← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 112

Sashe 101

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai datai shiru batareda kowannensu yace komaiba kafin ta bude baki da muryanta data sake tsimar da gangar jiki da zuciyarsa tace

'Yaya jikin Sultan??
Yaji sauki sosai yanzu?
Kana lafiya?

Jinginar da bayansa yayi gabaki daya jikin gadon dayake kai yaji inama baiji muryanta a daidai wannan lokacinba da bazai iya tsallake komaiba ya tafi gareta dan zuciyarsa kawai ta rasa duk wata nutsuwanta yanxu babu wanda zai iya gane kansa matiqar ba saka Sultana dinsa yayi a idanuwansa ba.

Bude baki yayi ya amsa bata da cewa

'Sultan Alhmdlh yana samun sauki'

'And you?? Tafada tana daukan wayar a hannunta tana riqewa da tafin hannuwanta duka biyun cikeda sanyi.

'Ni bana tareda nutsuwa da kwanciyan hankalina,ina tsaye ne kawai but I'm not myself,i miss you to the core My queen and I'm still missing you Ayanah Bahar ghaz'

Wasu hawayen ne suka gangaro mata masu sanyi da tsantsar kaunarsa da soyayyarsa dake cinta itama ta bude baki tace

'Naso biyo Ammi dubiyan amma bazaa barniba saina sake samun sauki inji Ammi'

'Bakida lafiya?
Meya sameki?
Menene yake damunki?
Meyasa bansaniba?
Meyasa ba wanda ya fadamun?
Meyasa aka boyemun?sosai ne?

Girgiza masa kai tayi kaman yana ganinta sbd batasan wace tambayan zata amsaba tace

'Naji sauki ba wani ciwo bane kawai yanayi ne'

Shiru yayi baice komaiba yace mata ta koma ta kwanta ta huta anjima zai sake kiranta.

Gyada kai tayi cikin sanyi tana cewa

'Allah ya qarowa sultan lafiya'

'Amin' yace yana kashe wayar.

Itama ajiyewa tayi gefenta tana sake kwantawa daidai tareda rufe idanuwanta tana samun kwanciyan hankali da nutsuwa.

**NUAB kuwa yana gama wayar ajiyewa yayi ya ziro kafafunsa qasa yana saukowa gadonsa ya nufi bathroom kai tsaye ya shige.

Dukkanin abubuwan daya saba yi yayi yai wanka ya fito daure da towel gashinsa na tsiyayar ruwa ya zari towel qarami yafara gogewa yana nufar gaban dresser.

Shirin kusan mintina talatin yayi harma da qari kafin ya fito cikin wasu Navy blue native kaya da hularsu da suka nutsu iya nutsuwa a jikinsa.

Aleey yana palon farko inda dining room yake yana jiransa table a cike da breakfast da aka jere a natse.

Kallo daya aleey yayi masa ya sauke ajiyan zuciya sbd nutsuwan ubangidan nasa data fara dawowa,

Gaidasa yayi a lokacinda ya iso gurin
Amsawa yayi yana zaunawa kafin masu serving abincin suka shigo a jere suka fara zuba komai a tsare a natse kansu a qasa dan basuda iko ko daman dagowa daga abinda suke sbd baa buqatan kuskure ko daya a gaban sultan me boyem.

Suna gamawa suka fice a natse sukabar gurin sai angama su sake shigowa gyara gurin,

Suna ficewa Aleey ya dauki ruwa ya bude ya zuba a glass cup dake gurin ya ajiye a gaban NUAB sbd babu me taba cup din dayake kaiwa a bakinsa matiqar yana zaune idan ba Aleey ko keelah ba sai kuma iyayensa uku dinnan mata sai kuma matarsa da zata karbi ragamar hakan a gaba.

Fara breakfast din sukai a tare cikin nutsuwa,

Bai wani ci sosai ba sbd har yanxu cikinsa bai gama dawowa nasa ba dan haka tea yasha sosai kafin ya dauki tissue yana goge bakinsa ya dago kyawawan idanuwansa masu haske ya kalli Aleey yace

'Ka bincika su waye likitocin da Sultan ya mayar doctors na ghaz kwata kwata,
Iya na cikin masarautar ghaz din nake nufi bana asibitin da aka gina a garinba,
Idan ka ganeso ka nema contact nasu kayi magana dasu inason sanin meya samu ghaz princess'

Dagowa aleey yayi yana tabbatarda angama.

