← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 112

Sashe 24

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wasu hawayen nata ne masu zafi suka gangaro a sanyaye suka sauka akan fatar hannunsa datake rufe da bakinta ya gangara da idanuwansa akan hawayen dake kan fatar tasa suna gangarawa zasu sauka kafin ya dawo da kallansa akan fuskarta da itama shi din ta dago ta sake tsayar da idanuwanta kafin wani irin kuka me tsananin tsima zuciya ya taho mata ta fasa a hankali tana rintse idanuwanta da karfi babu abinda ruhi da zuciyarta da idanuwanta da gangar jikinta suke tsananin nema da muradi a lokacin bayan bayyanar abaas a gabanta.

Qamqame hannuwanta Sultan yasar yayi yana sauraran kukanta da sautinsa suna ratsa sa idanuwansa na sauyawa kafin ya saketa a hankali tareda zaunawa a gefenta a wata irin nutsuwa ya bude hannuwansa ya zagayota a natse ya shigar da ita jikinsa ya rungume da sanyayyar nutsuwan data isa gareta ta rintse idanuwanta tana sake fasa wani kukan dayake jinsa har tsakiyar kirjinsa data toshe.

Kuka takeyi sosai wanda yake na tsantsar tsananin tsoron dayake shigarta wanda bata shirya ji ba koma menene ya kawo bahar gareta batareda abaas ba  dan haka zuciyarta ke wata irin karyewan da bazata taba gyaruwaba.

Dukkanin kukanta da radadin dayake tafe dashi ratsasa yakeyi yana karbansa hannu bibbiyu da radadin da quncin da komai duk karba yakeyi a zuciyarsa idanuwansa jajir yana sake rungumeta da karfi a jikinsa.

A haka ya qarar da kutsawa a cikin kowane quncinta daya shirya rayuwa a cikinsa har qarshensa tareda ita.
#MAMUH
09033181070
[12/01, 10:50 am] Asia ahmd: HAYATEEM
Mamuhgee

95
Acan bangaren ma SULTAN NUAB a zaunen ya kwana batareda rintsawa ko ta second dayaba idanuwansa a kafe guri daya zuciyarsa a nauyaye da abinda baisan ya shigesa ba har akai asuba tukuna ya iya miqewa dan sallah.

Kai tsaye masallacin masarautar dayake duk wani sultan acan yake sallah tareda manya ayau shima da yaransa can suka nufa dan gabatar da sallarsu acan sabanin tasu da suke hada jam'i suyi a nasu masallacin da suka tadarwa kansu a bangarensa.

Ba dukkaninsu suka tafi ba wasu anan bangaren sukai sallarsu shi kuwa da aleey da keelah tareda wasu daga securities dinsa masallacin suka nufa a karan farko sbd a yanzu shine me masarautar gabaki dayanta.

A lokaci daya ya iso masallacin tareda mahaifinsa wanda ya kallesa da idanuwansa da basu gama dawowa daidai ba shi kuwa bai dagoba sbd baya buqatan kallan kowa a yanzu bare wata hayaniyar da zata qarawa kansa nauyin dayake ji,

Ganin securities dinsa suna kokarin cike rabin masallacin yasa kusan kowa iya kansa yana bin sahun sallah a natse dan tada sallan da zaayi batareda tsayawa kallan kwaf ba zuciyarsu na shiga rudanin ganinsa a masallacin tareda tsananin tsoro da fargaba da zullumin abinda suke ganin kaman yana shirin tabbata cewan shine Sultan din boyem a a yanzu.

A guri daya ya tsaya sahu kafada da kafada da mahaifinsa wanda shima yake cikin yanayi na rashin son hayaniya,

Sallah akai aka kammala kowa yayi tsit da adduar da kowa yake sanarwa ubangiji har gari ya fara haske wanda kowa ya fara silalewa daya bayan daya suna barin masallacin dan tafiya fara shiri sbd da safiya ake nadin sarautar qasar wadda a cikin tsakiyar daren dukkanin labarin nadin sarautar goben ya fita yana isa ga duniya da duk inda ya kamata ya isa sbd akan dole manyan fada basu rintsa ba suka kwana aikin nadin mulkin sbd dolensu ne.

