← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 112

Sashe 99

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A tsaye take amma kafafuwanta sukai wani irin sanyi da sanqarewan data zame ta zauna kan kujera da karfi tana dora hannunta daya akan kirjinta cikin tsananin jin wani irin radadin datasan zafi da ciwonsa a baya sbd radadi ne kadai datake kasu idan wani abin ya samu daya daga cikin jininta su abaas da nurat da zuhrah.

Ja idanuwanta ke rikidewa sunayi ta kasa bude baki tace komai ta kashe wayar kawai tana sakinta idanuwanta na neman rufewa da duhu tayi saurin jingina bayanta tana rufe ido dan numfashinta dake neman toshewa.

Maa sakinah ya kira ya sanar da ita abinda ya faru da kuma fada mata ta kula da Ammin kada ta shiga wani halin hakama duk tsanan kada Ammin taxo Anjom zaa taho da sultan din anan zai qarasa jinyarsa dan haka su jira kowane lokaci zaa iya isowa da sultan.

Tashi hankalin maa sakinah yayi ta fito a rikice jikinta na rawa ta fadawa tenya da zuhrah abinda yake faruwa sai a lokacin suka samu damar fidda tashin hankalisu da suketa dannewa dan haka suka taru suna shiga damuwar bayyane da tsoro da mamakin haile.

Ammi dai kusan kasa dauka zuciyarta tayi sbd numfashinta daya ringa sarkewa yana neman daukewa dole sukai gaggawan neman likita ya iso ya fara bata taimakon gaggawa daya kamata.

Bahar da saida jikin Ammin ya rikice tasan meyake faruwa kusan itama zubewa tayi saida Maa sakinah ta riqeta jikinta tana kallanta da kulawa tace

'Ki kula da kanki fa'

Tsoro me tsananin gaske ta shiga na kwatanta halinda LEUL ya shiga a kwanakin batareda kowa da zai kula dashi ba a kwanakin musamman daya boye musu ya shiga tashin hankali da quncinsa shi kadai
Ga kuma halinda Ammi take shiga ayanzu..

Zazzabi me karfi ma taji yana rufeta sosai dan haka kafafunta suka tsananta rawa ta kasa tsayuwa ta sake zubewa jikin maa sakinah tana jin mararta na wani irin murdawa da karfi take jini kawai ya balle mata.

Zuhrah ce ta fara lura da jinin dayake biyo kafafunta ta kalla da kyau tana bude baki cikeda sabon tashin hankali tace

'Me nake gani ni zuhrah?

Maa sakinah da tenya tare suka kalla inda take kalla take suka qarasa rikicewa da tashin hankali mai tsananin gaske sakinah na cewa

'Ciki ne fa a jikinta ita kanta batasan dashiba mun shiga uku ze fita?

Ita kanta Ammi dake kwance tana jin hakan yunqurawa tayi cikin wani irin karfin hali tana cewa ayi gaggawan kiran likitocin da aka tanadarwa masarautar suzo a taimaketa kada cikin ya zube indai shine da gaske.

Waya zuhrah ta fidda hannuwanta na rawa tenya kuwa da kanta zata bazata iya jiran kira ba sakinah kuwa riqota tayi hakama Ammin dole ta miqe cikin karfin hali suka kama Bahar din wadda jikinta ke rawa sosai tana jin wata irin azaba a mararta mara iyaka amma zuciyarta shi kadai takeson jin muryansa a lokacin.

Koda doctors biyu suka iso tafara jin jiki sosai wani zufa take fiddawa tana qanqame Ammi da azaba me tsananin gaske amma ta kasa bude baki tace komai.

Kiransa ne ya shigo wayar Ammi a lokacin wanda take itama ta kasa dagawa dan batason ya sani dan haka kasa dauka tayi suna jiran tsammanin jiran abinda likitocin keyi gurin tsaida cikin zullumi da fargaba.