Fitowa Yayi dukkanin tsaro da fadawansa suna bayansa ya nufi bangaren sultan ya dubasa cikin kauna da kulawa.

Sultan din yana zaune akan wheelchair cikin dan shirin da Kadir yayi masa.

NUAB da kansa ya basa magani bayan yasha tea kadan.

Basu guri kadir yayi sukai magana wadda akan bayar da mulkin da NUAB yaso yi ne ga Asim Sultan ya yanke maganar kwata kwata tareda bayyanarda qin amincewansa a bisa hujja me karfin cewan Asim bazai iyaba yanada rauni ke yawa musamman yanxu daya rasa mahaifiyarsa bazai taba zama mai zarrar da zai iya mulkan karagar mulkin boyem datake da karfin gaske a duniya.

NUAB a rayuwansa baida raayin dawwama a cikin mulkin amma idan har iyayensa zasu zauna dashi a boyem suyi rayuwa zai rungumi kaddarar da Allah ya haifosa a cikinta a karo na biyu,
Zai rungumi kaddarar data saka Allah ya tarwatsa zuriar mahaifiyarsa da jarabawa me karfin data kawo ta boyem ta haifesa sbd kawai Allah yayi zai zamo a cikin tarin jerin sunayen da suka mulki boyem a tarihin duniya.

Numfashi ya sauke tareda kallan mahaifinsa yana gyada masa kai cikeda kauna da kulawa.

Shima sultan din wani farin ciki da nutsuwa yaji ta shigesa a wannan karan 'dansa LEUL NUAB ALMAZZ BOYEM ya yadda da mulkar boyem akan raayinsa ba akan kowane irin sharadi ko tirsasawaba.

Fitowa sukai NUAB din ke tura kujeran Sultan din da tarin securities masu yawa da fadawa masu yawa dake biye dasu zuwa bangaren Asim a karo na farko da dukansu suka taba zuwa.

Ko da suka isa an riga an iso an sanar dashi zuwan mahaifinsa da dan uwansa Sultan me boyem dan haka yana xaune babban palonsa na farko shikadai sai matarsa dake tsaye akansa tin jiyan tana hana zuciyarsa shiga mummunan duhu.

Gabaki daya tsaron dake biye dasu a wajen bangaren suka tsaya daga NUAB sai sultan da kadir da aleey da keelah ne suka shiga ciki.

A palon suka zauna cikin nutsuwa mulki da izza na dukan juna da zallan nutsuwa da kamewa tareda bayyananniya kulawa da bayyanarda alhini.

Kallansa sukai a lokaci daya kaman yanda ya dago cikin nutsuwa da kamewa shima ya kallesu sbd tin jiyan Allah ya taimakesa yau ya tashi da karfin zuciya da tawakkali da nutsuwa tareda barwa Allah yana mata fatan saduwa da rahamar ubangiji.

Cikin kulawa sukai masa gaisuwan rasuwan gabaki dayansu hadda su aleey cikin girmamawa da mata fatan saduwa da rahamar Allah ya kuma yafe kurakurenta.

Amsawa yayi a natse yana miqa godiyansa ga Sultan NUAB da mahaifin nasu bayan shima yai masa gaisuwanta sbd shima matarsa ce ai.

Suna gama gaisuwan suka bar bangaren suka isa babban fadar masarautar da tarin dubban jamaa ke cike suna jiran fitowan Sultan NUAB ayi masa gaisuwan rasuwa sbd baa dauka sultan yasar zai iya fitowaba.

Tareda Asim suke wanda NUAB ya fara bayyanarda gaisuwansa garesa cikin girmamawa da mutuntawa tareda tausawa dan nunawa duniya matsayinsa da girmansa da dole a basa,

Hakan kuwa ya saka aka bayyanarda girmamawa da mutuntawa aka ringa masa gaisuwan mahaifiyarsa tareda adduoi masu kyau.

Anan zuka wuni ana gaisuwan ga sultan yasar da Asim harma da NUAB.

Sai yamma lis gap da magrib aka watse aka maida sultan bangarensa shima NUAB bangarensa ya nufa.

