← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 112

Sashe 37

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aleey ne ya iya dagowa kadai ya kalli fuskar LEUL din nasa yaga alaman zuciyar da fushin a sama suke kuma da alama ghaz princess ce ta kunnosa dan haka ya dan maida kallansa akan bahar itama yaga fuskarta a hade take sosai dan haka ya dauke kansa daga kansu yana shigewa gabansu tarea keela sauran fadawan na bayansa sai securities a bayansu suma.

Kokarin barin hanyar bangaren sukeyi Asim da da nasa sabbin securities din suka sako kai hanyar dan isa bangaren mahaifiyarsa da suka iso a cikin daren ranar batareda sanar da ko sultan dawowansu ba sbd a yanxu sultan din kansa maqoyinsu ne da suke jin tsananin xafinsa sosai a zuciyarsu amma a zasu fuskancesa a ruwan sanyi kaman yanda a ruwan sanyi zasu fuskanci komai duk da ba lallai su iya hakan ba tinda zuciyoyinsu a zafafe suke tin asali akan komai da kowa ma,

Aslam ce da meryam a tareda Asim din sbd daga bangaren Sultan suke sai a lokacin sukaje suka gaidasa tinda suka dawo a jiyan,

Akan Aleey idanuwan Asim suka fara sauka take yaji wani irin dumi me sanyi yana sauka a cikin jininsa sbd bayan Aleey daya isar da idanuwansa suka sauka akan Bahar wadda idanuwanta suka dago a natse itama ba tsammani ta gansa ta kallesa cikeda mamakin ganinsa sbd harma ta manta dashi a rayuwar duk da ita baida laifin komai a gurinta sbd bai taba cutatar da ita ba bare yi mata wani abin daya cutatar da ita din bayan imebēti dayaso maidata kuma tinda aka tafi da ita zuwa bangaren gyara a wancan lokacin bata dake jinsa ba bare ganinsa ba sai ayau din,

Ya sauya sosai sbd ya samu nutsuwa gangar jiki da hutu duk da jinya yayi batareda sanin kowa ba,

Yanda Asim din yake kallanta zuciyarsa na sake tsimuwa da wata tsaftacciyar soyayya da kaunarta me karfi da jin duka a yanzu duniya bayason komai harma da mulkin indai zai sameta ta ishesa rayuwar da duk yake so yayi a duniya,

Akan hannunta dake riqe cikin na Sultan NUAB idanuwansa suka sauka yaji wani irin zafi ya ratsa zuciyarsa me kaifin gaske yana dan yunqurawa zai nufota keelah ya dage gefe da gaban rigarsa da babu komai a jere jikinsa bayan bindigogi guda biyu da wasu irin daggers masu tsantsan hadari batareda ma ya kalli Asim din ba kaman baima san yunkurin dayake yi ba na nufosu suna cigaba da tafiya,

Aleey ma dan gefensa ya kalla yana kallan inda NUAB yake batareda ma ya juyoba sbd yana ji a jikinsa gurin ya qarasa daukewa da dumin dayake jin zai iya zama makashi duk da Babu alaman ko kallan inda Asim da yan uwansa suke yayi baima san sune a gurin ba dan baya kallan kowa bare bawa kowa mahimmanci dazai ganesa,

Aslam ce tayi saurin saka hannunta ta kama na Asim din cikin nata tana dakatar dashi daga kowane irin motsi batareda barin ma NUAB ya ankare dame yake shirin aikatawa ba tana jin zuciyarta na neman hawa da baqin cikin kasa hakura da Asim yayi da bahar wadda alamu duka sun nuna ba alkhairi bace sam a rayuwarsa da tasu gabaki daya harda mahaifiyarsu,

Suna tsaye cak Sultan me mulkin kujeran boyem ya gama wucewa da tsaronsa kafin Aslam ta wuce gaba idanuwanta a jajir hakama meryam kasa cewa komai tayi sbd mamakin da baqin cikin yanda NUAB yana qaninsu amma ko alaman yama sansu a rayuwarsa kwata kwata babu,

Asim ma daya kasa iya komai daga qafafunsa yayi yana bin bayan su aslam din zuciyarsa a toshe yana neman dalilin dazai fitar da Bahar boyem koma qasar gabaki daya ya bita ya kubutar da ita daga wannan rayuwar datake samun kanta a ciki ta rayuwa da NUAB wanda kwakwalwansa da hankalinsa basa aiki daidai sam sbd fushi dayake cikeda da rayuwarsa tin yana qanqani.

