← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 95

Sashe 64

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan awa 2 da zuwan FU'AD office jama'ar sa nata zuwa Mai ya k'arfin jiki ,Bayan mutane sun Dan sarara sai ga sakatariyar shi tazo tace Mai wata nason ganin shi ,kamar baze bada damar ace ta shigo ba amman sai yace "ace ta shigo"

Fuska FU'AD na kallon wasu files har aka shigo, be d'ago ba sai muryar humaira yaji Tana Mai sallama ,a sukwane ya d'ago Yana tuhumar meya kawo ta me tazo yi yau Kuma?

Sai tace" ko Zan iya zama?

Sai FU'AD ya d'ago yace "tsaya a inda kike ma ya Isa ,ya akayi da wacce Kika Zo?

Sai humaira tayi fari da Ido tace "dama tambayar ka nazo yi akan Yar uwarta ko ta dawo?

Sai FU'AD yace "daga Ina ta dawo? Sai humaira tace ba nemanta aketayi ba muma nemanta mukeyi ko Ina bamu ganta ba shine Mama tace nazo naji ko anganta?

FU'AD shiru yayi na wani Dan lokaci kafin yace "malama ALLAH ya bamu Alkhairi Husna Bata dawo ba shikenan na amsa tambayar ki?

Humaira zata sake magana yace "ke fitamin a office ranshi a bacce ,sata sake magana duk da ta tsorata da korar da ya Mata ,da ya daka Mata wata uwar tsawa sai da ta Rasa k'ofan fita a gigice ta fice Tana mita wallahi mama habee zata turo Mai.

Da taje gida karya da gaskiya ta kitsama mama habee da ta turo ta ,mama habee gyale ta d'auka suka koma office din FU'AD din Koda sukaje baya Nan har yabar office din ya koma gida.

Be jima da Shiga gida ba ,ya Kira wani a company sai yake sanar Mai wata Mata da budurwa sunzo neman shi ,har FU'AD ya tambaye shi yaa fasalta Mai yadda suke atake FU'AD ya fahimci wacce take tutiyar ita maman Husna ce ,sai cemai yayi toh shikenan ya fad'a Mai sak'on da zai fad'a Mai ya kashe wayar yana me dogon nazari Akan mama habee da humaira."

Ranar FU'AD kusan wuni yayi a sama Yana tunani Akan su mama habee da Husna da son sanin Wanda yaba husna turaren da ya fesa har ya Shiga cikin wanan Halin sanan ya zama Dole ya datse igiyar da takema su humairan jagoranci na zuwa office din shi daga ita har mayaifiyar ta."

Sosai FU'AD ya Kara matsuwa da son ganin Husna Dan Mata tambayoyi sosai yake kewar ayukanta na gidan atake kishin Auren shi ya sake motsawa Akan waima a Ina take da take yawo da igiyar Aure akanta meya hanata waigowa gida? Ko Tana nufin ta hak'ura da auren da mumcy ta musu?

FU'AD ba karamin tashin hankali ya Shiga ba akan son sanin inda Husna take ,burin shi tazo ta amsa Mai tambayoyin shi sai ta koma duk inda taga damar zuwa indai ya samu gamsasun amsoshi daga gareta, ya Jima a falo har gani yake kamar ze ganta ta fito daga d'akin shi Amman shiru.

***********
Aunty huwaila ta jajirce ba itaba ba sadeeq ba akan maganin baiwar ALLAH Nan ,Husna nata katatun ta tana son Kiran aunty sa'adiya Tana tsoron wani yasan inda take wani lokacin har gwada Kiran takeyi sai zuciyarta ta gargad'eta sai ta fasa,sosai ta saki jiki da mutanen gidan har abban su Affan dake mutum ne Mai barkwanci da son mutane ,gashi muhibat d Husna karama suna yawan zuwa d'akin matar Nan Mara lafiya suna d'ebe Mata kewa da Mata Hira ko su dinfayin hirar su a gabanta amman batare da suna hayaniya ba sai Dan haka likitan da yake dubata yace musu adinga Mata ,yauma kamar kullin sunata Hira a d'akin matar ta k'urama Husna ido ko kiftawa batayi har Abin ya tsorata Husna muhibat ma ta gani da sauri ta fita ta Kira aunty huwaila ,aunty huwaila da ta gani tace ALLAH yasa hakan na nufin wani abu.

