← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 95

Sashe 48

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

FU'AD bakin shi d'auke da sallama ya Shiga Bata falon Dan Haka ya Mata sallama a k'ofan d'akinta "yace gashi yazo tazo ta fad'i matsalar ta"

Sanaya dake jikin dressing mirror Tana gyara kanta sai cemai tayi "ka shigo Ina d'an wani Abu ne please"

Jin ta ambaci kalmar ban hak'uri yasa shi shiga.

Yana Shiga yayi tozali da gashin kanta yanata walkiya yaci uwar Mai anata ciyar dashi da mayuka masu tsadar kud'i ,hankalinta kwance ta nuna Mai wata 1seater a d'akin wai ya zauna.

Ganin besan manufarta ba Kuma Yana son sani sai ya biye Mata ya zauna, yace " Ina jinki Amman in magana zakimin ki rufe wanan abun tukunna Dan ba kasafai nafiye son ganin tsaraicin gashi ba,infa kina son na saurare ki kenan.

Sanaya cewa tayi "gashin ma wata duniya ne? Meye acikin gashi ?

Sai gani tayi FU'AD ya mik'e ze fice babu ko magana fuskar Nan kamar be tab'a dariya ba.

Sai sanaya tace "Ina zaka kuma ko duk akan gashin ne?

Kalon ta yayi ta gefen ido yace "bana maimaita magana in kin Gama Ina falo ..........

Be fita ba sanaya tace "toh na rufe Zo muyi magana ta fahimta Tana Mai sakaya gashin ta da gyalen After dress.

FU'AD cewa yayi "Ina sauraron ki ?

Sanaya sai cewa tayi ,so nake na tafi Egypt Nan da 1week Kuma so nake ka Fara sanarma dady sanan duk yadda dady zai tambayeka karka nuna Mai nice nakeson zuwa bisa ummarnin ka ne nakeson zuwa zaka cemai kaji?

FU'AD wani kalon shek'e k'e ya Mata Yana Mai tashi Yana tafiya cikin nutsuwa ya d'auko wani Abu a farar leda da wasu Akan takkada Fara ya dawo ya zauna Yana cemata "wanan Amman umarni kike bani ko ba shawara ba ko neman Alfarma?

Far sanaya tayi da Ido Tana ce Mai "babu ko 1 kawai magana mukeyi tsakanin Ni da kai"

FU'AD yace "aa umarni dai Dan yafi Kama da umarni"

Sai ko sanaya ta harzuk'a tunda Haka kace "eh shi ne Kuma aikatashi ya zama Dole nifa autenka ko Kai basa gabana kasa anzo antakura Ni a Nan 9ja ko a gidan yarin Egypt iya kacin takura da matsin da Zan Shiga be Kai Wanda kukamim ba Kai da dady,Tana magana kamar zatayi kuka kuma cikin gatsali take maganar Tata."

FU'AD sai da ya Gama k'arema Abin da ya d'ako kallo ya dubeta yace "meye wanan kike sawa a hannun ki?

Sanaya harara ta wurga Mai ,tace ohon maka da ka d'auka sai abin ya baka amsa Tana turo Baki Tana d'auke kanta daga kalon shi.

FU'AD mik'ewa yayi Yana Mai Shirin tafiya dashi,sai sanaya tace "Ina zaka min da Abu bafa a lefenka aka sako ba impact ga lefenka can ka d'ebe bana so bana buk'atan su Ni ka barni naje Naga iyayena kaji ko malam?

Juyowa Yana jifanta da wani mugun kallo Yana cewa "ALLAH ya shirye ki haramun ne saka farce gashin ma ALLAH yasa bana doki bane Dan Naga lamarin ki da gyara Kuma Babu inda Zaki matuk'ar Ni Zan taimaka wajen tafiyar ki ,maganar tafiya Kuma kifi Ruwa gudu ke Kika sani yasa Kai Yana Shirin barin d'akin."

Da sauri ta biyo shi Tana cemai "see u! 9ja man kawai ungo kataba kaji wuce na is natural from God ,ba'a tab'a ganin gashi ba angani an tsure shafi arziki Kar ka tafi baka dangwala ba ,sosai sanaya ta Sha gaban FU'AD Tana tura Mai kanta .

