← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 95

Sashe 89

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har sun Fara Hawa steps ,suka tsinkayo muryar mumcy nacewa ,sannu ku da dawowa ,Husna jikin da sauki ko?

Husna na mak'ale jikin FU'AD tace "eh mumcy nagode"

Mumcy ta sake tambayan ta Bata buk'atan komai? Husna tace eh Akwai malt a sama Zan dansha kafin na kwanta.

Sai mumcy tace"yauwa toh sai da safen mu"

Atare da FU'AD d Husna suka amsa da "ALLAH ya tashe mu lafiya"

Suna Shiga falon FU'AD ya nufi d'akin shi da ita ya rud'e har sun kusa Shiga Husna ta tirje tace "d'akina dai"

Sai a lokacin FU'AD ya fuskanci inda ya dosa da ita ya koma hanyar d'akin ta da ita.

Gyara Mata shinfidar yayi Yana cewa ko Zaki rage kayan jikin ki ? Husna cemai tayi "eh "

Ganin baida niyar fita sai ta Debi kayan ta nufi bathroom dashi taje ta canja , FU'AD nata Mata dariya Yana cewa yarinya meya rage Kuma kibada Kai mu Gina sabuwar rayuwa mu Kori duk wata gaba da kiyaya da fadace_fadace mu manta baya mu Gina rayuwa Mai inganci da Aminci mu Mori Rayuwar mu,duk cikin ranshi yake biya wanan karatun.

Bayan ta dawo tayi sallah duk Yana zaune.

Sai da zata kwanta take cemai "kaje ka kwanta dare yayi fa"

Agogon tsintsiyar hanun shi ya duba kafin yace "to babu damuwa nabarki ke kad'ai duk da Baki da lafiya?

Husna cemai tayi "eh zata iya kwana ai"

FU'AD yace "hakan ya Miki?

Ta sake cewa "eh" Hadi da nuna k'osawa da tambayar tashi.

Ficewa yayi Yana cemata sai da safe inda buk'atar wani Abu da takeji Yana sauraron ta ko yaushe ne.

"Toh" kawai tace Mai ya fice.

Itama kwanciya tayi tanata zuba tunani wai itace ke d'auke da cikin FU'AD? Ashe zata haihu Kuma da FU'AD shifa Daman Haka abun ALLAH yake"

Toh yanzu FU'AD Ya Dena tsanar ta ko har yanzu Yana d'aukan ta matsayin kazama, Yar Aiki,wacce mumcy ta aura Mai ala tilas? Ze karbi Dan kuwa?

Kasan zuciyan kuma tace"eh Mana bakiga wani kulawan Musamman da ya Fara Baki ba? Shima yanason yara fa ko kin manta ne? Ai kulawa har sai kince ta ishe ki"ALLAH yasa Inji zuciyar ta" afili Kuma ta amsa da Amin.

Sosai bacci ya d'auki Husna cikin baccin tayi wani irin mummunan mafarki wai ga mama habee ta biyota da tukunyar wuta ahanun ta tana gudu babu me ceton ta tanata tsala ihu har sai da ta Fadi kasa ,sai matar da aunty huwaila take taimaka ma tazo da sauri ta hankada mama habee Tana cemata" anan dai Kam Baki da nasara Nima ta ALLAH ba takiba"

Agigice Husna ta farka da hailala Mai k'arfi har sai da FU'AD ya jiyo ta Dan ba wani bacci Mai nisa yayi ba Daman da sauri ya nufo d'akinta.

Yana Shiga da sallama Yana tambayar ta lafiya?

Yaga gumi duk ya fito Mata tanata waige_waige Tana Addu'a.

Ganin batace Mai komai ba ya hauro gadon ya tallabo ta k'irjin shi Yana cewa menene?

Husna kuka tasa Mara sauti sanan tace "wani mafarki nayi Mai sarkakiya ka kiramin aunty huwaila dan ALLAH na tambaye ta"

FU'AD sake rungumeta yayi Yana cewa ,dare fa yayi karfe 3 dare ki Bari zuwa gobe ,Kuma mafarki ai ba gaskiya bane.

Sai Husna tace"na sani Amman mama habee nagani ta biyoni da tukunyar wuta fa sai Mara lafiyan gidan aunty huwaila ne ta taimakeni fa Ni kaina ya kulle.

