← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 95

Sashe 14

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiko ji yake kamar ya shak'o Ma'u ya had'a kanta d na k'adangaren dan ya fuskanci tsoron shi takeji ,kuma tamai rashin kunya kusan Kashi 3 be d'auki mataki ba ? Karta samu k'ofa fa ? Don Haka Yana huccin yasa tsunman ya damko wuyan k'adangaren ,shima a tsorace yake shahada kawai yayi ,Aiko da yaji k'adangaren zai fito ta Bayan hanun shi da sauri a razane ya wurgama Ma'u jikinta ,batare da yayi shawara ba ya koma gefe shi be d'iba da gudu ba kamar yadda su Hari wasu suka fita ta k'ofan waje na kitchen wasu kuma suka shiga falo momcy ce kawai Bata bar kitchen d'in ba ,itako Ma'u wani uwar k'ara da ta saki ,sai sumewa da tayi wajen ko numfashi batayi .

Momcy ce tayi kanta da sauri ta d'agota Tana Asma'u ,son kaga Abin d kaja Mana ko zaka kashe Yar mutane?

Baba Mai gadi ne ya shigo shida Hari ,ya fitar d k'adangaren ,saiko FU'AD yace abinda y kamata kuyi kenan kuka tsaya jiran Wanda be Saba ba ,Ni natafi office ,ko ya tsaya yabi takan Ma'u atunanin shi ai dama ta k'ular dashi yayi maganin Mara kunya ta sake yimai rashin kunya ,azahiri Kuma bada niya yayi ba kawai shima tsoron tsoro ne ,sai Abin yazo dadai Kan ma'un .

Asumen ya fice ya barta ,momcy ce ta dinga yimai masifa Tana cewa wlh yayi gagawan Kiran _family doctor_ d'in su yazo da gagawa in ba haka ba wlh zai gamu d fushin ta ,Jin furucin momcy yasa shi Kiran Dr din ya fice Yana cewa wai Yana zuwa .

Sa'adiya Jin hayaniya yasa ta shigo sashin ita d Yaya Jamil Bayan FU'AD y bar gidan .

Ma'u dai Ana kanta anata k'ok'arin ceto ranta Kuna Dr bai k'araso ba kowa hankalin shi atashe Banda Wanda ya asasa Abin Yama tafi aikin shi .

Hankalin momcy yafi na kowa tashi .

*Maman shaheed ce*👌🏻
[4/23, 4:00 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA*

_RUBUTAWA DA TSARAWA_
BY
*Fatima Abubakar Shu'aib*
(Maman shaheed)

_shafi na 15_

*shafin Nan sadaukarwa ne ga masu jajantama Ma'u ,Ma'u nayinku irin wujiga wujiga d'inan har Adana bayanan ku takeyi*
❤💚❤💚❤💚

Hankalin momcy yafi na kowa tashi ,Dan Haka sai da ta sake Kiran FU'AD ta Fara Mai Ruwan fad'a ,sai ga _family Dr_ su ya zo .

Bata Gama sauraron Abin d FU'AD yake cewa ba ta katse wayar ,ta Fara yimai mgn daga anmaida ma'un falo Kan doguwar kujera , FU'AD biyo Kiran momcy yayi Tak'i d'agawa ,ya Kira yafi so nawa Amman Tak'i ko kalon wayar .

Shiko Dr ya Fara aikin shi na duba Ma'u yanata Bata taimakon gagawa ,Jin momcy Bata d'aga wayar shi ba yasa shi ,canja hanya ya Kira Yaya Jamil ,momcy na Jin ringing ta d'ako ta kalli Jamil tace "indai son ne ya kiraka ban baka izinin d'aga wayar ba,daga Haka tamai d hankalin ta ga Dr da yake cukucukun ceto Rayuwar Ma'u .

Sai da aka kwashi kusan minti 30 sanan Ma'u tayi ajiyar zuciya Mai k'arfi d kusan kowa na wajen yaji ta ,su momcy da sa'adiya suka d'auki Hamdala suna godema ALLAH musamman yadda suka ga hankalin momcy ya tashi .

