← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 95

Sashe 55

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan komawar su gida ,Husna godiya tama FU'AD ,yace "ta meye godiyar? Tace na sadani da mahaifina farinciki na da kayi ALLAH ya saka maka da mafifucin Alkhairi, FU'AD sosai ya fahimci irin farinciki da yasa husnan ,amemakon ya amsa ko ya nuna Mata Jin dad'in shi shima sai yace "ki godema ALLAH da mumcy badan ita ba da Babu inda Zan kaiki,sai Husna tace "dama ai mumcy ba godiya kawai ba har Addu'a nake Mata a kulin Dan ta cancanci fiye da Haka a guri na........duk da kalmar shi Bata Mata Dadi ba ,sai ya katseta da cewa ba Dole ki Mata Addu'a ba tunda ta had'aki Aure da Wanda mafarkin ki be tab'a Baki ba kinyi dare_dare kin bararaje ba.......a fusace Husna tace matsayi_matsayi ne aman daraja kowa nada shi Dan kowane d'an Adam me daraja ne dukiya ko wani milki Kuma duk aduniya ake samun su Kuma duniya zamu barsu Kuma bawai zana ALLAH yakeyi ba ......Bata rufe Baki ba ya janyo gyaketa ze zalinceta akan gaskiyar ta dama Bayan sun shigo Fallon mumcy ne ,ya Kai hannu ze rankwasheta sai ga mumcy ta fito daga d'akin ta .........

Zuwa gobe insha ALLAH🤦🏼‍♀
[4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA*

```RUBUTAWA DA TSARAWA```
BY
*FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB*
(Maman shaheed)

💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥

Pg43

Sosai FU'AD ya ke dariya akan Abin da husnan tayi yau karon farko a iya zaman shi da ita.
Bayan ya Gama shiri ya fice tare da yima mumcy sallama tamai Addu'a kamar yadda ta Saba kulum.

Husna bata sakko ba sai da ta tabbatar da taci baccinta ta k'oshi Kuma dama tasan tuni FU'AD ya fice Dan ta duba agogo.

Bayan ta tashi ta gyara d'akinta taje d'akin FU'AD ta gyara Mai ta feshe da turarukan kamsasa d'aki da falo ta rufo Mai ta sauka k'asa ,suka danyi Hira da mumcy daga baya ta wuce sashin aunty sa'adiya Dan gobene tafiyan Aisha.

Sanaya dawowa tayi wajen mumcy Kan maganan tafiyan ta ,ko da ta Fara ma mumcy magiya sai mumcy tace "Kar ta samu damuwa ta shirya baze gagara ba insha ALLAH.
Sosai sanaya tayi murna karon farko da Tama mumcy godiya ,tace to yaushene tafiyan nayan nata?

Mumcy tace "ke yaushe kike ganin Zaki tafi? Da so nake ki Bari muje wani biki da za'ayi in angama sai ki tafi ko kina ganin da matsala?
Sai ko sanaya tace "Dan ALLAH abasu hakuri sahun giwa ya take na rakumi nafi bukatan tafiya ta da bikin duk da bansan matsayin bikin awajen ku keda FU'AD ba am sorry to say........sai mumcy ta dakatar da ita da cewa ko Fara bikin ne za'ayi dake inyaso sai ki tafi ko ana tsaka da bikin kiji ko?
Ran sanaya be so ba Amman tace to ya tsarin bikin yake?
Sai mumcy tace kinga yau muna laraba to Gobe Alhamis za'a Fara bikin Dan Haka ko program din goben sai ki samu inyaso sai ki tafi juma'a ko asabar yadda Kika gani dai?
Sanaya cewa tayi "toh zani goben sai na tafi Friday kawai.
