← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 112

Sashe 57

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'Taji sauki tana bacci ko da zata tashi insha Allah zata warware'

Tayi masa hakan ne sbd ba qaramar kunya zataji ba idan ya tambayeta Bahar koma wani abin daga cikin abinda ya faru dasu din dan tasan zai iya tambayar kai tsaye batareda yaji komaiba ita kuma cutatuwa zatai da kunya dan haka ta taqaitawa kanta da fada masa hakan.

Shi kansa daman abinda zai tambaya kenan sbd a zuciyarsa ya kasa samun nutsuwa da ganin kaman duka ma harsu maa din bazasu iya kulawa da itaba akan abinda ya sameta din amma ganin yanda Maa tenya tayi maganar da nutsuwan dake tattare da ita ya saka ya samu yadda da nutsuwa dan haka kai tsaye ya wuce bedroom dinsa sbd raba jikinsa da kayan jikinsa.

Anan ya bar Aleey tareda maa tenya tana masa fadan data kasa yiwa NUAB akan abinda yayi din duk da bata fito ta fadawa aleey komaiba amma hakanan ta fake da fadan sun wuni baa gida ba.

Mamaki kama aleey yayi sbd kaman lamarin ba daidai ba tinda take fadan dadewansu ba gida ba amma bai damu da fadan ba murmushi kawai yake mata na karfin hali sbd ya fahimci fushinta da bacin ranta tinda shima acan a gabansa likita yayi bayanin abinda ya samu NUAB din amma bai iya cewa komaiba ko nuna reaction sema yanzu da maa ke fadan yaketa murmshinsa.

Harta gama baice komaiba ya miqe yana barin palon ya nufi nasa dakin.
Itama yana ficewa miqewa tayi hakanan da fushin taje kitchen dan sake hada masa abinda zaici ko sha.
#MAMUH
09033181070
[13/01, 1:41 pm] Asia ahmd: HAYATEEM
Mamuhgee

130
Wanka yayi a natse batareda cikakken asalin karfinsa ya dawo duka ba dan haka nutsuwansa a komai ya qaru,

Yana fitowa a natsen yayi shiri a kaya narasa nauyi na gucci short yayi sallar laasar kafin ya fito a natse yana fidda wani hasken kwarjini da fresh kaman ba wanda baida lafiya ba.

Ko wayarsa har lokacin bai kunna ba yama barta a daki baida time tana tukuna,

Kai tsaye yana fitowa palonsa ya tadda Maa tana jere masa tea me zafi da snacks da akai masa da yamman sabbi na cake da banana bread sai indian samosas masu dan girma.

Qarasowa yayi ya zauna yana mata sannu tareda fasa fita dole.

A nate yasha tea din wanda ya ringa warware masa karfin jikinsa ahankali yana jin yana dawowa daidai sbd yanda yake zafinsa yake ratsa cikinsa da taste din bakinsa yana fara aiki a jikinsa dan hatta qamshinsa yana shiga hancinka ka shaqesa sai kaji ya shiga kanka wani iri.

Tea din kawai ya iya sosai sai cup cake 'daya daya dauka shima baici ba kadan yaci a bakinsa ya ajiye yana miqewa ya koma dakinsa yayi sallan magrib da time nata yayi.

Sanin ya dawo yana gidan ya saka daga maa tenya har maa sakinah basu sake fitowa daki ba bare yan aiki da tini sukaita kansu gidan yayi tsit.

Fitowa yayi qamshinsa na tashi yana ratsa gurare da dama a cikin palon ya nufi hanyar bedroom dinta kai tsaye.

Baiyi knocking ba budewa yayi kai tsaye yana saukan da idanuwansa a ciki kuma a daidai lokacin wani qamshin daya kama dakin na wuni guda da akai ana mata kusan abu daya ya sauka a hancinsa saida kansa ya sara a cikin wani yanayi sbd qamshine da ko a daren jiya ya tabbatarda shine ya qarasa rikitar da lissafinsa sbd shine yake fitowa ta karkashinta yana shiga hancinsa daga lokacinda ya rabata da doguwan wandon kayan baccin jikinta.

