← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 112

Sashe 69

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babu abinda ya fara sauka a wayar tasu bayan tambayarta data saka wayoyin nasu shiru.

'NUAB meya hadaka da Bahar daka zo??

Shiru yayi na mintina maganar na amsa kuwwa mara karfi a cikin kunnuwansa ya sauke numfashi mara sauti yana bude kyawawan idanuwansa masu kwarjini ya ajiye file din dayake hannunsa yana dubawa ya bude baki da muryansa me sanyi yace

'Ammi zaki iya jin amsar tambayanki???

Kashe wayar tayi da sauri tana jifa da wayar sbd zai iya bata amsar da zata kasheta kafin safe dan haka gwara ta jira garin ya waye su isa boyem din ya fuskanci fushinta sbd ga dukkan alama yafara lalata karatun yarinyar nan san taga alama amma bata dauka aikinsa bane.
#MAMUH
09033181070
[19/01, 11:29 am] Asia ahmd: HAYATEEM
Mamuhgee

142
Dukkaninsu ba wanda yayi baccin arziki musamman da a daren ta sanar dasu tafiyan gabaki dayansu zasuyi yanzu zuwa boyem din.

Bahar sake shiga fargaba da tsoro da damuwa tayi sbd fargaban abinda zaa tafi yi,
Idan ta hadasu da NUAB ta tambayesa zai iya fada mata amsar duk abinda zata tambayesa wanda kila bazata taba iya sake kallan fuskar Ammi ba har abada dan haka taji tana fatar masa magana kafin Ammi ta hadasu guri daya ta tambayesa.

Sanyi jikinta yayi tanajin bata taba tafiyan dataji hankalinta yana tsananin tashi ba faduwan gaba na kamata ba idan ta tina irin wannan.

Kasa komai tayi dan haka maa sakinah ce ta hada mata kayanta a suitcase guda daya tinda acan tanada kaya sosai kuma sunyi waya kafin su isa su Naimah da salmah zasu fidda komai akai a wanke a sake gogewa da tirarawa na sitirarsu.

Washe gari ansiya duka tickets dinsu na tafiyar dan haka da dare jirginsu zai tashi amma kusan tinda safen suka gama shirin komai.

Breakfast ma sama sama sukai a dining din duk da Tenya da sakinah hidimar gabansu kawai sukeyi tinda dai ba yanda zasu iya yi,
Ammin ce taketa bacin rai da zafinsa sbd taji ciwo da tsananin zafin abinda NUAB din yayi matiqar gaske duk da ta kasa zaunawa ta tambaya taji cikakken bayanin komai a bakinsu sakinah sbd zuciyarta bazata iya daukan jin ba hakama shima datake son yiwa maganar dakyau sbd alkawarin da yayi mata akan zai jira har dai bahar ta gama ko nisa da kama karatun sosai tukuna zaaji raayinta akan shi da aurensa matiqar bata so sunyi alkawarin ba dole zaa sauwake auren a barta ta jira lokacinda duk ta tashi sbd tayi alkwarin bazata bari alkwarinsu itada Abaas ba ya tauye Bahar tinda ko babu komai sun cika nasu alkawarin tinda dai anyi auren.

Yanzu ta tadda wannan labarin da aka boye mata me daga hankali gashi karatun yana neman rikicewa tin baa kusa kammalawa ba,
Qarin tashin hankalinta na biyu da shikenan sedai ta tsinci ciki a jikin Bahar.
Dalilinsa na karya mata alkawarin daya daukan mata tana matsayin uwar data haifesa takeson ji dan kuwa ya saka mata radadi me zafi da hakan da yayi na watsi na alkawarin.

Bahar ma bata iya fitowa cin abinci ba seda Ammin ta saka aka kirata akan umarni ne ta bada.

A silale take tahowa jikinta a sanyaye kaman mara lafiya tana sauke kanta qasa.

