asma'u kamawa takeyi ai a d'aure Alkali ,inta Kama Dole amiki ,Amman Ina Miki fatan Samun Sauki ma insha ALLAH kinji?

Da murmushi "Husna ta amsa da to nagode hajiya barin je na d'iba tayi hanyar kitchen.

Bata tsaya Hira d su Hari ba gudun Kar FU'AD ya dawo ya sameta ta d'iba ta haura sama ,Tana Shiga falon ta tayi wata ajiyar zuciya na ta tsira daga hannun Zaki FU'AD.

FU'AD be shigo gidan ba sai da yayi sallah isha'i sanan ya shigo sai da ya lek'a part d'in sanaya yaga tanata cika tana batsewa yasan akan maganar tafiyar da yaki Amincewa ne inya zauna ma fada zasuyi Kuma ga Abin fada can ya baro wato Husna, Haka ya fito yazo hukunta Husna kafin ya kula sanayan."

FU'AD na shigowa yaga mumcy ita kad'ai ya tambayeta Husna" tace ta haura yin sallah Amman ba lalai ta sakko da wuri ba Dan ta d'ibi abincin tama kanta ne yake Mata ciwo.

FU'AD sai cewa yayi a gaban mumcy barin haura in duba ta "mumcy tace to ka k'ara Mata sannu, yace" toh"

FU'AD buga k'ofar ya dinga yi Yama Rasa wanne irin bugawa zeyi Dan ta bud'e ,ya buga yafi so 5 Amman Babu niyar bud'ewa , sai cewa yayi munafuka tasan Abin da tayi Tana jina har da haurawa sama wai ita munafuka me ciwon Kan k'arya ya Jima Yana bugawa kafin ya tafi Yana takaicin Abin da ta aikata Mai b'acin Rai Kan b'acin Rai.

Yana sakowa wajen mumcy ya dawo yake cemata "ta Jima d haurawa ne?

Mumcy tace "eh tun tafiyar ka masalaci"

Azuciya FU'AD yace "tasan me ta aikata ,sanan afili yace "to har yaci ace tayi bacci na buga yafi so 5 Bata bud'e ba?

Mumcy sai cewa tayi "Ina Jin tayi baccin.

Sai FU'AD ya Mik'e zai Tafi Yace Sai Da Safe Mumcy , Mumcy tace "Allah ya bamu Alkhairi"

Har FU'AD yaje k'ofa ya dawo yace ", mumcy bani phone d'inki na d'auki number aunty murja Dan naji kunya da ta kirani shekaranjiya ban Gaya Miki ba Kuma yanzu na Rasa gane number ta Dan na samu Kira daga mutanen da bani da numbers d'in su da yawa ,bani nayi saving Kar ta sake Kira naji kunya taji dad'in yimin tsiya Dan tace Tana Nan zuwa ma.

Mumcy wayar ta mik'a Mai Tana cewa "ato gara da Tama Haka , ALLAH ya kawota lafiya.

FU'AD ya Jima Yana laluben number da yafi buk'ata ayanzu Dan aiwatar da wani k'udirin shi ,be Gama tabbatarwa ba ya d'auki number sanan ya d'auki ta aunty murjan daga baya ya tafi Bayan Yama mumcy sallama ta 2."

FU'AD da sallama ya Shiga part d'in sanaya ,cikin Kin haushin me sallamar ta amsa ta Mai Maraba da harara tare da oyoyo da kalon banza ,neman waje yayi ya zauna yace "ba akawo Mana dinner bane?

Sanaya cewa tayi sun kawo Yana inda ka Saba ganin shi ,kazo ka baje a kujera kace kana neman girki?

FU'AD beja magana ba ya nufi Kan dining sai da ya cika tunbin shi sanan yace ,mutum ko yaci abinci Dan ya Kori yunwa ko Kar yaci duk d'aya ,ita dai yunwa Bata da hankali inji yaran malam Dan har targad'e takeyi ,kulin bazakici abinci ba in ankawo Amman hakan baya sa nakasa Jin motsi tsakar dare ,Ashe ba'a fushi da ciki dasafe ma Ina duba Naga an wawiki wani sashi na abincin.

Sanaya ta gama zuwa wuya da gugar zanan da FU'AD yake mata,sai cewa tayi ,maganar ciki ai ba magana bace afito fili agaya Mana tsoro ya hana.

FU'AD sai cewa yayi kowa yayi zagi a kasuwa ai yasan da wanda yake yi ,ganin laushi ai baze Hana Tankad'e ba yarinya ,ya tashi ya nufi hanyar d'akin shi Yana Mata wani kallon raini."