Sai FU'AD yace toh kiyi hak'uri zuwa gobe ,kuma watakila bakiyi Addu'a ba Kika kwanta Koh?

Husna eh tace babu musu.

FU'AD yace "kin gani ko? Ai karki dinga sakaci da Addu'a Musamman yanzu.

Husna cikin kuka tace"kamar ya Musamman yanzu?

FU'AD Babu kunya yace "Ina nufin yanzu da kike d'auke da .........sai ya kasa iarasawa.

Husna ma runtse ido tayi Daman Tana jiran ya karasa.

Sai yace "kawai kiyi bacci Zan tayaki kwana sanan Zan sanar ma mumcy atayamu Addu'a Akan wanan algungumar matar baban Dan bazan sake yadda da ita ba muguwace babu ALLAH aranta kema karki sake amincewa da ita na Gaya Miki.

Husna tunani ta dingayi akan mafarkin.

FU'AD ne yace"ki kwanta anan sai kiyi Addu'a Nima Zan Kara yi Miki Kinga kina buk'atan hutu kisamu kiyi bacci ya ishe ki.

Husna kwanciya tayi, sai da FU'AD yaji hanun Husna cikin nashi ta damke kamar Wanda ze gudu ya barta sai yace Mata"ko natafi d'akina?

Da sauri Husna ta k'ara damke hannun shi tana cewa "aa Dan ALLAH" dariya yayi cikin ranshi Yana ayyana tsokanar da ya Mata.

FU'AD dai a d'akin Husna ya karasa kwanan shi har makara yayi be samu sallan asuba a jam'i ba Abin da baya wuce shi.

Bayan y tashi yayi sallah ya tashi Husna itama tayi ,yaga ta nufi fridge ta d'auko malt ta bud'e Tana Sha yace in yunwa takeji taje kasa tanada umarnin a dafa Mata wani abun Mana?

Husna cemai tayi wanan ma ya isa.

Bayan sun koma bacci sun tashi sukayi wanka Husna nata samun kulawar FU'AD suka sauka kasa suka tarar da aunty sa'adiya da mijinta d mumcy,suka gaisa anata ma Husna ya jiki tanata amsawa ciki_ciki Dan kunya tanata sunkuyar da Kai Bayan sun Gama karyawa FU'AD da Yaya jameel suka tafi unguwa.

Da Rana Husna ta kasa jurema mafarkin da tayi ta Kira aunty huwaila ta sanar Mata ,aunty huwaila tace gata Nan zuwa gidan taga jikinta.

Bayan awa 1 sai ga aunty huwaila da matar Nan dasu Yaya sadeeq su Affan d muhibbat d Husna sun tafi gidan kanuwar huwailan ta haihu.

Suna isowa mumcy ta dinga karema matar kallo Tana hango Kama da Husna atare da ita Bayan sun Gama gaishe da mumcy ta musu umarnin su haura sama husnan na sama.

Shigar aunty huwaila Husna da sauri ta taso ta rungumeta da murna farinciki far ranta da fuskar ta.

Can taga matar Nan Mara lafiya ,sai taji wani irin faduwar gaba Amman hakan be hanata rungumeta ba Tana Mata sannu da jiki.

Cikin Jim Dadi da ganin samun lafiyar matar Husna ta dinga janta da Hira Tama manta da su sadeeq .....suko kallon ikon ALLAH kawai suka tsaya yi suna ayyana tsakanin uwa da 'ya sai ALLAH.

Aunty huwaila ce ta dawo da Husna daga mafarkin ta da cewa "Husna kinsan kuwa cewa mahaifiyar ki Bata mutu ba? Mafarkin ki daidai yake da amsa ta.

Husna cikin kaduwa da razana ta Fara kallon aunty huwaila Tana cewa "Ammin su muhibbat kice min baiwar ALLAH da kike Kira Yaya itace mamana Kuma Yar uwarki?

Huwaila tsayawa tayi Tana Mata kallon mamaki.

Can Husna tasa kuka Tana Kama hannun huwaila Tana cewa Dan ALLAH kice min itace kafin zuciyata ta tarwatse na sake fahimtar hakane ta mafarkin da nayi da Kuma shak'uwa da nakeji akanta tun zamana daku a India.