Momcy ta Kira sunan ta "Asma'u y meke damun ki ? Ma'u ta kalle su sosai sai ta tuno da abin da ya faru sai ta duk'unk'une momcy Tana cewa Dan ALLAH ku cire min shi banason shi .

Momcy taga Alamar afirgice take tace ,sannu Asma'u Babu komai ajikin ki Kinga ma Babu hijabin ai y sauka anfita dashi ma ,sannu kinji ,badan dg bakin momcy taji furucin ba d k'aryatawa zatayi Dan ta tsorata sosai d k'adangaren.

Sanan ta tashi ta zauna ,momcy tace ma Dr Babu wani abudai ko ya dubata da kyau ? Yace kawai firgita ce kawai normal Babu komai gashi har kina Mata mgn Tana amsawa ai Alhmd!

Momcy tamai godiya Abin yazo da sauki ,ya tafi Yana musu ALLAH ya Kara kiyayewa.

Jamil Kam har silent yasa wayan sbd Kiran d FU'AD yake tayi Mai ,ga momcy ta Hana d'aga wa.

Bayan Ma'u taci abinci ta k'oshi momcy tace ko zataje gida ta huta? Ma'un kamar kad'an take jira tace toh ,momcy ta had'a Mata su fruits ta cika Mata leda tace ta gaishe da mutan gidan , ALLAH ya kiyaye gaba ,Ma'u tayi Mata godiya ta tafi cike da zulumin k'iyayar da ke tsakanin ta da FU'AD Haka?

Koda ta Shiga gida mama habee ta ganta ta dawo da wuri sai ta Fara cewa ,anyi d'an Halin ? Naga kamar wacce aka Koro ,Suma da jarabar naci sai kace Dole su salamaki daga gidan Abu yaci tura ,Ni banyi zaton zaku Jima Haka bama ,gida kamar gidan hajiya babba Amman ta yadda take zaune dake kalan ki bad'a Mata kwarkwata ,ko bashin tsamin ki ma Bata ji ,ke naci suma naci maga Mai saki dai .

Ma'un dai ba maganganun mama habee babe a gaban ta ,sai wucewa tayi kawai ,Tana ce Mata bana Jin dad'i ne wlh ,mama habee tace hannun ne ya dawo? Ko shawarar ce ta motsa? Sai ko ma'un tace aa kawai kaina ke ciwo .

Mama habee tace banza bata Kai zomo kasuwa ,inkinyi wanke wanken can Kya huta kafin lokacin d'aura na dare Dan ciwon Kai ai baze Hana aikin gidan uba ba .

Ma'u tabita da kallo tace to barin ajiye hijabi na fito , ta nufi d'aki Tana Dana sanin dawowanta gidan,Amman ya ta iya haka zatayi Dole.

Bayan ta Kamala wanke wanken ,ta koma daki ta Dan ci ayabar ta sakamakon rashin Gama abincin Rana d ba'ayi ba har to 3 ,har Tasha lemun ta ma ta danji cikinta yad'an d'auka sanan ta fad'a dogon nazari ta inda zata Rama Abin da FU'AD ya Mata koda hakan na nufin barinta gidan.

FU'AD yaji Babu dad'i da momcy tak'i d'aga wayar shi ,yasan Tana Nan Tana ciki dashi ,don haka Dole ya Nemo ruwan sanyaya zuciyar momcy shi yau .

Yamma lis FU'AD ya taho ma da momcy wata sasanyar fura da ake damata da su ayaba da su inibi da Madara ta had'u sosai momcy nason furar ga gasashiyar hanta gashin Ruwa Ruwa Mai dumi duk na toshiyar bakin momcy ne .

FU'AD da d'an k'arfin shi ya shigo gidan ya ki Hawa sama ma don yau so yake ya wanke lefin da be d'auke shi laifi ba ,Amman yasan ya zama laifi a wajen momcy don Haka maganin zaman lpy kawai y nuna Mata shifa bada niya yayi ba .