Mumcy tace to ALLAH ya nuna Mana ya kaimu da Rai da lafiya, mumcy ta Kara cewa"goben event din na yamma ne around 5:30pm sai ki shirya da wuri Abin da kike bukata Wanda Zaki bikin dashi sai kimin magana inyaso sai atanadeshi tun yau ,wai mumcy tana Mata duk Dan tayi adalci ,sai ko sanaya tace Bata da Abin buk'ata da ya wuce tajita a Egypt ,Koda FU'AD baze Mata komai ba na tafiyan tanada kudin da zatama kanta komai Kar su damu.
Sai mumcy tace "Aiko lalacewar FU'AD Bata Kai haka ba ,yama wani ma bare Wanda suka had'a wani Abu?
"FU'AD ya wuce yadda kike zato kedai ki Adana kudinki ya Miki magani Kinga ko tsaraba kyayima kannenki ran mumcy fes tunda ta Bata amsa daidai maganar ta .
Sanaya tashi tayi kamar Mara gaskiya ta wuce part dinta.

Sosai su Husna sukayi Hira da Aisha sunata Wasa da baby mamy tanata bangala musu dariya.

Bayan sunci abincin Rana ma sun Jima a wajen mumcy har mumcy tabama Aisha wasu tsadadun turaruka da shadoji da atamfofi tace tayi tsaraba , Aisha da aunty sa'adiya nata godiya har Husna ma tayasu godiyar tayi da yamma lis suka koma part d'in aunty sa'adiya.

Bayan FU'AD ya dawo mumcy take gayama FU'AD Gobe su Husna zasu raka Aisha Airport Kuma zasu biki Gobe Dan Kar ya dawo gida yaga ba Mata ya tafi filin cigiya da sanarwa Dan haka ta sanar Mai tunda yasan da zancen.

Sai ko FU'AD yace ko Baki fad'a ba ai kin isane Ina muku fatan dawowa lafiya ,sai ko mumcy tace"ALLAH yasa bada biyu kake zancen Nan ba.

Washe gari da sasafe FU'AD ya Gama Shirin tafiyar shi office har yayi sallama da mumcy Yama sanaya sallama har ya Shiga mota ze tafi sai ya tuna da gargad'in da zema Husna sai ya fito a fusace y nufi d'akin ta ,Yana haurawa ya sameta a falo Tana Shirin fitowa sai da ya karema inda ya jimata jiwo kallo sanan yace "ke saura in Zaki fata kiyi wanan shigar kisan dai Akwai auran da mumcy tasa aka d'aura Miki akanki duk abunda kikayi Akwai me kallon ki ,ke kimayi duk Abin d zakiyi ki gani nasan zaku rakiya keda aunty sa'adiya kuma kisa hijab wata Yar ficiciya dake Amman kin iya hada fitina da kin saka hijab kinji na Gaya Miki,Yana Mai Kama kunnen shi irin alamun gargadi dinan.

Husna abun sai yamata wani iri sai tace "wai wanan ne ya dawo dakai? Sai FU'AD yaga Tana neman ta rainashi daga tambaya sai yace "wanan din banza ke har kin Isa ki dawo Dani Abu nazo yi , dole ya wuce d'akin shi badan Yana son d'auko wani Abu ba ko yin wani Abu ba Haka ya fito salin alin ya fice Yana hararar ta.

Bayan FU'AD ya Isa office ,tunanin yadda take kasancewa tsakanin shi da Husna ya Fara a'iya atunanin shi ya Rasa gane hakan me yake nufi yayi imanin Kuma ba kishinta yakeyi ba to Amman Damme ze dinga Jin haushi in wani ya kulata?
Yana cikin tunanin wani abokin aikin shi ya shigo ya tsayar Mai da tunani cak.

Bayan Husna tayi wanka ta shirya sauka tayi kasa Dan zuwa rakiyar Aisha Airport ,ganin mumcy Bata kasan sai ta wuce part d'in aunty sa'adiya ta samu Suma sun Gama shiri Ana shirya baby mamy ,sai ko Husna tace kawota na karasa Mata ,aunty sa'adiya ta mik'a Mata komai nata .