A daidai wannan lokacin koina ya dauki tsit a masarautar boyem sbd lokacin fitowa da haile yayi zaa kaita bangaren azabar bayi acan zaa yanke mata hukuncinta ta hanyar rataya amma baa gaban jamaa ba sbd sirrinta yanayinta sbd yayanta wainda zuwa yanzu ma Aslam tana kwance jiri ya debeta ta sume tana bangarenta batasan inda kanta yake ba bayi biyu ne akanta.

Shiga akai fitowa da ita anan ne sultan duk da baya iya magana sosai ya bude baki ya nema mata sassauci daga NUAB wanda ya zubawa sultan din ido yana kallansa sbd yanda yake maganar cikin tausaya mata sbd yayansu da kuma zaman auren da sukai.

Dauke idanuwansa yayi daga sultan yana maidawa akan Asim wanda yake tsaya a gefensu idanuwansa jajir ya dago kansa ya sauke idanuwansa akan NUAB wanda shi yake kalla.

Shiru sukai dukkaninsu kafin Asim ya motsa ahankali ga tsananin mamakin NUAB da sultan da kadir dake tsaye takowa yayi cikin sanyi da nutsuwa ya inda NUAB yake zaune ya sai kawai yakai gwiwowinsa qasa ya zube da karfi gabaki daya yana yin qasa da kansa cikin bayyanarda mafi qasqancin yanayi a gaban dan uwansa akan mahaifiyarsa ya dago ya kalli NUAB din wanda yake kallansa da mamaki me tsanani da shock.

Sultan ma dayake kwance cikin wani irin mamakin da karfin hali ya miqawa kadir hannunsa yana son ya tadasa zaune yana son magana daqyar.

Shi kansa kadir shock din ya shiga sbd babu wani jinin boyem da duk duniya yake durqusawa wani idan ba ubangijinsa daya haliccesa ba gurin ibada.

Hannuwansa biyu yakai yana kokarin dafa kafafun NUAB zai bayyanarda tsantsan rokonsa akan sassauci wa mahaifiyarsa NUAB ya riqd hannunsa cak da karfin gaske yana kallansa shima nasa idanuwan suna ja sosai har hannuwansa suna rawa ya bude baki da yanayi me bayyanarda zafin abinda Asim din yayi yace

'Kada ka yadda ka sake durqusawa kowa duk duniya haka,
Kai namiji ne da babu abinda zaka bayyanarda rauninka irin haka harka durqusawa waninka koshi waye'

Sakinsa yayi yana cikin zafi me tsanani a bayyane yana jin baqin cikin shedar da hakan ga wanda yake kalla a matsayin wanda zai mulki boyem.

Shiru dukkaninsu sukai sultan na kallan Asim din a karo na farko da wata irin tsantsar tausayawa me karfin gaske da kauna yana jin inama zai iya sauya kaddararsa zuwa me kyau da aminci ba irin wannan da mahaifiyarsu ta saka su a ciki ba gashi zata tafi tabarsu da kuncin da zai lalata rayuwarsu shikenan ba har abada.

Kadir NUAB ya kalla yace ya karbo masa sako a hannun Aleey.

Asim kasa dagowa yayi ya kalli mahaifinsa da NUAB din sbd jikinsa dake wata irin rawa kowace daqiqa dake wucewa ayau da bushewan jinin jikinsa take tafiya,da hankali da tinani da kwakwalwansa suke tafiya duka yana jin yana rasa kansa wanda bazai taba dawowa daidaiba.....

Zaunawa NUAB yayi tareda nunawa Asim din guri ya zauna ya dago ya kalli sultan wanda shi yake kalla ya bude baki cikin nutsuwa da sanyi da bayyanarda soft yanayinsa na tsananin kaunar jininsa da bai taba bayyanarwa kowa duniya ba hatta mahaifiyarsa batasan yanada wannan bangaren na tsananin son jininsa zuciyarsa sai ayau gaban mahaifinsa da dan uwansa dake kallansa suna neman alfarma da dukkanin sassauci da rahamarsa.

