← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 95

Sashe 73

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lura da yanayin FU'AD yasa aunty huwaila kiran Husna ,Bayan tazo ta umarce ta da tataunawa da mumcy da mijinta Tama tashi tabarsu Bayan ta Mata bayanin duk Abin da suka tatauna akai.

Husna sosai ta dinga Jin son mumcy uwar datako FU'AD ko be ce mata komai ba. itama Bata ce Mai ba , mumcy nata mamaki da Halin da ya nuna kamar ba Wanda ya Gama Mata magiya Akan zuwa ba yamaga husnan memakon murna sai kunci da yaketayi har yanzu be cemata komai? Ko dayake itama ta birgeni da Taki kulashi Naga ta sake samun wayewa da sabuwar rayuwa ma ai bazan shiga maganar ku ba har sai ka magantu sai ta dinga Jan Husna da Hira kawai ,Husna nata tambayar su aunty sa'adiya.....

Bayan aunty huwaila ta dawone sunata Hira da su mumcy muhibat da su Husna karama da Affan sukazo suka gaishe da mumcy Affan hannu ya mik'ama FU'AD ,da kamar baze bashi ba sai kawai suka gaisa adole...

Husna ce ta Fara gabatar ma da mumcy Affan matsayin yayanta sai sadeeq Wanda baya Nan sai muhibat Yar uwart sai husana autar su takwarar ta Kuma.

Sosai mumcy ta Nuna Jin dad'in ta tana sa musu Albarka cikin Rayuwar su."

FU'AD ne ya Fara tsokano maganar cewa Husna ta shirya tare zasu tafi Gobe zasu koma....

Husna tayi tsallen Albarka tace ita ba Gobe zata koma ba ,ganin zata Mai gaddama shi Kuma yace dolenta ba Aure ne akanta ba?

Aunty huwaila na sane Taki saka Baki , mumcy ma da biyu Taki magana ,su Affan ma ganin manya basuyi magana ba Suma sukayi shiru.....

Ganin sunki saka Baki ga Affan da yaketa binta da kallo Yana so ta dago ta kalle shi ya Mata magana da Ido Akan tabi mijinta ta koma dakinta, Amman Taki d'agowa....

Hakan ya k'ara k'ular da FU'AD yace sai fa kin tafi Gobe in har da igiyar aurenki a hannuna kiji na gaya Miki Kuma Dole ki Amince,sai ko Husna ta d'ago ta kalli Affan ya dinga rarashinta da Ido ,Amman Husna ta kalli FU'AD tace wallahi bazan tafi Gobe ba Tama fashe da kuka ta mik'e da sauri ta nufi d'akin ta ,muhiy d Husna suka bita da sauri suna Kiran sunan ta."

FU'AD ko shak'o wuyan Affan yayi Yana huci Yana cewa me son Rana sunna me ka Gaya Mata da Ido? Eye Meka gayamata nace........?

Da sauri mumcy ta Mike ta nufi inda suke Tana Kiran sunan FU'AD da k'arfi...............

