← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 95

Sashe 9

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aiko FU'AD ma yace kawai ka tafi d matar ka ai bazata sake damu ba nake gani tunda Bata Saba ba damu ba sai ahankali ,Amman yadda kuka Gama shawarar dai ,barin Shiga nayi wanka n fito gaba d'aya kafin Nan na harbo yarinyar Nan ta gyara min falon yau har d'akin ma zata gyara wancan ne kawai bazata gyara ba Dan ba sosai nake Shiga ba ,big bro yace sai ka sakko ...

Bayan yayan y sakko ,y zauna suka hau fira da momcy ,amaryar yayace ta Fara cewa Ina wanan _cuty girl_ d'in ta tayani gyaran sashin mu momcy ? Momcy ta gane Asma'u take nufi ,sai tace "Asma'u? Tace "eh Asmah ita, sai momcy tace wlh Bata Zo ba yau Ina kyautata zaton hannun tane y hanata zuwa ,lokacin da yayi daidai d sakowan FU'AD ya katse musu hiran ta hanyar gaishe d momcy da amaryan yayan shi cikin raha d sakin fuska , sai momcy taci gaba da cewa , "tunda har takai yanzu Bata Zo ba Akwai dalili Mai k'arfi ,Amman Zan sa Harri taje ta dubo min ita be kamata a barta ba Kuma anji shiru tunda Bata tab'a yin hakan ba tunda hafeeza tamin canji da ita ,sai ko FU'AD yace ...

"Wai yarinyar Nan kin zuwa tayi naji kunata dogon tataunawa akanta ? Momcy tace eh ,kawai t Rabu dashi , sai ko yace dama tsintacen mage baya mage ne ko meye Inji hausawa ,Haka kawai kika rakib'o Mana ita momcy Ni gwanda karta k'ara zuwa ma karki sa kowa ya bita please momcy.

Kafin momcy tayi mgn yayan yayi saurin cewa , FU'AD wai me kazama ne ? Ina Ruwanka momcy tafika sanin dalilin d yasa ta karbeta ba taimaka Mata takeyi ba? Baka Jin dad'in taimakon d takema mahaifiyar Kane? Kuma yanzu kasan dalilin d ya hanata zuwa ne Ana cemaka taji ciwo Ana tunanin ciwon ne ya hanata zuwa ,Yana d kyau a tabatar ai ko? Kuma yanzu Naga kaima Tana amfanar ka ko acikin gidan?

FU'AD Yana Kai Loma Dankalin turawa soyaye da kwai har ze kware ya kurbi tea kakaura ,yace yaya Dame take amfana na a gidan Nan? Wlh babu amfanin d ta tab'a min ko zatamin anan gaba ...yayan y katse shi d cewa Amman FU'AD bakai ne FU'AD d'in momcy da muka Gama Hira d'azu ba Koh? Waye yace ze Kira Asama take kowa? Ta Mai gyaran falo da d'aki ? Ba Kai bane?

FU'AD yace oh wanan nine Mana to ai Daman aikin tane ,ba wai taimakona zatayi ba ,aikin tane Daman ,da ta samu na barta ta haumin sama ma batayi arziki ba ,yarinya kamar aljana ga gulmar shiru shiru ko had'a ido da mutum Bata yi sbd gulmanta fa ,hmmm can tagane .

Amaryar yayan CE tace ,is good ai hakan means tanada halaye masu kyau Bata tsatsare mutum da ido irin n rashin Tarbiya Kuma respect ne ai take baka ,Kai K'anina akwai Wanda ze iya maka kuwa? Ko ka yadda ko kak'i Tana maka Amfani har momcy ma dole ma ka yadda ,kowa ya amsa da kema Kya fad'a ,shi ko FU'AD yace Sam bazaku gane bane kawai abar zance wanan Abun , da sauri momcy ta wurgo Mai tambaya mekace son? Cikin tunawa da mgn da sukayi a baya yace oh no sorry momcy wlh mantawa nayi Asama take ko ma'ule , ALLAH y huci zuciyar uwa ta gari na tab'a Yar Aikin ta Mai yi Mata hidima _double sorry momcy_ Yana sake loman abincin shi ...