Kafeta da ido Ammin tayi tana qarewa tafiyanta kallo data sauya kwata kwata ba kaman da tana budurwanta ba a baya,
Dauke idanuwanta tayi daga kallanta tana jin wani iri duk da tasan su tenya zasu gyara mata ita su bata kulawa fiyeda yanda ya kamata amma dai jin takeyi tayi babban baqin cikin da bata nan ta kula da ita da kanta sannan shi kansa yaga bacin ranta yanda ya kamata dan kuwa duk namijin dazai sauya tafiyar mace bayan maidata cikakkiyar macensa to ba qaramar karfi da wuya tasha ba a hannunsa da nacewa.

Bahar din na isowa zaunawa tayi gefen Ammin tareda bude baki a sanyaye ta gaidata kafin ta gaida maa tenya sbd maa sakinah ita tana dakinta ma tin dazu.

Ammin ce da kanta ta zuba mata abinci da wani kakkarfan hadin madara me zafi datace daga yanzu kullum shi zaa ringa bawa bahar din kullum,

Daman tenya shi take bata tinda abin ya faru tafiyar da sukai ne ta dena sha sai kuma da Ammin ta dawo shima suka dena bata sbd kada ta gani tasan Bahar ta san Namiji kenan sbd hadi ne da kadai ake bawa wadda ta zama macen cikakkiya a cikin masarautar boyem.

Madaran kadai tasha sama sama sai abinci kadan tace ta koshi zata miqe Ammi tace ta sake ci ta koshi.

Sake cin abincin tayi ta tura ta gama ta miqe saita kasa komawa daki taxo gurin Maa sakinah ta lafe gefenta sbd har lokacin ba fuska sosai a gurin Ammi gashi taqi mata fada jira takeyi su isa ta hadasu su biyun kila wanda hakan ke daga hankalin Bahar sosai taji tana shiga damuwa.

Haka suka wuni har dare sukai sallolinsu magrib da ishai suka fiddo komai aka saka a mota suka bar gidan.

Suna ficewa kai tsaye ba doguwan bata lokaci da tafiyan slow suka isa airport daga nan ma ba bata lokacin suka bar qasar zuwa qasar Boyem.

Baccin da basu samu yiba a daren kusan dukansu suka samu a jirgin dan haka hankali kwance sukai baccinsu sbd suna first class,.

Ammi ce batai wani bacci ba sbd abubuwan dake kanta kala kala dana NUAB dana sultan dana Bahar ma ga damuwan da Zuhrah take ciki itama dan haka kanta ya dan dauki zafi da damuwa.

Bayan asuba har gari ya fara wayewa suka sauka dan haka already motocin sultan yasar guda biyu data securities daya suna airport suna jiransu,

Shiga motocin sukai aka bar Airport dasu zuwa masarauta kowannensu na sauke ajiyan zuciya me sanyi da nutsuwan sauka lafiya.

Ita kanta Bahar datake cikin sanyin jiki ajiyan zuciya ta sauke a daidai lokacin da aka wangale musu makeken gate din masarautar na farko wanda yaji sauyi da wasu zafafan securities hakama babu inda bai sauyaba a masarautar tin daga gate din komai ya sauya ya zama na asalin zamani dake ihun ilimi da wayewa dan kuwa wata nutsuwa ma ba shakka ko tsoro irin na baya ba masarautar take ba a yanzu dan a baya kana shigowa zakaji kanajin tsoro da shakka sbd koina karfin ikon mulki kawai yake bayyanawa sabanin yanxu da shaawa da burgewa da wani irin ikon mulki me burgewa zakaji kana gani da ji.

Parking motocin akai suka fito bayin bangaren nasu suna jere a tsaye suna jiran isowansu dan haka cikeda girmamwa suka fara musu barka da zuwa suna karban hadbags din kowacensu kansu a qasa kafin suka tafi suka fara jan suitcases dinsu a natse zuwa ciki.

Kamar daga sama suna daga kafa ko taku hudu basuyiba wata lafiyayyan sautin qarar dawowan Uwar sultan me mulki a yanzu me boyem ta fara karade masaurautar tana ratsa koina.

