← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 95

Sashe 36

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Babu shiri FU'AD ya koma saman shi da niyar hak'ura da fita dama neman magana ne ,ya kwankwasa k'ofan d'akin Ma'u bisa umrnin mumcy yace ki tashi ki karya Inji wacce ta aura min ke in kin tashi ruwan ki in kin cigaba da kwanciya kaman Ruwa ke Kika sani nadai isar Miki da sako "ma' u Dan ta k'ular dashi sai cewa tayi to naji Dan aike " FU'AD a kufule da zai tura k'ofan d'akin ya Shiga ko ya mayar Mata da amsa sai kawai zuciyar shi ta rarashe shi Akan karka kulata kuyi sa'in sa har ranshi ya b'aci wajen mumcy Dan haka ya rabu da ita yayi kamar beji me tace ba sai ma barin wajen da yayi ya koma d'akin shi .
Sai da Ma'u ta tabbatar Babu alamun motsin mutum a falon sanan ta fito Dan tasan Dole zata buk'aci abinci ,tayi sa'a ta gansu dama ita suke jira ta bubud'e taga Wanda zata iya ci taci ta k'oshi sanan ta gyara falon yayi tas sanan ta koma bathroom d'in dake falon shima ta gyare shi ta feshe da kayan k'amshin band'aki sanan ta koma nata d'akin ta gyara FU'AD da Ma'u kowa na d'akin shi in anga sun fito motsi sukaji a k'ofar falo alamun wani ze shigo ko in sunji sallama ,Amman Babu wata Hira tsakanin su Haka har wani dare ya sake yi .

Yau kwanan FU'AD 3 da Aure Amman tsakanin shi da matan shi kadatan kada han ,su dady Kuma sun Gama Shirin komawa Egypt sanaya nata tsula iskancin ta sai dady ne yake zazabirar ta da masifa Akan Babu inda zata bisu da aurenta Kuma wlh yaji wani mumunan labari ranta ze b'aci ,sanaya ranar kwana tayi Tana mita adakeka a hanaka kuka Haka kawai to wlh itama zata musu Abin da bazasu so ba .

Maman shaheed😍😘
[4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA*

```RUBUTAWA DA TSARAWA```
BY
*FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB*
(Maman shaheed)

💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥

Pg32

Tunda FU'AD ya Shiga d'aki be fito ba sai da ya tabbatar sanaya ta bar falon Dan tun Tana mita har ta hak'ura har dadyn ta ya kirata tadinga Mai shagwaba Yana ratashin ta ,har ta gaji ta tafi kwanciya itama .
FU'AD futowa yayi ya samu Abin da ze sama cikin shi ,Bayan ya k'oshi yayi Kat ya koma d'aki duk tunani ya dabaibaye shi ,ya Rasa gane wanne irin Aure yayi ko Dame zai Kira Auren da kyar ya samu bacci yayi gaba dashi ,bai farka ba sai da ya tashi ya ji Ana Shirin Shiga sallah asuba da gagawa yayi alwala ya fice masalaci don sallah cikin jam'i baya wuce shi sai da dalili.
Chapter 36 · 0% Book details