Momcy kwafa kawai tayi ,itako Amarya Abin dariya y Bata d sha'awa yadda yaran ke girmama mahaifiyar su itama take jansu ajiki sabanin tata mom d'in Dan ita mahaifinta yafi janta ajiki .

Yayan FU'AD d'in ne yace ,Haka ka zama ko ,yanzu kayi laifi ka wanke laifin ka ,momcy tace ka manta da son ne ? Halin shinan na dabara Yana Nan har yanzu ,duk suka sa dariya ,ya b'ata ma ya wanke ma ,duk shi kad'ai ...

Momcy ce ta Kira Harri tace taje ta Taya Amaryar yayan FU'AD gyaran sashin su ,in ta gama Kuma zataje ta dubo Mata lpy Ma'u ,Harri ta amsa da to hajiya ,suka nufi sashin ita d matar yayan .

FU'AD ko cewa yayi yanzu dole sai kin aika ? In ta damu ai zatazo d kanta ,Dan ALLAH Kar ki ........be k'arasa ba momcy tace son kafita idona na rufe wlh zaka jama Kanka zuwa dubiya ko Aiken dole Dan umarni Zan baka zazzafa ,wlh zakaja na dawo da Aiken Kanka na umarce ka da kaje ka dubo min ita , in Kuma ban Isa ba sake furta kalmar A Akan Asma'u na shayar da Kai Ruwan mamaki yanzunan ...

Aiko FU'AD ya zaro ido ,har Yana sa yatsun sa yana Kama bakin shi yasan kad'an daga aikin momcy in ta d'au zafi Akan Abu ,Dan Haka y kame bakin shi ,be k'ara cewa ufan ba ,har yayan shi na tsokanar shi Amman yak'i cewa komai sai murmushi d nuna Mai momcy da yatsan shi ,yayan ya dinga Mai dariyar mugunta momcy tayi maganin shi ...

Anan yayan FU'AD d'in yake gayama momcy zeje wani aiki a Abuja na wata6 ya take ganin za'ayi zai tafi da madam ne ko ya barta anan? duk Abin d tace shi za'ayi Yana nuna girmanta a gare shi .

Shidai FU'AD nashi kunne , momcy tace da d'an uwanka ya girma ya kawo min surika ai da ya isheka shawara to be sa niyar girman ba bare ya zama abokin shawara in yayi hankali sanadin Auren ,.....

FU'AD yace hmmmm momcy yanzu a Mara hankali Ashe kiketa d'auka na? Ya taso daga inda yake karyawan y zauna kusa d yayan shi yace ai shi kenan ,Ni ban yi girman da Zan ajiye mace ba bawai Dan Banda Abin d Zan ciyar d ita ba ,in Mata 4 ne Zan iya ciyar dasu Dan dai Basu shinkafa,taliya,doya ,sai musu atamfa,shadda duk Zan iya kawai matar ce batazo ba sai tazo tukunna Yana wani shagwaba ..

Momcy ce tace duk Abin d zakayi dai kayi kana sani ,sakon daga Alhaji ubayyu Zan baka da ya bani ,
yayan mahaifin ka duk ranar da ya diro k'asar Nan to da mgn aurenka ze Zo ko kazaba ko ya zab'ar ma ,kuma sai an d'aura zai bar k'asar ,Niko kasan bazan iya tijarar shi ba ,na gama Shan takaicin su tun Rasuwar mahaifin ku in Kuma so kake ka dawo min da abun da ya wuce ne toh ,ayanzu duk wata burga da tijara da zasu min be wuce akan Auren ka ba inaganin aurenka shi ze bani kariya da katanka Mai k'arfi ta karshe daga duk wani tuggun su ko tijarar su yazama na anyi na farko anyi na k'arshe Dan babu wani abun magana daga Haka nasan ,ka ajiye wanan a ranka shi yisa na sanar maka be fad'i watan zuwan shi ba Amman kasan zai Zo d'in tun da y furta Dan kasan yafi kowa rashin son zaman lpy.