NUAB da zuciyarsa ta qarasa fusata suna isa bangarensa cikin tsakiyar palonsa da babu wanda yake shigowa sai shi sai aleey sakinta yayi yana tareda rintse idanuwansa yana kokarin rage fushinsa ta hanyar hadiyesa yana yana jan numfashi me sanyi a natse kafin ya juyo ya kalleta itama shi take kallo a fusacen zatai magana ya fasa tasa ya sake kama hannunta ya nufi daki da ita yana isa dakin kai tsaye tsakiyar dakin ya ajiyeta ya juya ya fice daga dakin tareda rufe kofar da karfin gaske yana nufar nasa bedroom din.

Baqin ciki hanata motsawa tayi bare fitowa daga dakin dan batajin ma zata iya batawa kanta karfin zuwa kofar fita dan ba barinta fita zaayiba hakama bazata iya tsayawa rokar kowa ba zata qyalesa zuwa da safe wanda dolensa zai barta fita sbd tafiyar da zasuyi wadda baida ikon hanawa.

Zaunawa tayi a kujera tana jin kanta ma na sarawa da fitinarsa da haka kawai ta tashi a cikin daren.

Bataso rintsawa ba ko kadan sbd bacin ran datake ciki amma haka baccin ya dauketa anan kan kujeran wanda bata farka ba sai bayan sallan asuba wadda tayi lattin tashi ma,

Toilet ta fada tayo alwala jikinta na dan mata ciwo kadan sbd kwamciyan kujeran datai ba daidai ba bata wani miqe dakyau ba,

Kayanta na sallah dake dakin ta nude Closet ta dauko ta saka tafara sallah cikin nutsuwa,

Tana idarwa tayi adduoi da azkhar dinta ta miqe ta koma kan kujeran ta zauna tana jiran sakon kira daga Ammi kokuma shi kansa yaxo kiran nata idan Ammi ta kirasa sbd tafiyarsu ta safe ce karfe 9 na safe dan haka dole da wuri zasu shirya.

Shiru taji ba alaman motsin komaima a bangaren kaman yanda akeyi indai yana bacci baa kowane dogon motsi me sauti ko qara,

Gari ya waye sosai batajin motsin komai alaman ma bai tashi ba tin bayan komawansa asuba.

**Ammi dasu leylah da duka sukai kwanan zaune lokaci ta kalla tana kasa yadda da NUAB din ya manta lokacin tafiyarsu da baa buqatan bata dogon lokaci haryanzu bata ga Bahar ba,

Wayarsa take kira kusan a karo na goma sha amma sam bata shiga a kashe take,

Leylah datake jin tsananin ciwon kan kasa bacci taya Ammin kiransa takeyi da tata wayar amma sam babu alaman ma ita tata wayar zata shiga har a sanar da ita a kashe take,

Tsuru tsuru kowa yayi anata jiran tsammani sbd kowa ya shirya dan kaf dinsu sunyi wanka breakfast kadai suke jiran yi,

Babban abin tashin hankalin shine sam baa zuwa bangarensa a yanxu dayake sultan batareda wika neman izinin hakan ba bare a tafi kai tsaye dubowa.

Ammi ce da kanta takeson zuwa amma itama tana jin bazata iya zuwanba sbd ita data haifi NUAB tafi kowa sanin baisan menene jin nauyina bare sakaya kowane irin lamari dan haka take shakkar zuwa taga yayiwa 'yarta wani abin wanda ranta zeyi mummunan baci da hakan.

