← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 112

Sashe 39

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A cikin nata bedroom din bayan ta shiga batabi takan kayanta ba sai zuwa da safe baiwar da suka taho da ita me suna Hafsat zata gyara mata su a wardrobe dan haka bathroom kai tsaye ta nufa bayan ta zare duka kayan jikinta.

Wanka tayi da ruwan zafi sosai batareda wani bata lokaci ba a gurin wankan sbd akwai salloli akanta,

Tana fitowa body oil kadan ta shafa tareda tirare me sanyi ta saka kayan bacci ta dora doguwan rigar sallah akai ta kalli inda taga anyiwa kowane dakin gidan alaman gabas sbd gurin da aka kebe dan sallah a tsare yake kowane daki da lallausan dadduma da Al'qur'an a gefe wanda yake cikin tsarin duka gyaran da aka saka akai musu a gidan kafin isowansu dan kada su shiga kowane stress na buqatan sanin komai an tanadar musu dan haka kai tsaye sallah ta tada a natse.

Duka sallolin dake kanta tayi tana idarwa tayi addua ta gama ta miqe tareda fitowa batareda ta cire kayan sallan jikinta bama sbd yunwa take ji daqyar take iya doguwar motsi ma.

Kai tsaye inda aka jera abincin ta nufa daidai nan itama Ammi ta fito tareda su maa sbd kowa yunwar yake ji sosai duk da sun danci abinci a jirgi.

A dining din suka zauna gabaki dayansu suka fara kokarin cin abincin wanda ayshah tazo tayi serving nasu duk da kusan Bahar ma ce tayi rabin aikin.

Abinci suka ci suka koshi tareda shan ruwan dumi sosai bana sanyi ba tukuna kowa ya shige dan hutawa.

Tana shiga daki brush taje tayi ta dawo ta haye gadonta tayi kwanciyanta take bacci ya dauketa me karfi da dadi.

Bacci me karfi kowa yayi daqyar suka iya tashi sallan asuba suna gamawa kowa ya sake komawa daga nan kam ba wanda ya fito sai karfe goma da mintina tukuna Tenya ta fito a shirye cikin wankanta ta zauna palo tana kunna wayarta a natse.

Ayshah ce taxo ta gaidata cikeda girmamawa ta gama komai na aikin gyaran gidan da breakfast sbd babu abinda babu an tanadar musu komai kuma itama ta samu tayi baccin sosai ta huta ba laifi a dakinta dake ta cikin hanyar kitchen dan madaidaici mara girma sosai.

Maa sakinah ce ta fito itama tana wayar da Zuhrah tana sanar da ita sai yanzu suka samu kunna wayoyinsu suka fada wani zancen tana tambayar leylah wadda tin jiyan take jin duniyarta ta dawo sabuwa sbd Bahar ta tafi NUAB kuma yana nan tareda su a boyem.

Shuraim ma nutsuwan hakan yaji ya samu sosai fiyeda yanda ma ya tsammata dan kuwa tafiyar bahar ma ta saukaka musu komai dan haka shima shirin komawa Oxford kawai yaji yana son farawa sbd rayuwa a can.

Aysha ce ta hada dafaffiyar madara da zuma da tea spices masu kyau da qamshi ta jera a tray ta nufi dakin Ammi dasu,

Ko data kai Ammin na zaune a kan lafiyayyan sofar dakinta tana waya a natse cikin kwanciyan hankali,

Da NUAB take waya dan haka Aysha ajiye kayan tayi akan table din dayake gaban Ammin ta saka hannu a natse ta zuba mata ta ajiye a gabanta ta juya ta fice batareda bada kowace irin sound da zata damu wayar ta Ammin ba.

Kitchen ta koma ta sake hadowa ta kawowa su Maa dake palon kafin ta koma ta sake hada ta Bahar daban ta nufi dakinta tana fatar ta tashi.

Bahar din bata tashi ba dan haka ta juya dashi sbd dole idan ta tashi sai ansake dumama sa.

Tana fita bahar ta farka ta miqe itama toilet tafara fadawa tayo wanka ta fito tana fidda qamshin wani tsadadden shower gel dasu bodyscrub da set set na skin routine dake jere a toilet din kaman ansan nan din zata zauna an jere komai da aka tanada dan ita a gurin.

A natse ta shirya cikin doguwan riga mara nauyi har qasa ta fito tana jin gajiyanta ta sake gabaki daya,

Gaida su Maa tayi cikeda girmamawa da kulawa kafin ta nufi dakin Amminta wadda har lokacin take waya.

Tana shigowa Kallanta Ammin tayi fuskarta na cikewa da farin ciki ta miqa mata hannunta daya ta taho ta kama tana zaunawa gefenta kusan cikin jikinta sosai.

Muryansa taji ahankali ta ratsa kunnuwansa a daidai lokacin dayake sanar da Ammin baida ranar da zasu gansa sbd bazai bar boyem ba saiya seta abubuwan daya fara setawa da dama dan haka su kula da kansu kuma akwai mota da driver da aka tanadar musu yana nan zuwa ayau din shima.

Cikin kulawa da kauna me tsafta da ba sirki Ammin tace

'Ka kula sosai da kanka,
Ka rage fushinka illa ce ga lafiyarka da imaninka,
Ka sassautawa kanka akan mahaifinka,
Ka ringa cin abinci akan lokaci da samun hutu sosai
Allah ya baka kariya daga kowane sharri Hayateem'

Ajiyan zuciya nai hade da numfashi ya sake cikin nutsuwa wanda har cikin kunnuwanta taji saurin saukan numfashin nasa da yayiwa Ammin ya bude baki a taqaice yace

'Love you Ya Ammi'

Murmushi Ammin tayi tana ajiye wayar sbd ya kashe tana kallan Bahar wadda tayi shiru a jikinta tana hana zuciyarta tina abinda ya faru a tsakaninsu sbd zata iya kasa hada ido da Ammin wanda zai iya saka a gano wani abin ma.