An rage hasken dakin daidai misali dan haka a kame da ya daga kafafunsa cikin ikon daya gama ratsashi ya zama jikinsa ya tako cikin dakin wanda tsigar jikinsa ta wuyansa suka miqe gabaki daya sbd dumin da dakin ya dauka tareda qamshin wanda yakejin bazai iya dadewa a cikinsa ba sbd kansa baya iya dauka dawo masa da asalin farkon jinsa a jikinta yakeyi.

Bata dakin ba kowa a dakin amma jin alaman tana toilet ya sanyasa qarasowa ya zauna a sofa nasa qamshin shima yana ratsa dakin yana hadewa da wanda yake ciki,

Lafiyayyan qaramar hotonta datake tareda Ammi dayake gefen gadonta ya zubawa idanuwansa yana kasa daukewa,

Amminsa da bata tareda shi ta zabi wanda take ganin shine daidai a rayuwarta bayan irin rayuwar datai a hannunsa ya zubawa idanuwansa yana jin zafi da damuwa me zafi duk da babu zazzafar kaunarta ko daya data fita a zuciyarsa kafin ya dauke idanuwansa daga kan tata fuskar ya sauke akan fuskan Bahar data saka zuciyarsa tsayawa cak daga bugawa kuma daidai lokacin ta bude bathroom din ta fito sanye da rigar bacci mara tsayi qarama amma me kauri da socks me kauri a kafafunta blac data rufe tafin kafafun kafafunta da ita wani sirrin qamshi na fita daga jikinta hakama shi kansa bathroom din data fito qamshin ne a cikinsa daya bugo masa ya sakasa dauke idanuwansa ahankali daga kan hotonta yana dan rufe ido kafin ya budesu akanta daidai lokacinda take takowa ahankali batareda ta ankare dashiba duk da qamshinsa ya shiga hancinta amma bata taba tsammanin shi yana gurin ba sbd tinda ta dawo hankalinta kowane irin motsi tayi kamshinsa ne take ji a jiki da kwakwalwanta duk da kuwa tayi wanka nawa amma hakanan sai tanajin kaman har lokacin qamshin na nan wanda a cikin kwakwanta tinanin hakan yake shiyasa take ji kaman har a hancinta tana jinsa.

Harta kwanta ta tina batai alwalan data saba yiba duk dare kafin tai bacci ba dan hakane ta tashi taje tayo alwalan da ruwan zafi sosai ta sako socks ta dauko qaramin towel a hannunta da zata goge fuskarta ta fito.

A hankali take takawa bata jin daidai a cikin jikinta sam duk da abubuwan da ake mata na al'ada da suka sakata jin kafafunta da jikinta duk sun qarasa mutuwa bama wai karfi ba,

Haryanzu dumin da aka ringa gasata dashi ne a wunin take jin na ratsa jikinta koina ya saka har lokacin yanayin jikinta yaqi sanyi sai dume yakeyi kaman yanda akeson jikin kowace mace ya kasance da sanyayyan dumi musamman duk lokacinda mijinta zai taba ta yaji dumi a jikinta.

Kasa hade kafafunta sosai tayi kaman yanda su Maa ke mata fadan tayi tin safe taci gaba da takawa kafafun a dan bude,

Fuskarta da har lokacin take a kumbure ya fara saukewa idanuwansa yana mata kallan tsaftar da bai taba yi mata ba batareda ya motsa ba data zaman da yayi,

Yanayin yanda take daga kafa a hankali ya sakasa saukar da idanuwansa zuwa tafiyarta wadda ta saka wannan karan tsigar hannuwansa tashi ya kafeta da ido yana kallan yanda fararen cinyoyinta masu daukan ido ke tafiya a buden,

A daidai lokacin ta isa gap dashi sai lokacin ta lura dashi ta tsaya cak cikin wata irin shock da firgicin da bata tsammata ma ba,