Sultan NUAB dinne da kansa dayake zaune a daya daga cikin lafiyayyun sofas dake office dinsa a hawa na karshe dake building na offices nasu yaji saukar sautin yana ratsa kunnuwansa ya tabbatarda Ammin tasa ce ta iso sbd ya samu labarin barowansu daga daga drivern Bahar dan haka lumshe idanuwansa yayi ahankali yanajin wata niimar sanyi na ratsa gangar jiki da zuciyarsa sbd daga karshe dai matarsa ta iso garesa a maimakon tafiyan da zaiyi zuwa gareta a satin wanda ya shirya tsaf dan fuskantar Amminsa shima.

Sake sauke numfashi yayi me sanyi da nutsuwa yana dago kyawawan idanuwansa da harsun sauya sbd sabuwan nutsuwa da niimar data shigesu ya kalli Aleey da keelah dake gabansa sukai qasa da kai a natse sbd bazasu iya daukan idanuwansa a cikin nasu ba musamman da wani sabon yanayin yake bayyana a cikinsu.

Files din hannunsa ya ajiye a gabansu a natse yana maida bayansa ya jinginar a kujeran dayake ya bude baki yace

'Na duba duka abarsu a yanda tin farko aka tsaro,
And bazasu samu ganina ba sam a yanzu ko a kusa ba sai munga yanda business dasu din zai kasance,
Keelah kaine zaka hadu dasu a Moscow din ka gudanar da komai daidai yanda kasan muna komai na sealing deal din.'

'Yes LEUL' keelah ya fada yana daukan files din a hannunsa yana karanta wasu a ipad din hannunsa sbd daman sun saba dik businesses dinsu sune masu zuwa shi keelah ko Aleey sai manyan ne kokuma wainda suke na mahaukatan daloli yake zuwa da kansa hakama idan har tattaunawansu akan businesses nasu ne na GHAZs basa ambatarsa da sultan da LEUL kaman yanda suka saba suke kiransa wato Zaki sai idan harkar sarauta ce suke tsayawa kansu a qasa su ambacesa da Sultan LEUL boyem.

Su kansu tinda sukaji sautin isowan Uwar me boyem din suka shiga sabuwar nutsuwansu musamman aleey daya san lokacin haduwan NUAB din da sultan yasar yayi sbd Ammin dake tsakani ta iso.

Gama tattaunawa sukai kusan a office din suka kwana suna aiki sosai dan haka yanzune suke kokarin tafiya kowa ya kwanta ya huta dan yau sultan NUAB din bazai fito office ba kwata kwata sai gobe.

Fitowa sukai tareda hawa lift suka sauko securities da fadawan sultan din na masarauta suka miqe tsaye dukansu sbd suma anan suka kwana din suna gadi.

Gaba yayi a natse cikin kamewa da wata irin kwarjini da kyansa na sanyin safiyar dake hana kowa sauke idanuwansa akansa sbd tamkar wani sabon tauraro me haske haka yake haskawa yana daukan ido sbd lafiya da hasken fatarsa da kyau da jan hankali da cika ido.

Kai tsaye bangarensa su nufa sabo wanda girmansa yafi kowane bangare girma sbd girman ginin da akai da tsarinsa tareda zagayesa da qaramar katangar datai kyau da tsari ta kuma ji security.

Suna isowa aka bude masa kofa wangale duka securities na bangaren suna miqewa tsaye cikin girmamawa ya shige batareda ya bude baki ya amsa gaisuwansu ba da hannu kadai ya iya amsawa sbd yana buqatan hutawan gaske da samun nutsuwa a cikin kwakwalwansa.

Yana shigewa main kofar palonsa na farko tareda keelah da aleey iyakacinsu palon ba farko suma suka dakata tareda kai abubuwansa da suka shigo dasu a hannu inda ya kamata su ajiye suka juyo suka fice.
Chapter 69 · 0% Book details