Maa sakinah dole aka wakilta ta tafi kiran Bahar din.
#MAMUH
09033181070
[12/01, 10:50 am] Asia ahmd: HAYATEEM
Mamuhgee

110
Koda ta isa baa hanata shigaba sbd ankira aleey an sanar masa da itace ya fito daga bangarensa dayake maqale dana NUAB din ta taho ya tsaya cikin girmamawa ya sanar da ita umarnin LEUL na babu wanda zai fitar da Bahar matiqar ba shine ya fito da ita da kansa ba.
Shiru maa tayi batareda jin haushi ko zafin bare damuwan hakan ba tace ba damuwa ta shige.

Tana shiga kai tsaye dakin Bahar din ta nufa wadda tana jin motsin kofar ta bude idanuwanta da suke a rufe da dan sauri tana miqewa zaune.

Ganin maa sakinah ta sauke ajiyan zuciya da sanyi tana miqewa.

Gaida maa din kawai tayi tana kama hannunta cikin sanyin jiki zata nufi kofa maa ta dakatar da ita ta hanyar dawo da ita tana kallanta ba lokacin batawa ta kalleta a natse da dukkanin hankalinta tace

'Bahar babu wanda ya isa ya fidda ki anan idan ba NUAB da kansa ba dan kuwa ko iyayensa kila bazasuma fara ba tinda umarni ne ya bada akan hakan dan haka babu maganar tafiyarki matiqar ba kece zaki je ki tadosa ba sbd bama ya tashi bare fitowa kila sai after 10 kuma kinga zuwa lokacin ba maganar tafiyar.'

Wasu irin zafafan hawayen damuwa ne suka ciko idanuwanta ta kalli maa din zatai magana maa ta katseta da cewa

'Karki ce komai bahar sbd mafita daya ce kije ki samesa ki masa magana zai bari ki fita ki taho ku wuce zuwa ga burinda kikeso ayanzu na karatu da wata rayuwar daban,
Kar kiyi fushi karkiyi gardama sbd kece me tsananin buqatar alfarmarsa a yanxu,
Kije ki samesa din zan koma na sanar da Ammi zamu qarasa shirye shiryen kafin ki iso kinji??

Wani nauyin kirjinta ta hadiye tana hadiye hawayen da suka ciko idanuwanta jikinta na mutuwa da yanda zata iya fuskantarsa har ciki dakinsa ta rokesa kuma zai iya hanata ma.

Ficewa maa sakinah tayi bayan ta sake rarrashinta da nasihar kar tayi taurin kai taje ta samesa matiqar tanason tafiya ayau din.

Sai data dauki mintina a tsaye kafin ta sauke ajiyan zuciya tabar dakin a sanyaye tana jin zuciyarta da kirjinta na 2 da jiya da yanzu bata cikin wannan bacin ran tayi tafiyarta hankali kwance amma yanxu gashi yana neman sakata jin bacin rai a iska shi yanacan yana baccinsa hankali kwance.

Ko data isa kofar bedroom din sauke numfashi da ajiyan zuciya tayi a karo na babu adadi sbd tinda ta ratson hanyar da zata isar da ita bedroom din nasa qamshinsa yake ratsa koina da sanyin Aircon ya gama kamawa.

Mintina ta sake batawa a bakin kofar tana yaqar zuciyarta kafin ta iya saka hannunta tai knocking,

Shiru ba motsi ta sake Knockin har so kusan uku amma ba alaman ma yana dakin,

Bude dakin tayi tareda saka kai a natse ta shiga idanuwanta kai tsaye akan lafiyayyan gadonsa suka sauka dan ganin idan ma yana nan take buga kofar amma kaman bame rai a cikin dakin,

Ganin alaman akwai mutum kwance a kan gadon me fadi sosai dayaji beddings masu laushi da girman gaske farare qal ya sakata nufar gadon kai tsaye,
Chapter 37 · 0% Book details