Baya tayi kokarin ja tana dauke idonta akansa wainda take suka sauya suna,

Hannunta daya ya kama batareda ya motsa ba kuma batareda ya dauke idanuwansa daga tafiyarta ba wanda ke tabbatarwa da bayyanar masa da abinda yayi,

Batada kuzari sosai dan haka hannunta ta zare tana sake dan ja da baya da karfi wanda ya saka wata radadi ratsata tayi saurin dauke numfashi tana rintse ido da karfi,

Hannuwansa biyu ya saka a qugunta ba tsammani ya dagota cak ya dorata a kafafunsa batareda ya tashi ba sbd kadama ta taka ta sake jin abinda taji wanda yaji yana ratsa har tsakiyar kansa dan shima saida ya dan rufe idanuwan dan kuwa a jikinsa yaji abinda taji,

Jinta akan kafafunsa ta bude ido tana qin kallansa ta kalli hannuwansa biyu da suka zagaye qugunta akan kafafun nasa ya zuba mata ido shikuma yana kallan fuskarta tareda bin ruwan dayake kan fuskarta da kallo yana jin dumin fatarta tana shigarsa,

Gangarowa ruwan yayi a wata slow zai diga akan cinyarta dake bayyane gabaki daya sbd kusan rigarta da batada tsayi ta dan sake daukewa ya saka hannunsa akan cinyar tata yana bude tafin hannunsa ruwan suka diga akai ya kallesu kafin ya dawo da kallansa kan fuskarta da itama sai a lokacin ta dago ta kallesa idanuwanta na cikowa da hawayen laifin abinda yayi mata.

Bude baki yayi muryansa me sanyi da kauri ta ratsa kunnuwanta da suke kusa da bakinsa yace

'Yaya?yaya jikinki?you feeling better right??

Janye fuskarta zatai ahankali ya riqeta da hannunsa yana hade fuskarsu da kyau zafin numfashinsa na daukar mata direct a fuska ta sake rufe ido tana jin komai na dawo mata cikin kwakwalwan dan haka zuciyarta ta fara bugawan dayake jin kirjinta yana sama yana gogarsa yana komawa.

Rufe ido yayi ya budesu da wata slow a fuskarta kafin ya saka hannunsa daya ya zare towel qarama dake hannunta ya dagosa yafara goge mata sanyin ruwan dake fuskarta wanda hakan ya saka jikinta dan fara rawa sbd yanda yake bin fatar fuskar tata da slow yana bata waiwayi.

Jin yanayin yayi mata yawa ya sakata dora hannunta ta riqe nasa cak ta tsayar dashi tareda bude idanuwanta a kansa wanda daman hakan yake jira ya kalli cikin idanuwanta da take suka bugar dashi ya sake feso mata numfashinsa me zafin daya sakata jan numfashi mara sauti da karfi kafin ta fitar ya mannata da jikinsa ya bude baki ya sake tambayarta lafiyanta sbd yaji idan saiya nema manyan likitoci mata.

Rufe idonta tayi tana girgiza masa kai alaman ya zaketa tukuna amma baima fahimci hakan ba dan haka ya sake maimaita tambayarsa sbd tafiyarta ta saka shakka da wani irin yanayin me karfi a cikin kansa zai kaita kowace qasar dake duniyar dan tabbatarda dawowan tafiyanta daidai indai su maa sun kasa.

Ganin ya kasa sakinta ya sakata bude baki ta tattaro kalmar da gabaki daya yinin yau su maa batai musu magana ba can qasa tace

'Naji sauki'

Shigar kalmanta kunnuwansa ya sakasa dan dagota kadan yana kallanta yace

'Then meyasa kike tafiya ba daidai ba'

Wani iri taji ta rasa amsar basa kawai ta dago ta kallesa tana tsiyayo masa hawaye daya kalla dakyau yana basu matsayin bata warke ba kenan.
Chapter 57 · 0% Book details