Husna ta tambayeta me take nufi da Haka?
Sai tace "Ina nufin ALLAH yasa sauki ne yazo Mana ta haka" su Husna sukace ALLAH yasa Amin.

Affan sosai ya Fara nunama Husna ra'ayin shi Dan baya tsoran kowa ya gane ma yanzu Dan har aunty huwaila ta Fara fuskanta alokacin da ta Fara zargin hankalinta ya matuk'ar tashi duk da taga husnan na baya_baya dashi ,Amman sai aunty huwaila ta sake tsananta zargin ta Dan ta tabbatar shin hakanne sai take sama Affan Ido sosai Dan gano gaskiyar zargin ta.

**********
Washe gari da FU'AD ya tafi office , still Mama habee ta sake dawowa , FU'AD ya Mata fata fata har bakin gate din company ya rakota Yana Mata gargadi me tsanani yanama masu gadin company da sakatariyar shi gargadi Akan karsu sake barinta ko yarta su Shiga Mai company inba hakaba abakin aikin su Dan ya nuna musu b'acin ranshi sosai,cike da nazari da tunani kala_kala ya koma office ,mama habee nata tsine Mai Tana cewa ya rabu da Husna kenan rabuwa na har abada asarare me zuciyar tsiya kana attajiri ka makalema matsiyaciya Dan rashin sanin darajan arziki,
Indai nice kayi da 'yar halak Kuma zamu gauraya ne.

Bayan FU'AD ya koma gida da damuwa fal a fuskar shi in an tambaye shi yace "babu komai"

FU'AD sosai yake son ganin Husna ko sanin inda take ,ya kirata har ya gaji ya Mata massage yafi so nawa Amman Babu reply yau har gidan su sukaje d Yaya Jameel ,suka yi suka dinga tambayar mutane makotan shi sai aka kwatanta musu wajen shagon shi sukaje suka tambayi mak'ocin shi yace wallahi baida labarin shi dayan Kuma yace shima sabone a wajen ,Suma har gidan shi sukaje suji ko lafiya Amman matarshi ta musu hauka suka kyaleta shine har yau babu Wanda ya sake komawa."

Sosai su Yaya Jameel suke neman Wanda yasan inda baban yake ko Husna komawa sukayi sukaje unguwar akace su nemi wani abokin shawarar shi a Bayan layi wata kila yanada masaniyar inda yake,suka rankaya aka rakasu.

Bayan sun gaisa suka tambaye shi inda baba yake ko ya sani?

Atake yace gaskiya be sani ba ,su FU'AD har suna Shirin tafiya Bayan sunmai godiya da sallama sai ya kirasu yake tambayar su ko su suwaye?

Sai Yaya Jameel yace "wanan mijin yarsa ce ni Kuma yayan shine"

Har zasu sake tafiya mutumin ya sake cewa , mijin Ma'u kenan? Sai Jameel yace "eh"

Sai FU'AD yace "Yaya tashi muje kawai"

Sai mutumin yace "Dan ALLAH ko Zan iya sanin dalilin neman shi da kukeyi ?

A fusace FU'AD yace "babu mutafi Yaya kawai"

Sai mutumin yace "haba yaro fushin fari ba naka bane matam bayi baya Bata,inda Rai da rabo ku gayamin ko Akwai temakon da Zan iya muku ,baban Ma'u amini na ne nasan sirin shi yasan nawa ku gayamin ko Zan iya taimaka muku?