Kad'an ta buge Mai fuska ,sai tureta yayi Yana cewa ,matsa can kazama Ina abun yake? Farce Kuma karna k'ara ganin kinsa ki dinga sanin hukunci ALLAH aduk Abin da zakiyi Kar Rayuwar wasu a waje ta Rud'e ki ko kasashen wajen ma ba kowane Mara tarbiya ba ke zuwa kikayi ma wajen muko haifar mu akayi acan ma inkin manta na tuna Miki inbaki da labari kije asanar Miki keda kaiki akayi daga baya ma har wani felek'e zakiyi muku 'yan can ne munada takaddun mu keko duk daga baya aka Miki ki Kama kanki karya gudu ya barki yarinya,ya fice yabar Mata falon.

"Sanaya sai cizon yatsa takeyi da mita kamar tayi ihu take ji ,can tace inkasan wata bakasan wata ba wlh sai na maka sharri wajen gyatumar ka wallahi kuma sai nabar k'asar Nan Koda tsiya Koda arziki.

FU'AD komawar shi part d'in mumcy ya had'u da mumcy da Husna sunata hira cikin nishad'i da birgewa har ze haura sama Bayan Yama mumcy sannu ,sai mumcy ta Kira shi ta tambaye shi lafiya ? Sai yayi gagawar sake fuskar shi yace "Mata lafiya Lau" tace Mai "yau bazashi office bane?

Sai FU'AD yace "mata eh wata unguwa zasu da B2k abokin shi zezo gida ya d'auke shi"

Sai mumcy tace "toh shikenan ALLAH ya kawo shi lafiya"

FU'AD yace "Ameen"

Mumcy da Husna anata Hira FU'AD na tsomo Baki sama_ sama yanayi Yana galama husna Hara ra itama Tana mayar Mai duk ba tare da mumcy tasan sunayi ba har B2k ya shigo bak'in shi d'auke da sallama.

Yana Mai k'ok'arin rusunawa ya gaishe da mumcy fuskar shi d'auke da fara'a, sa'anan tun shigowa shi yake kalon Husna FU'AD ma ya lura da haka.

sai ko FU'AD ya Harare shi Yana Mai cemai dalla malam ka fad'o ma mutane cikin iyali Babu neman izini gwauron banza kawai."

Sai ko B2k ya juyo yace Mai "iyeee yaushe akayi Abu da har........Bari dai nayi shiru Yana sake tambayar shi Kai abokina tambayar ka zanyi Dan ALLAH seriously babu zancen Wasa wanan ba itace Dan girl ba babu Kama suna nasan ka fahimta Dan hoton ta baze taba bace min ba, please kace min itace abokina?

FU'AD ya Fara hassala , mumcy ma ta Fara gano hakan lamarin ya Mata dad'i sai tace sandar da wani ya Raina ,wani ita yake nema ya samu ta duka ai,ta tafi d'aki Tana cema Husna tasa akawo ma B2k Ruwa.

Husna da sauri ta amsa tana Mai niyar zuwa su gaisa da B2k da biyu ta nufi inda yake.

Batayi aune ba sai muryar FU'AD ta tsinkayo Yana cemata ke Ina Zaki?

Ci gaba tayi da tafiya Tana cewa ,zamu gaisa ne da abokin ka,sai yace dalla malama bazaku gaisan ba,shima B2k yace aa gaisuwa dai abokina ? Kar muyi Haka dakai Ina wuni Asma'u kamar Haka naji mumcy tace ko?

Asma'u gyad'a Kai tayi tace hakane sunan , FU'AD yazo iya wuya sai tasowa sukaga yayi Yana cewa "wallahi kina k'ara amsa Mai ranki ze b'aci wacce batasan mutuncin kanta ba kawai,bace min anan.

Husna d sauri ta nufi kitchen da aiwatar d umarnin mumcy ranta fes har da ita ake tusawa FU'AD haushi.