Duk sai da FU'AD d yayan shi suka tuno wasu abubuwan da suka shud'e tun Kan Rasuwar mahaifin su har Bayan Rasuwar mahaifin su Wanda hakan ya gadar ma da momcy hawan jini shiyisa har yau suke gudun Abin da ze b'ata Mata Rai ..

Yayan FU'AD ne yace kaji ko ,sai kasan Abin yi ,in kana gudun b'acin Ran mahaifiyar ka in baka manta tak'addamar da akasha Akan Aure na ba...shiko FU'AD cewa yayi ku Rabu dashi can ya gane masifafe kowa baya Jin dad'in ka a family har Abin d ka Haifa ,in ya mutu kafin zuwan shi mu maje ta'aziya da buhuhunan shinkafa da lemuka kala kala Yana fad'a Yana b'ata Rai ...

Ganin tsakanin shi d ALLAH yake magana yasa ,momcy Bata balbale shi d fad'a ba ,Amman sai tace in beyi mutuwar ALLAH ba sai kaje ka kashe shi ai kuje da buhuhunan shinkafar kwa had'a har d na gero ,kai Kuma kayi gadin duniyar tun da Kai bazaka mutu ba ...

FU'AD yasan momcy magana ta Gaya Mai Dan Haka be k'ara furta komai ba ,gudun sake b'ata Mata Rai.

Shi ko yayan shi cewa yayi , FU'AD yaro man kaza ,Amman komai yarintar ka Haka zamu aurar da Kai ko ga yarinya ne kuje kuyita yarintar ku ,shi dai bai cemai ufan ba y shiga b'acin ran maganar Alh ubaiyyu ..

Har su momcy suka Gama shawara ,momcy ta umarci yayan y tafi d matar shi yace amgama Haka za'ayi , har Harri tazo Bayan sun Gama gyaran sashin ,momcy ta aikata gidan su ma'un dubo ko lpy , FU'AD bai k'ara cewa uffan ba sai Danna wayar shi d yake tayi ....

Bayan Harri taje t dawo ,ta zayyane ma momcy komai na jikin Ma'u ne babu dad'i ga hanun ya samata zazzab'i shine ya hanata zuwa ,kowa sai d ya tausaya Mata Amman Banda FU'AD .....

Maman Shaheed ce👌🏻
[4/23, 4:00 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA*

_RUBUTAWA DA TSARAWA_
BY
*Fatima Abubakar Shu'aib*
(Maman shaheed)

_shafi na 11_

*Wanan shafin nakune kuyi yadda kuke so dashi*

_Namcy ummu Qaseem_
_ummi Abeeha_
_mmn Ameer_
_Mrs sulaiman_
_daugter ummu ammar_
_maryam bello_
_mmn hafeeza_
_mmn sadiq_
_Aisha_
_mrs nuur_

Kunada yawa💋💋

Teemah namcy team FU'AD😀😉

Washe gari ma Haka ma'u Bata samu zuwa gidan momcy ba ,sai momcy ce ta sake tura Hari don dubo jikin ta har da kayan dubiya tace, amata sannu .

Ma'u taji dad'in tubiyar da momcy ta Aiko ,Tana k'ara girmama momcy da darajata Dan irin su Basu da yawa a Halin yanzu ,tace amata godiya sosai da sosai ,sanan Hari ta tafi .

Baban Ma'u akai akai yake tmby jikinta da hannun ta in be dawo gida d kanshi ba to zai Aiko haidar ya dubata da jiki Dan ko ya Aiko Aminu Mai bima humaira ma yasan ba zuwa zeyi ba Dan Halin su guda d su humaira d su mmn habee.
Chapter 9 · 0% Book details