😍😍😍🥰🥰
[4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA*

```RUBUTAWA DA TSARAWA```
BY
*FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB*
( Maman shaheed)

💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥

Pg57

Bayan su Affan sun sauke mumcy ,sun dawo gida suka samu Ammin su nata ma Husna nasiha akan bin mijinta Husna nata kuka Tana nuna batason binshi a yanzu tafison zuwa wani lokaci Amman ba yanzu ba sanan bataso tayi Nisa da Yaya matar da batasan ko wacece ba Amman jikinta na sanar da ita matsayinta Dan yanzu sun shak'u Dan har abinci take Bata a Baki gashi wani lokacin Tana yunk'urin yi Mata magana bakin ne kawai baya bud'uwa sai ta hak'ura.

Affan da sadeeq ma hak'uri suka dinga ba Husna da mata Al'k'awarin duk Abin da ya dameta tayi gagawan sanar musu ko menene zasu Mata maganin shi iya k'arfin su ba Akan FU'AD ba kawai ko Akan waye ma har uwar Rik'on ta mama habee ,sanan zasu iya zuwa har 9ja su dawo da inta indiya daga yanzu ta saka acikin ranta family ta suna indiya in 9ja ta k'iki indiya na mararin ki.....

Wanan maganganun sun sanyaya ran Husna ,Kuma sun k'ara Mata karsashin Jin ta shirya kwatoma kanta 'yanci a wajen FU'AD da duk wani da yakeson kawo turnik'i cikin Rayuwarta inko har abun yafi k'arfinta da gudu zata sanar musu kamar yadda suka buk'aci hakan.

Muhibat da Husna sunata nuna rashin Jin dad'in Rayuwar da zasuyi da Husna ,sanan yanzu Basu da wajen Hira sai dak'in Yaya matar Nan cikin nutsuwa da nuna rashin hayaniya har hirar tafiyar Husna suke ,matar ta zuba musu ido kamar Tana fahimtar Abin da suke cewa ,daga baya ma tasa musu kuka Husna ce taje ta dinga rarashin ta tana tanbayarta meyasa take kuka ?
Ci gaba tayi da kuka babu magana ganin bazata ce komai ba inda sabo ta Saba yasa Husna ta samu ta zame jikinta da kyar ta d'ebo Mata abinci ta dinga Bata abaki Tana ci ta Bata ruwa Wanda akayi Addu'o'e aciki ta Mata bissimillah tasha....

Husna ido ta zuba
Mata Tana tambayan kanta dalilin da yasa takejin wasu abubuwa game da ita ? Rashin samun gamsasuiyar amsa yasa tabar d'akin ta koma falon Tana kallon tv tare da su Husna da muhibbat Dan sun fito sun barta aciki."

Suna zaune ne har Affan ya fito ya zauna suna Hira Yana tsokanar Husna wai matar boss ,Husna ta Harare shi tace "ai bada ita yakeyi ba"

Affan yace "eh da wata nakeyi dama bance dake nakeyi ba"

Sai ga sadeeq ya fito shima ya zauna kusa da Husna Yana cewa "ya k'anwar mu medame kike buk'ata ne na tsaraba ko Abin amfanin ki mu Fara tanadar Miki kafin zakin mijinki yazo tafiya dake Dan wanan gani nake baze barki ki wani Jima batare da ya tasa k'eyar ki zuwa 9ja ba"

Husna kalon shi tayi kafin tace "har da Kai ya sadeeq ,Ni fa kubarni ba yanzu Zan barku ba Kuma ma kozan tafi bana buk'atar komai Inna rik'e tsaraba ne na ma baba tsaraba bayanshi Banda kowa a 9ja sai 'yan mutunci kawai."

Affan dariya yayi kafin yace 'yan mutuncin dama yake nufi Kuma dai ki zama cikin shiri kinsan Ammi Bata Isa ta hanaki bin mijin ki me........sai Ammi tayi saurin cewa me me? Tana Shirin zama nesa dasu,zaka farane?

Sai Husna karama tace "Yaya Affan ya koma me tsokana sai tsokanar namcy na yake kamar wata abokiyar wasan shi ya mayar da ita ,sai ko yace "in ban tsokaneta ba k'anwar wa kukeso na tsokana?

Duk suka saka dariya Banda Husna ....