Bayan shigar Husna kitchen FU'AD masifa ya farama b2k har ma'un ta fito da kwalin juice da glass cup a hannun da Harri Kuma na biye da ita a baya suna nufan inda B2k yake sai k'ara murmusawa yakeyi , FU'AD ya Gama zuwa iya wuya ganin Harri ne kawai yasa shi tsayawa da surfa musu masifa Amman Husna nata karb'an uwar harara da mugun kallo.

Husna ce tace abokin mu ga Ruwa kasha ko?

Ita Kuma harrin ta ajiye ta fita ,sai ko FU'AD ya shak'o Husna Yana cemata a gidan uwar wa k'ato ya zama anokin ki? Kema wuyanki ya Fara kauri ko yaushe kikaci Kika k'oshi da har Zaki goge bakin ki?

B2K ne ya taso Yana cemai "haba abikina ba'a rik'e mace Haka Mata rarashin su akeyi."

Sai ko FU'AD ya juyo Yana cemai wallahi karka karaso inda muke balle ka rik'e matar mutane Dan ihun gardi Zan maka Naga gama nema Shiga gonar da ba taka ba har ka zarme."

B2K dai cemai yayi "naji Amman dai saketa daga mugun Rik'on Nan naka ,kamin Kuma bayani yadda Zan fuskanta shin wacece ita awajen ka a yanzu? Amman tabass wanan itace matar da kamin kyauta.........be k'arasa ba ...... FU'AD yace Kar ka k'arasa wallahi kana k'arasawa Ina maka wulak'ancin da baka tab'a tsammami ba ,tambayar ka akayi? Suda sarkin labari? Aku kuturu.....

B2K dariya kawai ya Fara yima FU'AD.

Sai FU'AD ya koma kanshi ya sake Ma'u ,Yana cemai Kai Zo kabar Min gida na fahimci tada zaune tsaye kazoyi har cikin gida na fita inzo in sameka, Yana nuna Mai hanyar waje da hannun shi."

Ma'u na kwacewa tayi d'akin mumcy Tana murguda ma FU'AD Baki da hararar shi Tana cema B2k ,abokin mu ka gaida gida sai gani na biyu ,a zafafe FU'AD ya biyota ta k'arasa d'akin mumcy da sauri, B2k cewa yayi "to madam sai gani na biyu sai kin ganni"

Yana matana FU'AD na tura shi waje Yana cemai malam na fasa fitar Dan Isa kawai ,Kai sai nayi shari'a ma dakai Dan iskan banza.

FU'AD ya juya ze Shiga falo , B2k yace "To tafiyar Tamu fa? Sai ko FU'AD "yace bazanje ba" B2k yace Dan ALLAH kazo mu tafi kasan Ana jiran mu"
FU'AD cewa yayi "akwana Ana jira Mana Kai namaka ta mahaukaci wallahi bazanje ba sai gobe inaga da Hali yau tsare gida na zanyi saboda tsaro badan tsoro ba ,yayi hanyar shigewa falon.

FU'AD jiyo muryar B2k yayi Yana cemai ,lailai mutumina ka shak'a da yawa ,kayi hak'uri goben muje nazo gida mu tafi ko na jiraka?

Harara FU'AD ya juyo ya wurga Mai yace ,ka jirani Kar ka k'ara zuwarmin gida inba haka ba ihun barawo zansa amaka." Ya shige falo ya turo k'ofa da k'arfi.

B2K cewa yayi Kai ,na Tabo abokina fa da yawa wai ya suke da yarinyar Nan ? Yanzu ya kashe Mana fitar mu ? Dole na bada hak'uri kenan ince sai gobe zamu Zo in yaga dama? Ya zanyi Dole na nayi hakan ya d'aga kafad'a ya d'auki motar shi yayi waje Yana ma FU'AD muguwar dariya har da gyaran Kiran waya FU'AD har ta tsinke FU'AD be daga ba.

Share
And
Comments
[4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA*

```RUBUTAWA DA TSARAWA```
BY
*FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB*
(Maman shaheed)

💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥

Pg40

*Special thanks to all my Fanc*❤ # ONE LOVE# *SON SO FISABILILLAHI*🥰😍😘........

FU'AD ya fusata iya fusata ,hankalin shi be kwanta ba sai da yaga fitar B2k daga gidan.
Chapter 48 · 0% Book details