Koda ya koma bangarensa babu wanda ya sake zuwa fara shirye shirye kawai akeyi tako ina wanda ya saka koina ya dauki wata irin harama da hayaniya amma banda bangarensa wanda yake tsit babu kowace hayaniya duk da su aleey wani irin zazzafan shirin sukeyi tareda tsananta wani irin tsananin tsaro da securities tako ina,

A bangaren ayanah tinda sultan ya fice su tenya suka sanar da ita NUAB ne sultan na yanzu wanda zaayi nadinsa ayau.

Wani irin sabon nauyi taji ya danne kirjinta amma tin da kansa ne ya karba ba dole aka dorasa ba tasan an cika mata alkawarinta,

Tausar zuciyarta tayi daga dukkanin abinda takeji zata jira ayi nadin sarautar ayau din a gama kafin ya fuskance ta shi da Sakinah su sanar da ita menene yake faruwa wanda bata saniba dan haka ta saka dukkanin karfin hali da taurin zuciyar da batada ta danne abinda takeji dan barin Hayateem dinta ya fuskanci wannan ranar da zata zata fara gina tarihi me girma a rayuwarsa.

Manyan baqi daga qasashen kusa dana gari da duk wani jinin boyem dake duniya fara halarta sukai a qasa da masaurautar boyem wanda yake tsananta tsaron qasar ayau gabaki dayanta da masarautar sbd tsaron har yayi yawan da hankali ma bazai daukaba,

Kayan nadin sarautar da sultan ya jima da tanadar masa aka aiko daga bangarensa wanda sakon ya iso da bayi kusan sama da ashirin tareda kadir suna daukan idanuwa tamkar zinari sai asalin zoben zinarin dayake dauke da adon black diamonds a cikinsa na sarautar wanda wata narkakkiyar dukiya me tarin yawan gaske sultan ya batar gurin qerosa daga qasar Kuwait me dauke da sunan SULTAN NUAB 40 wanda kowane sultan me mulki saiya mallaki nasa.

Isowan sakon bangaren Amminsa ya saka ammin tasa bada tukuicin dukiya me tsananin gaske hakama su tenya da maa sakinah saida kowannesu ya bada tukuicin zinari me yawan gaske kafin daga baya suka dauki kayan Ayanah na gabansu suna bayanta dauke dasu da bayi sama da goma suka nufi bangarensa dan mahaifiyarsa ce zatai shirinsa a bisa al'adah.

Koda suka isa ya fito wanka yana sanye da fararen kaya tas riga body hug da farin dogon wando fuskarsa tayi wani irin haske asalin kwarjininsa yana fita a natse yana kwantar da tsigar dukkanin wani me kallansa.

Amminsa ce kadai ta iya isa palonsa na kurya sai Maa sakinah da tenya wainda suka tsaya daga nesa Ammin tasa ta tako tana isowa garesa yana tsaye ya kasa motsawa ya zuba mata idanuwansa yana kallanta dukkanin jikinsa na mutuwa da wani irin dumi da zafi.

Itama wasu hawaye ne suka cika idanuwanta tana qarasowa rungumesa tayi ahankali tareda sauke ajiyan zuciya tana bude baki tace

'Daga yau ina rokon allah ya baka dukkanin kariya har ranar da ranka zai bar jikinka,
Ina rokon ka samu dukkanin kariya da rayuwa me albarka da jin dadin da kwanciyan hankalin da baida kishiya har ranar da zaka sauka wannan mulkin lafiya.'

Hannuwansa biyu ya saka ya qanqameta jikinsa sosai yana rufe idanuwansa yana rokon allah ya karbi adduar mahaifiyarsa akansa.