Huwaila rikota tayi Tana cewa "eh Husna itace yayata mahaifiyar ki amaryar baba kishiyar anamimiya mama habee.

Da gudu Husna ta tafi ta rungume ta tana Kuka,itama kukan takeyi Tana cewa "ALLAH sarki Asma'u ta Ashe Zan sake ganin ki ,nasan kinsha gwagwarmayar rayuwa hanun habee wacce babu ALLAH aranta Amman naji labari komai yazo k'arshe awajen k'anwata tilo wacce samun kamarta sai antona ta Mana gatan da ba kowane ze Mana ba bamuda kamarta har mu gushe bazamu bar Mata Addu'a ba.

Sosai kowa ya tausaya musu ,da sauri Husna ta sauka ta Kira mumcy tazo taga mayaifinta ,da sauri hajiya babba ta hauro har aunty sa'adiya akama waya tazo itama suka dinga tayata murna duba da Jin labarin asiri aka Mata ta hanyar hayaki aka kashe ta har aka sallace ta aka birne ta duk da sun Rasa yadda akayi ta dawo da ranta matsayin me rangwamen hakali kuma.

Huwaila ce tace wanan amsar habee ce zata iya amsawa idan muka Mata diran mikiya Dan bazanbar Abin ya tafi abanza ba Dole ta girbi tashin hankali yayin da take Jin taci bulus.

Sai Husna tace "ya kamata Kam aunty Amman abari sai Bayan bikin humaira Dan Gobe za'a daura Mata Aure.

Sai huwaila tayi wata she was kafin tace "shine daidai ta girbi shukar da ta bama Ruwa ,alokacin da take cikin farinciki lokacin zamu tarwatsa Mata shi naji dad'in labarin nan,maman Husna zatayi magana huwaila ta dakatar da ita da cewa"nifa duk Wanda ze dakatar Dani daga kudirina kamar ya hanani cimma burina ne kawai aunty kiyi shiru inbaki da gudumawa.

Aunty sa'adiya ma tace "gaskiya Kar a saurara Mata dari bisa dari tabada goyon baya rafiya yakin Nan ma da ita za'ayi.

Mumcy ma tace ya kamata a nuna Mata annabi ya faku Kam Amman ta hanyar lumana Dan ALLAH,huwai toh kawai tace.

Sadeeq ma yace "Dole tasan tayi babban tabargaza akuma gyara Mata atanar da batayi tunanin Akwai me gyara matan ba.

Bayan sun Gama maganar huwaila d sadeeq d maman Husna suka tafi da niyar gobe zasu hadu a gidan baba suka bama junan su lokaci.

Mumcy d sa'adiya cike d mamaki suka dinga tatauna maganar a kasa wajen mumcy.

Bayan FU'AD ya dawo Husna ta rokeshi Akan zata gidan su baba ta gaishe shi , FU'AD cewa yayi bazata ba gidan muguwar matan Nan ita da Bata da lafiya ma?

Jin suna takaddama a falon mumcy ,sai mumcy ta fito tashiga maganar har takema FU'AD bayani Akan samun mayaifinyar Husna da Kuma zuwan da sasuyi gobe har tamai umarni da ya barta taje.

FU'AD badan ranshi yaso ba ya hak'ura ya sake kafa huja da matarkin Husna , mumcy hakuri ta bashi sanan tace Akwai ALLAH da Addu'a za'adage insha ALLAH alkadarinta ya karye.

Ranar ma FU'AD a d'akin Husna ya kwana yanata bata kulawa.

Washe gari gidan mama habee ya dinke anyi party jiya yau daurin Aure angon ma be samu zuwa ba wai yayi tafiyar gagawa.

Gidan mama habee ancika antunbatsa baba yaba wani walicin Auren humaira andaura Aure kowa ya sheda aka dinga raba alewa da goro.

Aranar za'akai Amarya ,Amarya sai rawar Kai takeyi ta Gama hada kayanta tsaf na barin gidan zuwa gidan Alhajin birni taci kaza ta kora da juice ta gaji da cin tuwon datsan mama habee.

Su aunty sa'adiya d Husna sun shirya Dan anti sa'adiya tace kallo baze wuceta ba,suna jiran wayar su aunty huwaila.
Chapter 89 · 0% Book details