Yana Shiga ya rage kayan jikin shi ya Shiga bathroom ya watsa Ruwa ya fito yanata kamshi ya Fara duba wasu takaddu sai kawai al'amarin Husna da B2k ya dawo Mai ,atake ranshi ya b'aci sai kawai ya cafko wayar shi ya Fara laluben number da ya sato a wayar mumcy ya Danna Kira.....

Ringing 1...2....3...sai aka d'aga cikin Sasauk'ar murya Mai Amo Mai dad'in sauraro yaji ance,

"ASSALAMU ALAIKUM"
FU'AD da ya Fara tantama anya ya samo number daidai kuwa?
Can yaci an sake cewa waye Dan ALLAH?

Anan ya ji kamar itace ,yayi k'arfin Halin cewa ,shine Kika gudu ko Baki iya neman gafara ba sai guduwa kina ganin hakan tsira kikayi?

Jin anyi shiru ba'ace komai ba sai FU'AD ya Fara zargin Kar fa ba number husnan da yake zargi bane?

Yana cikin tinanin katse wayar ma ,sai yaji ance "Ni ai ba guduwa nayi ba kainane yake min ciwo."

Wawan ajiyar zuciya FU'AD ya sake kafin yace "karya kike ba gashi kin iya d'aga waya ba Amman so nawa na buga Miki d'akin Baki bud'e ba sai kace da kudinki aka Gina min Fallon ?

Husna sai cewa tayi "to ai bacci nayi Kiran wayar nanne ya tashe ni,Kuma Ni Babu ko sisi na cikin Gina maka benen ka me nakedashi ,sai dai kawai nasan inhar da Rai da rabo."

Da sauri FU'AD yace " karya kike makaryaciya ,Kuma karkimin Rashin kunya Dan me tarin lefice ke"

Husna tace "Ni ba makaryaciya bace Kuma lefin me nayi maka?"

FU'AD sai cewa yayi "yi Rashin kunyar ki son ranki kafin na had'u dake Gobe ,sai kinyi Dana sanin zamanki a gidan Nan ma gaba d'aya Zaki gayamin in B2k ne ya kawo ki gidan Nan ba mumcy ba"

Budar bakin Husna sai cewa tayi "nifa Banga Dalilin kishi a Kan Abin da mutum be damu dashi ba,kafito a mutum sak kawai ko....Bata Gama ba FU'AD ya katse ta.

Ke waye yake kishi?
Ina Abin yake?
Meye Abin kishin?

"Husna sai cewa tayi to Babu Rami me ze kawo Rami?

FU'AD be Bata amsa ba sai Jin sanaya yayi ta shigo d'akin babu sallama Tana cemai" wallahi baka Isa ba kazo d'aki ka tasa waya da 'yan matanka sanan Ni ka kuntatamin ka rabani da kowa nawa kazo kana enjoyment d'inka da wasu banzaye acan wallahi baka Isa ba........

Duk Abin da sanaya take fad'a Husna najin ta tayi tsuru tanajin drama ta cikin waya..........

FU'AD ko a zuciye ya taso yace "ke uban waye yake shashancin da 'yan matan?
Tukunna ma waye banzar? Matar tawa ta sunna da shedu suka sheda aurena da ita kamar yadda tsiraru suka sheda naki ?

Get out of my room now.......
Ya nuna mata hanyar waje.
Ya sake cewa
I said get out ......... nonsense kawai .....

Sanaya fita ta farayi Tana cewa "wallahi talihi wether u like it or not wallahi sai na tafi Egypt wether u agree or.......Bata k'arasa ba FU'AD ya turata waje ya rufe k'ofa Yana Kara wayan shi a kunne Yana cewa."
Kina Nan ,kijirani da safe kin k'arama kanki laifi.......be k'arasa ba........yaji Husna tace Ni ka rabu Dani kaje kaji da matarka Kar ka karbi hukunci yau.....Bata jira me zece ba ta katse wayar."

FU'AD mamaki tare da Tambayoyi ya tsaya yi ,Ashe taji shirmen sanaya? Kuma me take nufi da Kar na karbi hukunci? Karfa tayi zaton kishinta nakeyi?
FU'AD yace "Kai Ina" me zesa tayi wanan zargin ma bare takai ga ta gaskata Tama San bazan taba kishi akanta ba har mezanma kishi?

Sosai kwanyar FU'AD ta Shiga lugude da kid'a,ga tunanin Abin da sanaya tamai da ya d'auka a matsayin shirme ,Yana sake tambayan kanshi meye hakan tayi kishi kenan ko hauka?

FU'AD ya Jima Yana tufka da warwara Kan abubuwan da suka kawo Mai farmaki na hargitsin B2k da Husna ga sanaya itama.
Chapter 49 · 0% Book details