Washe gari FU'AD har Airport ya Kai mumcy ya Mata fatan sauka lafiya , mumcy nata Mai fad'an yabi komai ahankali ya kwantar da Kai batason Halin Nan da ya aro in yasan bazeyi Abin da ya Dace ba ya batta ta zauna ta taho da ita shi ya tafi yanzu."

FU'AD sai cewa yayi " haba mumcy wanan ai ba akin ki bane ke ai kin Gama naki sauran nawa ne" mumcy tayi murmushi tace toh Ina sauraron ka naji yaushe zaku taho kasan sanaya Tana can itama jiranka take a matsayinta na matarka Dan Haka Kar ashiga hakinta Ayi maza a dawo ,a fili FU'AD sai cewa yayi to ace Mata Ina hanya insha ALLAH ,a zuci kuma yace wai hakki Ni na Gama Bata hakkinta babu Abin da babu a gidan in kud'ine tamin magana na Mata transfer ko nawa take buk'ata...

Bayan jirgin mumcy ya tashi FU'AD ya koma hotel duk sai yaji zaman hotel d'in babu dad'i Dan Haka ya Kira Yaya Jameel sukayi magana sosai Akan Husna Yaya Jameel ma jamai kunne ya dingayi har Yana cemai kodai yazo su tafi gidan su k'ara Basu hak'uri? FU'AD yace aa ya Bari ai angama komai tahowa ma zasuyi , Jameel yamai fatan Alkhairi da Mai nasihar rik'e matan shi da aka aura Mai da kyau."

FU'AD har ya kwanta ya sakejin duk babu dad'i ya fita ya shiga gari ya nemi wani abokin shi da suka tab'a karatu tare da Yama manta dashi sai yanzu ya tuna yaje gidan shi suka Gama Hira har yake cemai shima matarshi Tana Nan be boyemai komai ba ya Gaya Mai ,abokin nashi me suna musbahu kingkhan yace ya Kama ya karbi matarshi su tafi ta hanyar soyayya da nuna kulawa in ba hakaba wallahi zata iya bijirewa tace bazata bishi ba inya matsa Tana iya cewa Bata son Auren shi tafison d'an uwanta ......

Musbahu kingkhan be rufe bakiba FU'AD ya Fara huci Yana cewa yabar maganar Haka ,Dan bama ze tab'a faruwa ba ,musbahun yace Mai kana sonta kenan yanzu? FU'AD yace "ko Ina sonta ko bana sinta hakan ko sanin hakan ba abun da ya shafeka bane ,kawai kazo muje kamin rakiya sanan karka wuce makad'i da rawa Dan nasanka tun muna school Nima Kuma kasanni ,toh ban canza ba nine dai FU'AD basaraken da kuke min lak'abi da naci ubanku kuka goge sunan da kyar........

Dariya sosai musbahu yayi harda rike ciki ,Yana cewa "Kai abokina sunan fa ya Dace da Kai halinka dai Wanda yasanka kumafa baka canza ba wallahi kana Nan yadda nasanka , FU'AD ma yace "Haka zalika kaina kanari sarkin surutu halayenka duk suna Nan na tsallake gona da iri......

Bayan su Gama komai musbahu ya d'auki mota Yana tak'i FU'AD na gefen shi sunata hiran school life d'in su har suka Isa gidan...

Jin ance FU'AD ne Ammin su Affan tace "amai iso ya shigo har parlour ya shigo ,ya gaishe ta shida musbahu cikin girmamawa,tasa aka cikasu da Abin tsa Baki ,sanan tasa aka Kira Mai Husna ita Kuma ta tashi ta Basu wuri."

Husna abokin ta Fara gaisarwa kafin FU'AD Abin ya k'ular da FU'AD Amman ya basar ,gashi tun da ta fito ko fara'a tak'iyi , musbahu ko ya saki Baki ya dinga zuba kamar bakin indararo har sai da FU'AD ya dakatar dashi sanan ya tsaya ,Husna nata Mai dariya a zuciyarta."

FU'AD ne yace "ya maganar tafiyar mu kin Gama shiryawa?

Husna cewa tayi aa da saura ,sai Fu'ad yace sauran me ?

Husna tace" Akwai abin da nake jirane"

Sai FU'AD yace "shi Abin bashi da suna ?

Sai musbahu yace kaima kamar bakasan Mata ba shirinsu baya k'atewa sai su d'au tsawon lokaci suna shiri hatta powder shafawan su sai su zagaye store suna nema sucema Basu samu type d'in su ba.......
Chapter 73 · 0% Book details