FU'AD ya Gama hassala gani yake mutumin Bata musu lokaci kawai zeyi ,sai jameel yace "dama baban muke nema Dan munaso musan ko Husna Tana tare dashi?

Sai mutum ya firgita yace "meya Sami Ma'u badai Bata tayi ba"

FU'AD a fusace yace "ba Bata tayi ba nemanta dai muke"

Sai Jameel yace "eh nemanta muke munga baban ma baya Nan shine muke zaton ko duk inda yake suna tare Dan hankalin mu ya kwanta"

Sai mutum yayi ajiyar zuciya yace "ki gafarce Ni kaima abokina ka gafarce Ni kace karna gayama kowa amman Dole na fada Dan Abin ya shafeka ma'un ka ake nema Inna b'oyema zakace ban kyauta maka ba."

Dai FU'AD ya juyo Yana cewa "me kake cewa?

Sai mutumin yace "shi yace karna Fadi inda yake Amman Dole na muku jagoranci duk da bansan gidan ba Nima sai kwatance da ya bani ,Dan Yana kyauyen karmanje masifa da bala'in matarshi yasa ya tafi yabar Mata garin Dan yadda yace min badan haidar da Ma'u ba da yabar su kenan baze dawo ba duk da can din duk Yan uwansa sun mutu sai wasu kalilan ,Amman fa da tafiya inkun shirya ko yaushe ne sai kuzo muje ko ALLAH zesa mu Dace.

FU'AD wani wawan ajiyar zuciya yayi gani take anma Dace kawai ,sai Yaya Jameel da ya Riga FU'AD magana toh Gobe sai mu tafi da safe Babu matsala?

Sai mutumin yace babu insha ALLAH, FU'AD ba haka yaso ba beki a tafi alokacin ba ,Amman sai yayi shiru tunda Yaya ya Gama magana ,sukama mutumin sallama suka tafi , FU'AD nata ayyana rashin kirkin da zema Husna inta Bari suka had'u tasa Ana ta wani nemanta kamar 'yar gwal wata dirty girl da ita badan tsoron Kar ALLAH ya tambaye shi ba da babu wani neman ta da ze Bata lokaci yanayi tunda babu Abin da take tsinana Mai ,dai gyaran d'akin da k'oshi ze iya Abin shi ita baga tuwo ba bare Miya sai dai adafa tashi yanzu kawai ta tafi daga Mata gatse kamar dama jira takeyi ta tashi hankalin uwa tagari kawai.

*Maman shaheed*👌🏻
[4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA*

```RUBUTAWA DA TSARAWA```
By
*FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB*
( Maman Shaheed/

💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥

Pg51

Hannun dady na rawa ya dailing number d sanaya ta bashi ya mayar wayar shi,
Kira 1,2......aka d'aga cikin nutsuwa mumcy tamai sallama."
Dady sai cewa yayi meya Sami FU'AD d'in ance min bashi d lafiya har anfita da shi dafatan ba struck y samu ba ko?

Mumcy ajiyar zuciya tayi da ta fahimci me maganar sanan tace "ALLAH ya raba FU'AD da wani Abu me Kama da Haka ma , FU'AD dai kawai baida lafiya ne da izinin ALLAH Kuma ya kusa samun sauki."

Sai dady yace "toh bani shi" sai mumcy tace "ai baya iya magana"
Sai dady ya sake cewa "kince matsalar karamace gashi yaro karami Yana neman zama wani iri akan wani lisafe_lisafen shi ,ki gayamin gaskiya Akan Abin da ya Sami Dan d'an uwana?

Sai mumcy tace "kawai turare ya shak'a over sai yazo Mai da matsala shine aka turo mu Nan India Kuma mun Fara ganin nasara da yadda ALLAH."

Sai dady yace "toh ashaa Aiki ya b'aci Abu beyi Dadi ba ,Zan kawo Mai matarshi don tayi jinyar shi jibi INSHA ALLAH muna hanya......
Chapter 64 · 0% Book details