← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 112

Sashe 105

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maa sakinah data kasa nutsuwa da rashin dawowan bahar din batai bacci ba sai dataji sun dawo ya fice tukuna ta samu nutsuwa ta kwanta tana fatar ma ayi bikin da zaayi idan su Ammi sun dawo bahar din ta tare kowama ya huta.

Washe gari bata tashi da wuri ba kaman yanda shima bai tashin da wuri ba sai guraren 10 suka hadu a gurin cin abincinsa dayaxo da kansa ya dauketa suka tafi acan sukai breakfast sbd daman maa sakinah ba kunyarta suke ji ba kuma itace bata saka musu ido ko saka musu iyaka dan haka tinda suka gaidata da safen suna bangarensa bata sake ganin kowannesu ba sai dare da bahar ta dawo ta kwanta.

Kulawa ma da komai na tattalin datake mata komawa yayi hannunsa dan haka maa ta kama kanta ko doguwan fitowa batayi dan kadama tsautsayi ya sakata ganinsu tinda so daya idanuwanta suka ganar ma da dawowa da bahar dinma a hannuwansa yake daukota yakaita har dakinta ya gama shiriricewa acan kafin yafita ya fice.

Bayin masarautar kaf gabaki daya tinda yazo suka dena fitowa koina idan ba aiki zasuyiba suna gamawa suke bacewa bame sake fitowa sai an nemesu wani aiki dan haka masarautar tayi tsit iya su kadaine ke shaaninsu a bangarensa cikin wata fitinanniyar soyayyar dake neman kashesu amma har lokacin ya kasa saduwa da ita sbd bayason abinda zai taba lafiyar cikinsa ko daya duk da kusan likitocin duniya sunfi goma daya tintiba sun tabbatar masa da babu komai dazai faru insha Allah.

Wata fitinanniyar soyayya suke zubawa ako yaushe bangarensa cikin zafafan yanayi da shauqi su wuni suna abubuwansu kafin dare yayi ta koma.

A wannan yanayin da suke ciki ya share kusan sati daya harda qarin kwana dan haka gabaki daya hakurinsa da juriyarsa neman qarewa takeyi gashi bayason mata komai sai angama bikin da akace zaayi an basa ita zai tafi da ita Moscow inda yakeda likitocinsa a villa dinsa ta yanda kome zai biyo baya zasu duba masa ita batareda sanin kowaba dam bayason duniya tasan da 'dansa sai haihuwansa saiya gama tabbatarda tsayuwan cikin nasa ko bayan yana nunawa mamansa soyayyarsa tukuna zai koma da ita.

Ita kanta zuwa lokacin yafara bata tausayi sbd ba qaramin hali yake shiga ba amma ya hana kasa kasancewa da ita dan haka ya fara shirin komawa dan shi su Ammi suke jiran komawansa su taho gabaki dayansu da sultan kansa.

Tinda ya fara maganar komawa ita kuma taji kaman zata kwanta ciwo sbd mutuwan da jikinta da fara kewansa tin bai tafi ba.

Shi kansa yanajin yanayin nata amma dole daman zai koma yana tabbatar mata tareda mata alkwarin daga ranar da aka daura auren Maa sakinah a ranar zai dauketa su tafi dan fara nasu zaman auren na har abada.

Rungumeta yayi a jikinsa yana kissing tsakiyar kanta da babu komai kamshin cikin gashinta na bugo masa ya lumshe ido tareda kama fuskanta ya dago ya kalla kafin yakai bakinsa akan nata ya tsotsa tukuna ya sake rungumeta yana cewa

'I love you Ayanah Bahar Ghaz'

Tashi tsigar jikinta sukai gabaki daya suna miqewa sbd yanda ya fada kalman da wani sauti mara hayaniya da zallan taushi da ratsawa tareda qarashi yana dora bakinsa akan fatar kunnenta kalmomin na shiga kunnenta direct.

Dagowa tayi cikin slow ta kalli fuskansa ya lumshe mata kyawawan idanuwansa masu haske da zafin kwarjini yana sake rungumeta itama ta rungumesa tana lafewa sosai a jikinsa.