Aisha ce take cema Husna "Ashe matar mijin ki tafiya zatayi ? Sai Husna tace au haba? Ina zata?
Sai Aisha tace "k'asar su ta gado Mana *Egypt* jiya aunty ta tursasani wai sai naje na Mata sallama saboda Hakin musulunci shine fa take cemin itama gobe zata bar k'asar har taso muyi Hira akan 9ja da matsalolinta nace Mata Ni bani da matsala da 9ja Dan babana d'an Ghana ne Amman mamana 'yar 9ja ce kimga ko 9ja ta gama min komai ,shine fa tayi shiru ,yanzu dai tanata murna zata koma k'asar gado ,sai suka bushe da dariya aunty sa'adiya ta jiyo su take cewa wacce gulmar akeyi wanan irin kyakyatawa.....
Aisha ce tace no! Aunty wanan hirar muce cigaba da soyewarki awaya da angon nesan ki tunda baya kusa ,sukaci gaba da dariyar su.

Husna na zaune taji alert ya shigo wayanta na 50k sai ta duba taga daga aunty huwaila ne sai murna ta kamata duk da Bata da abinyi ko buk'atar kud'i ayanzu saboda ta godema ni'imar da ALLAH yayi Mata ma ahaka na zama karkashin mumcy da FU'AD Bata nemi komai ta Rasa ba Dan Haka Bata da bukatar kud'i ,Amman tayi murnar ganin kudin ,Bayan sun gama shirya baby mamy sai suka fito.

Gaba dayan su suka jema mumcy sallama Dan har Airport zasu rakata har mumcy ta Basu sak'o a cam in suna dawowa ,driver Daman su kawai yake jira Bayan ya Gama saka duk wani Abu a motar Wanda Aisha zata tafi dashi,sai suka Shiga Suma sai tafiya.

Sosai Husna da Aisha akaji Rashin dad'in Rabuwar su ,sukayi bankwana ta tafi suka wuce wajen sakon mumcy daga Nan suka juyo gida.

A falon mumcy suka zauna suka huta suka Sha hirar su har suka ci abinci Rana Bayan sun Harri sun Kamala.

Yamma nayi Bayan la'asar mumcy ta umarce su day su shirya Dan tafiya wajen bikin ,Husna tayi sama aunty sa'adiya ta wuce part d'inta Dan nata Shirin ,Bayan sun shiryo sun fito ,sai aunty sa'adiya taja Husna samanta tace wanan kwaliyar da gyara ta mata makeup Mai kyau ta gyara Mata ko Ina ita kanta Husna sai yau ta yadda Ashe ita Mai kyau ce Dan anfitar da komai babu algus acikin kwaliyar zallar madarar kyawuntane ya bayyana tsirara ga d'auri da ta kashe ta dashi Mai steps ta had'a Mata komai perfect match suka sakko kasa Ashe mumcy nata jiransu Dan sanaya Bata fito bane da ta aika Suma su fito ,Dan ta aika Harri ta Kira sanayan su tafi.

Sanaya nacan na Shirin tafiya Egypt ba'ason ranta ta sake ba ta canja Kaya Babu wani mugun kwaliya wai Tana alfahari kyawunta is natural ,batasan in kanada kyau to ka Kara da kwaliya ba Inji mlm bahaushe ta sake abinda takeyi ta fito Dan su tafi.

Mumcy ma taga zallar kyawun Husna yau sosai ta birgeta ,sai sanaya ma da ta karaso taga Husna sai da kirjinta ya buga amman Bata d'auki hakan komai face kodan ita ba ma'abociya kwaliya da fente fuska bane, Amman dai kyawunta yaso firgitata sharewa kawai tayi ,ganin su had'u sai mumcy tace su tafi ,Husna ta karbi mamy Tana hannun ta ko amotar.
Chapter 55 · 0% Book details