Ya mik'o ma momcy ledar yace momcy ga hantar Nan Kar ta huce nafi son kici da duminta Dan ALLAH kinji uwa ta gari ,ta k'arba babu wani walwala ,tamai godiya ta bud'e ta Fara ci ya tashi d kanshi ya d'auko Mata _glass cup_ ya zubo Mata furar ya m'ik'o Mata ta k'arba Tana cewa ALLAH yayi Albarka ,hankalin FU'AD a kwance yace "Ameen momcy in ban Miki ba wa zanyima? Dole nane na Miki momcy ...

Hankalin FU'AD kwance gani yake ya Gama cinikin momcy da hanta da furar shi Mai sanyi ,ya mik'e zai haura saman shi momcy tace "dawo ka zauna cinikin be yiwu ba ,wanan toshiyar bakin sunmin kad'an da har zasusa naki fad'ama gaskiya son.

FU'AD ya dawo ya zauna ,Yana cewa hmm momcy Babu mantuwa na sani ai Daman,azuciyar sa ,afili Kuma yace ,momcy nifa ........ta dakatar dashi da cewa.

"FU'AD meyasa ka Aikata Abin da kayi d'azu kakuma nuna Halin ko in kula Kan lamarin ,kamar amanace agareni fa ,inda yazo da k'arar kwana kasan komai zai iya faruwa?

FU'AD yace "momcy ki yadda Dani wlh banyi da manufa ba karyewa ne yazo daidai gab'a ,Amman banyi Ina sani ba ,Nima kaina naje ceto Dan kinsan bana son k'adangaren Nima momcy ,fitowa zaiyi y tab'ani na tsorata na sake Mata a Kai bawai don Ina sani ba wlh,Naga kin d'au zafi , ALLAH y huci zuciyar uwa tagari .

Momcy tace ,na yadda sbd rantsuwar d kayi ,Amman ka rage Mata tsananin Nan bana so ,kaji na Gaya maka.

FU'AD yace" za'a kiyaye insha ALLAH .

Momcy tace ,akiyaye inba hakaba zamu sa kafar wando guda da Kai wlh .

Sanan FU'AD y haura saman shi y rage kaya ,Yana mamakin yadda momcy take Mai Akan Ma'u .

Itako Ma'u duk tunanin ta bai wuce Dame zata Rama Abin d FU'AD y mata ba ,inta barshi ma tace ta hak'ura da Aiki a gidan ,shine yaci blus Kuma ita tayima kanta Dan ba momcy ce ta koreta ba ,Kuma b hafeeza ce ta dawo ta karb'i aikinta ba ,kawai ta nemar ma kanta mafita ,Amman ta Yaya hakan ze yiwu ? Zuciyar ta tace sai kin cire tsoron shi da nuna Mai kema mutum ce kamar shi,girman shi da tsoron Nan duk ki ajiye ku goga Wanda yaji tsoro ya hak'ura.

Washe gari ,shine ranar da k'anwar mamar Ma'u tazo ,Dake da wuri tazo Ma'u ko Aiki tak'i fita ,saima aikawa da tayi baba yazo su gaisa ,dake mama habee an lek'a mak'ota tsegumi ,Dan Haka ma'u ta sake da aunty tata har baba ya shigo mama habee ba'a dawo ba .

Bayan sun gaisa da huwaila da baba ,tamai gaisuwa suka dinga hirar yaushe gamo ,sun Jima suna Hira har hirar k'iyayar da mahaifiyar su takema mahaifiyar ma'un Bata canja ba har yau da ta canja d ma'un ta dinga Kai musu ziyara ta dinga Jin dad'i itama tanada Kaka a kusa d ita ,Amman Inna baza ta karb'eta a jika ba ,watakila sai zuwa gaba ...

Baba da aunty huwaila sun Jima suna tataunawa ,mama habee ta dawo ,wani ya mutsa da b'ata Rai ta dingayi Tana Harare Harare ,Haka dai Ma'u da su baban suka fita harkar ta .
Chapter 14 · 0% Book details