A gurinsa ta kwana a ranar kuma maa batama bi ta kansu ba bare ta gane hakan hakan.

Da safe bayan sun gama komai sun fito hannunta yana cikin nasa suka fito fuskansa sanye da wani tsadadden black versace shades fuskansa a kame da wani irin zallan iko da isa da mulki.

Har palo suka isa gurin maa sakinah tayi saurin dan zare hannunta tana tahowa gurin maa din ta zauna gefenta duk jikinta a sanyaye kaman ma zatai zazzabi.

Gaidata yayi sukai magana sosai kafin yayi mata sallama ya miqe ya fice.

Bata iya rakasa ba shima cewa yayi kada ta fito suka wuce tareda securities dinsa suka bar anjom.

Maa sakinah dataga tayi wani sanyi bata ce mata komaiba saima gyaran da tenya ta bari data fara yi mata dan kuwa alamu sun sake tabbatarda ana gama bikin tarewa zatai shikenan.

******Su Ammi ma dik wani shirin tafiya sun kammala dan haka shi din kadai suk jira gashi sultan yana samun sauki sosai ga kulawan dayake samu daga matarsa ta musamman,

Ba shi kadai ba hatta Asim sun tsayu akansa da nuna kulawa me yawa da kauna sun saka ya sake sosai ba laifi musamman da Ammin ta tsaya a tsakiya ta sake shigar da kauna da shakuwa sosai harma da tausayi a tsakaninsa da sultan.

Sosai yake samun nutsuwa da kwanciyan hankali tareda rayuwan dabai taba samu a baya ba duk da ciwon rashin mahaifiyarsa daban yake har abada bazai goge ba amma ya samu nutsuwa sosai fiyeda yanda bai tsammanata ba daga mutanen dabaiyi tsammani ba.

A cikin qanqanin lokacin har yan uwansa yayi kokarin jansu a jiki yana shigowa mutane dasu da sake bude rayuwansu da idanuwansu ga rayuwa da mutane da zuciya daya ba kaman baya ba da sukaita fama da lalurar wahala.

Maraki ko sultan bata iya kira tai masa gaisuwaba bare jajanta masa da jin lafiyarsa sbd sanin yanzu ayanah ghaz ce dashi tako ina dan haka ya sake ficewa daga ranta tanajin ta sake tsanar jin ko sunansa bare sake rayuwar aure dashi ta hakura kwata kwata bazata yadda ta qare irin yanda haile ta qareba.

Mai girma yunar shima ya iso da nasa iyalan duka tsaf dama wasu manyan jinin boyem haka suka ringa isowa daya bayan daya dan abubuwa da yawa,dagaisuwa da dubiya da kuma daurin auren da akaiwa manyan gayyata zuwa anjom ghaz.

Manyan boyem ne suketa dira suna sake saka qasar daukan manyan qasa da tsaro sbd hidimar bikin kusan tanata matsowa.

Tenya ce da zuhrah suka fara wucewa da zuriar Tenya da suma suna nan sun iso suka fara isa dan fara shirin daya dakata sbd rasuwan.

Cikin saa tafiyar su Aslam suma ta kammalu zuwa umrah dan haka cikin kwanciyan hankali suka shirya mahaifinsu ya basu kudi masu yawa duk da dukkaninsu sunada dukiyar,
Asim ma kudi ya basu masu yawa hakama Ammi da kanta ma sai data basu tana musu fatar dawowa lafiya sbd kusan saaninta ba wani girmansu tayi ba sosai.

NUAB dukkanin wannan hidimar da akeyi nasu ayyukan sarauta sunyi masa yawan dayake son clearing nasu kafin lokacin daurin auren sbd daga can tafi zaiyi zai kuma kwana biyu baya nan.