Cikin kokarin basarwa ta gaida Ammin tana daukan cup din dayake gabanta tana bata cikeda kulawa.

Amsawa tayi tana karban cup din bata sha ba takai bakin bahar din tana cewa ta fara karyawa tukuna.

A tare suka shanye duka madaran a different cup da aka ajiye kafin Zuhrah ta kira Ammin suka dan jima suna waya tukuna aka bawa bahar itama sukai magana sosai kafin suka fito.

Breakfast sukai suna gamawa driver yaxo ya dauki bahar din suka fita tana dan jin tsoro da shakkar fita daga ita sai wanda bata saniba a qasar da bata taba saniba bare xuwa hakama batada doguwar ilimi da wayewan muama sosai da mutane dan haka a sanyaye sukai fitar.

Makarantar da zatai karatun ya kaita kai tsaye gurin wanda akace a kaita,

Suna zuwa sauran formalities aka qarasa cikewa da kammalawa akai komai da komai harma ta shiga class din karshe da dagashi an tashi.

A gajiye ta fito suka bar makarantar zuwa gida sbd ko ruwa bata iya sha ba sbd rashin sukunu da fargaban datake ciki,

Suna dawowa bata wani iya tsayawa palo ba gurin su maa dakinta ta wuce ta fara ajiye su laptop da ipad da sauran tarkacen karatun da zata duqufa dayi kafin ta fada bathroom tayo alwala tazo tayi sallah ta fita taci abinci ta zauna tana fadawa su Ammi duk abinda ya faru a makarantar tana jin kaman bazata iya karatun ba,

Karfin gwiwa Ammi da maa sakinah suka bata sosai sbd tenya tana kitchen tareda Aysha dan ita sam bata wani son zaman hutawan nan sosai hakama idan ba ita tabawa Ayanah abinci ba ganin takeyi sam batada nutsuwa.

Sosai suka bata kwarin gwiwa tareda tabbatar mata da zata iya idan ta dage sbd tana buqatan karatun da ilimin a yanxu datake da sauran kuruciyanta.

Da wannan ta sakawa ranta zata daure ta dage tayi karatun insha Allah.
#MAMUH
09033181070
[12/01, 10:50 am] Asia ahmd: HAYATEEM
Mamuhgee

112
Washe gari da wuri ta shirya sbd karfe 8 zata ringa shiga aji dan haka bata tsaya bacci ba bare jiran Maa sakinah taxo tada ita ta fito a shirye maa sakinah na kitchen da kanta ta hada mata breakfast mara nauyi ta kawo mata tareda zaunawa gefenta tana taimaka mata gurin ci akan lokaci.

Tana cikin breakfast din Ammi ta fito ta iso gurinta tana miqa mata jakarta me kyau data hado mata yan abubuwan buqata da wayar data bude mata sabuwa dal ta saka mata numbers nasu duka a ciki tana mata addua.

Ammi da maa sakinah kaman zasu bita makarantar haka suka rakata har kofa ta fice da sauri tana musu sai anjima.

Mota ta fada suka wuce makarantar tana saka ipad dinta a jakarta.

Koda suka isa da farko taso ta sake karaya amma wadda aka hadata da ita Neesah yar qasar ghana ce a makarantar dan ta taimaka mata sosai sai ta sake mata sosai tareda nuna mata itama zata iya dan haka saita sake sakewa dan daukan kowane darasin dazai taho mata ta karatun.

Bayan fitowansu class din farko da kusan bata gane komaiba library suka nufa ta zaunar da ita can ta fara fahimtar da ita komai da abubuwa,

Bata dawo gida ba sai yamma sosai sbd lesson din da aka wuce da ita wani gurin daban wanda shima kullum daga school can zaa ringa kaita tana koyan turanci da ilimin muamala da mutane da duk inda zaka shiga.

Acan baa hadata da kowa ba dan haka shiru kawai tayi tana saurare tareda recording komai sbd neman cikakken qarin bayani idan ta isa gida.

A gida babu sauran lokacin kowane irin hutu a gurinta sbd a gidanma tanada online class da shima aka tanadar mata komai na turanci da larabci wanda zaisa tafi ganewa.

Har dare bata fito ba dan haka Ammi da kanta ta saka aka hada abincinta takai mata har dakin tana zaunawa kusa da ita suna duba karatun tare tana ganar da ita abinda ta sani itama kafin suka qarasa kammalawa ta sakata taci abinci ta koshi cikin kulawa ta goge mata bakinta da tissue.

Anan gurin daga fira bacci ya dauketa jikin Ammin cikin gajiya da dan ciwon kan rashin sabon abinda dole ya zama rayuwarta kuma.

Sai data dan yi me nisa ta rage ciwon kanta tukuna ammin ta tada ita tayi shirin bacci tayi sallar ishai da akai tini tukuna ta kwanta take baccin ya sake dauketa.

Washe gari ma haka ta tafi tinda safe bata dawo ba sai 6 na yamma a gajiyenda saida maa sakinah ta kamota jikinta ta rungume ta rakata har daki ta tayata zare kayan jikinta ta fada toilet tayo wanka da alwala tayi sallah Amminta ce ta bata abinci kaman zata tayata ci harta koshi tukuna ta fada online class dinta wanda tayi har kusan 8 tukuna tai sallah ta sake kwantawa.
Chapter 39 · 0% Book details