Ana magrib motocin da suka dauko su Ammi daga Airport suka iso masarautar suka fito batareda NUAB ma yasan da isowansuba sbd yana masallaci tareda mutane.

Bangarensu suka nufa wanda tin kafin su iso bayi sun isa sun gyarasa tsaf leylah ta sakasu.

Zuhrah ma anan bangaren tayi xamanta dan haka kowannesu daki ya shige

Wanka da alwala sukai suka fito sukai salloli suna idarwa tini aka cike dining da abinci masu lafiya da yawa.

Tenya ce ta sakasu cin abincin dole cikin nutsuwa kafin suna gamawa anyi sallar ishai sukai sallah.

Sai a lokacin ne NUAB yasan da isowansu a wayar Ammin data kirasa dan haka ya kira kadir ya sanar dashi isowan Ammin.

Kadir take ya saka akaiwa bangaren sultan sabon gyaran da duk yake buqata koina ya dauki tsit kowa yabar bangaren fadawan dake tsaron kofar gurin kadai aka bari shima ficewa yayi daga bangaren ya tafiyarsa dan bawa Ayanaah ghaz daman zuwa duba maigidanta wanda daga shi har itan a cikin tsantsan matsuwa da ganin junansu suke sbd zuciyarta kaman zata dena bugawa haka takejinta shikuma ganinta kadai ne abinda yake ganin yana buqata a yanxu sbd zuciyarsa ta samu karfin halin data rasa.

Bangaren Haile dukkaninsu suka dunguma suka tafi dan miqa gaisuwansu akan rasuwanta da babu wanda bata girgiza ba a tsakaninsu.

Cikin tausayawa da nuna kulawa sukai gaisuwa a gaban mahaifiyarta dake zaune ta tsufa sosai Su Aslam dukansu suna zaune tareda ita.

Dukkaninsu zubawa Ayanah ghaz idanuwansu sukai suna kalla cikeda sanyin jiki sbd daga karshe ubangiji ya nuna musu bazasu iya cutatar da wanda shine da kansa yake bata kariya ba sbd batada haqqin kowannensu kaman yanda kakarsu ta fada musu.

Amsawa gaisuwan sukai babu wanda jikinsa baa mace ba dan haka sukai shiru dukkaninsu.

A lokacin ne Asim ya shigo tareda leylah sbd kiransu da akai akan ayanah zasu musu gaisuwan.

Zaunawa yayi a natse yana dan sauke kansa agaban sirikan nasa duk da iyaye suke a gurinsa tinda basu fara da yar jin nauyiba akwai sakewa a tsakani.

Gaisuwa cikin tsananin kulawa su Ammin sikai masa dukansu ya amsa yana miqa godia.

Sun dauki lokaci a bangaren dan nuna kulawansu kafin suka fito.
#MAMUH
09033181070
[16/01, 3:55 pm] Dasoo: HAYATEEM
Mamuhgee

175
Karfe goma da mintina kadan Ammin ta isa bangaren sultan cikin nutsuwa da sanyin jiki,

A lokacin data shiga koina tsit ba haske sanyin ac da qamshin NUAB ne daya dan kama bangaren sbd yanda yake wuni da zama acikinsa na kwanakin ke tashi.

Kai tsaye kofar bedroom dinsa ta nufa kowane takunta bugun zuciyarta qaruwa yakeyi yana saka mata tinani kala kala da halinda zata gansa.

Hannu ta saka ta kama handle din kofar dakin ta bude tareda saka kafarta ta dama tana takawa sautin sarkan kafarta da bata taba cirewa ba yana bada sautin daya sakasa dagowa ya sauke mata idanuwansa yana zubawa takunta su kowane taku na dawo masa da ranar farko data fara sako kafarta a cikin wannan dakin nasa tirakarsa dan zamowa cikakkiyar mallakinsa wanda sautin sarqar kafarta ne ya fara sakasa dagowa ya kalleta ko a ranar farkon.

Ita kanta kallan dayake mata ne ya sakata dakatawa kadan tana tsayuwa a inda take tsayen kaman yanda ranar farkon hakan ta faru bama tareda tasan tayi hakan ba.
Chapter 101 · 0% Book details