Mintina suka bata a hakan kafin suka saki juna ta kama hannunsa ta zaunar dashi sai lokacin su maa suka iso suka fara bata komai na sarautar a hankali tana saka masa tana shiryasa.

Hannuwanta biyu ta saka ta dauki zoben dayake daga mahaifinsa ta saka masa kafin ta zaro nata kyautar ta chain din asalin azurfa da aka saka sunansa a jiki da manyan baqaqe da larabci wanda tin a shekaru tayi masa shi ta saka masa a hannun da agogon dubban daruruwan dollars suka siyesa ta kama hannun takai bakinta tayi kissing ahankali tareda jero masa wata irin adduar data sakasa sake rungumeta yana kissin tsakiyar kanta.

Maa sakinah ce ta dafa kansa a hankali itama ta karanto masa adduoi masu kyau da tsafta kafin maa tenya itama tayi masa a daidai lokacin komai ya kammala masarauta ta hallata ta cika maqil da wasu irin manyan mutane tako ina ga medias daban daban da bazasu taba kirguwa ba hakama mutanen NUAB din da turawan kasashe daban daban kusan duk sun bayyana wainda zasu iya zuwa a short lokacin da aka sanar.

Duk wani babban fada na yanzu dama wainda sukai retire da murabus suna bakin kofar bamgarensa a jere a tsaye tareda wasu irin securities dan jiran fitowansa dan rakiya garesa zuwa fada wanda haka tsarin yake.

Aleey ayau din tsaron daya zuba a masarautar boyem ya wuce dukkanin hankali sbd tako ina yaronsu ne a cikin shirin da basu taba zamaba na rayuwarsu,

Idanuwan aleey da duk wani ghaz member a bude suke sharp suke hatta yaransu da duka suka qasashe da sukai isowan gaggawa a shirye suke tsaf da bawa kowace daqiqa ta ranar kariya a ransu.

Karfe goma sha biyi daidai ne lokacin fitowansa dan haka dago manyan idanuwansa da ayau tsantsar mulkin dake jininsa yake bayyana yayi ya kalli agogo sha biyu da hamsin da tara,

Juyawa yayi ya kalli hanyar kofar dakin da babu wanda ya shiga har lokacin sbd har lokacin bata farka ba sbd kwanan datai da wani mummunan zazzabi me karfin daya hanata baccin lafiya sai bayan asuba.

Juyo da kansa yayi ya daga kafafunsa yana takawa a natse da kamewa tareda tsantsar ikon dayake yawo a jininsa ya nufi kofa wadda yana isowa aleey ya wangale ta take dukkanin mai rai dake gurin suka gyara tsayuwa suna sauke kansu kaf a lokaci daya cikeda wata irin girmamawa da wata qarar da aka saki data tabbatarwa duk wanda yake ciki da wajen masarautar jiran nadin SULTAN LEUL NUAB ALMAZZ ya fito.

Take masarautar ta dauki wani irin tsit duk da dubban daruruwan mutanen dake cikinta da zagayenta shiru koina yayi.

Securities kuwa take suka sake dauke wuta da qamewa cikin kowane position nasu.

Aleey dayake shine a gaban NUAB din da wasu securities da bama sa jin kowane yare bayan na harbewa without any second thoughts,

Wasu irin qananun zafafan full loaded pistols ne a jikin aleey a boye kusan guda hudu da wata wuqar da kai tsaye zata yanka ko jijiya nawa ne a inda aka sokata tayi musu yankan cin ledar bera.

Keelah ma dayake daba bayan NUAB din tareda manyan boyem da suka taho rakiyar sultan din zuwa fada a loade yake da munanan makamai a cikin jikinsa fuska babu sauki ko a kadan a wannan lokacin.

Kai tsaye fada suka isa wadda yan jarida daga nesa inda aka kebe musu suka fara hasko hasken flashers nasu tako ina kowane sahu da motsi yana daukewa saina isowan sultan me boyem da ghaz da Moscow.
Chapter 24 · 0% Book details