Asim zai barwa ayyukan daya gama yadda dashi akansu sbd yana son fara cire masa kowane rauni da saka masa karfin hali tsayayyar zuciyar da babu rauni ko girgiza ko daya a cikinta hakama shine wanda zai bawa mataimakinsa da har lokacin baa nada ba na baya ne tin lokacin sultan akai har yanzu bai fidda takardar hakan ba sai bayan dasu Sultan suka tattara suka wuce Anjom tukuna.

Hakan ya saka duniya ta sheda baa bawa Asim din matsayinba sbd mahaifinsa dan uwansa yaga cancantarsa ya basa dan haka take aka fidda labarai da jaridu ana yadawa cikeda mamaki da farin ciki harma da fara manta abinda ake neman riqewa akansu sbd mahaifiyarsu.

Asim ba qaramin mamaki da shock ya shigaba daya samu takardar daga sultan LEUL NUAB dan abune da bai taba tsammani ba a daidai lokacinda yake kokarin barin qasar gabaki daya musamman da ayanzu baida mahaifiya.

Leylah kanta zubewa qasa tayi tana yiwa Allah sujjada sbd farin cikin ganin wannan ranar dan kuwa a matsayin da Sultan LEUL ya basa kusan cika masa burinsa akai na zama me mulkan boyem dan kuwa a duk lokacinda NUAB baya nan shine me ikon da mulkin boyem dan haka kasa riqe farin cikinta tayi ta rungumesa tana fidda hawayen farin ciki.

Mai girma yunar ma yayi farin wanan lamarin sosai take ya fara shirin qaddamar da taron nadin Asim din da zaayi kafin ranar Bikin Sultan LEUL NUAB din da matarsa da zaayi acan anjom dan kusan shine yafi yada duniya ba asalin auren da zaa daura ba na kadir.

Bayan isarsu sultan anjom lafiya labarin ya samesa shine da kansa ya kira NUAB ya miqa masa dukkanin godiyansa ga abinda yayiwa Asim din kafin Asim din shima yaje da kansa yasaka hannun karban matsayin wanda akai agaban dukkanin manyan fadar masarautar boyem ana farin ciki da tayasa murna.

Dole leylah ta jira daga tafiyanta anjom sai idan ya tashi su tafi tare sbd hidimar bikin da zaayi na nadin.

Su aslam suna can suka ji dan haka suka shiga farin ciki da murna amma basa nan dole nysah ne ta tattaro ta dawo da yayanta duka sbd hidimar.
#MAMUH
09033181070
[19/01, 11:47 am] Dasoo: HAYATEEM
Mamuhgee

179
Securities masu zaman kansa aka ware masa na masarauta sbd sabon matsayinsa da kuma ba musamman da NUAB ya basa a matsayin kyautar sabon matsayinsa dan haka take rayuwar ta sauya masa dan kuwa babban bangarensa da bayi ne suke gadinsa take ya samu sauyi securities masu karfi suka maye gurbin bayin.

Ita kanta leylah take tafara jin kanta da matsayinta ya sauya dan kuwa hadda securities mata itama guda biyu aka ware baya dan haka hidima sukeyi sosai itada nysah da sauran zuriar haile da suka taho.

A ranar da akai nadin sarautar a ranar duniya ta sake tabbatarda karfin da LEUL NUAB yake dashi dan kuwa fitowansa da tsakanin tsaronsa daban yake hakama aura dinsa daban take ko acikin dubbannin mutane sbd kwarjinsa kadai sai daya saka gurin da duniyar cikin boyem din daukan tsit daya bayyana.

****Anyi hidimar bikin nadin matsayin Li'uli Asim Almazz cikin farin ciki da babban taro da miliyoyan jamaa da zubar da dukiya kaman baa san zafinta angama lafiya kalau masu tafiya sun tafi masu shirin tafiya ma sunata yi kafin kuma a sake tafiya bikin Sultan me boyem da kansa.

Tinda aka gama hidimar bikin Asim din babu wanda ya sake ganin Sultan LEUL saida aka kwana biyu yana hutawa sbd yana buqatan cikakkiyar nutsuwa da hutunsa ya dawo daidai kafin tafiya haduwansa da Sultanah dinsa.
Chapter 105 · 0% Book details