'Ka tin a ranar farko daka bani kurjeranka dan nayi mulkin qasarka ka roke ni alfarma daya daya akan 'danka Asim na inganta rayuwarsa na basa girma da matsayi da mutuncin daya kamace a karkashin mulki na,
Ban baka amsaba sbd ban taba karban kujeran mulkin boyem da riqewa har abada ba,
Shine yake da buri da shauqi da nacin mulkinta tin kuruciyar,
A baya yana son mulkin ne sbd raayin mahaifiyarsa wanda matiqar yana bin kowace irin rayuwan da zata sakasa har abada bazan bari ya mulki boyem ba nima kaman yanda kaima har abada bazaka basa ba,
Ayau sabon mutum ne a gabanmu,
Ayau baya tareda kowane raayi na mahaifiyarsa saina kansa,
Ya kasance me kishi da sanin darajar kai da fatan kawo sauyin cigaba a rayuwansa wanda hakan na nufin zai kawo cigaba da sauyin da ake nema ga alumma,

Mulki da sarauta ba nawa bane,
Ba burina bane,
Yanci da walwalata nake nema bayan kawo sauyi da cigaban da masarautar ke nema kuma wanda mahaifina yake fatan a kawo boyem na kawosu na sauya su dan haka kaddarata zata tsaya ne daga nan sbd zaman boyem da mulkinta ba nawa bane.,

Dawo da idanuwansa da sukai jajir yayi akan Asim wanda yake wata jijjiga me sanyi har lokacin sbd duniyarsa kowane second collapsing takeyi da wani sauti daya ratsa kunnuwansu su duka tsigar jikinsu suka miqe ya ajiye takardun daya amsa daga hannun kadir ya ajiye gabansa yace

'Bazan iya janye hukuncin mahaifiyarka ba sbd hukunci ne daya fito daga bangaren sharia da hukunci na saka hannu ne kawai,
A yanxu babu wanda zai iya janye hukunta kaf duniya amma idan ka saka hannu anan a yanxu zaka zama sultan Asim Almazz zaka iya daga ranar hukuncin zuwa lokacinda zuciyarka zata iya dauka......

Shock ne me firgicin gaske ya shiga dukkaninsu a lokaci daya da sultan baisan lokacinda ya tashi zaune da kyau ba yana kallan NUAB din hannuwansa na rawa,

Kadir ma firgita ya shiga ya juyo gabaki daya yana kallan NUAB din,

Asim kuwa rinte idanuwansa yayi ya bude jikinsa bai dena rawa ba saima wata irin tsananta da yayi abin yana yawa kafin kowanensu yayi kowace yunkuri aka buga kofar bedroom din.

Aleey ne a tsaye idanuwansa jajir ya kalli kadir daya bude ya sanar dashi mummunan labarin daya zo dashi dan isarwa na rasuwan Haile wadda koda aka isa daukanta Allah ya mata rasuwa sanadin bugawan zuciya suke saka rai.
#MAMUH
09033181070
[15/01, 9:45 pm] Dasoo: HAYATEEM
Mamuhgee

173
Kaman saukan aradu haka kadir yaji zancen ya dakesa ya juyo da sauri ya kalli sultan wanda duka kofar suke kalla kuma sultan yaji abinda aka fada sbd hankalinsa da idanuwansa dake kofar dan haka rife idanuwansa da sukai jajir yayi a hankali yana jingina bayansa da gado hannuwansa na fara rawa kadan kadan.

Asim kadir ya juya da dukkanin idanuwansa ya kalli wanda ya zubawa takardar gabansa idanuwa yana jin babu komai na kaunar sarauta dayayi saura a zuciyarsa yanxu dan hakanne shima yake da raayin barin boyem yayi rayuwan da babu dauri a cikinta,

Takowa kadir yayi ya tsaya gaban sultan NUAB yana qasa da kansa cikin tsananin girmamawa ya bude baki da alhini yace

'Allah ya karbi rayuwar Queen haile koda akaje.......

Bai qarasa ba Asim ya dago cikin mugun slow na rashewan da duniyarsa ke yi a take ya kallesa yana miqewa da wani irin sauri ganinsa na daukewa ya juya baya ko ganin gabansa ya fice daga dakin koina nasa na jijjigar rawa me karfi.
Chapter 99 · 0% Book details